الجمعة، 24 أبريل 2020

ROKON ALLAH WARAKA


أمين سعد عبد الله
17-8-1441ه، الهوسا

Hudubar Juma'a a Masallacin Annabi 17-8-1441AH / 10-4-2020AD  na shaikh Ali Bin Abdurrahman Alhuzaifi

Hudubar farko
Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai yawan gafara Mai karamci, Mai yawan godiya Mai hakuri, Mai gudanar da halittunSa da mashi'arSa da rahamarSa da kudurarSa, kuma Shi Masani ne ga dukkan komai.
Ina kyautata yabo ga Ubangiji na kuma ina gode masa, bisa ni'imominSa da ba mai iya kididdige su sai Shi, wadanda muka sani da wadanda bamu sani ba, Allah Ma'abocin falala ne mai girma.
Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, Ubangijin al'arshi mai girma, kuma na shaida Annabinmu kuma shugabanmu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, ma'aboci halaye masu girma, ya Allah ka yi salati da aminci da albarka ga bawanKa kuma ManzonKa Muhammad da iyalansa da sahbbansa ma'abota tafarki mikakke, Bayan haka, ku ji tsoron Allah ta hanyar  tashi da wajibabbu, da nesatan haramtattu, za ku rabauta da alheri a rayuwa da bayan mutuwa, kuma zaku zauna a gidajenku a cikin aljanna, Allah Madaukakin Sarki ya ce : ((Wanda ya ji tsoron Allah zai kankare masa laifukansa kuma ya girmama ladansa.)
Ya ku mutane, wanda ya kasance yana son lahira to lahira na hanun Allah ne shi kadai ba shi da abokin tarayya, Allah ya bayyana Mabuwayi da daukaka ayyukan da zaa yi don ita kafin mutuwa, to madallah da aiki kuma madalla da ladan,  wanda ya ke son duniya ya manta da lahira to wanda ya mallaki duniya  shine Ubangijin talikai,Allah zai bashi wani rabo daga ciki kuma bai da rabo a lahira Allah Madaukakin Sarki ya ce :(Wanda ya kasance yana nufin duniya sai mu gaggauta masa a cikinta,abin da muke so ga wanda muke nufi, sa'anan mu sanya masa jahannama ya konu da ita yana abin zargi abin tunkudewa. Kuma wanda ya nufi lahira, kuma ya yi aiki saboda ita, irin aikinta alhali kuwa yana mumini to wadannan aikinsu ya kasance abin godewa. Dukansu muna taimakon wadannan da wadancan daga kyautar UbangijinKa kuma kyautar UbangijinKa bata kasance abin hanawa ba),    
Allah Mabuwayi da daukaka  ya ce : ((Wanda ya kasance yana nufin noman lahira zamu kara masa a cikin nomansa, kuma wanda ya kasance yana noman duniya zamu tsammasa daga gare ta alhali kuwa ba shi da wani rabo a cikin lahira)
Allah Madaukakin Sarki ya ce : (Kuma lalle gare mu lahira take da duniya) To duk wanda zai neme su to kar ya neme su a gun wani ba Allah ba, to musulmi yana jin dadi ne da abin da Allah ya hore mishi a nan duniya jin dadi mai kyau, ba zai tsallaka abubuwa na halal zuwa haram ba. Ya lizimci tsakaitawa ya  nesaci almubazzaranci da alfahari, ya gyara a rayuwa abin da Allah ya bashi, ya habaka alheri cikin arzikin Allah ya sanya abin da Allah ya bashi na kaso a nan duniya guzuri ne don lahira gidan ni'ima,  Allah Madaukakin Sarki ya ce : (To daga cikin mutane akwai wanda yake cewa : ya Ubangijinmu ka ba mu a cikin duniya, kuma bai da wani rabo a cikin lahira, kuma daga cikin su akwai wanda ya ke cewa : Ya Ubangijin ka bamu mai kyau a duniya da mai kyau a lahira kuma ka tsare mu daga azabar wuta.kuma wadannan suna da rabo daga abin da suka sana'anta. Kuma Allah Mai gaggawar sakamako da yawa ne.)
 Allah Madaukakin Sarki ya ce : (kuma ka bida a cikin abin da Allah ya baka gidan lahira kuma kada ka manta da rabonka daga duniya, kuma ka kyautata kamar yadda Allah ya kyautata a gare ka, kuma kada ka nemi barna a doron kasa lallai ne Allah ba ya son masu barna).
  Ya ku mutane ! Lalle ba a riskan abin da ke hanun Allah sai ta hanyar yi masa biyayya, kuma ba a tunkude sharri daga mutum sai da falalar Allah da rahamarSa, Allah Madaukakin Sarki ya ce : (kuma idan Allah ya shafe ka da wata cuta to babu mai yaye ta face shi, kuma idan ya nufe ka da wani alheri to babu mai mayar da falalarSa, yana samun wanda ya ke so daga cikin bayinSa da shi, kuma shi ne Mai gafara Mai jinkai).  
Ina fadakarwa da hakikanin da ko wani mutun zai yi kokari ya yi aiki don shi, shine dukkan ko wani mutun yana aiki ne ya yi kokari domin ya riski alheru kuma ya rabauta da abubuwa na falaloli da abubuwan karramawa kuma ya tsira ya kubuta daga sharrori da abubuwa masu halakarwa , sai dai wan rabauta mai girma  ba a'a riskan shi kuma ba ya tabbatuwa face ta hanyar bin Manzanni tsira da amincin Allah su tabbata a gare su,  kuma cikiamakinsu shi ne Annabinmu kuma shugabanmu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi duk wanda ya bi shi zai rabauta da alherin duniya da lahira ko da wani abu ya same shi da ya ki na daga cikin musibu, an karbo daga Suhaibu dan Sinan Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (Abin mamaki da al'amarin mumini, dukkan al'amarin shi alheri ne hakan ba ya kasancewa ga wani face mumini idan abin  farin ciki ya same shi sai ya yi godiya sai ya zama alheri a gare shi idan kuma cuta ta same shi sai ya yi hakuri, hakan sai ya zama alheri a gare shi) Muslim ne ya rawaito.
Duk wanda ya kuskure hanya ya haramtu daga  imani  to hakika ya yi hasaran duniyarsa da lahirarsa ba zai amfane shi ba duk abin da ya riska ko abin da ya samu a nan duniya, don jin dadin duniya wani abu ne mai gushewa mai kaucewa, kuma jin dadi ne wanda ya ke cakude da bakin ciki da kuma abubuwa na bacin rai Allah ta'ala ya ke cewa ; (kuma rayuwar duniya ba wani abu ba ne face jin dadi na rudi) , ya kai mutun ka yi kwadayi zuwa ga UbangijinKa ka dawwama bisa ga addu'a da rokon Allah Madaukakin sarki dukkan alheri da kuma neman tsarin shi daga dukkan sharri, Ubangijin mu Mai rahama ne Mai jinkai ya na so a roke shi abubuwa mafi daukaka Allah Madaukakin sarki ya ce a hadisul kudusi (Ya ku bayi Na, da na farkonku da na karshenku da mutanenku da aljanunku za su hadu su hallara a kan kasa guda suka roke ni sa'an nan na basu na bawa ko wanne bukatarsa to ba abin da zai rage na daga abin da ke gare Ni face kamar abin da zai rage ne idan aka sa allura aka kamfata daga cikin kogi) Muslim ne ya rawaito daga Abu Zarri.
Na daga cikin adu'o'i mai amfani na kiyaye addini da kuma lafiyan jiki da kiyaye maslahohin duniya da kuma lahira  rokon Allah Madaukakin sarki waraka musamman a irin wadan nan musibu da su ke sauka na gamagari da 'irin bala'u masu girma, An karbo daga Abbas dan Abdulmuddalib Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : na ce ya Manzon Allah ka sanar da ni adu'an da zan roki Allah da shi , sai ya ce : (ka roki Ubangijinka lafiya sai na zauna  wasu ranaku sannan  na zo mishi , sai na ce ya Manzon Allah ka sanar da ni wani abu da zan roki Allah da shi sai ya ce ya Abbas ya baffan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ka roki Allah waraka a duniya da lahira) Tirmizi ne ya rawaito ya ce wan nan hadisi ne sahihi.
(Hakika Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana girmama Abbas kuma ya na son shi kuma ya na bashi matsayi matsayin mahaifi ya kasance yana cewa ya baffa ka yawaita adu'a na neman waraka). Dabarani ne ya rawaito , sahabbai sun kasance su na girmama Abbas sayyidina Umar da sayyidina Usman Allah ya kara yarda a gare su idan su ka zo wucewa wurin Abbas sai su sauka daga kan abin  hawan su domin girmama shi, Imamul kurra'a da muhaddisai na zamanin shi Muhammad dan Aljazari Allah ya mar rahama ya ke cewa mai hankali ya yi dubi ga mikidarin wan nan kalma wanda Manzon Allah ya zabe ta  ga baffan shi domin duk mutumin da aka ba shi waraka to ya rabauta da abin da ya ke fata kuma da abin da ya ke so ciki da waje duniya da addini kuma za a kare shi daga abin da ya ke tsoro a duniya da lahira.
Ilimi na yakini hakika ya zo ta hanya mutawatiri daga gare shi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi adu'arSa ta neman waraka ko lafiya ya zo daga gare shi lafazin da ma'anan duka ta fiskoki da za su kai kaman hanyoyi hamsin, wannan hakika shi da an gafarta mishi abin da ya gabata na daga zunuban shi da abin da ya jinkirta kuma yana katangagge hakikatan to ta yaya kuma mu wadanda mu a ko yaushe mu na kai kan mu ga kifiyoyi na kaddara ma'ana zunubai da kuma abubuwa da su ke na tsakanin rayi da kuma shaidan da son rai ) maganan shi ya kare.
An karbo daga Abubakar Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (ku nemi Allah waraka ta lafiya lallai wani ba a ba shi wani abu ba bayan yakini da ya fi alheri akan waraka) Tirmizi ne ya rawaito da Ibnu Hibban da Hakim kuma ya ce isnadin shi ingantacce ne.
Yakini shi ne imani da Allah da mala'ikunSa da littatafanSa da ManzanninSa da lahi da ranar lahira da imani da kaddara na alheri da na sharri, da gaskatawa gaskatawa na yanke da abin da Annabi ya zo da shi na Alkur'ani da sunna wanda ba wani abu da zai cakudu da shi na shakku a cikin haka da kuma karkata zuwa ga Allah a dukkan komai da maida al'amari gaba daya zuwa gare shi, An karbo daga Anas Allah ya kara yarda a gare shi cewa wani mutumi ya zo wurin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ya Manzon Allah wani adu'a ne ya fi? sai ya ce (ka roki Ubangijinka lafiya da waraka a duniya da lahira)
san nan ya zo mishi a rana ta biyu, sai ya ce : ya Manzon Allah wani adu'a ne ya fi? , sai fada mishi kwatankwacin haka , sannan ya zo shi a rana ta uku , sai ya ce da shi kwatankwacin wancan ya ce: ( Idan an baka waraka na  duniya to an baka ita a lahira hakika ka rabauta )Tirmizi ne ya rawaito.  
An karbo daga Ibnu Umar Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :( Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bai kasance ya kan bar wadan nan adu'o'in ba a lokacin da ya ke yammaci haka nan lokacin da ya ke wayan gari: ya Allah ina rokoKa lafiya a duniya da lahira ya Allah ina rokonka afuwa da kuma waraka a addini na da duniya ta da iyalaina da dukiya ta, ya Allah ka suturce al'aura ta ka amintar da tsoro na, ya Allah ka kiyaye ni ta daga gaba gareni haka nan daga bayana haka nan daga dama ta haka nan daga haguna haka nan daga sama ta kuma ina neman tsarinKa da kasaitanKa da a min  kisan gilla ta kasa ta ) Hadisi ne ingantacce Abu Dauda ya rawaito shi da Ibnu Majah da Hakim da Ibnu Hibban, Da adu'a Allah yake tunkude wan nan annoba da waninsa, An karbo daga Salman Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (Ba abin da ya ke maida kaddara sai adu'a, ba abin da ke kara tsawon rai sai biyayya) Tirmizi ne ya rawaito da Hakin da Ibnu Hibban.
 Ambaton Allah da nau'ukansa duk gaba daya addu'a ne na ibada, Allah na tunkude bala'i da shi, ka yi lura da fadin Annabi tsira amincin Allah su tabbata a gare shi ga Abu Musa Al'ash'ari , ya ce ka ce: (Ba dabara ko karfi sai ga Allah , domin ita taska ce daga cikin taskokin aljanna) Buhari da Muslim ne suka rawaito,  da hadisin Abu huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (La haula wa la kuwwata illa billahi waraka ce daga casa'in da tara na daga cututtuka, mafi saukin shi shi ne damuwa) Dabarani ne ya rawaito a cikin littafinsa Al'ausat haka nan Hakim ma a cikin littafin sa Almustadrak kuma ya ce sahihin isnadi ne, cikan amfani a zikiri akwai bukatan halarto da zuciya da kuma yakini wato sakankancewa, Hakika Allah Ta'ala ya umarci musulmai da adu'a da neman alheri da tunkude dukkan wani abu ya yi umarni da dogaro bisa ga Allah Madaukaki da kuma gaskiyar  komawa zuwa gare shi da dogaro na zuciya a gare shi , sai ya ke cewa:( ka dogara ga rayin da ba ya mutuwa) Allah ya ce (ka bauta mishi ka dogara a gare shi) Allah kuma ya lamuncewa duk mutumin da ya dogara a gare shi dogaro na gaskiya ya nemi mafaka zuwa gare shi da gaskiya Allah ya lamunce mishi isarwa , sai Allah subhanahu wa ta'ala ya ke cewa (Dukkan wanda ya dogara ga Allah to shi ne zai isam masa) kuma shari'a ta yi umarni da rungumar abubuwa na sababi tare da dogaro ga Mahaliccinta.
 An karbo daga Usama dan Sharik ya ce : Na kasance a wurin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai larabawan kauye suka zo suka ce : ya Manzon Allah shin muna yin magani ? sai ya ce ( ya ku bayin Allah ku yi magani lallai Allah Mabuwayi bai saukar da wata cuta ba face ya sanya mata waraka banda cuta guda daya , sai suka ce menene ita ? sai ya ce tsufa) Ahmad ne ya rawaito da Tirmizi ya ce wan nan hadisi ne ingantacce.
Addu'a da neman tsarin Allah daga sharrace - sharrace dukkaninta na gaba daya da kuma na kebe na daga cikin sabuba wanda su ke abin da ya ke mukaddari wanda Ubangijinmu ya umarce mu da  mu yi aiki da su tare da magunguna, An karbo daga Abdullahi dan khubaib Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (kul a'uzai biyu ka fade su yayin da ka yi yammaci haka nan yayin da ka wayi gari ka karanta su sau uku za su isam maka daga dukkan komai) Abu Dauda  ya rawaito shi da Tirmizi .
Ka karanta kul huwallahu Ahad  ka yi tawassuli da sunayen shi Madaukaki da kuma muawwizai guda biyu; Neman tsarin Allah ne daga sharrace - sharrace na gaba daya da kuma na kebe na daga cikin sabuba na sharri dukkanin su da kuma dukkan wasu sabuba na sharri dukkaninsu , ya zo a hadisi ba wanda zai roki Allah da kwatankwacin su.
Na daga cikin abin da ya dace maimaita tunatar da shi, shi ne; taimakekeniya bisa ga daukan mataki na kariya ta hanyan bin nusarwan bangaren lafiya domin a samu daga kowa da kowa a tsallake wan nan musiba mai tsanani da kuma wannan tsanani wanda ke mai ban wahala, Allah ya  saka da alheri ga jagorori shuwagabanni - Allah ya kiyaye su - bisa ga kokarin da su ke yi na a yaba wurin fiskantar wannan annoba mai dauke jama'a da kuma kwadayin su mai tsanani wurin ingancin samun lafiyan 'yan kasa da kuma mazauna to lallai kiyaye koyarwansu da ka'idodin su zai karanta daga wan nan cutan na wan nan fairos din kuma Allah zai daga wan nan bala'i da izinin Shi, to rahamar Allah tana da yalwa kuma farin ciki na kusa Allah Madaukakin sarki yace : (Allah Ubangijinku ya ce ku roke Ni zan amsa muku lallai wadanda su ke girman kai bisa ga roko na za su shiga jahannama suna masu kaskanci) Allah ya sa mana albarka bisa alkur'ani mai girma .
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya halicci dukkan komai ya kaddara shi kaddarawa, kuma ya yalwaci dukkan komai a ilimi ya iyakance dukkan komai a adadi , Allah ya kasance Mai ji kuma Mai gani ina kyautata yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa bisa ga ni'imomi da ba mai iyakance su sai shi, da abin da muka sani cikinsu da wanda ba mu sani ba, na shaida ba bu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya ba abin da zai gagare shi a kasa ne ko a sama na daga bada agaji da shi kuma duk wanda ya nemi agaji na gaggawa a wurin Allah to Allah zai tsirar da shi wanda kuma ya roki Allah kariyarSa to Allah zai kare shi wanda ya nemi taimakon Allah to Allah zai shiryar da shi ya bashi mafaka, haka nan kuma UbangijinKa ya isa mai shiryarwa kuma mai taimako na shaida Annabinmu kuma shugaban mu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, Allah ya turo shi da albishir kuma da gargadi, ya Allah ka yi dadin tsira da albarka ga bawanKa kuma ManzonKa Muhammad da iyalanSa da sahabbanSa dadin tsira da aminci mai yawa bayan haka ; ku ji tsoron Allah Mabuwayi da daukaka domin da tsoron Allah ne Allah ya ke bada kyautan lada kuma ya tsiratar daga azaba.
Ya ku mutane lallai ku kuna ji kuma kuna gani abin da ya faru a doron kasa na daga bakin ciki mai tsanani lallai annoba bala'i  na gamagari ba mai dauke shi sai Ubangijin talikai , na daga cikin sabuba na dauke shi shi ne taimakekeniya wurin daukan sabuba na shari'a da kuma na ilimin  rayuwa da su ke na halal mafi girman sabuban da su ke sa a dauke shi shi ne tuba na gaba daya daga  al'umma dukkansu, Allah Mabuwayi da daukaka ya na tausayawa ta hanyar  tuba da adu'a, abin da bayin shi ba za su iya dauke shi ba Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Halal a bayyane ya ke kuma haram a bayyane ya ke) Allah ya bamu kissa na dauke azaba daga mutanen Yunus ta hanyan tuba sai Allah ya ke cewa : (Ba don wata alkarya ta kasance imaninta ya mata amfani ba face mutanen Annabi Yunusa yayin da su ka yi imani mu ka yaye musu azaban walakanci a rayuwan duniya mu ka jiyar  da su dadi zuwa wani lokaci) .
Ibnu kasir Allah ya mishi rahama ya ke cewa: yayin da su ka rasa Annabinsu suka zaci cewa lallai azaba fa ya kusa zuwa gare su sai Allah ya jefa a cikin zukatansu tuba suka sanya rigar masu ibada Su ka rarraba tsakanin dukkan dabbobi da 'ya'yayensu san nan su ka yi ta ambaton Allah suna komawa zuwa gare shi har dare arba'in, yayin da Allah ya ga haka daga gare su da gaskiyan zukatan su da tubansu da nadama bisa ga abin da ya shude sai Allah ya yaye musu wannan azaba bayan an zuro azaban kusa gare su.
Ya ku bayin Allah lallai Allah da mala'ikunSa suna salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce.            

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق