الأحد، 22 مارس 2020

KIYAYE HARSHE A MUSULUNCI


Hudubar Masllacin Annabi na SheikhAbdulmuhsin Bin Muhammad Alkasim 4-7-1441AH / 28-2-2020 AH
Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna gode maSa kuma muna neman taimakonSa
Muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu  da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, wanda ya batar kuma babu mai shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya,kuma na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa. Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa.
Bayan haka, ku ji tsoron Allah -ya ku bayin Allah- cancancin tsoronSa, duk wanda ya ji tsoron Ubangijinsa zai tsira wanda ya bijire daga ambatonSa zai fadi.
Ya ku musulmai :
Ni'imomin Allah ga bayi basu kididdiguwa, (kuma duk wani abu da ke gare ku na ni'ima to daga Allah ne).
Harshe na daga cikin ni'imomi masu girma da wasu ludufa na daga aikin Allah masu ban mamaki, Allah ya baiwa da shi ne ga bayinSa sai yace :(Ase bamu sanya idanuwa biyu gare shi ba da harshe da lebba biyu)?
da shi ne ilimi da bayani da karrama Dan-Adam ke samuwa Allah Madaukakin sarki ya ce :(Mai-rahama, ya koyar da Alkur'ani, ya halicci mutum, ya sanar da shi bayani.)
Duk abin da ya ke fada ana kiyaye shi a sahifarsa wacce da ita zai hadu da Ubangijin Shi ranar Alkiyama, Allah Madaukakin Sarki ya ce :(Ba ya furuci da wata magana face like da shi akwai mai tsaro halartacce) sabo da haka ne Allah ya umarci bayinSa da su fadi magana madaidaiciya, sai yace : (ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah ku fadi magana madaidaiciya) kamar kuma yadda ya umarce su da fadi magana mafi  dadi mafi kyau, (kuma ka ce wa bayiNa su fadi kalma wacce take mafi kyau)
Na daga cikin wajibabbun imani kiyaye harshe face daga alheri, Manzon Allah tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Duk wanda ya kasance yana imani  da Allah da ranar lahira to ya fadi alheri ko ya yi shuru.) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
   Allah ya yabi bayinSa muminai da suke bijirewa wasa na fadi ko aiki sai yace : (Da wadanda suke juya baya ga lagawu(wasa).  
Musulmi shine wanda ya kiyaye harshensa, Manzon Allah tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Musulmi shine wanda musulmai suka kubuta daga sharrin harshensa da hannunsa).  Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Ta hanyar kiyaye shi ne ake samun fifikon matsayi tsakanin bayi, an tambayi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wa ya fi alheri cikin musulmai sai yace shine wanda musulmai suka aminta daga harshensa da hannunsa).Muslim ne ya rawaito.
Kuma Aljanna sakayya ne ga wanda ya kiyaye harshensa. Manzon Allah tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Wa zai kiyaye min bakinsa da farjinsa  na lamunce mishi aljanna). Buhari ne ya rawaito.
Harshe karamin abu ne amma yana da amfani mai yawa.kuma ya kan iya kasancewa mai tsananin cutarwa sabo da haka Annabi ya nemi tsari daga sharrinsa sai yace : ,  (Ya Allah ina neman tsarinka daga sharrin harshe na) Abu Dauda ne ya rawaito.
Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tsoracewa sahabbansa da al'umarsa shi, Sufyan dan Abdullahi Assakafi Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :Nace ya Manzon Allah me ka fi tsorace min? sai ya rike harshensa ya ce :wannan).Tirmizi ne ya rawaito.
Bisa tsoronsa ne  sahabbai suka tafi, Abubakar Allah ya kara yarda a gare shi ya fitar da harshensa sai ya ce : (wannan shi ya kai ni ya baro ni).
Ibnu Abbas ya kasance yana rike harshensa sai ya ce :(kaitonka ka fadi alheri za ka rabauta ko ka yi shuru daga mummuna zaka kubuta, in ba haka ba to ka sani zaka yi nadama).

Harshe hadarinsa na da girma a duniya da lahira, sau da yawa kalma guda kan bata rayuwar mutane, Ibnu Mas'ud Allah ya kara yarda a gare shi yace : (Ba wani abu da ya fi bukatar kulle shi a kurkuku na tsawon lokaci kamar harshe na).   
Magana kan halaka ma'abocinsa har ya hadu da Allah yana Muflisi Manzon Allah tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi ya ce : (ko kun sansa muflis sai suka ce Muflis shine wanda bai da dirhami ko wani abu na kayan jin dadi, manzon Allah yace : Lalle muflis a cikin al'uma ta shine wanda zai zo da sallah da azumi da zakka, ya zo a halin ya zagi wannan yayi kazafi ga wannan, ya ci dukiyar wannan ya zubar da jinin wannan ya daki wannan, sai a bawa wannan daga kyawawansa, wancan ma a bashi daga kyawawansa, idan kyawawansa sun kare kafin a kare biyan bashin da ke kansasai a dauko daga laifukansu a dora kansa sannan a jefa shi wuta.) Muslim ne ya rawaito.
An tambayi Annabi game da abin da ya fi shigar da mutane wuta sai yace baki da farji) Tirmizi ne ya rawaito.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :(lallai bawa zai yi magana da kalma ba zai bayyana mishi (hadarinta) ba, zai zame cikin wuta a dalilinta fiye da nisan mahudan rana da mafadanta) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Mafi girman laifi na harshe shine kiran wanin Allah da sanya mishi kishiya Allah Madaukakin Sarki ya ce :(wa nene ya fi bata sama da wanda ya ke kiran wani komabayan Allah wanda ba zai amsa mishi ba har zuwa eanar alkiyama a halin su sun gafala daga adu'arsu)
(Duk wanda ya mutu a halin yana kiran wanin Allah to zai shiga wuta.) Buhari ne ya rawaito.
Na daga cikin rokon wanin Allah akwai neman ruwan sama ta hanyar amfani da taurari, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : Allah Madaukakin sarki ya ce a hadisul kudsi ( An wayi gari cikin bayi na akwai mai imani da ni da kuma mai kafurci, to duk wanda yace : Mun samu ruwa ne da falalanAllah da rahamarSa to wannan shine wanda ya yi imani da ni kuma ya kafurcewa taurari)  Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Neman tsari daga wanin Allah ba abin da ya ke karawa mai yinsa sai tsoro da rauni, Allah Madaukakin Sarki ya ce : (Kuma lalle ne shi, wasu maza daga cikin mutane sun kasance suna neman tsari da wasu maza daga cikin aljanu, saboda haka suka kara musu girman kai).
Na daga cikin shirka da Allah a magana akwai rantsuwa da wanin Allah, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :( wanda ya rantse da wanin Allah to  hakika ya kafirta ko kuma ya yi shirka).Muslim ne ya rawaito
(wanda ya rantse da wani addini ba musulunci ba bisa karya da gangan to shi ya zama kamar yadda ya ce ) bukari ne ya rawaito
(wanda ya rantse da amana to baya tre da mu) abu dauda ne ya rawaito
Allah tsarki ya tabbata a gare Shi ya na da cikakken kamala na mulki na saki waiwai wanda ya sa suna irin wanda Allah ya kebanta da shi  to Allah zai kaskantar da shi manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ya ce : (mafi kaskancin suna a wurin Allah shi ne mutumin da zai sa suna sarkin sarakuna ba wani mai mulki sa Allah) bukari da muslim ne suka rawaito al'mari na Allah ne shi shi kadan shi ba a' hada shi da wani a mashi'arSa tsarki ya tabbata a gare Shi a ta bangaren daidaitawa a lafazi ne ko a ma'na Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ya ke cewa (kada ku ce Allah ya so wane ma ya so sai dai ku ce Allah ya so sa'an nan wane ma ya so) Abu Dauda ne ya rawaito.
Kaddara kudura ce daga gurin Allah da imani da shi kuma rukuni ne cikin rukunan imani, baa cewa ina ma da na aikata kaza da kaza zai faru da kaza," ba don ba" na bude aikin shaidan.
Fushi bisa abin da Allah ya kaddara na daga magana na cikin al'amarin jahiliyya.
(mai kukar mutuwa in bata tuba ba daga aikinta zata tashi a ranar alkiyama tana tare da rigar karfe na harshen wuta). Muslim ne ya rawaito.
       Allah ke tafiyar da dare da wuni, kuma zagin zamani na warware imani ko kuma yana raunana shi,
 Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ya ke cewa (kada ku zagi zamani domin Allah shine zamani). Muslim ne ya rawaito.
Wanda ya munana zato ga Allah ya kuma yankewa halittun Allah tsammani daga rahamarSa, to hakika ya kai kansa ga ukuba ta Allah, wani mai ibada a cikin banu isra'ila yace da wani mai sabo a cikinsu : (wallahi Allah ba zai gafarta wa wane ba, sai Allah yace da shi wane ne ya ke min shishigi da rantsuwar bazan yafewa wane ba, to lalle hakika na gafarta masa kai kuma na rusa aikinka) Muslim ne ya rawaito.
Abu Huraira –Allah ya kara yarda a gare shi yace : "Na rantse da wanda rai na ke hanunSa ya fadi kalmar da ta halaka masa duniyarsa da lahirarsa"
(Wanda yace mutane sun halaka to shine mafi halakarsu)
Sanin ilimin gaibi ya kebanta ne ga Allah subhanahu wa taala, Allah Madaukakin Sarki ya ce : (Kace babu wanda ya san abin da ya faku a cikin sammai da kasa face Allah),
  (wanda ya je gun mai duba ya tambaye shi daga wani abu  to ba zaa karba mishi wata sallah har dare arba'in). Muslim ne ya rawaito.
(wanda ya je gun boka ko mai duba kuma ya gaskata shi cikin abin da ya ke fadi, to hakika ya kafirta da abin da aka saukarwa Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)Ahmad ne ya rawaito.
Na daga cikin mafi girman muharamai fadin magana game da Allah ba tare da ilimi ba,
Allah Madaukakin Sarki ya ce : (Kace abin sani Ubangiji na ya haramta alfahasha abin da ya bayyana daga gare su da abin da ya boyu da zunubi da rarraba jama'a ba , da wani hakki ba kuma da ku yi shirki da Allah ga abin da bai saukar da wani dalili ba gare shi , kuma da ku fadi abin da ba ku sani ba , ga Allah ) izgianci da addini ya na  fitar da ma'bocin shi daga cikin addinin Allah madaukakin sarki ya ce : (Ka ce shin da Allah da kuma a'yoyinSa da ManzonSa kuka kasance kuna izgilanci ?) (kada ku kawo wani uzuri hakika kun kafirta a bayan imanin ku)
Kuma karya na daga cikin munanan zunubbai da alfasha masu aibi kuma shi ne asalin dukkan sharri shi ne kuma ya ke cikin alamomi na munafunci yana shiryarwa zuwa ga fajirci , lallai fajirci yana shiryarwa zuwa ga wuta mutum ba zai gushe ba ya na kirdadan karya har a rubuta shi a wurin Allah makaryaci .
Mafi munin karya shi ne wanda ya kasance a kan Allah da Manzon Sa Allah subhanahu wa ta'ala yana cewa (kuma a Ranar Kiyama kana ganin wadanda su ka yi karya ga Allah fuskokinsu suna masu yin baki . Ashe, babu mazauni a cikin jahannama ga masu girman kai ) Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( duk wanda ya min karya da gangan to ya shirya makomansa a cikin wuta) Muslim ne ya rawaito ,( duk wanda yarantse bisa karya yan mai tune ga al'marin da ya shudai to rantsuwanSa rantsuwa ce ta gamus (nitsatstsiyan rantsauwa cikin zunubai )
(duk wanda ya rantse bisa ga dukiyan mutum musulmi ba tare da hakki ba zai hadu da Allah ahalin Allah ya na fushi da shi ) Bukari da Muslim ne suka rawaito , na daga cikin karya shi ne iddia'a'I wurin dangantaka Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(ba wani  mutumin da zai jingina kanshi ga wani mahaifinshi a halin yana sane face ya kafurta ,ko ya yi da'wan wani dangin da ba nashi ba to ya shirya makomansa a wuta ) Bukari da Muslim ne suka rawaito .
Na daga cikin manyan zunubbai shaidan zur Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Ashe ba zan baku lbarin mafi girman zunubbai ba? sau uku sai suka ce iye ya Manzon allah sai ya ce : hada Allah da wani da kuma cin zarafin iyaye sai ya zauna da yana kishingide ne sai ya ce ku saurara da fadin zur bai gushe ba yana ta maimaitata har muka ce ina ma da ya yi shuru ,) Bukari da Muslim ne suka rawaito . dukkan  musulmi a kan musulmi haramun ne jininSa sa dukiyanSa da mutuncinSa , na daga cikin manyan zunubbai mutun ya zagi iyayensa suka ce : ya Manzon Allah yaya mutun zai zagi iyayenSa ?( sai ya ce iye , (ya zagi baban wani wanin kuma ya zagi babanshi ya zagi uwar wani wanin kuma ya zagi mamanshi ) Bukari da muslim ne suka rawaito .
Na daga cikin abubuwa masu halakarwa akwai kazafin mata katangaggu gafalallu mumunai Allah madaukakin sarki ya ce (lallai ne wadanda suke jifar mata masu kamun kai gafilai, muminai an la'ne su a cikin duniya da lahira kuma suna da azaba mai girma) kage jifan wanda ya barranta ne daga abinda bai tare da shi Allah madaukakin sarki ya ce (kuma wanda ya yi tsiwir-wirin  kuskure ko kuwa zunubi sa/annan kuma ya jefi wani barrantacce da shi to lalle ne ya tattali kirkiran karya da zunubi bayyananne)
 Cin naman wani shine ambaton dan'uwanka da abin da bai so, kuma yana cikin manyan zunubai Allah madaukakin sarki ya ce (kada sashenku su yi giban sashe) Ibnu Abbas Allah ya kara yarda a gare shi shi da mahaifin shi- yace : (Allah ya haramta giba kamar yadda ya haramta mushe)
 Na daga cikin laifuka na harshe kai komo da annamimanci tsakanin halittu Allah Subhanahu yake cewa : (kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, walakantacce. Mai zunde mai yawo da gulma mai hana alheri mai zalunci mai zunubi).
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Mai annamimanci ba zai shiga a ljanna ba) Bukari da Muslim ne suka rawaito.
Yahya bin kasir Allah ya mishi rahama yace :(Mai annamimanci kan bata cikin saa guda abin da mai sihiri ke batawa a shekara guda.)
Zagin Musulmi fasikanci ne (ba wani da zai jefi wani da fasikanci ko ya jefeshi da kafurci face ta dawo zuwa gre shi muddin bai kasance wan nan ma'bocin shin hakan ya ke ba) Bkari ne ya rawaito tsine wa mumini kaman kashe shi ne duk wanda ya tsine wa wani wanda ba ahlinta ba to tsinuwan za ta dawo kanshi mumini bai kasance mai yawan suka ba ko yawan tsinuwa ba Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (lallai masu yawan tsinuwa basa kasancewa masu ceto kuma basa zama masu shaida a ranar alkiyama ) Muslim ne ya rawaito .
Izgilanci ga halittu yana cikin nau'in girman kai ya isa sharri mutum ya rena dan uwanshi musulmi Allah madaukaki ya ce (ya ku wadanda suka yi imani kada wadansu mutane su yi izgili game da wadansu mutane mai yiwuwa ne (abin yi wa izgilin) su kasance mafifita daga gare su (masu izgilin), kuma wadansu mata kada su yi izgili game da wadansu mata mai yiwuwa ne su kasance mafifita daga gare su , kuma kada ku aibanta kanku , kuma kada ku jefi juna da miyagun sunaye na lakabobi tir da suna na fasicci a bayan imani kuma wanda bai tuba ba to wadannan su ne azzalumai) abubuwa guda hudu ya cikin abubuwan jahiliyya alfahari da dangi da suka da nasaba da kuma neman saukan ruwa ta hanyan amfani da taurari da kuma kukan mutuwa .
Kamar yadda musulunci ya harrama zagin rayayyu haka ma kuma ya harrama zagin matattu Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (kada ku zagi matattu, domin sun riga sun shude zuwa ga abinda suka kaddamar) Bukari ne ya rawaito . kai musulunci ya hana zagin iska ma da ma zazzabi da kuma dabbobi da ma wasun hakan duk wanda ya bayyana mummuna to hakika ya kai kanshi ga tonon silili daga wurin Allah Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (dukkan aiumma na suna samun waraka amma banda masu bayyana sabo) Bukari da muslim ne suka rawaito .  

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق