Hudubar Masallacin Annabi na shaikh Abdullahi Bin Abdurrahman Albuaijan 18-7-1441AH /12-3-2020AC
Hudubar Farko:
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Mai amsa adu'a Mai yaye bakin ciki
da bala'i ina gode mishi bisa ni'imomi daban daban, muna neman tsarin Allah daga
sharrin abin da ya halitta na daga bala'i
da annoba yana sanya shi ga wanda ya so kuma ya tunkude shi daga wanda ya so.
Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke bai da
abokin tarayya, kasaita da yabo nashi ne da buwaya da girmame girmame da
dawwama da wanzuwa duka nashi ne, na
shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne cikamakin Annabawa ma'abocin
isra'i da mi'iraji da tabki da kuma lema, tsira da amincin Allah su tabbata a
gare Shi da iyalansa da sahabbansa da wanda ya bisu da kyautatawa a halin sauki
da kuma halin cuta.
Bayan haka:
lallai mafi kyan zance shi ne littafin Allah mafi alherin shiriya shi ne
shiriyan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbatauma a
gare shi mafi sharrin al'amura sune fararrunta, dukkan bidi'a bata ce kuma
dukkan bata na wuta.
ya ku bayin Allah : ina muku wasiyya da ni kaina da tsoron Allah, domin ita ce mafaka, kuma
da bin sunnar Annabi ne tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
ake samun kubuta (Ya ku wadanda suka yi imani ku ji
tsoron Allah rai ya dubi abin da ya kaddamar sabo da gobe, ku ji tsoron Allah,
lallai Allah Masani ne ga abin da ku ke aikatawa).
Ya tawagar musulmai …
Duniya gida ce ta musibu da kuma bala'u da kuma jarabawowi da kuma fitintinu gida ce ta jin zafi da kuma haduwa da ba-
zata, gida ce ta radadi da kuma azaba da kuma lafiya da kuma cuta da rashin
lafiya da kuma waraka da sauki da kuma bala'i gida ce ta farin ciki da bakin
ciki, gida ce ta jin rashin dadi da kuma bacin rai da tsanani da wahalar duniya,
kurkuku ce ga mumini kuma aljanna ce ga kafiri, akwai yawan musibu da kuma
jarabawowi wanda Allah ke jarraba mai
da'a da fajiri da su, na mumini da kafiri, ba a jira bayan lafiya sai rashin
lafiya bayan samarta sai tsufa, bayan wadatuwa sai talauci da rashi, hanyan
rayuwa da ba ta canjawa kuma bata sauyawa daga su ne a duk yanda ilimi ya ci
gaba aka samu habaka a'aha ko da dan adam ya kaura ne zuwa sarari na sama da
kuma wata ko da ya kutsa cikin nitson karkashin kasa da koguna ya zauna a can
dole ne zai hadu da tawaya da kuma gazawa kuma ilimi da hankali yana i'itirafi
da gazawa irin na duniya.
(ya ku jama'r
aljanu da mutane in kuka samu damar ku fita daga sassan sammai da kassai to ku fita, baza ku fita ba sai da karfi ).
Lallai ita ce kudura ta Allah
wacce take tana da girma mashi'arSa da iradarSa
al'marinSa da hikimarSa dukkan wani abu a hanunsa ya ke al'mari nashi ne
kafin da bayan, abin da ya so ya ke kasancewa, abin da bai so ba bai kasancewa,
ba wani abu da ku ke so face abin da Allah ya so ba'a tambayan shi game da abin
da ya ke aikatawa, sai dai al'marin shi idan ya so wani abu zai ce da shi ne
kasance sai ya kasance tsarki ya tabbata ga Allah wanda mulkin komai ke hanun shi
kuma zuwa gare shi za ku koma .
Ya ku bayin Allah :
Ya dace ga mumini a lokacin tsanani da yalwa da kunci da yalwa da wadata
ya tuba zuwa ga Allah ya fawwala al'amarinshi zuwa gare shi ya nemi mafaka a
wurin Allah ya dogara gare shi duk wanda
ya dogara ga Allah to Allah ya isam mashi kuma ya sani cewa duk wani abu da ya
same shi bai kasance da ya kuskure shi ba duk kuma abin da ya kuskure shi bai
kasance da ya sameshi ba abin mamaki da al'amarin mumini dukkan al'amuransa
alheri ne a gare shi idan abu mai dadi ya same shi sai ya gode sai ya kasance
alheri a gare shi idan kuma cuta ko wani abu mara kyau ya same shi sai ya yi
hakuri hakan sai ya zama alheri gare shi (Ba wani
abu da zai samu na musiba a doron kasa ko kuma a kan kawunan ku face yana
rubuce a littafi kafun a halicce ta lallai hakan ya ke gudana a wurin Allah, domin kada ku yi
bakin ciki bisa ga abin da ya tsere muku ko kuma ku yi farin ciki bisa ga abin da
ya zo muku Allah ba ya son mai takama mai
alfahari )
To ya wajaba a gareku ku yarda ku
nemi lada a wurin Allah ku nemi lada daga wurin Allah da sakayya ku mika wuya
ga abin da Allah ya kaddarta ya hukunta ku sakankance ladan Allah bisa ga
musiba da kuma cuta. Allah ya ce (ka yi albishir ga
masu hakuri wadanda idan musiba ta same su sai su ce daga Allah muke kuma gare
shi za mu koma wadan nan suna da kyakkyawan yabo daga wurin Ubangijinsu da kuma
rahama wadannan su ne shiryayyu).
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya shar'anta halal da
haram, Mahaliccin rayuka da jikkuna ya tunkude musibu da kuma rashin lafiya Mai
yin ni'ma ga bayinSa da lafiya daga abubuwa masu bijirowa na dare da wuni
daga cikin bala'i ya sanya mishi rahama
da daukaka da kankaran zunubai daga
cikin cuta ya sanya lada da kuma adana
da tsarkaka bisa ga lafiya da waraka ku kasance masu godiya bisa ga bala'i da
azaba ku kasance masu hakuri, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu
Muhammad amintacce da kuma bisa alayensa da sahabbansa da tabi'ai.
Ya ku bayin Allah :
Lallai annoba shi ne abin taimako ga bakin ciki da kuma tashin hankali sa'an nan
da ci baya da kuma tashin tasina gashi ya rikita sashi da yawa na duniya a
cikin yan tsirarun kwanaki to ku yi kokari wurin tumbuke shi da kuma iyakance
shi, An karbo daga Sa'd dan abi wakkas cewa ya tambayi Usama dan zaid ya ce menene ka ji daga Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa game da annoba,
Usama sai ya ce na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi yana cewa (Annoba wata tsoratarwa ce
ko kuma azaba ce da Allah ke turo ta ga banu isra'ila ko kuma ga wadanda suke
kafin ku, to idan kun ji wani abu makamancinta a kasa to kada ku je kasan idan
kuma ta faru a wata kasa kuna cikinta to kada ku fita domin guje mata)
Muslim ne ya rawaito
Ya tawagan musulmai
Ku ji tsoron yada jita- jita, kage da kuma kambama abu da kuma
tsoratarwa da isgilanci ku gode wa Allah bisa ga lafiya kada ku kai kanku ga
bala'i ku ji tsoron sabuban yaduwar cuta da kuma wuraren annoba ku roki Allah
lafiya da waraka da sauki ku katangu da
zikirori da adu'oyi duk wanda ya yi fata a wurin Allah ba zai yi hasara ba, ku
gujewa kaddaran Allah zuwa wata kadarar Allah ku kankan da kai zuwa ga Allah
kada kuma ku yanke tsammani daga rahamar Allah.
** ya ma'boci bakin ciki
lallai bakin ciki yana yayewa ****
** albishirinka da alheri domin mai yaye bakin ciki shi ne Allah
****
**shi yanke tsammani wani sa'i ya kan katse ga
ma'bocin shi****
**kar ka yanke tsammani domin Allah shi ne mai isarwa
****
** Allah yana kawo sauki bayan bakin ciki****
**kar ka gaza ka gajiya lallai mai yayewa shi ne Allah****
**idan an jarrabeka to ka zama kana da aminci da Allah
ka yarda da shi****
**lallai wanda ya ke yaye bala'i shi ne Allah****
**idan Allah ya hukunta kawai ka mika wuya bisa ga
kudurarSa ****
**mutum baida wani hila ko dabara cikin abin da Allah
ya hukunta ****
**na rantse da Allah ba ka da wani koma bayan Allah ****
**Allah ya isan maka a ko wani abu kana da Allah ****
** ya ma'aboci bakin ciki lallai bakin ciki abin
yayewa ne ****
** albishirinka da alheri lallai mai yaye bakin ciki
shi ne Allah ****
Ya Allah Mai yaye bakin ciki ya mai amsa adu'a ka yaye
mana bala'i ka dauke mana cuta ka gaggauto mana da waraka ka hore mana magani
ba abin bautawa da gaskiya sai kai, tsarki ya tabbata a gare ka, mu mun kasance
cikin wanda suka yi zalunci
Ya Allah ka tunkude mana tsada da annoba da riba da
zina da girgizan kasa da bala'u da mummunan fitina abin da ya bayyana daga gare
ta da abin da ya boyu daga gare mu musamman haka ma da sauran garuruwan
musulmai baki daya.
Ya Allah ya Mai bada mulki makwarkwadan mu na hanunka
hukuncin mu a hanunka ya ke abin da ka hukunta game da mu shi ne a'dalci muna
neman tsari gareka daga mummunan kaddara da kuma fadawa kololuwa na tsiya da
dariya na makiya da kuma saukan bala'i da yaduwar annoba , ya Allah ma'aboci kasaita da girmame girmame ya Mai saukar da
kyauta kai ne ka isar mana madalla kuma da abin dogaro ka gyara mana sha'ninmu
gaba daya kar ka kyale mu zuwa ga kawunan mu ko da kebtawan ido ne muna rokonka
amincin da bayansa babu jirkita , da
yarda wanda bayansa ba fushi da kuma yaye bakin ciki wanda bayansa ba bakin
ciki , ya Alla gareka muka dogara kuma zuwa gareka muka mika wuya kuma zuwa
gareka ne za mu koma muna neman tsarinka daga sharrace- sharracen kawunanmu da
kuma sharrin ko wace dabba da kai ke rike da makwarkwadanta .
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق