اللغة : الهوسا
التاريخ 8/9/1441هـ
Hudubar
masallacin Annabi na shaikh Abdullah Bin
Abdurrahman Albuaijan
8/9/1441 AH 1/5/2020
AD
Hudubar farko
Dukkan yabo da
godiya sun tabbata ga Allah wanda ya sanya da'a gare shi ya zama dalili ne na
samun yardarSa, ya sanya yardarSa kuma a matsayin dalili ne na rabauta da
AljannarSa ya kuma datar da mumunai zuwa ga bauta masa, sai suka kauracewa
ababan jindadi da sha'awe sha'awensu suka fifita samun yardarSa.
Na shaida ba
abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya abin
godiya abin girmamawa, shaidawar da zan hadu da Allah da ita a halin ina ni kadai na tilo. Na shaida
Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne Allah ya isa Mai shaida. Tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa da aminci abin
kari mai yawa.
Bayan haka,
lalle mafi alherin zance shine maganar Allah, kuma mafi alherin shiriya ita ce
shiriyar Annabinmu Muhammad dan Abdullah, kuma sharrin al'amura sune fararrunta,
kuma dukkan bidi'a bata ce, kuma dukkan bata na wuta,
ya ku bayin
Allah ina muku wasiya da ni kai na da tsoron Allah Mabuwayi da daukaka, to ita
ce wasiyar Allah ga mutanen farko da na karshe, (Hakika
mun yi wasiyya ga wadanda muka baiwa littafi kafin ku da ku kan ku da ku ji
tsoron Allah).
Ya
ku bayin Allah! Biyayya ga Allah ita ce mafi alherin ganima da abin ribata,
kuma yardarSa ita ce mafi alherin riba da abin nema, Aljanna an kewaye ta da
abubuwan ki, wuta kuma an rufe ta da abubuwan sha'awa, abin sani za ku samu
ladan ku cike a ranar alkiyama, to duk wanda a ka nesatar daga wuta aka shigar
Aljanna to hakika ya rabauta.
Ya ku masu
azumi!
Allah ya karbi
biyayyarku, ya gyara halayenku, ya datar da ku cikin abin da ya rage a wannan
wata, ya kuma rubuta muku tabbatuwa bisa
da'a a gare shi a tsawon ranakun zamani.
Ya ku jama'ar
musulmi!
Ramadan wata ne
na ibada da tuba, watan neman kusanci ne da komawa ga Allah, wata ne na tuba da dawowa ga Allah da ikhlasi da
khushu'i da sujudi da ruku'i, wata ne na azumi da tsayuwa, wata ne na biyayya da kyautatawa da karatun Alkur'ani.
Ya ku masu
azumi!
Karbabbiyar
ibada na da tasiri a imani, tasirinta na ga zuciya da rai , gyara niyya da
tsarkake rayuka da takawa da ikhlasi da khushu'i ga Allah Mafi daukaka.
Tasirinta da ke
gabbai da jiki; kamewa daga ayyukan sabo da abin da aka haramta da jurewa gun
aikata ayyukan alheri da da'a.
To ku sa Allah
a idanuwanku cikin ayyukanku, to shi Allah bai dubi ga surorinku ko jikunanku
sai dai yana dubi ne ga zukatanku ne da ayyukanku , so da yawa wani mai azumin
baida wani abu a azuminshi sai kishin ruwa da yunwa da gajiya sau da yawa wani
mai tsayuwan dare bai da wani abu na daga tsayuwan shi sai hana ido barci da
wahala.
Ya jama'ar
musulmai :
Lallai Allah ya
saukar da Alkur'ani a watan azumi sai yace:
(watan ramadana ne wanda aka saukar da Alku'ani
yana shiriya ga mutane da hujjoji bayyanannu daga shiriya da rarrabewa)
kuma Allah ya ce : (lallai mu muka saukar da shi
a daren lailatulkadri ) (wa ya sanar
da kai menene lailatulkadri)(lailatul
kadri mafi alheri ne daga wasu watanni
dubu) (Mala'iku da Ruhi suna sauka a
cikinsa da izinin Ubangijinsu saboda kowane umurni) (sallama ne shi daren har fitar alfajiri)
kur'ani ya sauka a daren lailatul kadari na
ramadana zuwa baitul izza a sama ta duniya san nan ya sauka zuwa doron
kasa a rarrabe cikin shekaru ashirin da uku
gorgodon abubuwan da ke faruwa da kuma sabuban sauka, to karatun kur'ni
a watan da aka saukar da shi , na daga cikin mafificin ayyukan kusanci saboda haka ne Annabi tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi ya kasance yana fiskantan karatun kur'ani a cikin watan
ramadan Jibrilu ya kasance yana zuwa mishi a ko wani dare a cikin watan ya yi
bitan kur'ani da shi .
An karbo daga Ibnu
Abbas Allah ya kara yarda a gare su ya ke cewa:( Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance mafi kyauta cikin
mutane kuma kyautansa ya fi kasancewa ne
a watan azumi a yayinda ya ke haduwa da Jibril , jibrilu ya kasance yana haduwa
da shi a ko wani dare na ramadan sai ya yi bitan Alkur'ani da shi to Annabi na
da yawan kyautan alheri a yayin da ya hadu da shi sama da iska da ake turowa)
.
To ya ku bayin
Allah ku riki karatun Alkur'ani ku
karanta shi da tajwidin shi kuma ku nemi fahimtar ma'anoninsa ku yi tadabburinsa , to an karbo daga abdullahi dan Mas'ud Allah
ya yarda da shia ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbat a a gare
shi ya ce:(Duk wanda ya karanta harafi yana da kyakkyawa , kuma kyakkyawa na da
kwatan kwacinta guda goma, ba zan ce alif lal mim harafi ne sai dai alif harafi
ne lam harafi ne mim harafi ne) Tirmizi ne ya rawaito shi kuma ya
inganta shi , kuma aga gare shi Allah ya kara yarda a gare shi ya ce Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(lallai wan nan alkur'ani wani abin ci ne to ku koya daga
wan nan abincin iya iyawan ku lallai wan nan alkur'ani igiyan Allah ne kuma
haske ne mai bbayyanawa komin kuma
waraka ne mai amfani kuma kariya ne ga wanda ya yi riko da shi da kuma tsira ga
wanda ya bishi ba zai zame ba har ya zama abin zargi, ba zai kuma karkace ba
har ya zama abin mikarwa ,kuma
abubuwan mamakinsa ba za su kare ba kuma yawan maimaita shi ba zai tsufar da
shi ba to ku yi tilawarsa , don lallai Allah zai ba ku lada bisa ga tilawarsa
kyakyawa goma ga ko wani harafi amma ni ba zan ce alif lam mim sai de da: alif,
da lam, da mim …. ) Dabrani
ne ya rawaito .
An karbo daga
Abdullahi dan Umar Allah ya kara yarda a gare su ya ce : Mazon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (Ana
cewa ga ma'abocin Alkur'ani a ranar alkiyama , ka karanta ka haura kuma ka yi
tilawa kamar yanda ka kasance kana
tilawa a duniya domin matsayinka tana a'ayan karshe da ka karantata) Tirmizi ne ya rawaito .
To ku karanta
Alkur'ani bayin Allah kar ku kaurace masa , na hore ku da kar ku da yankewa alkur'ani, na hore ku kada manta Alkur'ani don hakan hasara ne da nadama, da
juyawan hankali ne da abin zargi.
Muna neman
tsarin Allah da mu kasance cikin wadan da Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi zai kai karan su wurin Allah , sabo da kauracewa kur'ani da suka yi :- (kuma Manzo ya
ce : Ya Ubangijina! Lalle mutanena sun riki wannan Alkur'ani abin kauracewa).
Ya ku bayin
Allah ! Mafi girman ambaton Allah Mabuwayi da Daukaka shine Alkur'ani, barin karanta shi kaura ce masa ne da kuma juya masa baya Allah madaukakin sari
ya ce :- (Duk wanda ya kauda kai daga ambato na (Alkur'ani) , to lallai ne rayuwa mai kunci
ta tabbata a gare shi ,kuma muna tayar da shi a ranar kiyama yana
makaho. Ya ce Ubangiji '' don me aka tayar da ni makaho ,
alhali kuwa na kasance mai gani ? . Y a
ce '' kamar wancan ne ayoyin mu suka je maka
sai ka mance su , kuma kamar haka
a yau ake mance ka.
An karbo daga
Abu Musa Al-ash'ari Allah ya kara yarda a gare shi ya ce:- Manzon Allah tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :- (misalin
muminin da ya ke karanta kur'ani kamar
misalin tanjarin ne kamshin shi na da dadi dandanon shi ma na da dadi , kuma misalin muminin da baya karanta
kur'ani kamar misalin dabino ne, bai da
kamshi kuma dandanon sa na da dadi , kuma misalin munafiki da yake karanta
kur'ani kamar turaren wuta ne kamshin
shi na da dadi kuma dandanon shi na da dadi) Buhari da Muslum ne suka rawaito .Hakika
Magabata sun kasance suna kwadayin karanta kur'ani da lura da ma'anonin shi suna da wuridin da suke yi ko wani rana ba sa yankewa daga gare ta musamman a wannan
watan.
Watan ramadana da aka saukar da alkur'ani a cikin
ta , to ku kwadaici yawaita tilawar sa kada
na'urori na zamani da shirye-shirye masu shagaltarwa su yi gogayya da
shi
YA
KU BAYIN ALLAH:
A halin kuna
wannan yanayi to ku nemi magani da waraka
da karatun alkur'ani domin shi
waraka ne da rahama ga muminai .
Ku dukufa a kan shi a gidajen ku, a lokacin da
ku ke kadaicen ku ko a bayyanen ku , ku karanta shi kuma ku saurare shi a sauran lokutan ku .
Kuma wanda
hakan ya mi shi nauyi , ko karanta
kur'anin ya gagara a gare shi to, ya
saurari tilawar sa , domin shi ma mai sauraron abokin tarayyan mai karantawa ne
a lada da sakayya .
Allah yana cewa
: (Idan an karanta Alkur'ani to ku saurare shi
ku yi shuru ko za ku samu rahama)
HUDUBA TA BIYU
Dukkan yabo da
godiya sun tabbata ga Allah Masanin
gaibi Mai yafe zunubai da sauran kusakurai da laifuka , kuma Mai yaye bakin ciki
yana shimfida hanunSa da dare don mai
laifin yini ya tuba , kuma yana shimfida
hanunSa da rana don mai laifin dare ya tuba .
YA KU BAYIN
ALLAH:
Ku yiwa kanku
hisabi kafin a mu ku hisabi , kuma ku
auna ayyukanku kafin a aunaku kuma kafin ayi kira gare ku : lallai su
dinnan ayyukanku ne muke kididdige mu ku , sa'annan mu cika muku ita duk wanda ya samu alheri to, ya godewa Allah
, kuma wanda ya samu koma bayan haka to, kada ya zargi kowa sai kansa.
(Duk wanda ya
aikata wani aiki kyakkyawa kwatankwacin
kwayar zarra zai gani, haka kuma duk wanda ya aikata mummuna kwatankwacin
kwayar zarra zai gani)
YA KU BAYIN
ALLAH:
Tsayuwar dare
kusanta ne ga Allah ba mai kiyaye ta sai
muminai , haka kuma sunna ce da ba mai juriya
a kanta sai masu tsoron Allah , (Wadan da suke kwana don Ubangijinsu suna
masu sujada da tsayuwa )
Wadan da Allah
ya ce game da su :- (sasannin su na nisanta
daga wuraren kwanciya , suna
kiran Ubangijin su bisa ga tsoro
da tsammani, kuma suna ciyarwa daga abin da muka azurta su . )
Sabo
da haka wani rai bai san
abin da aka boye musu ba , na sanyin idanu , domin sakamako
ga abin da suka kasance suna
aikatawa .
Wadan da Allah
ya daukaka su (Lalle masu takawa suna a cikin
lambunan ita ce da maremari. Suna masu
karbar abin da Ubangijinsu ya ba su ,
sun kasance masu kyautatawa a gabanin
haka (a duniya). Sun kasance a
lokaci kadan na dare suke yin barci . Kuma a lokutan asuba suna ta yin istigfari)
Bayin Allah
lokacin yin Tahajjud cikin dare
shi ya fi sabo da lokuta irin na kusanci Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Lalle ne
tashin dare shi ne mafi
tsananin natsuwa , kuma mafi
daidaituwa ga magana )
Kuma lokaci ne da a cikin shi Allah yake saukowa zuwa saman duniya yana kira; shin akwai mai
roko na amsa mishi, shin akwai mai neman gafara na
gafarta masa ? shin akwai mai tuba na karbi tubansa ?
, kuma lokaci ne wanda ake bude kofofin sama ana amsa adu'a.
karatun kur'ani shi ne mafi girman
kusanci da munini zai nemi
kusanci da shi a wan nan lokaci, maganan Allah da kuma salla, mafi lokacin da
kuma bawa ya fi kusa da UbangijinSa shi ne a lokacin da yake sujada (shin, wanda ya ke mai
tawali'u sa'o'in dare , yana mai sujada kuma yana mai tsayi ga sallah yana
tsoron lahira kuma yana fatan rahamar
ubangijinSa ).
Mafificin tsayuwa shi ne tsayuwan dare (sallar nafila)
na ramadana, shi ne ya fi karfi a cikin sunnoni kuma na daga cikin mafificin
nafilfilu, to an karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (Duk wanda ya yi tsayuwan ramadana yana mai imani kuma da
neman lada za a gafarta mishi abin da ya gabata na daga zunuban shi kuma wanda
ya yi tsayuwan lailatul kadri yana mai imani da neman lada za a gafarta mishi
abin da ya gabata na daga zunubansa) ya zo a ckin sahihu muslim daga
Urwatu dan Zubair cewa Ummul mu'minina A'isha Allah ya kara yarda a gare ta ta
bashi labarin cewa:( Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya fita cikin dare sai ya yi salla a masallaci
, sai wasu mutane su ka bi sallansa suka yi koyi da shi sai da aka wayi gari sai mutane suka bada labarin
hakan sai mutane suka hallara sama da wadancan sai manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya fito a dare na biyu sai mutane suka yi
koyi da sallanSa sai mutane suka wayi gari suna ambaton hakan sai mutane suka
cika masallaci a wannan dare na ukun sai Annabi ya fito ya yi sallah sai mutane suka yi koyi
da sallan shi yayin da aka zo dare na hudu masallacin ya kasa daukan jama'a
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai bai fito ba har zuwa
lokacin da aka fita zuwa sallan asubahi yayin da aka kare sallan asuba sai ya
juyo ya fiskanci mutane san nan ya yi Tashahhudi (Ashhadu alla ilaha
illaallah wa ashhadu anna muhammadarrasulullah) sai ya ce : bayan haka lallai
bai boyu mini ba sha'aninku na daren jiya sai de na tsoraci kar a farlanta muku
sallan dare ne ku gagara yinta).
Mutane sun
kasance bayan haka suna sallatanta
jama'a kashi –kashi, kuma a
daidaiku har zuwa lokacin da Umar dan kaddabi Allah ya kara yarda a gare shi ya
hada su a mai karatu guda daya ,
An karbo daga
Abdurrahman dan Abdu Alkari cewa ya ce : na fita tare da Umar dan kaddabi a
cikin watan ramadana zuwa masallaci sai ga mutane su na warwatse a rarrabe wan
nan na salla shi kadansa wasu jama'a
na koyi da sallan sa , sai Umar
ya ke cewa wallahi ; ni ina ganin da kun hada wadan nan mutanen bisa ga
makaranci guda daya da zai fi dacewa sai ya hada su ga Ubayya dan ka'ab .
Bayan haka ya
ku bayin Allah duk wanda niyarsa ta kasance ta gaskiya gurin azama ga yin salla
a daya daga cikin masallatayya biyu masu alfarma, ko wasunsu na daga masallatayya , amma ; hakan
ya gagara yiwuwa a gare shi ko wani abu ya yi shamaki tsakanin shi da hakan sai
ya yi salla a gidan sa to lallai ladansa na nan cikakke a rubuce insha Allahu ;
domin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke cewa:( lallai abin sani kawai ga ko wani mutum yana da abin da
ya nufa ) kuma ya ke cewa :(Duk
mutumin da ya himmatu da aikata wata kyakkyawa bai samu aikatata ba to za a
rubuta mishi kyakkyawa guda) Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ke cewa : (Idan bawa ya yi
tafiya ko ya yi rashin lafiya to za a rubuta mishi kwatankwacin abin da ya
kasance yana aikatawa a halin yana mazaunin gida mai lafiya) .
Hakika Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke cewa yayin da ya
kusanto Madina yana dawowa daga yakin tabuka(
lallai a garin Madina akwai wasu mutane da ba ku tafi wata tafiya ba ko kuma
kuka keta wani kwari ba face kun yi tarayya da su a lada sai suka ce: ya Manzon
Allah ahalin suna Madina ? sai ya ce : E, suna Madina uzuri ne ya hana su )
to ku yi albishir
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق