Hudubar farko
Ya
ku musulmai
Hakika
an yi suka ga duniya a huhunshi da wani irin cuta na korona wanda ya cire fatan
ido saboda tsana ya ragewa jiki karfinta ya yaki garurruwa kuma ya shigeta ya
yi kaca kaca da yanayi ya keta farfajiya kuma ya lalata iska tsarki ya tabbata
ga wanda ya ke saukar da cuta kuma ya bada izini da yaduwa idan ya so ba don
komi ba sai don jarabawa da godawa da kuma tunatar wa da tsoratarwa to ku
tsorata zuwa ga ambaton Allah tare da neman gafaranShi ku koma zuwa ga Allah ku
nemi kariya daga gareShi ku kiyaye ambaton Allah ku roki Allah da addu'ui wanda
suka tabbata daga sunna ba abunda ya fi amfani wajen magamce annoba kamar
adduwa da kuma gaskiyar komawa ga Allah
ya ku musulmai:
wadan nan
annoban suna kasancewa ne san nan kuma suna zama ba komai ba so dayawa annoba
ta kan sauka kuma ta zo ta fi ta bayyana kuma ta zo ta boyu ta bibiyo kuma
sannan ta zo ta juya baya , an karbo daga Anas dan Malik Allah ya kara yarda a
gare shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(fatan alheri na burgeni sai suka ce menene fatan alheri
sai ya ce : kalma mai dadi) Bukari da muslim ne suka rawaito
larabawa suna ambaton abu na dafi da mai lafiya suna ambato abu karyayye da
wanda aka mikar da shi aka gyara shi ba don komi suke yin hakan ba sai don
neman fatan alheri suna ambaton mutane masu tasowa ga tafiya kafila saboda
fatan alheri Allah ya dawo da su lafiya ma'na ana fatan dawowansu , to ku yada
abinda ya ke na fatan alheri da kuma natsuwa kada dayanku ya zama na kamar
raidiu ma'na mai yada abinda ya ji ko kuma mutumin zai falga ya firgita mutane
a duk lokacin da ya ji wani labari sai ya yada shi ya baza shi
ya ku musulmai :
Ku ji tsoron cututtuka da za su iya cutarwa da
wurarenda annoba su ke, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi ya ce (duk wanda ya ji tsoron sharri to za a
bashi kariya daga gare ta) Ibnu abiddunya ya fito da shi ga hadisin
abu huraira yanada kuma shahid da za su karfafeshi .
Ku rufe fusakanku yayin atishawa ko tari ku rufe da
hankacif da makamantansu domin kada dayan ku ya cutar da abokin zaman shi ta
hanyan tartsatsin da ke fita daga bakinsa ko hancinsa da wadannan kwayoyin cuta
wanda ke yaduwa ta hanyan atishawa ko kuma tari ana iya samun yaduwar da
umarnin Allah ta hanyan shakan numfashin burbushin kwayoyin cututtuka ta iska da kuma ba
haya da suka barbazu na mutumin da ke tare da wannan cutan An karbo daga abu
huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce: (idan dayanku
ya yi atishawa to ya saka tafin hanunshi akan fiskanshi kuma yayi kasa da
sautinshi) Hakim ne ya fito da shi , ku wanke hannaye kafin cin abinci da bayan
shi da bayan biyan bukata (bayan zagawa ban daki) da bayan shafan wanda ake
tsoron yaduwan cutan ta hanyan tabashi da duk wani abinda ya taba hannaye biyu
na cuta na daga zufa ne ko kuma na kazanta ko kuma ko wani abu makamancin haka
, An karbo daga A'isha Allah ya kara yarda a gare ta ta ce:( Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan ya nufi ci ko sha a
halin yana halin mai janaba sai ya wanke
hannayenshi san nan sai ya ci ko ya sha)Imamunnasa'I ya fito da shi
, an karbo daga Abu huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (duk wanda ya kwana a hanunshi akwai gamru bai wanke ba
wani abu ya same shi to kar ya zargi kowa sai kanshi) Ahamad ne ya fitar da shi.
Kuma gamru shi ne warin abinci ko danshin abinci da
maikonsa ko dankonsa domin kananan kwari su kan iya nufoshi da wasu abubuwa
masu dafi a halin mutum yana bacci sai su cutar da mutum ko su harbeshi ko su
ma mishi illa su sa mishi rashin lafiya
Ya ku musulmai :
Yin shamaki daga wanda cuta mai raba ke tare da shi
bisa ala'da ba laifi an karbo daga Abu
huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce: (ka gujewa
kuturu kamar yanda za ka gujewa zaki) Bukari ne ya fito da shi .daga
sharid dan suwaid alssakafi ya ce : ya kasance cikin wasu tawaga daga sakif
wani mutumi kuturu sai Annabi ya tura zuwa gare shi yana mai cewa (lallai mu mun karbi
mubaya'anka amma ka kom)Muslim ne ya fito da shi , Annabi bai
mishi mubaya'a ta hanyar runguma ba ko kuma hada jiki ba ko kuma fiskanta ba
saboda cakudayya da mai kuturta na daga cikin sabuban yaduwa a ala'dance , masu
tantancewa cikin malaman ilimi su tafi akan cewa kutare idan sun yawaita ana
iya hana su zuwa masallatayya da wuraren sallan juma'a har sai lokacin da aka
tabbatar ba zai raba ba , ba zai yadu ba
wasu daga cikin malaman ilimi suka ce game da kuturtako kutare to idan sun
yawaita za a iya akama musu guri na daban kamar yanda aka yi da marasa lafiyan
makka , kuma an karbo daga Abu huraira Allah ya kara yarda a gare shi Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(kada a shigar da marasa lafiya cikin masu lafiy)
Bukari da Muslim ne suka rawaito , shi mara lafiya shi ne ana nufi a nan
wato rakumin da ya ke mai cuta shi kuma
mai lafiya a nan ana nufin rakumin dfa ya ke ingantacce bai da cuta Annabi ya
hana a hada su rakuma marasa lafiya tare da masu lafiya domin tsoron yaduwan cutan da kuma kiyayewa daga
juyawa na cututtukan da kuma annoba kuma annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya yi umarni da cewa idan annoba ta auku a gari mutum ba ya
ciki to kada ya shiga garin idan kuma ya kasance yana ciki kada ya fita daga
garin domin guje mata , an karbo daga usama dan zaid Allah ya kara yarda a gare
shi shi da mahaifinshi ya ce Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce : (annoba wani
tsawatarwa nr ko azaba ne Alla ke turota zuwa ga banu isra'ila koma wadanda su
ke kafun su idan kun ji ta a kasa to kar ku je garin idan kuma ta faru a kasa
kuna cikinta to kar ku fita daga garin domin tsoronta) Bukari da
Muslim ne suka rawaito .
Ya ku musulmai :
Mustahabbi ne kada mutum ya sha sauran mara lafiya
wanda cutansa na raba a ala'dance saboda
daukan kariya abu ne da shari'a yayi umarni da shi.
(Annabi ya hana game da
sha daga bakin tulu) Bukari ne ya rawaito shi , a wurin Hakim kuma
ya ce (saboda hakan yana doyayashi) a
wurin Tirmizi kuma (Annabi ya hana a numfasa a
cikin kwano ko kuma a hura a cikinshi ) Ibnu hajar ya ke cewa : (saboda ta iya yuwuwa numfasawan ya fito tare da wani
nyawu ko majina ko wani tartsatsi mara kyau sai ya bashi wani wari da bayi da
dadi sa ya kazantar da shi ko ko waninsa shi abin shas din)'' ya kare .
Amma hadisin da ya zo na cewa nyawun mumini ga mumini waraka
ne ko kuma sauran mumini waraka ne ma'na (sauran ruwan da mumini ya sha ya
rage) to wannan hadisi ne na karya kirkirarre ba yi da asali .
Ya ku musulmai :.
Ku rufe kwanuka ku daure bakin jaka saboda tsoron
annoba da cuta da kiyayewa daga kananan dabbobi masu cutarwa da kuma dafi , an
karbo daga Jabir dan Abdullahi ya ce na ji Manzon Allah tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce yana cewa (ku rufe kwanuka ku daure bakin jaka domin a shekara akwai
wani dare da annoba ke sauka baya wucewa a kwano da ke bude ba marfi face sai
ya sauka ko kuma jaka da ba a daure ba sai annoban ya sauka a cikin shi)
Muslim ne ya rawaito.
Allah ya kiyaye mu da ku daga masu bijirowa munana da
kuma abubuwa masu sauka na bala'I ina fadin abunda ku ke ji kuma ina neman
gafaran Allah ku ma ku nemi gafaranShi lallai shi mai karban tuba ne ga masu
komawa gare shi
Huduba ta biyu
Ya ku musulmai :
Runguma da sumbatan juna abu ne da ya halatta sai dai
likitoci sun yi hani game da shi a
wannan zamani da fairos korona ya bayyana saboda kiyayewa daga yaduwan shi ,shi
wannan annoba da kuma kula da hakan yana cikin hikima da kuma hankali da kuma
fikhu malaman fikhu sun yi amfani da maganan likitici amuntattu a cikin dayawa
daga cikin hukunce hukunce kaman fadin imamu shaf'I game da ruwa da aka sa shi
a rana ya ce : bana karhanta ruwanda aka dumama shi da rana sai dai idan ta
bangaren likitoci ne suka karhanta .
ya ku musulmai :.
Na daga cikin kariya da musulunci ya yi nuni zuwa gare
shi shi ne kiyaye jikuna da haramcin cin abunda ke da fika na daga zakanyu da
kuraye ko kerkece da kare da kuma kenwa
da makamantansu da dukkan wani abu mai faracuna na daga tsuntsaye kamar shaho
da jalbe haka nan kuma da cin abinda ya ke cin mushe da kazanta da najasa kamar
alhanzir da cin dukkan wani abun kazanta kamar duji da hudahuda da da kuma
jamagu da birrai da kwari da zanbur da makamantansu na daga dabbobi wadanda ba
sa cikin abincin musulmai an karbo daga ibnu Abbas Allah ya kara yarda a gare
shi , shi da mahainsu ya ce : Manzon Allah ya yi hani game da cin sdukkan wani
abu mai fika na daga zakayyu da kuma masu faracuna na daga tsutsaye) Imamu muslim da ibnu hibban suka fito da shi
kuma lafazin nasa ne wadannan namukan sun kumshi wasu kwayoyin cuta ne da
tsutsotsi da wasu dufailiyyat da suke sanya rashin lafiya wanda ke sabbaba
hadari ga hankali da kuma fahimta da jiki abun mamaki da irin girma na
musulunci, abun mamaki da irin falalolinshi da abubuwa kyawawa a cikinshi da
hukunce hukuncenshi da shari'ansa wanda ya assasa kiwon lafiya na kariya da
kuma yaki da yaduwan cuta da kiyayewa daga gare shi gudanarwa na bada kariya
wadanda wannan hukuma ta wannan kasa ta dauka mamlala al arabiyya assu'udiyya
don hana yaduwan wannan cuta na fairos korona daga ciki akwai dakatar da shiga
kasar saudiyya da manufan umra ko ziyaran masallacin Annabi tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi na sifa na wucin gadi na nuni ga hikima irin na
wannan doka din da aka sauke da kuma daukakan manufansa bayyanan manufofinsa da
girman fa'idansa da kuma abunda zai kai ya komo da abinda zai zama ya amfanar
bisa ga lafiyan jiki da kuma garurruwa
Ku roki Allah samun lafiya domin ba abawa bawa wani abu
ba bayan yakini da yafi sama da samun waraka da
** idan ka ga wanda Allah ya jarabeshi to ka nemi
tsari **ga Allah daga sharrin bala'i mai sauka
Ku yi salati da amunci bisa ga Ahmadu mai shiryarwa
mai ceton talikai gaba daya .
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق