الجمعة، 24 أبريل 2020

ALBISHIRINKU DA RAMADANA




 
الوصف: cbc250ed-6a0e-4037-8d54-a9eb3d0a0577المترجم : أمين سعد عبد الله

التاريخ :1/9/1441هـ
اللغة : الهوسا
Hudubar Masallacin Annabi 1/9/1441AH 24/4/2020 AD shaikh Salah Bin Muhammad Al budair
Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah,bisa ga riskan watan ramadan, godiyan da zata cika ni'imarSa da kyautarSa, ina gode masa bisa abin da ya kwararo ya yalwata na alheri, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke, ba shi da abokin tarayya, ba wani abin bauta bisa cancanci koma bayanSa, kuma na shaida Annabinmu kuma shugabanmu  Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne. Kuma AnnabinSa  kuma zababbe ne, abokin ganawarsa masoyinSa kuma yardajjenSa, kuma zababbenSa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbansa, har abada muddin safiya na bayyana haske na fitowa.
Bayan haka
Ya ku masu azumi!
Ku ji tsoron Allah ta hanyar yin aiki zuwa ga neman yardarSa, da nesatan saba masa, (Ya ku wadanda suka bada gaskiya an wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabtawa wadanda suka gabace ku ko zaku samu takawa).
Wannan watan ramadana ne ga ta ta kunno, wata ne na busowan alheri ga ta ta bullo,  ga haske mai ban kaye ya sauka, ga shaidan abin jefewa ya kaskanta, An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Idan ramadan ya shigo sai a bude kofofin Aljanna, a rufe kofofin jahannama a kuma daure shaidanu) Buhari da muslim ne suka rawaito. A riwayar Muslim (a bude kofofin rahama) a riwayar Tirmizi ( sai a rufe kofofin wuta ba za a bude ko kofa guda ba, a kuma bude kofofin aljanna ba zaa rufe ko da kofa guda ba daga cikin su).
  Allah Mai girma wani irin abin farinciki ne wannan ! wani irin abun kaye ne wannan! Wani irin kyauta ce wannan! Wani irin kawa ne wannan! Wani irin daukaka ce wannan!
Ya ku musulmai !
Barkan ku da watan ramadana da  ke cike da kamshi, mai kore gurbacewa, dukufaffen annoba ko dare mai saibi ba zai iya gurbata hasken shi da kayen shi da daukakan shi ba, kada ku ji a ranku kamar wasu 'yan fursina da ke kulle cikin bakinciki wadanda suka hadu da jarabawa, to alfijir zai bayyana ka zama kana da aminta, domin kyakkyawan fata na ga wanda ke da aminta, fatan ka na alheri na bakin ka, yin sika da Allah ya isanmaka,
Zamu rayu cikin yanayi mai dadi tamkar kaka bayan bakinciki *
Kai ka ce bamu dandani daci a jiya ba.
Ku yi fatan alheri  duk da samuwar annoba da firgicinta, to zaa kashe wutanta da giragizai,
 Ku yi fatan alheri da sannu zaa yaye mana bakinciki, jamaa da ke shaukin masallaci su dawo,
Ku yi fatan alheri Allah zai hada mu mu ji dadi da abokai da sa'anni.
Bushara zata zo sai mu samu sa'ada da aminci yayin safiya mai fara'a da iska mai dadi.
Ku taho zuwa ga kofofinku an bude su, duk matafiyi mai yawo garuruwa ya fire zuwa inda ya ke so.
Ku kankan da kai,Allah shine Mafi karamcin wanda aka roka, yana warkar da musibu duka da falalarSa. 
     Ku kankan da kai da adu'a don ba mai daukewa ko tunkudewa ko gusarwa,  kuma ba mai yaye wannan annoba sai Allah  wanda ke  mallakar cutarwa da amfanarwa,  wanda ke tasarrufi a cikin halittun sa da abin da ya so  wanda halittu suka  rusunawa kasaitarSa  da daukakarSa , kuma    dukkan halittu  suka zama ba komai ba a gaba gare shi  , suka  tsananta roko suna maimaitawa ya  Ubangijinmu ya Ubangijinmu,  Hasanul Basari yake cewa a fadin sa :-(Sai Ubangijinsu ya  amsa musu) ,  ba su gushe ba suna cewa ya Ubabngijin mu ya Ubangijin mu har aka amsa musu .
Ya mai yaye damuwa da bakin ciki £ Gare ka muke guduwa  don neman mafaka

To ya  Ubangijin mu wannan annoban ya illan ta kuma ya boye wasu abokai  ya Allah ka janye shi  kar ka tsawaita wani tsanani akan mu a hannun ka ne yayewa ya ke, ya Allah  kar ka nuna mana  cikin wanda muke kauna sai abin da muke so , ya wanda  muke so ya  mafi rahamar  ma su rahama.
 YA KU MUSULMAI:
Ku sanya Alkur'ani a gidajen ku kamar kukan zuma  ku sanya ambaton Allah a watan ku abin maimaitawa , ku yi mudarasan  Alkur'ani   tare da iyalanku  da 'ya'yan ku tun daga farkon sa zuwa karshensa  ku kamsasa lebban ku da shi, ku turara bakunan ku da alkur'ani , ku raya mazaunin  ku  , da  unguwannin ku   da  gidajen ku da tilawa da  tarawihi  da  kunuti.
Ku yi sallan tarawihi a gidajen ku a  daidaiku ko a jam'i ko da ya ke   haduwan ya fi  sa nashadi  ga  iyalai kuma ya fi kwadaitarwa, kuma ya fi zamewa abin koyi  idan har mutum bai da karfin yin ta sai ta hanyar koyin din kuma ya ji tsoron barin ta in har a shi kadai zai yi  to a sallace  ta jam'i din shi ya fi dacewa  kuma shi  ya fi falala wurin ribatan dararraki masu daukaka,  idan kuma mutum yana da karfin himma  na yi shi kadai kuma ya himmatu da haka , ya kwadaitu da  ya sallace  ta shi kadai don neman kushu'i ko tsawaita karatu da ruku'u da sujjada , to zai iya yin hakan , al'amarin a cikin shi akwai yalwa .
Baya inganta mace ta limanci maza ko da a tarawihi ne ko ga dangin ta a cikin zance  mafi inganci ,  amma za ta iya limantan mata a gidan ta .

YA KU MUSULMAI:
Idan larura ta saka killacewa mataki ne na kariya  da ya hana ku yawo da shawagi , da kaura daga nan zuwa can to, lallai kuna da  wani fage na rahama a watan azumi da ba  haramtattu ba  da kuma wasu alheri dake busowa wanda ba a iya killace su , kada ku kasance  cikin wadan da za su shagalta da abubuwa masu shagaltarwa, suka gafala daga watan  alheri da rahama , wayoyi na   cikin abubuwan da aka kirkira aka sana'anta wanda abubuwan ban mamaki   a cikin su  na da yawa ababen nema a cikin su sun yawaita , faratunan su sun ta'allaka da mu,  abubuwan da ake shiga a cikin su sun sha bamban to ku kiyaye kar ku bar waya ya cinye mu ku lokutan wata mai albarka , wanda ba da jimawa ba zai zo ya wuce .
Ya kai wanda ke jin radadi da bakin ciki bisa rufe masallatayya ya rasa haduwa da gamayya a sahu, da haduwa a juma'a da jam'i da tarawihi, kar ku yawaita abubuwan na makoki kamar wake, kada kuma  kururuwa  ta musiba ta dauke ku domin haka bai da wanin amafani,  ku yawaita ambaton Allah  da tasbihi a gare shi da girmama shi da tunani cikin ayoyinSa da daukan izna ku yawaita nuna bukatuwar ku zuwa ga Allah da istigfari  , da bada hanzari da lura da wa'azantuwa .
Duk wanda bai ba da hanzari ba a yau to yaushe ne zai bada hanzari
Abin da Ubangiji na ya so ya kasance sai ya kasance * mutum ya kan kai kan shi ga halaka wasu lokuta
Rana ba ta bullowa ko ta bace  fa ce da umarnin  wanda sha'anin sa abin mamaki
Muna da sarki mai kyautatawa a gare mu * mu su wane ne in ba falalar sa a gare mu ba , tsarki ya tabbata a gare ka ya Allah
Ka yi aminci ka yi aminci  ka cika ni'imomi a gare mu kuma  ka cika
Allah ne Ubangiji na kuma  shi ne mai mulki  ba yi da abokin tarayya cikin mulkin sa        

   YA KU MUSULMAI:
Mai yawan dauwama da dogewa akan da'a  wanda ba ta gushe ba tana cikin dabi'arsa da halin sa , bai datse ba daga gare su sannan wannan annoba ya yi shamaki ya killace tsakanin shi da su  tare da son sa na yanke zuwa aikata su , da an kadarta a gare shi ,  to ana sa ran Allah zai rubuta mishi ladan shi cikakke , to, ana muku albishir ya ku wadan da kuka kasance kuna raya masallatayya da salla  da tsayuwa da tarawihi da karatun alkur'ani   albishirin ku ya ku wadan da kuka kasance  kuna shimfida sufura  don shayar da masu azumi Ubangijin ku Ma'abocin da'a ne da tausayi da karamci.
An karbo daga Jabir Allah kara yarda a gare shi yace : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :- (Lallai a cikin madina akwai wasu mutane, ba wata tafiya da za ku yi  ko ku keta wani kori  face sun kasance tare da ku, '' rashin lafiya  ne ya tsare  su'') a wata riwaya face sun yi tarayya  da ku a lada,) Muslim ne ya rawaito. A  BUHARI kuma a  riwayar Anas. Allah kara yarda a gare shi (uzuri ne ya kange su).  
 Ibnul Munzir Allah ya masa rahama yace : (wanda bai samu zuwa ba sabo da uzuri to yana daidai da wanda ya je)
Muna kwadaitar da masu kyautatawa, masu abin hanu, da su yi tarayya a wannan hobbasa na aikin gidauniyar  ramadan na madina  wanda ke nufin ciyar da talakawa da miskinai  wadanda dalilin hana fita ya musu illa da  tsayawar ayyuka ,  mafi alherin sadaka shi ne sadakan cikin watan ramadana , (Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya kasance mafi kyautan mutane  kuma kyautan sa ya fi yin sa cikin azumi)
   Wanda ya shayar da mai azumi yana da kwatankwacin ladan shi ba tare da an tawaye  wani abu ba na daga ladan mai azumin ba, . shekul islam Ibn Taimiya Allah ya mishi rahama yana cewa  :- (''Abun da ake nufi da shayar da shi ; shi ne kosar da shi ''
An karbo daga salt Dan Basdam ya ce:- ''Hammad Dan Abi Sulaiman yana shayar da mai azumi hamsin  a ko wani rana a ramadan  , to idan kuma daren salla ya zo sai ya tufatar da ko wannen su tufafi –tufafi''.
Ku tausayawa  masu rauni da talakawa da gajiyayyu, to duk wanda baya tausayawa ba za a tausaya mi shi ba , ku sada zumunci da sadakoki .
Ba wata dukiya da  za ta saraya  idan ta haifar da godiya ga ma'abotan ta * sa dai dukiyan marowaci  ita take saraya ,  ina fadin abin da kuke ji kuma ina neman gafaran Allah  to ku nemi gafarar sa domin lallai shi ya kasance mai yawan gafara ne ga ma su komawa gare shi .




HUDUBA TA BIYU
Ya kai dan uwa na dan uwa na wanda aka shafe shi da wannan bala'i, aka  hada shi da wannan annoba aka killace shi aka yi nesa da shi  aka killace shi daga mutane  kada  ka kuntata abu mai fadi mai yalwa.
Duniya bata yi kunci ba gare ka da fadinta*
                                           Ba a rufe ma kofar yafiyar Allah ba


Ku yi bushara da waraka da lafiya, ku bazama zuwa ga sallah, ku kyautata zato ga Allah, ku debe kewa da ambaton Allah, da karatun Alkur'ani, kada ka yanke tsammani kada ka yanke kauna daga rahamar Allah, ku dogara ga rayayye wanda bai mutuwa.
Kada ka kashe kan ka da damuwa da bakinciki, domin damuwa ne dafi mafi hadari, ka nemi tsarin Allah daga damuwa da bakinciki, ba wani abu ba ne face wata musiba da ta sauka  kuma za ta gushe, kuma abin da iska ya dauko   sannan kuma zai bace  yarda da kaddara  kamar wata ganima ce na yammaci  kuma babbar itaciya ce ga maras lafiya ,  wannan firgici na tsorata  mara fasalin bayi da wani fa'ida  kuma ba a bada lada ga wannan cutan , lallai mafi girman sakayya  na ga mafi girman bala'i kuma idan Allah ya so mutane sai ya jarrabe su , duk wanda ya yarda to yana da yarda, duk wanda ya yi fushi  to, yana da fushi .
Muna mika jajen mu ga duk wani wanda ya rasa dansa da kuma   wacce ta rasa dan ta ,  abun kaunarsu  mai kima , muna  fatan shahada ga wanda ya mutu cikin  musulmai a dalilin  wannan annoba.
  An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah  su tabbata a gare shi ya ce:- (Shaihidai guda biyar ne ; wanda annoba ta kashe shi, da wanda ya mutu ta sababin ciwon ciki  da kuma  wanda ya mutu a ruwa  da kuma wanda gini ya fadi a kansa , da kuma wanda ya mutu a tafarkin Allah ) Buhari da Muslim ne suka rawaito
An karbo daga Rashid Dan Hubaish  Allah ya kara yarda a gare shi ,cewa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya shiga ga Ubadatu Dan Samid yana ziyartan shi a rashin lafiyan sa , sai  Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :-ko kun san shahidi a cikin al'uma ta? sai Ubadata dan samid ya ce ya Manzon Allah :- shi ne mahakurci mai neman lada a wurin Allah , sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :- ''  lallai shahidai a cikin al'umata in dai haka ne to, dan kadan ne  wanda aka kashe su a tafarkin Allah sun yi shahada , da wanda ya yi mutuwar annoba shi ma ya yi shahada, da kuma  mutuwa a ruwa shi ma shahada ne da mutuwa dalilin ciwon ciki shi ma shahada ne , da  mutuwa ta dalilin haihuwa dan na ta zai ja ta da cibiyar sa zuwa Aljanna
Abul Auwam ya kara da cewa '' da gobara da kuma ambaliya '' Ahmad ne ya fitar da shi
 YA KU MUSULMAI :-
 Ku lazimci matakan kariya da  nusarwa  da fiskantarwa , wanda ke hana yaduwan korona  ku kiyaye taruwa a wurin buda baki da sahur a cikin ramadana .
 Da kukan mutuwa gara killacewa a gida ,  ku yi salati da aminci bisa ga Ahmadu mai shiryarwa mai ceton bayi gaba daya
Duk wanda ya yi mar salati guda to Allah zai mar salati guda  goma.       










       

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق