|


التاريخ
:24/8/1441هـ
اللغة :
الهوسا
Hudubar Masallacin Annabi 24/8/1441AH
shaikh Abdulmuhsin Alkasim
Hudubar farko
Dukkan
yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna gode maSa kuma muna neman taimakonSa,muna
neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu
da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi,
wanda ya batar kuma babu mai shiryar da shi, na shaida ba abin bautawa da
gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke, ba shi da abokin tarayya, kuma na shaida
Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne. tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi da iyalan shi da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa.
Bayan
haka, ku ji tsoron Allah -ya ku bayin Allah- cancancin tsoronSa; to ni'ima na cikin bin shiriya, tsiya kuwa na
ga biyewa son rai.
YA
KU MUSULMAI:
Allah Mai
tsarki yana da kyau da kuma daukaka a cikin sunayen shi da siffofin shi da ayukan shi , ya halicci duniya ya kyautata
abin da ya kirkira ya sanya wasu sunnoni da ba sa canzawa ko sauyawa , Allah Madaukakin
sarki ya ce: (To ba za ka sami musanyawa ba ga hanyar Allah,
kuma ba za ka sami juyarwa ba ga
hanyar Allah).
Na daga cikin sunnonin sa yana jarraban bayi da yalwa don
su gode mishi ya kuma jarrabe su da cuta
don su juyo gare shi Allah Mai tsarki ya ce:- (Kuma
muna jarraban ku da sharri da alheri domin fitina , kuma zuwa gare mu ake mayar
da ku).
Hakika
kuma an jarabci wasu al'umu da haka Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Ko kuna zaton ku
shiga Aljanna kuma tun misalin wadan da suka wuce daga gabanin ku bai zo
muku ba wahaloli da cuta sun shafe su).
Ibn
Kasir Allah ya mishi rahama ya ce :-''Su ne
rashin lafiya da cututtuka da radadi da musibu
da tashin hankali ''.
Sai
Allah ya turawa Banu isara'ila ruwan dufana
; fari, da kwarkwata, da
kwadi da jini ayoyi ne daki-daki.
Kuma Allah Mai izza da daukaka yana bayyanawa bayinSa kasaitanSa
da mulkinSa da karfinSa da kudurarSa
ga halittunSa da buwayarSa da jabarutinSa a duniyarSa da kuma rinjayenSa da kuma
haimanarSa ga bayinSa , domin su girmama
Shi kuma su kadaita Shi, su kankan da kai zuwa gare shi, sai Allah ya tunbuke
dutse mai girma ya dora shi a saman banu isra'ila don su yi imani, Hasanul
Basri Allah ya masa rahama ya ce : ''Yayi da suka
ga dutsen sai kowani mutum ya fadi ya yi
sujada da saman giransa na hagu yana dubi da idonsa na dama ga dutsen tsoron
kada ya fado a kansa"
Allah Madaukakin
sarki ya ce: (Kuma
a lokacin da muka daukaka dutse sama da su kamar dai shi girgije ne, kuma suka
tabatar mai faduwa ne gare su, (aka ce) ku karbi abin da muka baku da karfi,
kuma ku tuna abin da ya ke a cikinsa ko za ku yi takawa)
Allah
ya turo mala'ikan duwatsu ga Annabinmu
Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da shi ya Muhammad idan ka so sai na kifa musu duwatsun na biyu Akhshabain
wasu manyan duwatsu ne guda biyu a
makka.
Kuma
Allah ya yi bayani game da saurin zartar da al'amarinsa a fadinSa;(UmarninSa idan ya yi nufin wani abu sai ya ce masa kawai
"ka kasance" sai ya kasance (kamar yadda ya ke nufi)
Domin
bayyana ajizanci irin na bani adam Allah ya kalubance su gabadayansu da su halicci kwayan hatsi, Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce Allah Mabuwayi da Daukaka ya
ce : (To in zasu iya su halicci kwayar zarra ko
su halicci kwayan hatsi ko sha'iri) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Da
Allah ya so da ya turo musu wata aya da zata tilasta musu su yi imani da karfin
tsiya Allah Madaukakin sarki ya ce: (Idan mun so zamu
saukar a kansu da wata aya daga sama sai wuyayensu su yini sabo da ita suna
masu kaskantar da kai).
Ibnu
Juraij Allah ya masa rahama ya ce''Da Allah Ya
so da ya nuna musu wani al'amari daga cikin al'amuranSa wanda bayan haka ba
dayansu da zai iya saba masa a cikinsu"
Allah ya yi wa bayinSa umarni da su rika yin
tunani kan abin da yake faruwa a duniya kuma su yi lura da abubuwan da ke
wakana, sai Mai tsarki ya ce : (kace Ku yi dubi ga
abin da ke cikin sammai da kasa)
Mumini yana daukan izina a
ayoyi kuma ya wa'azantu da su, Allah Madaukakin
sarki ya ce: (wannan
tafarki na ne mikakke hakika mun yi bayanin ayoyi daki –daki ga mutane masu wa'azantuwa)
Kuma
ya sakankance cewa dauraya ne a gare shi da daukaka daraja daga Allah, sai ya
siffatu da wata ibada da ladanta ba iyaka.
Allah Madaukakin sarki ya
ce: (Kuma da
sannu zamu jarabe ku da wani abu na tsoro da yunwa da tawaya na daga dukiya da
rayuka da 'ya'yan itace to ka yi albishir ga masu hakuri. Wadanda idan musiba
ta same su sai su ce : daga Allah muke kuma gare shi zamu koma. Wadannan suna
da wani kyakkyawan ambato daga Ubangijinsu da rahama kuma wadannan su ne
shiryayyu.)
Duk
wanda yayi imani da hukuncin Allah da kaddararSa to Allah zai maida masa
madadinsa da ya tsere masa a duniya, Allah Madaukakin sarki ya ce : ((Ba wata musiba da za ta samu face da izinin Allah, kuma wanda ya yi imani
da Allah Allah zai shiryar da zuciyarsa)
Ibnu
kasir Allah ya masa rahama ya ce:''Duk wanda
musiba ta same shi ya san cewa hukuncin Allah ne da kaddararsa, sai ya yi
hakuri ya nemi ladansa a gurin Allah, ya mika wuya ga hukuncin Allah to Allah zai shiryar da zuciyarsa, kuma ya
musanya masa abin da ya rasa a duniya da
shiriya a zuciyarsa da yakini na gaskiya, kuma ya kan maye masa da abin da ya
rasa ko ma abin da ya fi shi alheri.)
Mumini
a duk juyawan zamani ko dai ya zama yana da lada bisa yalwa ko ya yi hakuri
bisa ga abin da ya tsere na wani abin duniya na musiba ko jarabawa, Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Mamaki da al'amarin
mumini, lalle dukkan al'amarinsa alheri ne, haka bai kasancewa ga kowa sai
mumini, idan abin farinciki ya same shi sai ya yi godiya sai hakan ya zama
alheri a gare shi, in kuma cuta ce ta same shi sai ya yi hakuri hakan sai ya
zama alheri a gare shi) Muslim ne ya rawaito.
Kyautata
zato ga Allah cikin hikimarSa da gudanarwanSa da tausayinSa ga bayinSa da
tausasawarSa gare su da rahamarSa bisa halin da suke ciki na cikin mafi girman
sababi na dauke bala'i, Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : Allah Madaukakin sarki yace (Ni ina inda bawa na ya zace
ni)Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Kuma
dogaro ga Allah da maida al'amari gare shi wajen kauda bakinciki abin lamuncewa
ne. , Allah Madaukakin sarki ya ce : (Duk wanda ya
dogara ga Allah to ya isan masa)
Imam
Alkurdubi Allah ya masa rahama ya ce''wato wanda
ya maida lamari gare shi zai isar masa duk abin da ya sha gabansa".
Aikata sababi tare da dogaro
ga Allah na daga cikin abin da sharia ta zo da shi :
(Ya ku wadanda suka yi imani ku riki shirinku).
Na
daga cikin manufofi na musulunci akwai kiyaye rai da nesatar da shi daga duk
cuta mai rabuwa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (ka guje wa mai
kuturta tamkar yadda zaka gujewa zaki) Ahmad ne ya rawaito.
Zaman
gida a lokacin musiba da hadura shi ne hanyar kiyayewa da samun aminci,
tururuwa ma ta gano haka (Ya ku jama'ar tururuwa! Ku shiga gidajen ku kada Sulaimanu
da rundunonin sa su karkarya ku alhali kuwa
su basu sani ba )
Ya
dace ga musulmi a wannan halin da wanin sa
da ya raya lokacin sa da faragarsa
cikin abin da zai amfane shi , kuma
ya yawaita nusar da iyalan shi da
'ya'yansa .
Kuma duk wanda ayukan shi na kwarai suka
gajarta sabo da wani uzuri, to ladan sa
na wurin Allah cikakke, kuma shi ma'aboci falala ne mai girma , Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :- (Lallai a cikin madina akwai wasu mutane , ba wata tafiya da za ku
yi ko ku keta wani kori face sun kasance tare da ku, sai suka ce ya Manzon Allah ahali suna madina ? sai ya ce
'' e, uzuri ne ya tsare su'') BUHARI ne
ya rawaito.
Kankan da kai zuwa ga Allah da juyawa zuwa
gare shi don neman mafaka tare da
bayyana rauni da kankan da kai a gare shi
abu ne da yake gusar da bala'i,
Allah Mai tsarki da daukaka yana cewa:- ( Ina
ma da yayin da tsananin mu ya zo musu
sun kankan da kai ).
Adu'a
mabudi ne da ke canza yanayi zuwa yanayi
mafi kyau Allah Madaukakin sarki ya ce
:- (Kuma Ubangijin ku ya ce ku roke ni zan amsa muku
).
Ita sadaka tana kashe fushin Ubangiji Mai rahama da ita ne
lada kan ribanyu , kuma ake kankare
kusakurai da laifuka mai yin sadaka yana
cikin aminci a duniya da lahira , Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Wadanda suke ciyar da dukiyoyin su a dare da wuni a sirrace da bayyane to, suna da ladan su a
wurin Ubangijin su babu tsoro a gare su
ko bakin ciki).
Ciyarwa
yana yaye bakin ciki yayin da wahayi ya saukawa Annabi farkon
sauka sai ya cewa khadija Allah ya kara yarda a gare ta ( Hakika na jiwa kai na
tsoro , sai ta ce; a'a wallahi
Allah ba zai tozartar da kai ba har abada domin kai kana sada zumunci, kuma
kana daukan nauyin gajiyayyu kana kuma taimakawa gaskiya a lokacin musiba ,
BUHARI ne ya rawaito
Amfanin
ta na wucewa zuwa ga yaye bakin ciki na matattara (ranar alkiyama) , mai yin sadakan
sai ya zama yana karkashin inuwar
sadakarsa ranar alkiyama, wanda ya boye sadakarsa ko da dan kadan ne to
kuwa Allah zai karrama shi a wata inuwar
wacce ba inuwar sadakarsa ba , wato inuwar al'arshin Allah.
Tuba
zuwa ga Allah da komawa zuwa gare shi
tafarki ne na Manzanni Annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:- (Lallai
ni ina neman gafara ga Allah na tuba zuwa gare shi a rana sau saba'in) Buhari ne ya rawaito.
Kuma
yawaita da'a da tsoron Allah tafarki ne
na samun sa'ida, Allah Madaukakin sarki ya ce:-
(Wanda ya ji tsoron Allah toAllah zai sanya mishi mafita ).
Ibn
Abbas Allah ya kara musu yarda ya ce:- (Zai tsiratar da shi daga
bakin cikin duniya da lahira).
Idan
hanyoyi suka yanke jarabawa suka tsanan ta
bayi suka ta'allaka da Ubangijinsu Allah, sai Allah ya yaye bakinciki, Manzon Allah tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:- (Ubangijin
mu ya yi dariya sabo da yanke tsammanin bayinSa da kuma kusancin tsananinSa ,-wato tsananin su na kusanci tare da kusancin sanjawan halin su –Abu Razin
Allah ya kara yarda a gare shi ya ce:- ''Na ce ya Manzon Allah ashe Ubangiji ma yana dariya ya ce '' E'' to ko ba za mu rasa alheri ba
daga Ubangijin da yake dariya ). Ahmad ne ya rawaito.
Idan
bakin ciki ya yaye ya wajaba ga bayi su kyautata yabo ga Allah su gode mishi su
yi kyakkawan ambato a gare shi Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Ku gode mini kada ku kafurce mini )
BAYAN
HAKA YA KU MUSULMAI:
To
Allah mai girma ne ya iyakance dukkan
komai , babu gujewa daga gare shi sai dai dawowa zuwa gare shi , kuma yana yarda ga bayin shi da su mishi da'a kuma ya yi alkawarin bude alheru gare su daga
sama da kasa muddin suka nemi mafaka a gare shi , (Da
ace mutanen alkaryu za su yi imani su yi takawa
da mun bude musu albarkatu a gare
su daga sama da kasa ) ba
wanda zai amfane ka koma bayan Allah (Idan Allah ya shafe ka da cuta ba mai yayewa face shi , in kuma ya nufe ka
da alheri to ba mai maida falalar Sa ).
Ka ta'allaku
da Shi ta hanyar ayyukan da'a, ka girmama addininSa kuma ka yawaita tilawar littafinSa da kuma karanta sunnan ManzonSa
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi kuma ka yi riko da shari'arsa kuma ka yi
farin cikin da ita.
Ina neman tsarin Allah daga sharin shaidan abin jefewa
(Za mu nuna musu ayoyinMu a cikin sansani da kuma a cikin rayukansu, har
ya bayyana a gare su cewa lalle (Alkur'ani) shi ne gaskiya , ashe, kuma Ubangijin ka bai isa ba , ga
cewa lallai shi halartacce akan ko wani abu ne).
Allah
ya sa mini albarka ni da ku a cikin alkur'ani mai gairma.
HUDUBA TA BIYU
Dukkan
yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa kyautatawarsa, godiya ta tabbata a
gare shi bisa datarwarSa da baiwarSa, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai
Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, ina mai girmama sha'aninSa, na
shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne. Tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbansa da aminci tabbatacce mai kari.
Ya
ku musulmai!
Allah na saukar da cuta tare da sauki to gashi watan alheri ta fuskanto, tana kusa da ta bude kofofin ta, a duk lokacin da jinjirin
watan ta ya haska sai ya hasko tare
da iskan alheri da kyakkyawan fata , Musulmai na
jiranta rayukansu na cike da albishir zukatan su na cike da farin ciki da walwala,
ramadana mafi alherin watannin shekara ,
Allah ya turo Manzon sa a cikinta ya saukar da littafinsa mai girma acikin ta, kofofin sama a bude suke kofofin jahannama a rufe suke , a
cikin ta ne ake daure shaidanu wunin ta
na da falaloli daren ta na da albarka , a cikin ta akwai lailatulkadari wanda
tafi wata dubu alheri , wanda ya azumce
ta kuma ya tsaya mata yana mai
imani da kuma neman lada za a
gafarta mishi abin da ya gabata na daga zunuban shi, yawaita ambaton Allah yana daga cikin abu mafi alheri da musulmai za su fiskanci watan nasu da shi , da kuma neman gafararSa da azama bisa ga ribatan sa'o'inta ta hanyar biyayya da kyautatawa da kuma fiskantar da'a da tilawar Alkur'ani
da tsere a wurin aikin alheri a cikin ta , sa'annan ku sani Allah yana umartan ku da salati da aminci ga
AnnabinSa .
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق