Hudubar masallacin
Annabi na shaikh Abdulbari Bin Awad Assubaiti 10-8-1441AH/ 3-4-2020 AD
Hudubar farko:
AlKur'ani
na da girma a cikin ayoyinsa, yana da karfi a nusarwansa cikin izinansa da
wa'azuzzukansa yana haskaka basira kuma yana bayyana sunnonin Allah a duniya da
rayuwa da kuma rayayyu, na daga cikin ayoyinSa fadin Allah Ta'ala (Allah ne Mahaliccin dukkan komai kuma wakili ne ga dukkan
komai).
Allah tsarki
ya tabbata Mahaliccin dukkan komai dukkan abin da ya ke motsi da motsawarsa
haka nan dukkan abin da ya ke zaune gu guda da kuma zamantakansa, ba wani
kwayan zarra a cikin sammai ko kasa face Allah ne Mahaliccinsa ba mahalicci
koma bayan shi, ba kuma wani Ubangiji baicin Shi.
Yayin da
musulmi ya ke karanta fadin Allah Madaukakin sarki (ka
ce Allah shi ne Mahaliccin dukkan komai kuma shi ne guda daya Tilo Mai rinjaye) zuciyarsa na samun natsuwa kuma ya rusuna ga kasaitar
Allah wanda dukkan wata kasaita ta ke
zama ba komai ba gaba ga kasaitarSa.
Mutum musulmi
ya na karanta fadin Allah Madaukakin sarki (Ya
halicci dukkan komai kuma ya kaddarta shi kaddarawa) sai ya ga
tafiyar duniya a cikin tsari mai zurfi, haka nan kuma a irin tsarin tafiyanta a
kwai kyautatawa da kuma juyawan halayenta akwai kawatarwa da kuma ban kaye (lallai ko wani abu mun halicce shi da kaddara) Mahalicci
ya yi duniya da abin da ya dace da ita sai ya kaddara ta kaddarawa ya kimtsawa
dukkan wani halitta abin da ya halitta masa ya tabbatar da haka wa kanSa a
fadinSa (shi ne wanda ya halitta kuma ya daidaita
kuma ya kaddara ya shiyar), musulmai na karanta fadinSa (kuma Ubangijinka ya halicci abin da ya so kuma ya zaba)
to mutum zai yi lura ta yaya halittan Allah suka kasance nau'uka daban daban na
halittu da kuma iri daban daban na abubuwa da Allah ya halitta zai gani a ko
wani kwayan halitta a kwai bambanci da waninsa na daga sauran halittu wurin
sababin samuwansa da kuma kimansa da kuma ma'anansa, kuma fadin Allah Subhanahu
Wa Ta'ala (Halittan Allah yanda ya ke kyautata dukkan
komai, lallai shi Mai bada labari ne game da abin da ku ke aikatawa)
wato ya kyautata dukkan komai da ya halitta ya kyautata shi kuma ya sa a
cikinsa, akwai hikima na daga abin da ya sanya .
Musulmai na
jin fadin Allah (Ban halicci sammai da kasa ba da abin
da ke tsakaninsu don wasa ba, ban haliccesu ba face da gaskiya sai dai mafiya
yawan su ba su sani ba) sai ya gane cewa lallai Allah bai halicci
duniya don wasa ba, bai kuma bar halittu haka kara zube ba, kuma abin da ke
bayan wannan gudanarwa na ban kaye da kuma tafiyarwa wanda ya ke akwai hikima a
ciki, akwai haduwa na lahira da sakayya Mai adalci yayin da musulmi zai yi lura
da fadin Allah Madaukakin sarki (Allah wanda ya halicce
ku sa'an nan ya azurta ku) zai samu natsuwa a zuciyarsa, hakika Allah ya dauki nauyin azurta shi da
yalwata shi daga taskarSa wacce ba ta karewa, da wannan yakinin ne ba zai
fiskanci tambayan wani ba koma bayan Allah Madaukaki, musulmi yana sani a
lokacin da ya ke karanta fadin Allah Madaukakin sarki (Lallai ne mun halicci mutun cikn wahala) lallai
rayuwa tana haduwa da wasu abubuwa na wahalhalu gajiya na cakuduwa da ita
jarabawowi na kewaye da ita sai ya kawata da imani mai zurfi da hakuri mai kyau
Allah Madaukakin sarki ya ce (kuma lallai ne muna
jarabar ku da wani abu na tsoro da yunwa da tawaya na daga dukiya da rayuka da
'ya'yan itace kuma ka yi bishara ga masu hakuri).
Na daga
cikin abin da ya ke karfafa hakuri sakankancewan bawa cewa duk abin da ya same
shi imma ya kasance kankara ne ga zunuban shi ko kuma sababi ne na ni'iman da
ba a samu sai an bi gadan wahala da jarabawa sa'annan karshen ya zama abu ne
mai kyau.
Musulmi na
karanta fadin Allah Madaukakin sarki (wanda ya
halicce ni sa'an nan ya na shiryar da ni
wanda shi ne ya ke ciyar da ni kuma ya ke shayar da ni, kuma idan na yi rashin
lafiya shi ne ya ke warkar da ni, kuma wanda ya ke matar da ni sa'an nan ya
rayar da ni , kuma wanda na ke kwadayin ya gafarta min kurakurai na a ranar
sakamako). To sai ya tabbata a gare shi wannan ma'anan ya samu natsuwa da kwanciyan hankali to Ubangijin
shi yana ciyar da shi kuma ya na shayar da shi idan wani abu na rashin lafiya
ya same shi, shi ya ke warakar da shi, idan ya roke shi bukata zai bashi, kamar
kuma yanda musulmi ya sakankance cewa tunkude rashin lafiya da kawo waraka yana
hanun Ubangijinsa majibincinsa .
Musulmi na
karanta fadin Allah (Allah ne wanda ya halicce ku
sa'an nan kuma ya ke kashe ku), zai sani sani da ba shakku cewa, lallai
rayuwan duniya wata tasha ce kuma lallai za ta gushe duk tsawon wanzuwarta,
kuma cewa shi din nan zai kaura a yau ko gobe, don ya hadu da Ubangijinsa.
Musulmi kan karanta fadin Allah (An halicci dan adam da halin gaggawa, zan nuna muku ayoyi Na sabo da haka kada ku memi yin gaggawa)
sai ya san cewa abubuwa da suke faruwa da musibu lallai da ya yi a cikin
halittunSa a ko wasu sha'anunnuka haka nan kuma abubuwan da ya boye akwai
hikimomi masu zurfi, akwai na bayyane wasu kuma a boye ( kar ku zaci cewa sharri ne a gareku) a cikin
abubuwa da ke faruwa da musibu musulmi kan karanta fadin Allah (lallai ne mutum an halicce shi mai ciwon kwadayi, idan sharri
ya shafe shi ya kasa hakuri, kuma idan alheri ya shafe shi ya yi rowa , sai
kawai masu yin salla ,wadanda suke, a kan sallar su su masu dawwama ne)
sai ya ga siffofi na kwadayi da rashin hakuri tana galaba a kan shi ga wanda
rashin lafiya ya sauka gare shi ko kuma wani talauci ya same shi ko kuma wata
musiba ta sauka gare shi ya samu daman yin rowa da hanawa idan an bashi dukiya
wadata ko lafiya ta lullube shi da
waraka amma Allah sai ya toge daga cikin haka wanda su ke bisa ga sallolin su
suna masu dawwama, masu kiyaye salloli, su ne wadanda su ke samun sa'ida masu
kiyayewa Allah na kiyaye su a cikin abubuwa da ke faruwa na musibu, musulmi ya
kan tsiraita daga dabarar shi ko karfin
shi ya tabbatar da talaucin sa da bukatuwarsa zuwa ga Ubangijin shi da rashin
wadatuwansa daga shi kyabtawan ido, a hakan ne Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ke fadin adu'o'i na bakin ciki (Ya Allah rahamarka mu ke fata kar ka kyale mu zuwa kan mu
ko da kyabtawan ido ka gyara mini sha'ani na gaba dayan shi, ba abin bautawa da
gaskiya sai kai).
Huduba ta biyu :
A cikin wannan mawuyacin yanayi
da duniya ta samu kanta sakamakon abin da wannan annoba mai saurin yaduwa ta
haifar, duk wani mai hankali zai yaba da yadda mahukunta wannan kasa - masu son
kawo tsari da matakan kariya ga rayuka da maslahohi - suka zama tsintsiya
madaurin ki daya da talakawan su da suke wayayyu wadanda suka san ya kamata
wajen bin dokoki da ka'idoji har zuwa wannan bakinciki da bala'in ya wuce, mu
tsallake wannan tashin – tashina da matsanancin yanayi da falalar Allah da
rahamarSa da tausayawarSa, haka kuma ana samun karin dankon zumuci ne da ke
dauke da kambin sarauta ta gaskiyar komawa ga Allah da tuba.
A irin
wannan yanayi na gamagarin annoba ya zama wajibi akan masu fada a ji da masu
akwai da su ji nauyin da ke kansu na addini, mas'uliyyarsu
da sakonsu a irin wannan yanayi da ake jarraba imani, a haka ne imani da 'yan
uwantaka ke bayyana don a saukakewa
talakawa da miskinai da marayu radadin wannan musiba da yadda abubuwa suka ci
tura ya jefa wasu ciki kuma bai gushe ba yana jefa wasu, ga wasu ayyuka sun
tsaya, to a nan ne ake samun wasu ke tashi da hobbasa a bangaren tattalin arziki
da dukiya da sanin ya kamata a bangaren zamantakewa da kula da ruhi da iyalai
kowa ya yi gwargwadon fagensa da kwarewarsa a bigirensa ya bada nasa gudumawa
iya gwargwadon himmarsa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi ya ce : (Duk wanda ya yayewa mumini wani
bakinciki daga bakincikin duniya to shi ma Allah zai yaye mishi bakinciki daga
bakincikin ranar alkiyama, wanda ya yalwatawa matalauci shi ma Allah zai
yalwata masa a duniya da lahira, duk wanda ya rufa asirin musulmi to Allah zai
rufa asirinsa a duniya da lahira, Allah na taimakon bawa muddin bawa na
taimakon dan'uwansa). Muslim ne ya rawaito.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق