الجمعة، 29 نوفمبر 2019

HUKUNCIN SHAFA A KAN HUFFI A MUSULUNCI


Hudubar Masllacin Annabi na shaikh Muhammad Salah Al-budair 2-4-1441AH/29-11-2019AC

Hudubar farko
Ya ku musulmai!
Ku ji tsoron Allah, duk wanda ya ji tsoron Allah Matsayinsa zai daukaka har ya haura nisan taurari ya taka tsanin da zai kai shi kololuwa.(ku ji tsoron Allah zai ilmantar da ku,kuma Allah Masani ne ga dukkan komai).
 Fikihu guzuri ne na mai bautan Allah, kuma taimako ne ga mai neman shiriya. duk wanda fikihunsa ya karanta to aikinsa zai munana,  jahilcinsa kuma ya halaka shi  , idan hunturu ya zo  mutane sukan yi amfani da  huffi  da safa   da  mayafi  da abin dumama jiki .
Shafa akan huffi guda biyu abu ne da ya halatta ba mai musun haka sai dan bidi'a, mai sabawa jama'ar musulmai da malaman fikihu da hadisi.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya kasance yana shafa akan huffi, ya tabbata shafa akan safa daga wasu sashi na daga sahabbai Allah ya kara yarda a gare su .
 Halaccin shafa  a kan huffi biyu sauki ne  da kuma dadadawa da yalwatawa da  saukakawa   a cikin shari'a   sabo da bukatuwar  sanya shi   sannan kuma   za a hadu da wahala wurin  yawan cire shi.
Wanda ya ke son shafa a kan huffi to ya wajaba ya nemi sanin hukunce- hukuncensa  da  sanin tsawon  mudda (lokaci) da sifarsa da sharudan halaccinsa, da abin da ke warware shi  da hukuncinsa idan ya warware  da wanin haka na daga matsaloli .

YA KU MUSULMAI:
Huffi abu ne da aka sana'anta shi daga fata  ana ambaton shi  da huffi ne sabo da  rashin nauyinsa  ko kuma  kamar yadda  wasu suka ce '' sabo da hukunci ya yi sauki na in an sanya shi a yi shafa a madadin wankewa, ''
Amma ita safa aba ce da ke rufe kafa wanda aka sana'anta ta daga auduga ko gashi ko jawazkar gashi, ko kyalle, wanda aka fi sani a yau da Shurrab.
.
 An shardanta su zama suna da tsarki kuma sun suturce dukkan kafofi biyu da idon sawu, kuma su zama suna da kauri basu bayyana jiki, to idan huffi ya zama mai bayyana jiki, kuma danshin shafan da aka yi yana jika kafa, kuma yana bayyana launin fata, to bai halatta a yi shafa a kansa. idan ya kasance ba shara-shara ba ne kaurinsa bai barin ruwa ya jika kafa to ya halatta a yi shafa a kansa, a daya daga cikin zantuka biyu na malamai.
Kuma an shardanta ya sanya su bayan ya yi cikakken tsarki na ruwa, idan ya yi shafa akansu ba tare da yana da dahara cikakkiya na ruwa ba kafin sa su to alolarsa da sallarsa basu inganta ba.
Idan ya wanke daya daga cikin kafafuwarsa sa'anan ya sanya safa sannan ya wanke daya kafar kuma ya sanya ta cikin huffi ko safa to baya halatta ya shafa akanta a zance mafi inganci cikin maganganu biyu na malamai sabo da hadisin Abu bakrata -Allah ya kara yarda a gare shi-  ya zo cikin shi (Idan yayi tsarki sai ya sanya huffinsa biyu, to ya yi shafa a kansu) to harafin  Fa a hadidisin yana hukunta bin juna take hade da jerantawa : sabo da haka ya wajaba ya kammala tsarkinsa ya kuma kammala alolarsa ya kuma gama wanke kafafuwansa biyu sa'annan sai ya shigar da su cikin huffinsa biyu ko safarsa biyu.
Mazaunin gida na iya shafa akan hufi tsawon wuni da dare, matafiyi kuma zai iya shafa bisa huffi har tsawon kwanaki uku dare da wuninsu.
Muddar shafan na fara wa ne tun daga shafar farko bayan ya yi karamin hadasi a zance mafi inganci cikin maganganu biyu na malamai,
To zai yi ta shafa a kan su tun daga shafan farko bayan hadasi karami har zuwa misalin wannan lokaci na  washegari idan mazaunin gida ne. in kuma matafiyi ne to har zuwa kwatankwacin wannan lokaci na rana ta hudu.
Umar dan khaddabi Allah ya kara yarda a gare shi yace: zai shafa a kan su har zuwa kwatankwacin wannan sa'a  na wuninsa da darensa) Abdurrazak ya fitar da shi.
To idan Muddar ta kare to dahararsa ta warware a gun wasu malaman fikihu, wasu kuma suka ce: a'a, alolarsa bata warware ba ko da kuwa lokacin shafa ya kare ne a halin yana cikin salla to zai karasa sallarsa don karewar mudda baa sanya ta cikin masu warware alola, amma maganar farko ta fi zamewa Ahwad iyakantacciya don fita daga sabani ga sallar. Kiyayewa da yin taka tsantsan shi ya fi dacewa bisa a rasa tabbacin sharadi na inganci.
Idan ya yi hadasi bayan karewar muddar to ba zai yi shafa a kansu ba har sai ya cire su, ya yi cikakken tsarki sannan ya sa su.
Zai iya shafa cikin muddar muddin ba janaba ya yi ba, to idan ya yi janaba ta hanyar jima'i ko mafarki ko waninsu, to ba zai yi shafa akan su ba har sai ya wanke dukkan jikinsa, har da kafafuwarsa biyu, An karbo daga Safwan bin Assal Allah ya kara yarda a gare shi yace: (Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana umartanmu in mun kasance muna halin tafiya da kada mu cire huffinmu har tsawon kwanaki uku da dararrakinsu, sai dai don janaba, ba bahaya ko fitsari ko barci ba.
     Idan yayi shakku bisa muddar shafan to ba zai shafa ba tare da shakku, sabo da rashin tabbacin sharadin halaccin shafar.
  A duk lokacin da ya cire huffinsa biyu ko safanninsa biyu, ko kuma ya cire huffin daya daga cikin kafafuwa biyu to shafarsa ta warware alolarsa kuma ta baci, wanke kafafuwarsa ba zai isar masa ba da ya ci gaba da shafa a kansu, sai dai ya wajaba a gare shi ya sabonta tsarki na ruwa kafin ya halatta a gare shi ya yi shafa a kansu a   zance mafi inganci cikin maganganu biyu na malamai.
Don kiyayewa da iyakancewa ga salla, sabo da kuma mustahabbi ne fita daga sabani.

Ya ku masallata masu tsarki!
Idan har a huffi ko safa akwai huji ko yagewa ko kecewa wanda bigere na farilla ke bayyana to in har ya yi girma sosai to ba ya halatta a yi shafa a kansa sai in ya kasnce kadan ne. idan kecewar daga saman idon sawu ne to haka ba zai cutar da shi ba.
Abin da ya ke wajibi shine shafa a saman huffi ba kasansa ba, ko dunduniyarsa ko kwabrinsa ba,
Sifar shafar ita ce : ya dora jikakkun hannayensa yana mai bude yatsun hannayensa bisa yatsun kafarsa sai ya tafiyar da su tun daga saman  tsintsiyar kafar  har ya isa ga makyangyamarsa, ba sunna ba ne ya shafa kasansa ko dunduniyarsa ko kwabrinsa, a zance mafi inganci sabo da hadisin Aliyu Allah ya kara yarda a gare shi yace:(Da a ce addini ra'ayi ne da shafa kasan huffi shi ya fi dacewa a kan shafa samansa, hakika na ga Manzon Allah yana shafa bisa saman huffinsa) Abu Dawuda ne ya rawaito.
    Wanda ya bar shafar saman huffi to alolarsa bata inganta da ijma'in malamai, kuma ko da ya yi salla to sallar ta baci.
Wani mai waka ya ce : Mai barin shafan sama (huffi)  ka bata ,   zai yi shafa ne gaba daya dama akan dama hagu akan hagu  wasu suka ce :- sunna ne a gabatar  da dama .
       Imamu Ahmad  Allah ya mishi rahama ya ce:-
( Duk yanda ka yi ya halatta  da hanu daya ko hannaye biyu).
Ba mustahabbi ba ne maimaita  shafa  sabo da rashin zuwan hakan , ba a shafa akan huffi mai najasa .
     Ya ku masallata matsarkaka : wanda ya kasance matafiyi ya kuma fara shafan a muddar halin tafiya, ya yi shafa  kasa da  wuni da dare  sa'annan ya dawo garin  shi   zai cika wuni da dare.  idan ya yi shafan a halin tafiya wuni da dare  zuwa sama sa'annan ya dawo garin su zai cire safar sa biyu bisa wajabci, sabo da karewar lokacin shafa  da isowar sa zuwa garinsa, to idan kuma mazaunin gida ya yi shafa sai ya yi tafiya  kafin karewar muddar shafar  to sai ya cika shafa irin na matafiyi.
 ya ku masallata matsarkaka:
 Idan ya yi alola da ruwa cikakken alola sannan ya sanya safa  ba tare da yayi hadasi ba har ya sake dora wani safan daban  akan shi   to ya halatta yayi shafa akan safan saman ,  idan ya yi shafa akan safan saman sa'annan ya cire shi to alwalan sa ya baci .
   Idan ya yi alola cikakken alola da ruwa sannan ya sanya safansa , sannan ya yi hadasi sai kuma ya sanya safa a sama bayan yayi hadasin  to  baya halatta a gare shi ya yi shafa akan na saman,  sabo da ya sanya shi ne a halin bai da  tsarki , wato yana mai hadasi   to idan ya shigar da hanunsa   kasan safan saman   to ya halatta,  idan ya sanya safa a halin yana mai tsarki  na ruwa cikakke  sannan ya yi hadasi   ya kuma shafa akan shi  sa'annan ya sanya wani safan akan shi   to baya halatta yayi shafan akan  na saman  sabo da  ya sanya shi ne a halin yana da tsarki na shafa ba tsarki na ruwa ba.  wanda ya sanya safa a halin yana da tsarki na ruwa cikakke  sannan ya sanya  takalmin sau-ciki  mai tsawo a kan shi  ko but ko kambas, wanda duk sun rufe idon sawu, to zai iya shafa a kan su, idan ya cire  takalmin sau-ciki  mai tsawo  ko but ko kambas, bayan ya yi shafa a kan su to alolarsa ta baci.
 Idan ya sanya takalmi wato sau ciki wanda bai suturce idon sawu ba, to shafa a kanta ba zai isar mishi ba.
Idan a kasan akwai safa da ta rufe idon sawu kuma ya sanya ta da takalmin kafin ya yi hadasi zai shafa bisa takalmin da abin da ya bayyana na safanni biyu, saman gurin da ake wankewa ya kuma yi salla a cikinsu gaba daya, to idan ya cire takalman to alolarsa ta baci, sallarsa kuma bata inganta ba da safa kadai sabo da shafa ya ta'allaka da su.
 Allah ya sanya ni da ku cikin wadanda suke bautawa Allah bisa ilimi da basira.
Ina fadin abin da ku ke ji, ina nema mana gafaran Allah kuma ku nemi gafararsa, madallah da da rabauta irin na masu neman gafara.

Huduba ta biyu
Ya ku musulmai!
Ya wajaba ga mai salla ya rika bibiyar safarsa don tana da saurin yin wari, to a duk lokacin da safa ta yi wari ko doyi  to ya wajaba ya cire ta don kar ta cutar da mai salla ko musulmi da warinta.
Ko mutanen da sukan yi karin magana da warinta inda suka ce (ya fi wari a kan warin safa).sun yi zambo da shi sai dayan su yace :
Ibnu Umair ya yi yakin da ya bar suna  na yabo irin warin safa ketacciya.
Wani kuma ya ce :
Ki yi yabo a gare ni da abin da ki ka sani domin ni * ina yabon ki kamar yadda ake yiwa iskar safa.

Ya ku musulmai !
Muna nasiha da fadi da ya fi iyakancewa ga salla a babin shafa bisa huffi, idan ba wasu nassoshi na yanke ko bayyane, in har ba kunci  ko wahala mai tsanani da ke wajabta sauki wurin amfani da  Ahwad din sannan kuma in wurin amfani da Ahwad din akwai karin bauta da lada.
Hakika malaman fikihu sun nassanta cewa fita daga sabni abu ne mustahabbi.
Hakika Annabi ya yi amfani da Ihtiyadi  kuma ya yi hukunci da shi a waki'i da ya shahara
Na daga ciki akwai abin da Buhari da Muslim suka rawaito daga Anas dan Malik Allah ya kara yarda a gare shi yace:(Annabi ya wuce ga wani dabino ya fado sai yace : (Ba don ina tsoron kar ya zama cikin na sadaka ba da na ci shi).
  . Muna kira ga musulmi da zuciyarsa ta bude ta karbi sabani a irin wadannan mas'aloli, to in ba haka ba sai su zama sababi na sabani da kauracewa juna da fada da kiyayya da yankewa juna,   
. Ya ku musulmai ! ku godewa Allah bisa ni'imarsa mai yawa da falalarSa mai yawan zuba, ku tuna yadda mutane su ke tafiya huntaye ba takalma suna rasa abin jin dumi suna barci bisa duwatsu da safa, sannan kun wayi gari a bayan su kuna rayuwa mai yalwa.da gurin noma mai yawan alheri da 'ya'yan itace nunannu masu ganye, ku godewa Allah bisa yalwan falaloli da ni'imomi, to mai biyayya mai godiya yana ci gaba ne cikin falala da habaka da albarka, kuma mai sabo mai gujewa Allah na tafiya ne zuwa ga walakanci da talauci da halaka.
Ku yi salati da aminci ga Ahmad.


الأحد، 24 نوفمبر 2019

FALALAR SALLAMA DA LADUBARTA A MUSULUNCI


Hudubar Masllacin Annabi na SheikhAbdulmuhsin Bin Muhammad Alkasim  25-3-1441AH 22-11-2019 A
Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna gode masa kuma muna neman taimakonsa
Muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu  da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, wanda ya batar kuma babu mai shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya,kuma na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa. Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa.
Bayan haka, ku ji tsoron Allah -ya ku bayin Allah- cancancin tsoronSa, duk wanda ya ji tsoron Ubangijinsa zai daukaka da darajoji, makomansa zai dadada bayan mutuwa.
Ya ku musulmai :
Allah ya yi wa bayinSa ni'ima da addini mai girma wanda ya tattaro dukkan abubuwa masu kyau, kuma da shi ne halittu zasu gyaru, kuma da shi ne zasu samu sa'idarsu,  ya kuma karramasu da littafi mai haske mai shiriya mai waraka ya zaba wa wannan alumma mafificin manzonSa bai bar wani kofa na alheri ba face ya nusar da mu zuwa gare shi babu kofa na sharri kuma face ya gargade mu game da shi tare da cikan  nasiharsa da fasaharsa da rahamarsa. A addinin musulunci akwai laduba mafi daidaituwa da tsarkakuwa cikin al'amuran duniya da addini musulmi ya samu kamala a addininsa da halayyarsa da kuma ibadarsa da dabiunsa sai ya hada kyautata alaka a tsakaninsa da ubangijinsa    kuma da halittunsa na daga cikin manyan alamomi na wannan addini da kuma ladubansa akwai gaisuwa irin na aminci ta hanyan ambaton sunan Allah Madaukaki Assalamu da kuma neman kubuta da neman salama daga gare shi da kuma neman aminci daga gare shi tare da cikakken alkawari na aminci da cewa wanda ake yiwa sallama sharri ba zai riske shi ba ko wata cuta daga mai yin sallamar sabo da daukakar matsayi na sallama.
Allah ya yi gaisuwa da shi ga wanda matsayinsa ya daukaka a addini, Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :(Jibrilu ya zo ga  Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai yace ya Manzon Allah ga kadija nan tana zuwa maka da kwano cikinsa da abinci ko abin sha to ka isar mata da gaisuwa daga Ubangijinta, kuma ka mata albishir da gida na lu'ulu'u ba hayaniya a ciki ko wahala.) Buhari ne ya rawaito.
Na daga  cikin mafi alherin ni'ima a Aljanna Gaisuwar Allah  da aminci ga 'yan Aljanna, Allah Madaukakin sarki yace : (Aminci da magana daga Ubangiji Mai jinkai). Imamul Bagawi Allah ya mishi rahama yace : (wato Allah zai musu sallama ta hanyar magana)
Hakan kuma na sabunta a duk lokacin da suka hadu da shi, (Gaisuwarsu a yayin da suka hadu da shi ita ce Aminci)
 Jibrilu ya yi gaisuwa ga wacce ta tashi da hakkin Manzon musulunci tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, . Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da A'isha -Allah ya kara yarda a gare ta- Lalle jibrilu na gaisuwa a gare ki na aminci, sai tace, nace  :Amincin Allah ya tabbata a gare shi da rahamar Allah ) Muslim ne ya rawaito.
Idan an bude kofofin Aljanna farkon maganan da 'yan Aljanna zasu ji daga Mala'iku gaisuwa ce ta aminci gare su, (har zuwa lokacin da suka je a gare ta  aka bude kofofinta masu tsaronta su ce da su  : Aminci  ya tabbata a gare ku kun ji dadi ku shige ta kuna madawwama (a cikinta).)
A cikin lafuzan sallama akwai natsuwa da girmamawa da ni'ima,sabo da haka Allah ya umarci Mala'iku da su yi gaisuwa da ita ga 'yan Aljanna, a lokacin da suka shige ta don karin girmama wa a gare su, ta hanyar sauraron lafuza na aminci da taya murna,ta dukkan kofofi na Aljanna Allah Madaukakin sarki ya ce : (kuma mala'iku na shiga a gare su ta kowani kofa Amincin Allah su tabbata a gare ku to madalla da akibar gida.)
Sabo da matsayin sallama  da daukakar kimansa sai Allah ya zabe shi ga Adam da zuriyarsa, a farkon lokacin da Allah ya halicci Adam sai ya ce da shi, je ka yi sallama ga wadancan - tawaga na mala'iku – da ke zaune ka ji da me zasu gaishe ka da shi,to wannan ita ce gaisuwarka da zuriyarka,sai yace :"Amincin Allah ya tabbata a gare ku" sai suka ce Amincin Allah ya tabbata a gare ka da rahama sai suka kara da rahama.) Buhari da muslim ne suka rawaito.
Sai Allah ya kebanci shi a matsayin gaisuwa ne na musulmai a tsakaninsu, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:Ba abin da yahudu suke yi muku hasada game da shi kamar Gaisuwa da cewa Amin)Ibnu Maja ne ya rawaito.
Kuma ya hana su fara gaida wani da ba musulmi ba da shi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:( kada ku fara sallama ga yahudu da nasara) Muslim ne ya rawaito.
Haka kuma idan suka fara ba zaa maida musu da shi ba idan Ahlul kitabi suka muku sallama sai ku ce: kuma  a gare ku) Buhari da muslim ne suka rawaito.
Ba su rabuwa da sallama a cikin Aljanna kuma suna jin dadi da sun ji shi, (Ba su ji wata yasasshiyar magana a cikinta ko wani abu na laifi sai dai fadi na aminci aminci) ita  ce gaisuwa ga 'yan Aljanna a tsakaninsu, Allah Mabuwayi da daukaka ya ce : (suna masu dawwama a cikinta da izinin Ubangijinsu gaisuwarsu cikinta ita ce aminci).
A na samun alheri da albarka a cikin sallama, Allah Madaukakin sarki ya ce : (To ku yi sallama ga junanku gaisuwa daga Allah mai albarka ,tsarkakka.)
Na daga cikin albarkanta ma'abotanta na kusa da Ubangiji Allah, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:(Lalle mafi cancancin mutane kusantar Allah shine wanda ya fara sallama) Abu Dauda ne ya rawaito, Imam Addibi Allahya masa rahama  ya ce : " wato wanda ya fi kusancin rahamar Allah cikin mutane da suka gamu shi ne wanda ya fara sallama".
Matsayin sallama a musulunci na da girma, farkon abin da Annabi ya fara magana da shi da ya shigo garin Madina shine ya yi umarni da a yada sallama, Abdullahi dan salam ya ce :A yayin da Annabi ya zo garin Madina mutane sun yi cacarindo zuwa gare shi, ana cewa Manzon Allah ya iso Manzon Allah ya iso. Sai na shigo cikin mutane don na gan shi, a yayin da na samu ganin fiskar shi sai na tabbatar wannan fiskar ba na makaryaci ba ne,farkon maganar da ya fara da ita ya ce ne : (ya ku mutane ku yada sallama ku ciyar da abinci, ku sada zumunci, ku yi salla a halin mutane suna barci za ku shiga Aljannar Ubangijinku da aminci).Tirmizi ne ya rawaito, Imam Annawawi Allah ya masa rahama yace : A cikin yada sallama akwai haduwar zukantan musulmai sashinsu ga sashi, da kuma bayyana daya daga cikin manyan alamomi da ke rarrabe su da mabiya wasu addinai, wadanda ba su ba.
Annabi ya umarci sahabbansa da al'umarsa da ita (sallama) Albara'u dan Azib Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :( Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya umarce mu da abubuwa guda bakwai daga ciki akwai :" ku yada sallama").
Imam Annawawi Allah ya masa rahama yace: "yada sallama shine a yayata ta a yawaita a isar da ita ga kowani musulmi"
. sallama na daya daga cikin mafi alherin ta'ada na musulunci, kuma mafi darajan rassansa, Wani mutum ya tambayi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi:wani abu ne yafi a musulunci, sai yace : (ka ciyar da abinci, ka yada sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba,) Buhari da muslim ne suka rawaito. Imam Alkhaddabi Allah ya masa rahama yace: "ya sanya mafi alherin magana a da'a da karramawa shine yada sallama, wanda ke gamewa ba ya kebantarwa har ya zame don Allah kadai babu rabon rai da ko karya, domin wani alami ne na musulunci ya zama ruwan dare ne ga kowane musulmi".
sallama na kara imani, Ammar dan yasir Allah ya kara yarda da shi yace; "Abu uku idan mutum ya hada su to ya hada imani; Adalci a kanka, da yada salama ga duniya, da ciyar a halin talauci" Buhari ya rawaito.
Don yin biyayya ga Allah  da kaunar Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da girmama shi ya sa ake yin sallama  a gare shi, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Lalle Allah da mala'ikunsa suna salati ga Annabi, ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce"
Kuma Sallama a gare shi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a tahiyar salla rukuni ne daga cikin rukunnanta
Fara sallama da amsata na daga cikin hakki musulmi a kan musulmi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( hakkin musulmi a kan musulmi shida ne daga ciki idan ya hadu da shi ya yi sallama a gare shi) muslim ne ya rawaito .
A riwayar bukari da muslim (amsa sallama) kamar yanda sallama rayayye na amfana da ita haka nan ma matattu na da rabo a cikinta  annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya  kasance idan ya zo makabarta yana cewa (Aminci ya tabbata a gare ku ma'abota gidaje na daga muminai da musulmai ) muslim ne ya rawaito
Da sallama ne kauna da dunkulewa tsakanin musulmai ke dasuwa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce  (Na rantse da wanda raina ya ke hanunSa  ba za ku shiga Aljanna ba har sai kun yi imani, kuma ba za ku yi imani ba har sai kun so juna, ase ba zan nusar da ku zuwa ga abin da in kun yi shi za ku so junan ku ba ? ku yada sallama a tsakaninku ) muslim ne ya rawaito .(umar dan kaddab Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : abu uku za su tace ma kaunar dan uwanka ka mar sallama idan ka hadu da shi kuma ka yalwata mishi a majlasi kuma ka kira shi da sunan da yafi soyuwa a gare shi ) . 
sallama wata sifa ce ta karamci  Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi  ya ce : (mafi rowan mutane shi ne wanda ya yi rowan sallama  ) Ibnu Hibban ne ya rawaito. kuma shi dalili ne na alheri kuma shi ne mafi alherin magani ga wadanda su ka kaurace wa juna manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce  (ba ya halatta ga musulmi ya kauraci dan uwan shi sama da dare uku za su hadu su biyu amma wan nan ya juya baya wancan  ma ya juya baya mafi alheri a cikinsu shi ne wanda ya fara sallama ) bukari da muslim ne suka rawaito
Da sallama ne ake samun aminci da albarka  manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce(ku yada sallama za ku samu aminci tare da tabbatar da tauhidi da ingan cin imani sallama kan wajabta  aljanna ga ma'botnsa wani mutumi ya ce ga annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bani labari wani abu da zai wajabta min Aljanna sai ya ce ka kyautata zance kuma ka yada sallama ) ibnu hibban ne ya rawaito
Hasali ma sallama ya na kai darajoji na kololuwa a aljanna .
Lallai a cikin aljanna akwai wasu dakuna da ana ganin wajensu daga cikinsu kuma ana ganin cikinsu daga wajensu sai wani balaraben kauye ya tashi ya ce na waye ne su ya manzon Allah sai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( na wanda ya dadada zance kuyma ya yada sallama ya ciyar da abinci kuma ya yi salla da daddare mutane na bacci  )ibnu hibban ne ya rawito . saboda muhimmancin sallama da falalarta da girman fayidodinta aka shar'anta ga ko wani musulmi a ko wani hali duk wanda ya shiga gida zai yi sallama ga mutanen gidan Allah Madaukakin sarki ya ce : (To idan kun shiga gidaje ku yi sallama ga junanku gaisuwa daga Allah mai albarka ,tsarkakka.) kada wani ya shiga gidan waninsa sai bayan ya yi sallama kuma ya nemi izini Allah Madaukakin sarki ya ce : (ya ku wadanda su ka yi imani kada ku shiga gidaje wadanda ba gidajenku ba sai kun sami izini kuma kun yi sallama akan ma'abotansu wan nan ne mafi alheri a gare ku tsammanin ku za ku tuna ) wanda ya konkosa kofan waninsa don neman izini to ya fara da yin sallama sannan magana ta biyota  , wani mutumi ya zo ga annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a halin yana  gida sai ya ce in shigo ? sai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce ga mai mishi hidima (fita zuwa ga wan nan ka koya mishi yanda ake neman izini ka ce da shi: ka ce :assalamu alaikum in shigo ? sai mutumin ya ji shi sai ya ce assalamu alaikun na shigo ?sai annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi mishi izini   ) abu dauda ne ya rawaito kuma an sharanta haka a majlisai yayin shigansu ko fitansu manzon aAllah tsira da amincin Allah su tabbat a gare shi ya ce : (idan dayanku ya zo ga majlisi to ya yi sallama to haka ma idan zai tashi daga majlisin ma to ya yi sallama domin sallamar farkon ba ta fi na karshen ba ) abu dauda ne ya rawaito zai maimaita shi a duk masallatan shi har a masallatayya kamar yanda ya zo a hadisin mai bata  sallarsa .
 Sallama na daga cikin hakki ne na hanya ga wanda ya zauna a kanta manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (na horeku da zama a kan hanyoyi sai suka ce ya manzon Allah ba mu da mwuraren zamam mu muna tadi a cikinta sai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : idan kjun ki , dole sai kun zauna to ku bawa hanya hakkinta sa suka ce : to menene hakkin hanya ya manzon Allah sai ya ce runtsa gani  da kame cutarwa da amsa sallama da umarni da kyakkyawa da hani da mummuna ) buhari da muslim ne suka rawaito
To kaman yanda manya su ke da hakki na gaisuwa to haka yara ma suna da hakki, kuma a kan wannan ne sahabban Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi suka tafi, anas Allah ya kara yarda a gare shi ya wuce wasu yara sai ya yi sallama a garesu sai ya ce: annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance  yana aikata haka ) Buhari da muslim ne suka rawaito  manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana ziyartan lansarawa sai ya yi sallama ga yaransu  ) Bukari da Muslim ne suka rawaito
Sabo da muhimmancin sallama ga al'uma da daidaiku Allah bai sanya masa wani lokaci ba, sai dai kawai a duk lokacin da ya ga musulmi ko da bai san shi ba, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Duk wanda ya  hadu da dan'uwansa ya mishi sallama.)Buhari ne ya rawaito a Adabul Mufrad.
 (Idan dayanku ya hadu da dan'uwansa to ya mishi sallama.idan wata itaciya ta yi shamaki a tsakaninsu ko kango ko dutse sannan ya hadu da shi to ya mishi sallama)Abu Dauda ne ya rawaito.
Na daga cikin sifa na sallama akwai yada ta da yawaita ta  da yin ta ga kowani musulmi ba tare da banbantawa ba da wanda ka sani.
Ya ku Musulmai!
Musuunci Addini ne na alheri da aminci yana kira ga wanke zuciya da yada natsuwa da kwanciyar hankali ga al'uma, kuma yana kwadaitarwa wurin yada hadan kai da kauna tsakanin halittu, kuma yana sanya rahama a gare su da duk wani abu da zai iya tabbatar da hakan na daga sallama waninta, to musulunci na umarni da shi bisa wajabci ko mustahabbanci.
Ina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan abin jefewa.
(Idan an gaishe ku da gaisuwa to ku mayar da wacce ta fi ta ko ku maida irin ta lalle Allah ga dukkan komi mai kididdiga ne.)
Allah ya sa mini Albarka ni da ku cikin Alkur'ani Maigirma.


Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa kyautatawarsa, godiya ta tabbata a gare shi bisa datarwarsa da baiwarsa, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, ina mai girmama sha'aninSa, na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa. Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa.
 Ya ku musulmai! Farawa da sallama sunna ce da aka kwadaitar a kanta maida ta kuma wajibi ne. kari kuma wurin amsawa mustahabbi ne, maida irinta kuma farilla ne, na daga cikin laduban sallama karami ya gaida babba, mahayi ya gaida matafiyi a kafa, na tafe ya gaida na zaune, 'yan kadan su gaida masu yawa.idan na farkon ya bar sunna to na karshen mustahabbi ne ya gagauta aikata ta, an shar'anta maimaita sallama yayin bukata, kamar a taro mai yawa, ko zaton rashin isan sautin, Anas Allah kara yarda a gare shi ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan ya yi sallama ya kan maimaita sau uku.) Bukari ya rawaito.
Mustahabbi ne daga sauti yayin sallama, a farawa ne ko amsawa, don wannan abin da yada sallama ke hukuntawa kenan, Ibnu Umar Allah ya kara yarda a gare shi ya ce ;"idan ka yi sallama to ka jiyar, haka ma idan ka amsa to ka jiyar"
To jiyarwa kuma na kasancewa ne ba tare da cutar da wani ba,kamar mai barci da makamancinsa,hakika na daga cikin koyarwarsa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kan zo da dare ya yi sallama wanda bai tada mai barci kuma ya cjiyar da wanda ya ke fadake) Muslim ya rawaito.
Ba abin da ke hana sallama ko amsa shi sai hudubar juma'a, sabo da wajabcin sauraronta, haka kuma lokacin biyan bukata, don ba lwuri ne na gaisuwa ko zikiri ba, mustahabbi ne maida sallama ga wanda ya turo da wanda ya isar da ita :(Jibrilu yazo gurin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a halin yana tare da khadija, Allah ya kara yarda a gare ta.sai ya ce Allah na sallama ga khadija.sai tace lalle Allah shine Assalamu to amincin Allah ya tabbata ga jibrilu kai ma amincin Allah ya tabbata a gare ka da rahamarsa da albarkarsa )Nasa'I ne ya rawaito.
To ku sani Allah ya umarce ku da salati da aminci ga AnnabinSa.

الجمعة، 15 نوفمبر 2019

Gulma a musulunci


Hudubar Masllacin Annabi na Sheikh Husaini Alusshaikh  18-3-1441AH 15-11-2019 A

Hudubar Farko
Na daga cikin tushen na zaman lafiya da ka'idoji na tsira akwai kiyaye harshe daga sharrace -sharrace da laifuka da shaidan zur da karya da kage Allah Madaukakin Sarki yace :(Ba ya lafazi da wata magana   face tare da shi akwai mai tsaro halartacce)  Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (wanda ya kasance yana imani da Allah da ranan duk lahira to ya fadi alheri ko ya yi shuru) anyi ittafaki bisa ingancinsa.
kuma manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare  shi yace (wa zai lamunce mini harshensa da farjinsa sai na lamunce masa Aljannah) Bukhari ne ya rawaito.
Ma'abota ilimi suka ce: "Ba ya dace wa yayi magana sai idan akwai alheri a maganar, wato ita ce wacce maslahar yinta ta bayyana duk wanda yayi shakku bisa maslaharta to yayi shuru".

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :(lallai bawa zai yi magana da kalma ba zai bayyana mishi (hadarinta) ba, zai zame cikin wuta a dalilinta fiye da nisan mahudan rana da mafadanta) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
A riwayar Buhari kuma :(lallai bawa zai yi magana da kalma na daga fushin Allah Madaukaki wanda ba zai kula da ita ba zai fada a cikin jahannama adalilinta )
Ya ku bayi Allah ku saurara!
Na daga cikin abubuwa mafi girma da suke halakarwa kuma mafi munin laifin akwai (giba) yi da wani shine mutum ya ambaci dan uwansa musulmi abayansa da wani abu dake tare dashi wanda bazai soba ,wan nan abin sawa,u ya kasance game da jikinsa ne ko Addininsa ko duniyarsa ko kuma halinsa ko halittarsa ko dukiyarsa ko dansa ko mahaifinsa,
Duka daya ne wurin haramcin giba  da lafazi ne ko a rubuce ko da wata alama ko wani nuni.
Allah madaukakin sarki yace "kada wasu sashinku suci naman wasu" Hakika Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fassara da fadinSa (ko kun san menene gibah sai suka ce Allah da ManzonSa ne suka fi sani, sai yace shine :Ambaton dan'uwanka da abin da ba zai so ba, sai aka ce to idan ga dan'uwan nawa akwai abin da nake fadi tattare da shi, yace : idan har akwai tare da shi abin da kake fadi to hakika ka ci namansa, to idan babu tare da shi abin da ka ke fadi to ka mar kage) Muslim ne ya rawaito.
To ka ji tsoron Allah ya kai musulmi! Ka sani cewa mutuncin musulmi abin karewa a musulunci, ka kiyaye kada ka yi da wani a bayansa da abin da ba zai so a ambace shi da shi ba na daga abin da zai musguna masa ko aibata shi,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Lallai jinannakinku da dukiyoyinku da mutuncinku haramun ne ga junanku kaman haramcin wannan rana naku a wannan gari naku a wannan watan naku) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
To ya kai wanda ka saki wa harshensa linzami cikin cin mutuncin musulmi ka tuna abin da Annabi ya fada wa Aisha masoyiyarsa diyar masoyinsa Allah ya kara yarda a gare ta tace na ce da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,:(Ya ishe ka ga safiya sifanta na kaza da kaza,) wasu marawaita suka ce tana nufin gajeruwa. Sai Annabi ya ce: Hakika kin fadi wata kalmar da da zaa surka ta da ruwan kogi da ta jirkita ta. Sai tace sai na hakaito mishi wani mutum,sai yace ban so a ce kin kwaikwayi wani ba, kawai da kin ce ina da kaza da kaza)   Tirmizi ne ya rawito  kuma ya ce Hadisi ne Hasan kuma sahihi.
Imam Annawawi yace : Wannan hadisi na cikin hadisai mafi tsawatarwa game da yi da wani ko ma shi ne mafi girmansu, kai ni ban san wani hadisi da ya kai kololuwa na aibata gulma ba kamar wannan hadisi!
Ya 'yan Uwa musulmi! Lalle giba na kai mutum ga halaka, an yi alkawarin ukuba mai girma ga mai yinta da sakayya mai radadi Allah Madaukakin Sarki ya ce : (Da wadanda ke cutar da muminai maza da muminai mata ba tare da wani abu da suka aikata ba to hakika sun riki kage da laifi bayyananne.).
 Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (A yayi da aka Mi'iraji da ni zuwa sama na hadu da wasu mutane suna da faratu na karfe suna yagunan fiskokinsu da kirazansu, sai nace su wanene wadannan ya Jibrilu  sai yace : wadannan su ke cin naman mutane suna taba mutuncinsu"Abu Dawuda ya rawaito, ibnu Hajar da waninsa suka ce hadisi ne Hasan, Ibnu Muflih ya ce : Isnadinsa ingantacce ne.
Ya ku musulmai!
Ya haramta ga musulmi da ya bada dama a yi gulman wani a gaban shi ko ya saurari hakan ko ya karanta, sai dai ma ya zama wajibi a gare shi ya yi hani ga mai gulman, kamar yadda ka'idoji na sharia ya gandaya.
Allah Madaukakin Sarki ya ce : (kuma idan kaga wadanda suke kutsawa a cikin ayoyinMU  to ka bijire daga gare su har sai sun kutsa a cikin wani labari da ba shi ba, kuma lallai imma shaidan ya mantar da kai to kada ka zauna a bayan tunawa tare da mutane azzalumai).
 Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Duk wanda ya kare mutuncin dan'uwansa musulmi to Allah ma zai kare fiskarsa daga wuta ranar Alkiyama) Tirmizi ne ya rawito ya ce hadisi ne hasan Ibnu Hajar shi ma ya ce Hadisi ne Hasan.

Ya 'yan Uwa Musulmai!
Giba na halatta ne kawai da manufa ingantacciya ta sharia, wanda ba zaa iya kaiwa gare ta ba sai ta hanyar hakan, misali mutumin da aka zalunta yana neman a masa adalci a karba masa hakkinsa daga wanda ya zalunce shi. Haka ma a halin yin nasiha ga wanda ya nemi shawara game da tarayya da wani da muamala da shi ko aurar mishi.

Huduba ta biyu
Ka gaggauta tuba zuwa ga Allah daga dukkan wani laifi da kusakurai ya dan'uwa na musulmi, ka sani lalle tuba daga yi da mutum na bukatar ka nemi yafiyarsa idan yana da masaniya, to amma idan ya kasance bai sani ba ko kuma neman yafiyar zai janyo wata fitina da barna daga wanda aka ci namarsa, to sai a nema masa gafara a yi masa adu'a, kuma ka ambaci alherinsa da kyawawan halayensa da ka sani a wuraren da ka kasance ka ci namarsa, wannan shine zancen mafi yawan malamai, kuma wannan zancen shine zabin  shaihun malamin musulunci Ibnu Taimiyya da almajirinsa babban malami Ibnul kayyim Allah ya jikansu da rahama.
Duk wanda Allah ya san gaskiyar niyyarsa da ikhlasinsa cikin tuban to Allah zai saukake masa sabubanta sabo da falala irin nashi(Allah) da karamci da kyautatawa.  

الأحد، 10 نوفمبر 2019

khususiyya da Hurumi a musulunci


Hudubar Masllacin Annabi na shaikh Abdulbari Bin Awad Assubaiti 11/3/1441Ah 8/11/2019Ac
Hudubar Farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah… bayan haka.
(Sharri Ya kai sharri ga mutum ya rena dan'uwansa  musulmi, Haramun ne jinin musulmi ga dan'uwan shi musulmi, da dukiyarsa da mutuncinsa)
 
Musulmi wani rayayye ne da ke da karama da kima, wani halitta ne da sharia ta kare matsayinsa,ta mutunta abubuwansa kebabbu da suka shafe shi shi kadai  to ka kiyaye masa abubuwa da su ka shafe shi shi kadai, da basu kariya daga cutarwar duk wani mai dakon sharri ko yaranta da neman laifukan wani, Allah Madaukakin sarki ya ce :( ya ku wadanda suka bada gaskiya kada ku tambayi abubuwan da in an bayyana muku su ranku zai baci)
Abin nufi  tambayar da bata shafe ka ba na daga yanayi da hali na mutane, ta yadda hakan na iya kaiwa ga tona asirin su. Da tsinkayar sirrin su ko munanan halin su.
Nassoshi na shari'a sun karfafa game da toshe kofofin da zasu kai ga bankado asirin mutum musulmi, Allah  Madaukakin sarki ya ce :( kada ku leko asiri) kar ku bayyana abin da Allah ya suturce ta hanyar bincikowa game da laifukan mutane da bibiyan al'aurarsu da musu tonon silili.
To dukkan musulmi yana da alhurma a kansa da gidarsa da sum'arsa da dukiyarsa da maslahohinsa,wannan kyakkyawar dabia da ladabi kan daga darajar musulmi ya nesatar da shi daga kaskantattun halaye,na bibiyan sirrin mutane don kowa ya rayu cikin aminci da kwanciyar hankali a kansa da gidansa da sirrinsa da al'auransa. Abin da yake na bayyane shi zamu yi la'akari da shi,ba ya halatta mu binciko abin da yake na badini, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Ni ba a umarce ni da na tono abin da ke zukatan mutane ba,ko na zakulo abin da ke cikinsu ba).
Tajassus shine mutum ya rika bibiyar dan'uwansa musulmi don ya gano sirrinsa, ko da kuwa ta kowani irin fiska ne na leken asiri, to a cikin haka akwai cutarwa da hadari mai girma ga daidaiku da al'uma, sau da dama ya haifar da bala'i ya raba zumunci ya dasa gaba da kiyayya a tskani.ya rusa gida ya raba tsakanin dangi Allah  Madaukakin sarki ya ce :(Da wadanda ke cutar da muminai maza da muminai mata ba tare da wani abu da suka aikata ba to hakika sun riki kage da laifi bayyananne.).
A yayin da ka yi lura da fadin Allah Madaukakin sarki   (kada ku yi tajassus)  zai bayyana maka gamewa da ya tabo kowane bangare na rayuwa, zaka ga yana magana da uba uwa yana musu gargadi da kada su fada tarkon Tajassus da aukawa cikin keta hurumin wanda suke bawa tarbiya ba tare da izininsu ba da ketare iyaka ba da masaniyarsu ba, shi aikin tarbiya da gina al'uma da bada amana da sauke nauyi ba ya hukunta leken abin da ya halatta ka leka, da kete alfarma da shiga zarafin wani da kutawa cikin khususiyyar wani, Manzon Allah ya hana mutum ya kwankwasawa iyalansa cikin dare, (yana neman sanin ha'incinsu ko neman laifinsu,)  kuma ya ce: (Lalle idan ka bibiyi al'auran mutane zaka lalata su ko kuma kana kusa da ka bata su)
Leken asirin juna tsakanin ma'aurata a gidansu na aure ba tare da samuwar wani abu na hakika  da zai sa a yi hakan ba, ta hanyar binciken wasiku, maganganu, da sakonni, a waya dabia ce da ke rusa aminta da ke akwai a tskani, ya tafiyar da walwala ya gurbata alaka ya jefa shakku da juna.
Domin bada kariya ga khususiyya  a rayuwa ta iyali musulunci ya dasa kyakkyawan dabia na neman izini a zukatan yara maza da mata.    
Na daga cikin abu tabbatacce karfafaffe fadin Allah  Madaukakin sarki  :( kada ku leko asiri) ya hada har da masu shiga kafafen sada zumunta,da su kame daga keta hurumin musulmi da shige masa gona da iri cikin shaninnsa.sabo da abin da wannan dabi'a ta kumsa na matsanancin cutarwa da mummunar illa.wanda da shi ko ta hanyarsa ake jefa firgici da taaddanci da barna.
Kamar yadda mummunar zato ga dan'uwansa musulmi kan jefa shi cikin duhun leken asiri(Tajassus), mummunan zato bai gushe wa da ma'abocin shi har ya sa shi ya fadi abin da bai bayyana ba kuma ya aikata abin da bai dace ba. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Na hore ku da mummunar zato domin zato shine mafi karyar zance, kuma kada ku yi Tajassus.)
Mutun kan fada ga tajassusi da gabbansa ya keta alfarmar musulmi dalilin rashin abin yi da zurfafawa da tambaya game da rayuwan mutane daki daki sai ya rika bibiyan abinda baida ilimi game da shi kokoma ya yi sauraro zuwa ga wani abu ko ya yi dubi zuwa ga alauran da baida hakkin ya yi kallo zuwa gareta Allah madaukin sarki ya ce: (kada ka bibiyi abin da baka da ilimi game da shi lalle ne ji da gani da zuciya dukkan wadannan Allah zai tambayi mai su me ya aikata da su)
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce (na daga cikin kyautatuwan musuluncin mutum barinsa abin da bai shafe shi ba  )
Masifar tajassus na yaduwa cikin mutanen da fahimtarsu ta gajarta, ginshikan addininsu ya bace sakamakon maida hankali kan jita jita da yada shi ta hanyar tonon silili, Abin da ya ke wajibi a kan musulmi shine ya lazimci zaman lafiya ta hanyar  nesatan  Tajassus (neman laifin mutane) ya shagaltu da gyara laifukansa,domin kuwa lalle wanda ya shagaltu da laifukansa daga laifukan waninsa to ya hutar da gangan jikinsa kuma bai gajiyar da zuciyarsa ba, to amma wanda ya shagaltu da laifukan mutane ya manta da laifukansa sai zuciyarsa ta makance jikinsa kuma ya wahalta, kuma ya kasa barin laifinsa.
Imanin Musulmi na kare shi daga wannan cuta,ta hanyar tafiya bisa manhajin Annabi da ya tsara mana, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,a fadinSa (Allah ya karhanta muku abubuwa uku, jita –jita, da sarayar da dukiya, da yawan tambaya)
  Ya tawagar wadanda suka yi imani da halshensu,imani bai kai ga zuciya ba,kada ku ci naman musulmi kada ku bibiyi al'auransu, to duk wanda ya bibiyi al'auran nusulmi, Allah ma zai bibiyi al'auransa, duk wanda Allah ya bibiyi al'auransa to zai kunyata shi ko acikin abin hawarsa ne).
Magani mafi dacewa ga cutar Tajassusi da bin al'aurar mutane da kai komo wajen bankado kuskuren mutane,: shine musulmai su tashi da abin da yake na wajibinsu wurin gyara laifin 'yan 'uwansu da suturce al'auransu da nasiha, idan musulmi ya bar tajassusi a dabiunsa ya yi nesa da shi daga bibiyan sirrin dan'uwansa ya dauke kai zuwa suturce musu, sai Allah ya saka masa da kyautatawa mafi girma ,   Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :Duk wanda ya suturce musulmi Allah zai suturta shi a duniya da lahira). Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(wanda ya yafe wani kuskureAllah zai yafe masa kuskurensa ranar alkiyama)

 Huduba ta biyu
Ya wajaba ga musulmi ya sani cewa Alhurma da Allah ya kiyaye mishi ya bashi kariya tana hukunta kada ya keta alhurman Allah,a halin kadaitarsa, domin Allah ya san sirrinsa da ganawarsa, ba abin da ke boyuwa a gare shi,ya san sirri da aka boye wanda zuciya ta boye shi, An karbo daga sauban daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (na san wasu mutane cikin Al'umata zasu zo ranar Alkiyama da lada masu yawa kamar dutsen tihama fari fat sai Allah Mabuwayi da daukaka ya maishe shi kura tarwatsatsse, sauban ya ce : ya Manzon Allah! Sifanta mana su bayyana mana su don kada mu kasance cikinsu a halin bamu sani ba! Sai yace:Ai su din 'yan uwanku ne daga irin fatanku kuma suna tsayuwan dare kamar yadda kuke yi, sai dai su mutane ne da idan sun kadaita da abin da Allah ya haramta sai su keta ta).

الأحد، 3 نوفمبر 2019

FALALAN ZIKIRI A MUSULUNCI


Hudubar Masallacin Annabi na sheikh Aliyu Bin Abdurrahman Alhuzaifi 4-3-1441AH
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai mulki Tsarkakakke Mai aminci, Ma'abocin daukaka da karramawa, Ubangijinmu sunayenSa sun tsarkaka,sifofinSa sun daukaka,shi yana nan ne kamar yadda ya yabi kanSa, ba zamu iya kididdige yabo a gare shi ba, yabo ya tabbata a gare shi duniya da lahira a koyaushe,Ina kyautata yabo ga Ubangiji na kuma ina gode mishi,bisa ga abin da ya bada na baiwa da falaloli da alheri daban daban wadanda muka san su da wadanda ba mu san su ba,shine majibincin ni'imtarwa, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah.ba shi da abokin tarayya Ma'abocin buwaya da babu zalunci. Na shaida Annabinmu kuma shugabanmu Muhammad bawansa ne kuma manzonSa ne, wanda aka turo shi da haske bayyananne,wanda da shi ne Allah ya gusar da shirka da duhu, ya Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka bisa ga bawanka kuma ManzonKa Muhammad da iyalansa da sahabbansa masu karamci.
Bayan haka ku ji tsoron Allah ya ku bayin Allah ta hanyar kusantar shi da nagartattun ayyuka,da ki da nesatan munanan ayyuka, duk wanda ya ji tsoron Allah to Allah zai jibince shi,wanda ya bi son ransa ya fifita duniyarsa to ya yi kan shi hasara ya sarayar da ni'ima dawwamammiya a lahirarsa,Allah Madaukakin sarki ya ce :(To duk wanda ya yi dagawa ya fifita rayuwar duniya,to lalle (wutar) Jahima ita ce makoma,To amma wanda ya ji tsoron matsayin Ubangijinsa ya hana rayi ga sha'awe sha'awenta to Aljanna ita ce makoma.)
Ya ku musulmai ! Allah Tabaraka wa taala ya kiraye ku da suna na imani sifa mafi daraja ga mutum, da cewa ku yi tawassuli gare shi da ayyuka nagari ku kiyaye su daga abin da zai bata su sai Allah yace : :(ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah ku nemi kusanci zuwa gare shi ku yi jahadi a tafarkinSa ko zaku samu rabauta.)
Wasila :kusanci ya hada dukkan da'a: wato bin umarni da barin hani, wasila ta tattaro gabadayan hanyoyin da'a, da dukkan kofofin alheri  da abinda ke tsiratarwa daga ukuba.
 Kuma    abinda yafi  game dukkan hanyoyin ayuka na gari , da kuma yin katanga daga abubuwa masu halakarwa    shi ne ; ambaton Allah Tabaraka wa ta'ala , kuma shi ke kammala farillu da wajibabbu    ya kuma kankare tawaya  da aka samu a ibadodi,  ladan kewawan ayuka na girmama  tare da shi    kuma  ya goge munanan ayuka    ,   ladan shi ya kai lada  da  falalar sa da girman matsayin sa  wurin daraja da daukaka da haske da alheri   wanda ya kai har Allah ya farlan ta shi a salla  da hajji da kuma sauran ayuka na da'a  ,  kuma shari'a ta kwadaitar  bisa ga dukkan yanayi  ko hali , kuma  rukunin  addini na farko shi ne ambaton Allah madaukakin sarki  ,  da fadin na shaida ba abiun bautawa da gaskiya sai Allah madaukakin sarki , kuma na shaida Annabi Muhammadu Manzon Allah ne,  kuma dukkan  shari'o'i  na musulunci    ta zo da wannan zikiri  da kuma  rarrabewa game da wannan shahada , to shaidawa ba abin bautawa da gaskiya sai Allah  tauhidi ne ga abin bauta  tsarki ya tabbata a gare shi  kuma .

        (Ya ku wadan da suka yi imani , kada ku gabata (da kome) gaba ga Allah da Manzon sa kuma ku yi da'a ga Allah da takawa  lalle  Allah mai ji ne masani ) .
Allah bai yi umarni ba da a yawaita wani abu kamar yanda ya yi umarni da a yawaita zikiri  (Ya ku wadanda su ka yi imani ku ambaci Allah ambato mai yawa  kuma ku yi tasbihi a gare shi safiya da maraice ).
Face abinda ya zo na daga  sallama  , yawaita  salati da aminci ga shugaban halittu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ,    misali fadin sa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi (Ku yawaita yi min salati a ranar juma'a, domin ana bijiromin da salatinku a gare ne)Hadisingantacce Ahmad ne ya rawo da Abu daud  da ibnu ha ya rawaito Allah y7a kara yarda da shi, da kuma fadinSa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, duk wanda ya yi salati gud to Allah zai yi mishi salati goma kuma ya yafe masa kusakure goma, kuma a daga shi da darajoji goma) Hadisi ne ingantacce da Nas'I ne ya rawaito da ibnu Ha daga hadisin Annas dan Maiki).
Wamma salati da aminci sakayya ne gaAnnabinmu daga musulmi sakayya ga musulmi ga Annabi) kuma adu'a ne a gare shi bisa ga abin da ya tabbatar na addini, kuma ya yi jahadi mafi kamala, da abin da ya bada na ya daga   alheri mai yalwa  da nasiha na gaskiya  to dukkan alheri ga musulmi Allah ya gudanar da shi  ne, haka ma dukkan lada Allah ya gusdanar da shi ne ta hanu Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi , kuma  aljanna tafarkin sa ne .  Yin salati agare shi ibada  ne   ga Allah mabuwayi da daukaka na daga cikin abin da ya zo a falalar zikiri (ku ambaci Allah ambato mai yawa ko zaku rabauta).  Da fadin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,: misalin wanda ya ke ambaton Ubangijinsa da wanda bai ambaton sa, misalin matacce ne da rayayye,) Bukhari da Muslim ne suka rawaito. Daga hadisin Abu musa Allah ya kara yarda a gare shi

(Manzon Allah tsira da  amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce ase ba zan baku labarin mafi alheri da tsarkaka  na daga ayukan alherin ku , a wurin mamallakin ku  kuma ya fi daga darajojin ku  kuma ya fi alheri a gare ku daga ciyar da azurfa da zinari  kuma ya fi alheri a gare ku da ku hadu da makiya  a wurin mamallakin ku ,  ku sare wuyan shi   kuma ya sare wuyan ku  sai suka ce e , ya Manzon Allah   sai ya ce ambaton Allah ).
Hadisi ne ingantacce Ahmad  ne  ya rawaito shi  da Tirmizi  da Hakim  daga Hadisin Abi Darda Allah ya kara yarda a gare shi

(An karbo daga Abu sa'id Al-khudri Allah ya kara yarda a gare shi ya ce an tambayi  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wace ibada ce tafi daraja  a wurin Allah ranar alkiyama   sai ya ce ;-  masu ambaton Allah dayawa Tirmizi ne ya rawaito )

 An karbo daga Abdullahi Dan Busur Allah ya kara yarda a gare shi  ya ce :- Wani mutum ya zo wurin  Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce :- Lallae shari'o'i  na musulunci sun yawaita a gare ni  to a bamu kofa da zamu yi riko da shi gamamme  sai ya ce kada harshen ka  ya gushe yana danye daga ambaton Allah   mabuwayi da daukaka Ahmad ne ya rawaito da Tirmizi da Ibn Majah da Ibn Hibban ).



 Shi zikiri yana  tsarkake ayyuka kuma ya cika tawayanta da shi ne  ma 'abocin shi ke  riskan abin da ya sere, yana goge zunubai, Ambaton Allah mai tsarki da daukaka na da matakai guda uku: 1.Matakin farko Anbaton Allah daga wanda ya so.kuma saki, kuma zai bashi  lada Allah da karamcinsa da da kyautar sa.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,ya ce Allah madaukaki ya ce: (Ni ina inda bawa na ya zace, ni ina tare da shi,in ya ambace ni idan ya ambace ni a ransa sai na ambace shi a rai na.)Buhari da muslim ne suka rawaito daga hadisin Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi.
2 mataki na biyu shine mataki na tsakiya shine musulmi ya ambaci Ubangijinsa da harshensa, a wani lokaci ya gafala daga halarto da ma'anan na abinda yake anbatawa a zuciyarsa, to shi ma yana cikin alheri mai girma ladan wannan matsayi ba wanda zi kididdige shi sai Allah, shine ya fi lada akan mataki na farko sabo da karn furuci da harshe
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,ya ce: (Lalle mutum ya kan yi furuci da wata kalma ta yardar Allah ba tare da ya kula da ita ba amma Allah zai daga darajan shi da ita) Buhari ne ya rawaito daga hadisin Abu Huraira.
3. Mataki na uku na zikiri shi ne Harshe ya yi ambato na zikiri kuma zuciya na tare da shi wurin fahimta ta sakon zikirin tare da halarto da girman Allah Mabuwayi da Daukaka lokacin zikirin,wannan matakin na zikiri shi ya fi kowanne a matakan zikiri,ma,abocin shi shine na gaba gaba wurin alheri, mafi daukaka na darajoji.   Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,ya ce: (Bawa ba zai mutu ba a halin ya shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ni Manzon Allahyana mai gaskiya har zuciyarsa face ya shiga Aljanna.) Ahmad ne ya rawaito daga hadisin Rafa'at Aljuhani Allah ya kara yarda a gare shi. A wannan hadisi an samu daidaiton harshe tare da zuciya wurin anbato.
An karbo daga Abu Huraira cewa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da shi: (Duk wanda ka hadu da shi bayan wannan kango yana mai shaida wa ba abin bautawa da gaskiya sai Allah zuciyar sa na sakankancewa da shi to ka mar albishir da Aljanna. Muslim ne ya rawaito. Ma'ana anbaton Allah tsarki ya tabbata a gare shi, shi ne kyautata yabo ga Allah Mabuwayi da daukaka da Tahlili(cewa la'ilaha illallah) da Kabbartawa cewa Allahu Akbar, da godiya da tasbihi da lahaula wala kuwwata illa billah Ma'abocin girma da daukaka da yawaita istigfar da yawaita adu'a, da salati da aminci bisa ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi na daga cikin zikiri, da tsarkake Ubangijinmu Madaukaki daga dukkan tawaya da tsarkake shi daga dukkan abin bai dace ba da matsayinSa da kimarSa da buwayarSa da girmame girmamenSa da cikar kamalarsa da kyaunSa, da kore kamanta shi da daya daga cikin halittunSa Madaukaki da tsarkakakke. Mafi girman yabo shi ne tabbatar da godiya ga Ubangijin talikai shine a yabe shi da sunayenSa  kyawawa da sifofinSa Madaukaka, da ayyukanSa masu hikima,kamar yadda ya ke a Ayatul kursi da karshen suratul Hashri, da girmama Ubangijinmu. Ta hanyar anbaton Ubangijinmu shima ta haryar anbaton ni'imominSa ga halittu. Allah Madaukakin Sarki ya ce : (ya ku mutane ku tuna ni'imar Allah a kan ku, shin kuna da wani Mahalicci koma bayan Allah da zai azurta kudaga sama da kasa).
Allah mai tsarki da daukaka yace  (ku tuna ni'imar Allah a kan ku a yayin da kun kasance makiya sai ya hada zukatarku sai kuka zma 'yan uwan juna da ni'imar Allah bayan kun kasance kuna gaban rami na wuta sai ya tseratar da ku daga gare ta). Da sauran ayoyi da
Zikiri abu ne mai sauki a harshe mai nauyi a mizani ba a samun fa'idodi da shi kuma zukata basu tsarkaka da shi ayyuka su gyaru da rayuwa face akwai kaunar Allah da kaunar ManzonSa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,
Mafi falalan zikiri shine Karatun Alkur'ani, don shine ya kunshi dukkan yabo ga Ubangijin talikai, ya kuma ambaci ni'ima da da bayanin sharia daki-daki ya kwadaitar bisa dukkan alheri.ya yi gargadi bisa dukkan sharri.
Ya ku musulmai wannan shi ne ambato cikin alherinSa da albarkansa da amfaninsa da haskensa.
Amma game da ladansa yana da abin da ido bai gani ba zuciyar mutum bata taba hararo wa ba,na daga cikin ladan zikiri akwai abin da ya zo daga Abu Huraira  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,ya ce: (Duk wanda ya ce :"Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya mulki da yabo na shi ne yana da iko ga dukkan komai" a farkon wuninsa, zai kasance a gare shi daidai da 'yanta wuyaye goma kuma zaa rubuta mishi lada dari a goge mishi alhaki dari, zai zame kariya ne a gare shi daga shaidan a wannan wunin nasa, har ya yi yammaci kuma ba wanda zi zo da irin wannan abin da ya zo da shi face mutumin da ya yi  aiki sama da wannan.) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
An karbo daga Umma Hani Allah ya kara yarda a gare ta ta ce , na ce ya Manzon Allah: Umarce ni da wani aiki da zan yi ina zaune sai yace : ki tasbihi ga Allah sau dari domin yana daidai da 'yanta wuyaye dari ga 'ya'yan isma'il, ka gode wa Allah guda dari domin yana daidai da dawakai dari da sirjinsu da linzamin su suna dauke da kaya a tafarkin Allah, ki yi kabbarori dari domin yana daidai da rakumi dari da aka sa musu alama a wuyansu karbabbu,ki yi halala dari zai cika tsakanin sama da kasa,) Hadisi ne hasan, Ahmad ne ya rawaito da Nasa'I da Hakim.
An karbo daga Nu'uman dan Bashir Allah ya kara yarda a gare shi yace Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : Na daga cikin abin da ku ke ambatawa na girman Allah Akwai: subhanallahi walhamdu lillahi wa la'ilaha illalahu ana furta su a saman al'arshi da sauti kamar kukan zuma, ana anbata su da masu yin su, hadisi ne ingantacce ibnu maja ne ya rawaito da Hakim.
Daga Mu'azu Allah yarda da shi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :"yan aljanna basu da na sani face ga sa'a da ta wuce su basu ambaci Allah ba a cikinta,) Hadisi ne sahihi Dabarani ne ya rawaito. Da na sani da suke yi sakamakon abin da suka gani ne na girman lada na zikiri, Na daga cikin lada na zikiri yana kiyaye ma'abocin shi daga shaidanu,
An karbo daga Haris dan Haris Al'as'ari Allah ya kara yarda a gare shi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yace :Allah ya umarci yahya dan zakariyya da ya umarci banu Isra'ila da wasu kalmomi biyar daga ciki akwai ambaton Allah, domin misalin haka kamar misalin mutum ne, makiyi ya fito a bayan shi yana yakan shi har yazo wani katang da zai kare shi sai tare kansa daga gare shi, haka nan ne bawa ba ya iya kare kansa daga shaidan sai da mbaton Allah) Hadisi ne ingantacce.Tairmizi ne ya rawaito da Ibnu hibbanda Hakim.
Mafi girman lada na zikiri shine rabauta da Aljanna da tsira daga wuta kuma yardar Allah ya fi girma. Na daga cikin falalan zikiri Allah zai kare ma'abocin shi daga damuwoyi da tsanani da abubuwa masu halakarwa, Allah Madaukakin sarki ya ce: (kuma ba don ya kasance  cikin masu tasbihi ba da ya zauna a cikinsa har zuwa ranar da zaa tada su,)
  Na daga cikin ladansa Allah tsarki ya tabbata a gare shi zai daga anbaton ma'abocinzikiri a duniya da lahira Allah Madaukakin sarki ya ce: (ku ambace ni zan anbace ku ku gode min kada ku kafurce min)
Na daga cikin ladansa ya na kara karfin ruhi da gangan jiki, yana taimakawa wurin ibada yana kangewa daga abin da aka haramta, kuma yana saukake arziki da shi, An karbo dagaAbdullahi danAmrAllah ya kara yarda a gare shi  ya ce nuhu ya ce ga dan sa kuma ina ma wasiya da cewa tsarki ya tabbata ga Allah domin ita ce salati halittu da tasbihinsu da ita ake azurta halittu)Hadisi ne ingantacce nasa'I ne ya rawaito da Hakim  
Na daga cikin ladan zikiri akwai barranta daga munafunci, kuma shine musiba mafi girma a addini, manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Manzon Allah ya kasance yana zaben kalmomi dunkulallu a wurin adu'o'i da zikiri, na daga cikin dunkulallun aduo'i akwai abin da Annabi ya koyar da Juwaira diyar Haris Allah ya kara yarda a gare ta, Tsarki ya tabbata ga Allah da godiyarsa adadin halittunSa da yardar kansa da nauyin Al'arshinSa da tawadan kalmominSa,tsarki ya tabbata a gare shi daidai adadin halittunSa,tsarki ya tabbata a gare shi gwargwadon yardarsa tsarki ya tabbata ga Allah daidai nauyin Al'arshinSa. Tsarki ya tabbata ga Allah kwatankwacin tawadan kalmominSa. Muslim ne ya rawaito.
An karbo daga Abu Umama Allah ya kara yarda a gare shi yace: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :(Ashe ba zan koyar da kai fiye da zikirinka da ka ke yi dare zuwa wuni  da wuni zuwa dare ba, Tsarki ya tabbata ga Allah iya adadin abin da ya halitta, tsarki ya tabbata a gare shi cikin abin da ya halita, tsarki ya tabbata adadin dukkan komi, tsarki ya tabbata a gare shi cikin dukkan komai  tsarki ya tabbata a gare shi  adadin abin da littafin sa  ya kididdige , tsarki ya tabbata gare shi cikin abin da littafin shi  ya kididdige  godiya ya tabbata ga Allah adadin abinda ya halitta , godiya ya tabbata ga Allah cikin abin da ya halitta godiya ya tabbata ga Allah adadin dukkan komai ,  godiya ya tabbata ga Allah cikin dukkan komai , godiya ya tabbata ga Allah  adadin abin da ya  iyakance , godiya ya tabbat ga Allah cikin abinda  littafin sa ya kididdige  Hadisi ne Hassan    Bazzar ne ya rawaito shi da Dabarani .

Allah madaukakin sarki ya ce :- (Da masu ambaton Allah da yawa maza da masu ambaton Allah da yawa mata Allah ya tanada musu gafara da kuma  lada mai girma)  .
Allah ya sanya mini albarka ni da ku cikin Alkur'ani mai girma  .
HUADUBA NA BIYU:
 Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga  Allah  Ubangijin talikai majibincin salihai  a mishi biyayya ya gode  asaba mi shi ya gafarta  ina godewa Ubangijina  bisa ga ni'imomi  wanda wanin sa ba zai iya kididdige su ba  wanda muka san su da wanda ba mu san su ba  na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah    shi kadai yake ba shi d aabokin tarayya mai yawan azurtawa ma 'aboci karfi  kuma na shaida Annabin mu kum shugaban mu Annabi muhammad bawan sa ne kuma Manzon sa ne,  amintacce Ya Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka ga  bawan ka   kuma Manzon ka Muhammad da iyalan shi da sahabban shi har zuwa ranar sakayya .

 BAYAN HAKA:
Ku  ji tsaoron Allah  da aikata ayyuka na gari da  uyin nesa daga abubuwan da aka haramta .

 YA KU BAYIN ALLAH:-

Ku yi gudu zuwa ga Allah daga gafala  da juya baya  da rudi irin na dogon buri  domin ku dinnan kuna da lokaci da aka yanka mu ku ,  wanda ke kusanto da duk wani abu na nesa yake kodar da duk wani sabon abu ,  hakika Allah ya umarce ku da koyi da Manzo  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a fadin sa madaukaki :- (Hakika kuna da abin koyi mai kyau ga Manzon Allah ga duk wanda  ke fatan Allah da ranar lahira  ya kuma ambaci Allah da yawa  ).

An karbo daga Aisha Allah ya  kara mata yarda ta ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana ambaton Allah a duk  halin  da  ya ke . Muslim ne ya rawaito)
Zaid  Dan Aslam ya ce '' Musa alaihissalam ya ce:- '' Ya Ubangiji ka mini ni'ima mai yawa  to ka nusar da ni zuwa ga abin da zan gode maka mai yawa  sai ya ce ka ambace ni da yawa  ,  to,  idan ka ambace ni da yawa to hakika ka gode mi ni ,  idan kuma ka manta ni to,  hakika ka butulce mi ni  Baihaki ne ya rawaito a cikin Ashhu'ab .


   Magabata na kwarai Allah ya yarda da su sun kasance  suna dimantan ambaton Allah tabaraka wata'ala sabo da cikar kaunar su ga shi  .
(Abu Huraira ya kasance yana da wani zare a cikin shi akwai kulli dubu  ba ya bacci har sai ya yi tasbihi da shi , Abu Nu'aim ne ya rawaito a cikin Alhilya   )     .

Galibin maganan Ibn Sirin shi ne subhanallahil azim (tsarki ya tabbata ga Allah mai girma ), Khalid Dan Ma'adan ya kasance yana tasbihi ko wani rana dubu araba'in na tasbihi banda abin da ya ke karantawa na Alkur'ani   Abu Nu'aim ne ya fito da shi a cikin Alhilya .

Musulmi a wannan zamanin  ya fi tsananin bukatan  zuwa ga zikiri  sakamakon abin da ya yawaita na fitintinu   da kuma abin da ya ke zo ma zukata na gafala ,   da kuma  abin da ya sami  basira na  daga  sha'awe-sha'awe  da shubuhohi da bin soye-soyen rayuka   da kuma abin da ya yawaita  na rudi  da kawar duniya da adon ta,   ya dace  musulmi ya rika daga littatafan azkar abin da zai bude mishi ido   kuma ya  nemi fahimtar sa ya yi aiki da shi ,  na daga cikin mafi amfanin littatafai na ambato ko zikiri akwai TUHFATUZZAKIRINA   da wanin shi,

  
YA KU BAYIN ALLAH:-

Lallai Allah da Mala'ikun sa suna salati  ga Annabi
(Ya ku wadan da suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce …………………………) zuwa karshen adu'a.