الأربعاء، 20 مايو 2020

ABUBUWAN MAMAKI GUDA 4

 

 
الوصف: cbc250ed-6a0e-4037-8d54-a9eb3d0a0577                                                                                                                           

ترجمة الخطبة

اسم المترجم :أمين سعد عبد الله

اللغة : الهوسا

التاريخ : 15-9-1441هـ

 

Hudubar Masallacin Annabi Na shaikh Ahmad Dalib 15/9/1441AH/7/5/ 2020AC

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah muna gode masa kuma muna neman taimakonsa da gafararsa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi, kuma duk wanda ya batar babu mai shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, na kuma shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma manzonSa ne. tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da aminci tabbatacce.

(Ya ku wadanda suka bada gaskiya ku ji tsoron Allah cancancin tsoronSa kada ku mutu face kuna musulmai)

(ya ku mutane ku ji tsoron Allah wanda ya halitta ku daga rai guda kuma ya halitta matarsa daga gare shi ya yada daga gare su mazaje masu yawa da mata, ku ji tsoron Allah da ku ke roko da (sunan) shi. Da zumunci, lalle Allah ya kasance mai tsaro ne a kan ku.)

(ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah ku fadi zance na daidai. zai gyara muku ayyukan ku kuma ya gafarta muku zunubanku, duk wanda ya ke yi wa Allah biyayya da ManzonSa to ya rabauta rabauta mai girma.)

 

Bayan haka, lalle mafi alherin zance shine maganar Allah, kuma mafi alherin shiriya ita ce shiriyar Annabinmu Muhammad, kuma sharrin al'amura sune fararrunta, kuma dukkan bidi'a bata ce, kuma dukkan bata na wuta.

Ku sani ya ku bayin Allah lallai ba makawa bin hanyar zuwa lahira dole sai da ilimi wanda ke yaye wa zuciya makanci, da kuma aiki wanda zai dauke wa mutun shamaki na basira da iklasi wanda zai kubutar da mutun daga hasara na faduwa da kuma tsoro wanda zai sa mutun ya kiyaye bala'o'i na rudi.

 Dukkan halittu matattu ne sai malamai, malamai kuma dukkansu masu bacci ne sai masu aiki, masu aiki kuma dukkansu rudaddu ne sai wanda suke masu  iklasi, su kuma masu iklasi suna cikin wani hadari mai girma (shin , kuma wanda ya kasance matacce, sa'an nan Muka rayar da shi Muka sanya wani haske dominsa, yana tafiya da shi , yana zama kamar wanda misalinsa yana cikin duffai , shi shi kuma ba mai fita ba daga gare su ? kamar wancan ne aka kawata wa kafirai abin da suka kasance suna aikatawa).

Abin mamaki dukkan mamaki ga mutumin da ya ke aiki amma bai damu da sanin abin da ke gaba gare shi ba na daga al'amari ko labari, ko kuma ya nemi sanin abin da zai zo bayan mutuwa gaba gare shi ta hanyar nazari da dubi ga dalilai da kuma wa'azuzzuka da ayoyi da kuma gargadi ba. (shin ba su yi dubi ba a cikin mulkin sammai da kasa, da kuma abin da Allah ya halitta daga kome kuma akwai tsammani kasancewar ajalin su, hakika ya kusanta? to da wani labari a bayansa su ke yin imani) ( wanda Allah ya batar, to babu mai shiryarwa a gare shi kuma yana barin su a cikin batarsu suna dimuwa) abin mamaki ya kaiton makanci irin na zuciyarsa (shin to, ba su yi tafiya ba a cikin kasa domin zukata wadanda za su yi hankali da su da kunnuwa da za su yi saurare da su, su kasance a gare su ? domin lallai ne idanu ba su makanta, amma zukata wadanda ke a cikin kiraza su ke makanta).

Abin mamaki dukkan mamaki ga malamin da ba ya wa'azantuwa da abin da ya sani na yakini sai abin da ya ke gaba gare shi na daga musibu masu girma da kuma abubuwa na cikas da ke gaba masu fadi ya tsorata daga kasala ya gargadu zuwa ga jahadi da kuma aiki (ka ce, shi (Alkur'ani) babban labari ne mai girma. ku, masu bijirewa ne daga gare shi) ya kaiton hijabin idanuwansa (Bone ya tabbata ga masu nakkasawa) (wadanda su ke idan su ka auna daga mutane suna cika mudu)(kuma idan sun auna musu , da zakka , ko da sikeli , suna ragewa)(shin wadancan ba su tabbata cewa lallai su , ana tayar da su ba?) (domin yini mai girma) (yinin da mutane ke tashi zuwa ga Ubangijin halitta).

Abin mamaki dukkan mamaki, ga mai aiki wanda ya sarayar da iklasi ya sarayar da mabudin samun kubuta ta hanyar lalata zuciyarsa  (ka ce, ''Ni mutum ne kawai kamarku, ana yin wahayi zuwa gare ni cewa : lallai ne abin bautawarku Abin bautawa guda daya ne, saboda haka wanda ya kasance ya na fatan haduwa da Ubangijinsa, to sai ya yi aiki na kwarai, kuma kada ya hada kowa ga bautawa Ubangijinsa.) kaito da hasaran faduwan mutum ya rasa riba! (kuma aka halaka dukkan 'yayan itacensa, sai ya wayi gari yana juyar da tafunansa biyu , saboda abin da ya kashe a cikinta , alhali ita tana kwance a rassanta, kuma yana cewa , kaitona dadai ban tara wani da Ubangijina ba!) (kuma wata jama'a ba ta kasance a gare shi ba, wadanda ke taimakon sa baicin Allah, kuma bai kasance mai taimakon kansa ba) abin mamaki dukkan mamaki ga mai iklasi wanda ba ya duba zuwa ga mua'amalar Allah Madaukaki tare da masoyanSa da ManzanninSa wadanda su ne masu nusar da halittu daga wurin Allah sai ya halarto da tsoronsu, ga masoyi na farko yana cewa (kuma a lokacin da Ibrahim ya ce ,''ya Ubangijina! Ka sanya wannan gari amintacce, kuma ka nisata ni ni da 'ya'yana daga bautawa gumakai) ya na shaida tsoron su masoyi cikakke yana ce da shi (kuma an yi wahayi zuwa gare ka da kuma zuwa ga wadanda su ke gabaninka , ''lallai idan ka yi shirka hakika, aikinka zai baci ,kuma lallai za ka kasance daga masu hasara.)

To ya kai mai rudin kansa (To, a yau ba za a karbi fansa daga gare ku ba . kuma ba za a karba daga wadanda su ke kafirai ba makomarku wuta ce , ita ce mai dacewa da ku kuma makomarku din nan ta munana ) (shin, lokaci bai yi ba ga wadanda su ka yi imani zukatansu su yi tawaliu ga ambaton Allah da abin da ya sauka daga gaskiya ? kada su kasance kamar wadanda aka baiwa littafi a gabanin haka sai zamani ya  yi tsawo a kansu , saboda haka zukatansu su ka kekashe, kuma masu yawa daga cikinsu fasikai ne) .

Allah ya sa mini albarka ni da ku a cikin Alkura'ani mai girma .

Huduba ta biyu

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya isa, tsira da aminci su tabbata ga Annabi zababbe da alayenSa da sahabbanSa ma'abota da'a da kuma cika alkawari, da kuma wanda ya bi su da kyautatawa kuma ya bi sawu, lallai Allah ya kira ku da sunan imani kuma da tsoronsa ya kira ku Ya gargade ku game da faduwa irin na mantuwa da kuma radadi irin na hasara ya kuma sanar da ku tserewan yanayi da halaye a ranan komawa, girman tasirin Alkura'ani da an saukar da shi ne a kan duwatsu , ya kuma sanar da ku da kamalan sunayenSa Madaukaki da kyawawa.

(ya ku wadanda su ka yi imani ! ku bi Allah da takawa , kuma rai ya dubi abin da ya gabatar domin gobe, kuma ku bi Allah da takawa lallai Allah , Mai kididdigewa ne ga abin da kuke aikatawa) (kuma kada ku kasance kamar wadanda suka manta Allah shi kuma Ya mantar da su rayukansu, wadannan su ne fasikai) ('yan wuta da 'yan Aljanna ba su daidaita . 'Yan Aljanna su ne masu babban rabo) (Da Mun saukar da wannan Alkura'ani a kan dutse, da lallai ka ga dutsen yana mai tawali'u, mai tsatsagewa saboda tsoron Allahh , kuma wadancan misalai Muna bayyana su ne ga mutane, da fatan za su yi tunani) (wanda ya saukar da Alkur'ani shi ne Allah, wanda babu wani abin bautawa face shi, masanin fake da bayyane, Shi ne Mai rahama Mai jin kai) (Shi ne Allah, wanda babu abin bautawa face Shi Mai mulki Mai tsarki, aminci Mai amintarwa , Mai tsarewa , Mabuwayi , Mai tilastawa, Mai kamun kai, tsarki ya tabbata a gare shi daga abin da suke yi na shirka da shi) (Shi ne Allah, Mai halitta Mai ginawa, Mai surantawa, yana da sunaye masu kyau, abin da ke a cikin sammai da kasa suna tsarkake Shi , kuma Shi ne Mabuwayi , Mai hikima).

Tsarki ya tabbata gare Shi Madaukaki bai halicce ku don wasa ko kuma don kazanta ba sai dai kawai domin ku nemi gafaran Shi kuma domin a muku  rahama (shin, to kun yi zaton cewa Mun halitta ku ne da wasa, kuma lallai ku zuwa gare mu ba za ku koma ba?) (Allah Mamallaki, Gaskiya, Ya daukaka babu abin bautawa face Shi, Shi ne Ubangijin Al'arshi , mai daraja) (kuma wanda ya kira tare da Allah wadansu abubuwan bautawa na daban , ba yana da wani dalili game da shi (kiran) ba , to hisabinsa yana wurin Ubangijinsa kawai lallai ne kafirai ba su cin nasara) (kuma ka ce, ''Ya Ubangijina ! Ka yi gafara Ka yi rahama kuma Kai ne Mafi alherin masu rahama).                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                   

                                                                                                               


ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق