Dukkan yabo da godiya sun
tabbata ga Allah muna gode masa kuma muna neman taimakonsa da gafararsa, muna
neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah
ya shiryar da shi babu mai batar da shi, kuma duk wanda ya batar babu mai
shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah,shi kadai yake
ba shi da abokin tarayya, na kuma shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma manzonSa
ne.tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da aminci
tabbatacce.
(Ya
ku wadanda suka bada gaskiya ku ji tsoron Allah cancancin tsoronSa kada ku mutu
face kuna musulmai)
(ya
ku mutane ku ji tsoron Allah wanda ya halitta ku daga rai guda kuma ya halitta
matarsa daga gare shi ya yada daga gare su mazaje masu yawa da mata, ku ji
tsoron Allah da ku ke roko da (sunan) shi. Da zumunci, lalle Allah ya kasance
mai tsaro ne a kan ku.)
(ya
ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah ku fadi zance na daidai. zai gyara
muku ayyukan ku kuma ya gafarta muku zunubanku, duk wanda ya ke yi wa Allah
biyayya da ManzonSa to ya rabauta rabauta mai girma.)
Lalle zance mafi gaskiya
shine littafin Allah, kuma mafi kyaun shiryarwa shi ne shiryarwan Muhammad tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi, mafi sharrin al'amura shi ne fararrun su , kuma dukkan fararrun abubuwa
bidi'a ne , kuma dukkan bidi'a bata ce , kuma dukkan bata na wuta
Bayan haka:
Ya ku mutane
Ku sani lalle Ubangijinku Allah ne wanda ba abin bautawa da gaskiya sai
shi,ya yalwaci dukkan komai a rahama da ilimi, ya halicci dukkan komai ya
kaddara shi kaddarawa, ya iyakance dukkan komai a adadi, ya gudanar da shi
gudanarwa,
Ya yi ludufi da abin da ya so cikin abin da ya ke so zuwa ga wanda ya
so. Ya kasance da boyayyiyar kaddararSa da iliminSa mai zurfi goni ne Mai
tausayi ga abin da ya boyu na daga
halittunSa , da kuma zartarwa ga hukuncin sa .
Ya yi ludufi da basirarSa bisa ga
abin da ya ke na gani na hakika sai ya riske shi, yayi ludufi da jinSa ga boyeyyen sautuka sai ya tantance su , ya yi ludufi da ilimin
sa ga abubuwan da suke kananu masu halartowa a zuciya sai ya
banbance su ,
(Wanda ya fari halittan sammai da kasa, ta yaya zai kasance yana da Da a halin bai da mata , kuma ya halicci
dukkan komai a hali kuwa shi
masani ne ga dukkan komai. Wancanninku shi ne Ubangijin ku ba abin bautawa da
gaskiya sai shi mahaliccin dukkan komai
, to ku bauta mishi lallai shi wakili ne
ga dukkan komai, gani ba ya riskan
shi a hali kuwa shi
mai tausayi ne goni ).
(Kuma ku boye fadin ku ko ku bayyana shi
, lalle shi masani ne ga abin da ke
cikin kiraza . Ku saurara ashe , bai sani ba ; wanda ya yi halitta alhali kuwa
shi Mai tausayi ne goni).
Ya yi ludufi ga abubuwan da suka boyu na wahayin sa tun daga mulakutin sammai da ayoyinSa da ake
karantawa wanda aka sauke su a rarrabe ga matayen Annabi ma'abota dakuna tun
daga Baitul Izza har zuwa gidan Annabtaka
(Ku tuna abin da ake karantawa a
gidajenku na daga ayoyin Allah da hikima kuma lalle Allah Mai ludufi ne mai
bada labari).
Ya zartar da ludufin al'amarin shi, ruwa daga sararin sama zuwa doron
kasa inda ba tsirrai ko shuka, ya shayar
da shi zuwa ga tsirrai da
jijiyoyin itace masu koshi da ruwa ya isar da ruwa mai dadin sha ga lambuna.
(Ashe ba ka ga Allah ya saukar da ruwa
daga sama sai kasa ta zama koriya lallai Allah mai ludufi ne kuma goni).
Ya zartar da ludufin shi cikin halittun shi da irin ludufi na halittan sa zuwa ga
mai raya bitane ya fitar da su, da tsanani irin na jiki sai ya halaka ta, da kuma
gungu mai yawa sai ya rarraba su, kuma da dunbin dukiyaya halaka ya wargaza shi, Ya yi shawagi ga wuyan jabberawa sai ya kaskantar da su, da lafiya na yanayin su sai ya illantar da
ita, da tabbatattun kafafuwan su sai ya zamar da su, ya daga benaye abin
daukakawa sun tsawaita da runduna abin karfafawa, da masu yawan ibada da masu
bauta da masu keta iyaka da masharrata.
Ya haura zuwa ga biranen rayuka
masu cunkoso da jikuna da suke hade babu sauti na motsin kafa ko shafa, kamar ba a rayu ba a jiya.
Ya yi gaba da masoya ya muamalance su da halin makiya, sai suka zama sun yanke masa zumunci
sun yi nesa da shi, sai shamaki ya katange tsakanin masoya juna.suna yiwa rogo
kallon kitse tamkar yadda mai jin kishi ya ke kallon kawalwainiya.
Ba don komai ba sai don wani abu da ya faru daga gare mu, da wani abu da
ya dauke daga gare mu, kada ku zaci cewa makiyi ya yi galaba ne, sai dai Mai
kiyayewan ne (Allah) ya juya baya. Ko zasu kankan da kai, ko zasu komo, ko zasu
wa'azantu.
Tsatsan zukata ta yawaita, to sai Masanin gaibi ya tausasa, duk abin da ya yi tsauri zai yi
rauni, kuma duk abin da ya yi taushi zai yi tsauri, domin Allah ya dauraye
wadanda suka yi imani ya koke kafirai. Kuma ya san wadanda suka yi nifaka.kuma
ya dauki fansa daga wadanda suka yi laifi ya warkar da zukatar muminai,kuma ya
riki masu shahada a cikin su, lalle Ubangiji na Mai ludufi ne ga wanda ya so. lalle
shi Masani ne Mai hikima.
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya isa, tsira da aminci
ga AnnabinSa zababbe, da iyalansa da sahabbai ma'abota biyayya da wafa'i, da
wanda ya bi da kyautatawa ya bi sawunsu.
Bayan haka ku ji tsoron Allah cancancin tsoronSa, duk wanda ya ji tsoron
Allah zai sanya masa mafita kuma ya azurta shi ta inda bai zata ba. (Duk wanda ya dogara ga Allah to shi ya isan masa, Lalle
Allah Mai iyar da umarninSa ne,) Lalle Allah ya sanya ma'auni ga dukkan komai.(Wanda
ya ji tsoron Allah zai sanya masa sauki cikin al'amarinsa) (Wanda ya ji tsoron
Allah zai kankare masa laifukansa kuma ya girmama ladansa.)
Ya ku musulmai!
Allah Mai tausayi ne ga bayinSa yana tausaya wa mai karamin karfi
dalilin mai rauni cikin halittu, ko da masu karfi sun ki, yana zartar da ludufinSa
mai zurfi ga kaskantacce a cikin bayinSa ko da masu izza sun ki, yana azurta
wanda ya so Shi Mai karfi ne Mabuwayi tsarki ya tabbata a gare shi,.. yana
karanta ni'imomi masu yawa ga bayinSa kuma ya habaka kadan na daga da'a ga
bawanSa,
Iya gwargwadon zurfin ludufi iya gwargwadon riskarsa, shine wanda in ka
kira shi zai amsa ma, in ka nufe shi zai baka mafaka, kuma in ka kaunace shi
zai kusanto ka, kuma idan ka masa da'a sai ya saka maka, idan ka saba masa sai
yana iya baka waraka , idan ka juya masa baya sai ya kira ka, idan ka kusanto
shi sai ya shirye ka.
Yana sakanya a gare ka in ka kyautata yana yafiya a gare ka in ka
gajarta duk wanda ya rusuna a gare shi zai daukaka shi wanda ya nuna bukatuwa
zuwa gare shi zai wadata shi ba ya bukata daga masoya wasu hanyoyi ko kuma
sabuba umarninSa kusantarwa ne haninSa kuma ladabtarwa ne kyautanSa zabi ne
haninSa adana ne matattaran ludufanSa tausasawa ne da kusantarwa shi makusanci
ne mai amsawa duk wanda ya shaida Allah
ga zuciyansa to zai dauke masa
duk wasu abubuwa masu yawa mafi ludufi da kuma mafi girman shi mafi darajan shi
da daukakan shi shi ne ya yi ludufi
cikin bayinSa ta hanyan taimakawa a cikin kaddara kuma da yarda da kuma
tawali'u da tuba da kankan da kai da
komawa da rusunawa da imani.
Bayan haka ya ku bayin Allah
Ku sanya gidajenku alkibila ku tsaida sallah ku yi da'a ga wanda Allah ya jagorantar da al'amuranku a
gare su cikin da'a wa Allah ku yi sallah ku yi salati da aminci bisa ga
alkibila mafi tsarki da kuma mashaya na farin ciki da kuma Annabi mafi daukaka da kuma waliyyi mafi kusa
shugabanmu Muhammadu Annabi Ummiyi hakika Allah ya zabe shi, lallai Allah da
mala'ikunSa suna salati ga Annabi .
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق