الاثنين، 30 ديسمبر 2019

SABUNTA IMANI


Hudubar Juma'a  a Masallacin Annabi na shaikh AbdulBari Subaiti 1-5-1441AH
HUDUBAR FARKO
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, wanda ya halicci sammai da kasa, ya sanya duhu da haske  ina kyautata yabo a gare shi ina gode  mishi da  yammaci da safiya  da lokacin sammako, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah  shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, wanda yace : ( kuma rayayyu ba zasu yi daidai da matattu ba Allah na jiyar da wanda ya so, amma kai ba za ka jiyar da wanda yake cikin kabari ba)
 Na shaida shugabanmu Muhammad bawansa ne kuma manzonSa ne, ya yi gargadi a kan gafala da gajiyawa, tsira da amincin Allah su tabbata gare shi,da iyalan shi da sahabbansa wadanda suka samu babban falala da lada Bayan haka.
Ina muku nasiha da ni kai na da jin tsoron Allah Allah Madaukakin sarki ya ce:-(yA ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah cancancin tsoronSa kada ku mutu face kuna musulmai).
 Bibiyar imani da ba shi kulawa na daga cikin sifar musulmi kuma abin nanatawar masu hankali, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :(Imani na tsufa ya kode a cikin dayanku kamar yadda tufafi ke tsofewa ya kode, to ku roki Allah Madaukakin sarki : da ya sabunta muku imani a cikin zukatanku).
Kamar yanda tufafi ke tsofewa,  ai wato kamar yanda  sabon  tufafi yake tsofewa  sabo da dadewa ana amfani da shi, Manzon Allah tsira da amincin  Allah su tabbata a gare shi ya ce :- (An ambaci zuciya ne  kawai da zuciya  sabo da  jujjuyawa da yake yi ,  misalin zuciya kamar misalin gashi ne  da aka rataye ta a wani itaciya iska na kada ta  cikinta  da wajenta)
  Mumini na sabunta imaninsa , sabo da imani ba ya tabbatuwa a hali guda,  sai dai yana gajiyawa sabo da dadewa  ya raunana sakamakon gajiyawa a bangaren ibada , ko daina ibada ko kuma gafala daga Allah, da dulmuyar rayi a cikin sha'awe-sha'awensa  to mutum wani halitta ne da ke da iyaka a ikonsa, yana da rauni a fidirarsa  yana tsakanin gajiyawa da gajartawa  Allah Madaukakin sarki ya ce:-(An halicci dan adam a halin yana mai rauni).
Duk wani abu da zai sami musulmi na yanke ibada daga wani lokaci zuwa wani lokaci ko kuma zamewar kafarsa , to hakika baya kubuta daga hukunci na Ubangiji  daga ciki akwai komawa zuwa  ga Ubangiji da fadakar zuciya  Allah Mai tsarki da daukaka yana son masu yawan tuba yana farin ciki da tubarsu, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:-
  (Na rantse da wanda raina ke hanun shi  da badon kuna aikata zunubai ba  da Allah ya tafiyar da ku ya zo da wasu mutane masu yin zunubai , kuma suna neman gafara sai ya gafarta musu.)
  Imani na karuwa yana raguwa , yana karuwa da biyayya kuma yana raguwa da sabawa Allah , idan zuciyar dayanku ta farka daga gafalarta,  ya rika ayyuka na da'a ya riki sabuba na imani to imaninsa  zai karu ya yi karfi ko yakininsa ya yi karfi  idan ya yi dubi zuwa ga ni'imomin Allah  a  gare shi  sai kaunar sa ga Allah ta karu   sai ya yi  lafazi na ambaton Allah ya gaggauta cikin tuba da  ayyuka na alheri  domin ya riski abin da ya gajarta da abin da  ya tsere mishi a dalilin  gafala  sabo da haka ne lalle abin kwadayi ne   kwarai wurin bibiyan imani  da kuma aiki bisa  daga darajar shi  na daga cikin sifa na salihai  , Abu Darda Allah ya kara yarda a gare shi yana cewa: "Na daga cikin fikihun bawa  ya rinka bibiyan imaninsa da abin da ya tawaya daga gare shi , na daga cikin fikihun bawa  yasan cewa    yana karuwa ne shi ko yana raguwa". 
Umar Allah ya kara yarda a gare shi ya kasance yana cewa sahabban shi , ''  ku zo mu kara imani '' sai su ambaci Allah Mabuwayi .
Ibn Mas'ud Allah ya kara yarda a gare shi yana cewa a cikin adu'arsa (Ya Allah ka kara mana imani da yakini da  fahimta).
 Mu'az  bin Jabal -Allah ya  kara yarda  a  gare shi - yana cewa wani mutum (zauna tare da  mu , mu kara imani na wani lokaci).
Duk yanda imanin mumini  ya kai kololuwa a daraja to ba zai aminta wa kansa ba, tafarkinsa shi ne komawa zuwa ga Allah yana neman tabbatuwa a kan tafarki, Allah Madaukakin sarki yace a harshen bayinSa muminai: (ya Ubangijinmu kar ka karkatar da zukatanmu bayan ka shiryar da mu).
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana yawaita fadinsa.: ya mai juya zukata da basira tabbatar da zuciya ta bisa addininka).
Idan mumini ya san shaidan  na dakonsa ne, to ya yi kokari don yayi  yaki da fizgarsa, ya tunkude waswasinsa, ya toshe kofofin yaudarasa, kada ya mika wuya, kada ya samu karayar zuci, yana mai neman agaji daga Ubangijinsa, Allah Madaukakin sarki ya ce: ((To idan ka zo karanta kur'ani to ka nemi tsarin Allah daga shaidan abin jefe wa. Lalle shi bai da iko a kan wadanda suka yi imani, kuma suna  dogaro ne ga Ubangijinsa)
Mafi alherin guzuri ga wanda ya ke neman guzuri, kuma mafi alherin abokin tafiya a hanyar tabbatuwa bisa tafarki shine riko da littafin Allah da aiki da shi, wanda ya yi riko da shi Allah zai kare shi, wanda ya bi shi kuma Allah zai kubutar da shi.
Musulmi fadakakke yana yin kokari don ya ga ya fita daga yanayi na gafala, da sharri na rauni da gajiyawa, sabo da zai ji farinciki ne idan ya yi biyayya ga Allah, yana mai neman yardar Ubangijinsa, wani mutum ya tambayi Manzon Allah menene imani? Sai Manzon Allah ya ce :( idan kyawawan ayyukanka suka burge ka munanan ayyukanka suka bata maka rai to kai mumini ne).
  Ta yaya zai gafala daga Allah ya gajiya daga ibada wanda zuciyarsa akwai haske na Alkur'ani! Yana dandana halawar imani kuma ya san cewa yana da Ubangiji mai tausayi wanda ke yafe kusakuran masu tuba kuma yana gafarta zunubai, Allah Madaukakin sarki ya ce : (kuma wanda ya aikata mummuna ko ya zalunci kan shi sannan ya nemi gafarar Allah to zai samu Allah Mai gafara ne Mai jinkai)
Ambaton Allah da tunani cikin ayoyinSa yana farkar da zuciya kuma yana kara imani kuma yana tsarkake zuciya; Allah Madaukakin sarki ya ce : (Abin sani kawai, muminai sune wadanda suke idan an ambaci Allah zukatansu su firgita, kuma idan an karanta musu ayoyinsa sai su kara musu imani, kuma ga Ubangijinsu suke dogara.)
Ya dace ga musulmi ya dawo da ransa in ya gafala, da gabbansa idan sun yi rauni ko gajiya a ibada, domin tsoron fushin Allah da ukubarSa, na daga cikin Adu'ar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, (Ya Allah ina neman tsarinka daga gushewar ni'imarka da juyawar afiyarka da azaba bagtatan da dukkan abin da zai fusata ka,)
Zuciya kan karkata zuwa ga duniya a wasu lokuta tana ta neman abin duniya ido rufe wasu lokuta, sabo da haka ne Allah ya umarce mu da yawaita ambato, don a samu daidaito,  a gare mu tsakanin neman abin duniya da sauke nauyin wajibi na addini, : (ya ku wadanda suka yi imani ku ambaci Allah ambato mai yawa ku yi tasbihi safiya da maraice).
 Kamar yadda zurfafawa cikin abubuwan da aka halatta da barna da wuce gona da iri cikin al'adu yana haifar da gajiya Allah Madaukakin sarki ya ce : (ya 'yan adam ku riki adonku a gun dukkan masallaci ku ci ku sha kada ku yi barna, lalle shi bai son mabarnata.)
Ba ya boyu wa ga masu hankali cewa abota da masu raunin himma da marasa  manufa kan haifar da gajiya wa da gafala.
Idan musulmi bai ankara ba daga gafala da ya ke ciki ya gaza tunkude gaza wa da yake da shi da rauni to sai sifa ta tsauri da kekashewar zuciya ta yi galaba a kan shi da rauni da nauyi wajen sauke nauyin ibada,  da'a ta yi mishi wahala zuciya ta yi tsatsa ya dushe hasken imani
Allah Madaukakin sarki ya ce : (Bone ya tabbata ga wanda zukatarsu suka kekashe daga ambaton Allah wadancan suna cikin wata bata bayyananna).
 Idan musulmi bai magance zuciyarsa ba to zai dangana da halin nan da Allah  Mai tsarki ya bada labari game da ita, a fadinsa (sa'annan kuma zukatanku suka kekashe daga bayan wancan, sabo da haka suka zama kamar duwatsu, ko mafi tsanani  ga kekashewa, kuma lalle ne daga duwatsu hakika akwai abin da maremari suke bubbuga daga gare shi, kuma lalle ne daga gare su hakika akwai abin da ya ke tsatsagewa har ruwa ya fita daga gare su, hakika, akwai abin da ya ke fadowa domin tsoron Allah, kuma Allah bai zama gafili ba daga abin da ku ke aikatawa.)
Allah ya sa mana albaka ni da ku cikin Alkur'ani Mai girma kuma ya amfanar da ni da ku da abin da ke ciki na ayoyi da ambato mai hikima. Iya abin da ya sawwaka kenan cikin abin da zan fada tare da neman gafarar Allah, kuma ku nemi gafararSa domin shi Mai gafara ne Mai jinkai.
  
    HUDUBA TA BIYU
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya amsa kiran wanda ya roke shi, musulmi na gode masa a sirrinsa da ganawarsa, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya ba wani Ubangiji koma bayanSa, na shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne kuma  zababbenSa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa wadanda suka rabauta da kaunarSa kuma da yardarSa.  
Bayan haka :To ina muku wasiyya da ni kai na da jin tsoron Allah.
 Duk wani abu da ya samu musulmi na gafala kuma alama na gazawa ta afka mishi kafa ta zame, to lalle kofar tuba a bude take, hanyoyin alheri birjik su ke, Allah na son masu yawan tuba da komawa gare shi, kuma yana cewa a hadisul kudsi : (ya ku bayi na lalle ku masu yin kuskure ne cikin dare da wuni, ni kuma mai gafarta zunubai ne baki daya, ku nemi gafara ta zan gafarta muku).  
Ku yi salati ga Annabin shiriya. Hakika Allah ya umarce ku da hakan a littafinSa sai ya ce :(Lalle Allah da mala'ikunSa suna salati ga Annabi, ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce.)  

الجمعة، 20 ديسمبر 2019

FIDIRA


Hudubar Masallacin Annabi na Shaikh Aliyu bin Abdurrahman Alhuzaifi 23-4-1441 Ah 20-12-2019Ac
Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai.

Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mabuwayi Masani, wanda ya halicci mutum cikin mafi kyan tsari, wanda ya tausayawa mukallafai da saukar musu wannan littafi mai daraja, wanda ya yi baiwa ga halittu da ni'imomin da basu gidayuwa na daga falalarsa mai girma, ina kyautata yabo ga Ubangiji na kuma ina gode mishi bisa ni'imominsa da baiwarsa da alherunsa da muka sani da wadanda bamu sani ba, ba abin bauta wa da gaskiya sai shi, Ma'abocin kyautatawan da bai katsewa   da  kyautayinsa dadadde, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, Mai rahama Mai jinkai, na kuma shaida Annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne kuma ManzonSa ne, mai shiryarwa zuwa ga tafarki mikakke, ya Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammad da iyalansa da sahabbansa wadanda suka rabauta da daukaka na duniya, a lahira kuma suka rabauta da ni'ima na har abada.
Bayan haka, ku ji tsoron Allah wanda ya halicce ku ya baku duk abin da kuke kauna ya tunkude muku abin da kuka tsana, ya ku mutane! Ina tunatar da ku da ni kai na da ni'ima da ta fi kowacce, dukkaninta Allah ya ni'imta mutum da su, muddin ya kiyaye ta ya bata matsayinta cancancin matsayinta, ya kiyaye ta ya mutu a kanta to hakika ya samu sa'ida a rayuwarsa da bayan mutuwarsa sa'idar da bai zai taba tsiyacewa ba da ita har abada ya kuma rabauta da  alhairu, kuma ya tsira daga sharri da abubuwa masu halakarwa, Allah zai gyara dukkan lamuransa baki daya a rayuwarsa, kuma ya jikansa bayan mutuwarsa, kuma wannan shine babban rabo, idan mutum ya sauya wannan ni'ima mai girma ta hanyar kafurcewa ko munafunci ko da wani aiki da ke kishiyantar wannan ni'imar ya sarayar da ita da rashin kiyaye ta to hakika ya yi hasara mabayyaniyar hasara, ko da an hada mishi abubuwan jin dadin duniya da kyalakyalanta, to ba wani abu bane ita sai inuwa mai gushewa, kuma jindadi ne mai kaucewa, kuma ni'ima ce mai karewa jindadinta na tafiya ta bar hasara. Allah Madaukakin sarki yace (Rayuwar duniya ba wata aba ba ce face jindadi mai rudi) Allah Madaukakin sarki yace (ya ku mutane lalle alkawarin Allah gaskiya ne kada rayuwar duniya ta rude ku, kada wani mai rudi ya rude ku daga Allah.)
     Ya ku bayin Allah! Ko kun san wannan ni'ima mafi girma wanda Allah ya yi ga mutum ya kuma mutunta shi da ita? Lalle ita ce ni'ima ta fidira, to menene hakikanin fidira, ana nufi da fidira halin da Allah ya halicci mutum a kai, mai iya karbar kadaita Allah shi kadai ba Ubangiji koma bayanSa, kuma ba abin bauta bayan shi, mai kaunar Alheri mai kin sharri mai karkata zuwa ga biyayya, mai gano munin abubuwan da aka haramta, mai sanin gaskiya a dunkule, kuma masanin bata a dunkule, da ace wannan fidirar da Allah ya halicci mutum a kai ta kubuta daga shaidanun mutane da aljanu da abubuwa masu tasiri da ke iya sanja ta to da ta zabi tauhidi da musulunci, sai dai wannan fidira bata iya wadata da kanta wurin sanin gaskiya daki- daki daya -bayan daya kuma ta yi aiki da shi haka ma sanin sharri da bata daya bayan daya da nesatansu, to don haka ne Allah Mai tsarki ya turo manzanni, kuma na karshen su shine Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi don su kiyaye fidira  kuma su koyar da ita sharia su taimake ta da haske na wahayi a matsayin manhaji na rayuwa, na daga cikin dalili da ke nuni cewa fidira ita ce halin da Allah ya halicci mutum a kai da lafiyayyar dabi'a mai iya amsar addini mai son musulunci akwai fadin Allah Madaukakin sarki ( ka tsayar da mafiskantar ka ga addini kana mai totar izuwa gare shi kirar Allah ce wacce ya kera mutune a kanta, babu musanyawa ga addinin Allah)  Ibnu kasir Allah ya masa rahama yace a cikin tafsirisa : ( ma'anarsa Allah Madaukaki ya daidaita halittunsa gaba dayansu a kan fidira bisa dabia mikakkiya da ba a haifan kowa face a kan haka, ba fifiko tsakanin mutane cikin haka)  ta tike.
An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : Dukkan abin haihuwa ana haifansa ne akan musulunci to iyayensa ne ke yahudantar da shi ko kiristantar da shi ko majusantar da shi, kamar yadda dabba lafiyayya kan haifi lafiyaya babu wani abu da ku ke gani na gutsurarren hanci ko kunne.) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
 An karbo daga Iyad dan  Himar Allah ya kara yarda a gare shi, yace watarana Annabi ya yi huduba sai ya fada a cikin hudubar tasa : lalle Ubangiji na ya umarce ni da na sanar da ku abin da baku sani ba. dukkan dukiyan da na bawa bayi na na halal , lalle na halicci bayi na akan addini hanifiya gabadayansu sai shaidanu suka zo musu suka batar da su daga addinin su. suka haramta musu abin da aka halatta musu suka umarce su da su yi shirka da abin da ban saukar da shi ba na hujja)  Muslim ne ya rawaito
Imamul Bagawi Allah  ya mishi rahama ya ce a cikin tafsirinsa: "Ance ma'nansa dukkan wani abin haifa ana haifansa ne a farkon halittansa bisa fidra wato dabi'u masu lafiya da halaye da suke a shirye don karban addini da zai tafi ne bisa lazimtar ta sabo da wannan addinin kyanshi na nan cikin hankali sai dai kawai zai kauce ne daga wannan zuwa wanin shi sabo da wata musiba da ta faru na daban kamar koyi ko kwaikwayo, da mutun zai kubuta daga wannan musibun to ba zai kudurta wani abu ba sai addini) . maganar ta kare.
 wato fidra ana nufi da ita mahalli na imani wanda shi ne dabia'n da mutun ya tafi a kan shi wanda aka halicce shi akanta  a halinsa na dan adam kuma zuciyarsa a shirye ta ke don karban ilimi mai amfani da aiki na kwarai,  ma'ana na biyu a tafsirin fidra shi ne hasken wahayi da ilimin sharia.
Ibnu abbas Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : "Babu canji ga halittan Allah ai ga addinin Allah"
Imamul Buhari ya ce : "fadinsa la tabdila li kalkillah ma'ana babu canji ga halittan Allah lidinillahi wato dabiyun mutanen farko shi ne addinin mutanen farko addini da fidra kuma shi ne al islam .
maganan ya tike.
 To sai ya bayyana cewa fidra ita ce mahalli ko bigire na imani da addini shi ne abin da aka haifi mutun akai na daga halitta mikakkiya ko dabi'a mikakkiya wanda ana nufin da fidra shi ne halin da ya ke cikinta  na asali shi ne na shari'a da imani.
Zan koro misalai na wadannan ma'anoni biyu, kamar misalin fidira da aka haifi mutum a kai, kamar misalin fitila ne na wutan lantarki wanda aka sana'anta aka yi shi ya rika karbar  wutar lantarki, shi wutan lantarki kamar ilimi ne da wahayi da ke cikin zuciya idan aka hada kwan lantarki da wayan lantarki mai wuta sai ya yi haske ya haskaka ya bada launi, idan ba a hada su ba to ba dayansu da zai amfanar shi kadan shi wurin haskakawa, to haka nan ma fidira ba za ta amfanar da ma'abocinta ba sai da ilimi mai amfani da aiki na kwarai.
    Fidira ita ce abin da Allah ya karrama mutum da ita ya fifita shi da wannan fidira wacce da ita ne ya ke sanin ma'arufi ya ki abu na munkari  ya siffanta abu mai kyau da kyau ya munanta abu  mara kyau, idan fidira ta juya ta rushe to kuwa mutum ya zama mamaci ko da yana tafiya a  doron kasa, Allah Madaukakin sarki ya ce :( shin kuma wanda ya kasance matacce, sa'annan muka rayar da shi, kuma muka sanya wani haske dominsa yana tafiya da shi, yana zama kamar wanda misalinsa yana cikin duffai, shi kuma ba mai fita ba daga gare su.)
Fidirar mutum ba ta samun kiyayewa ta karu da haske da sheki ta cika a karfi da rayuwa face da ilimi mai amfani da aiki na kwarai, da imani da aiki na da'a, domin da'a ke ciyar da ita ta sanya ta ta yi karfi, kuma nesatan abubuwan da aka haramta na kare ta daga abubuwa  masu darkakewa, duk wani umarni na wajibi ko mustahabbi na kiyaye Fidira ya raya ta    Allah Madaukakin sarki ya ce :( ya ku wadanda suka yi imani ku amsa wa Allah kuma ku amsa wa  Manzo idan ya kiraye ku zuwa ga abin da yake rayar da ku).
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( Abubuwa goma suna cikin fidira : rage gashin baki da barin gemu da yin aswaki da shaka ruwa da yanke kumba da wanke matattara da ke tsakanin yatsu,da cire gashin hamata, da tsarki da ruwa, wato istinja'i) Muslim ne ya rawaito.
 Idan wadannan ta'adodin na cikin  Fidira to wasunsu na daga farillu sun fi dace wa su shigo ciki,
An karbo daga Bara'u dan Azib Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da ni :idan kazo kwanciya to ka yi alwala, alwala irin na salla, ka kishingida a baryarka na dama, ka ce : ya Allah na mika rayi na a gare ka na fiskantar da fiska ta a gare ka, na fawwala al'amari na zuwa gare ka, na komar da baya ta zuwa gare ka, halin kwadayi da tsoro  gare ka, ba mafaka da matsirata daga gare ka sai izuwa gare ka, na yi imani da littafinka da ka saukar, da Annabinka da ka turo, to idan ka mutu to zaka mutu ne a kan fidira ka sanya su karshen abin da za ka fadi.)Buhari da Muslim ne suka rawaito.
 Idan fidira ta kasance ita ce sa'adar mutum ta hanyar gyaruwarta to lalacewarta kuwa ita ce daidaicewar mutum da walakantarsa da hasararsa to ya wajaba mutum ya nesaci abin da zai sanja ta ya lalata ta, kuma mafi hadarin aiki da zai sanja ta ya lalata ta shine shirka, wato hada Allah da wani a bauta, ko sifanta Allah da abin da ya tsarkaka daga shi, na daga da ko aboki, kamar fadin mushrikan larabawa kafin turo Manzo na cewa : Mala'iku 'ya'ya mata ne na Allah, da wanda ya yi irin wannan zance,
 An karbo daga Abdullahi dan Abbas Allah ya kara yarda a gare su daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : Allah Madaukakin sarki ya ce :Dan Adam ya karyata Ni , kuma bai dace ya yi hakan ba, Dan Adam ya zage Ni kuma bai dace ya yi hakan ba, Amma karya ta Ni da yayi ita ce zaton sa da ya yi na cewa ba zan iya maida shi kamar yadda ya ke ba, amma zagi Na da ya yi shi ne cewa da ya yi ina da da, tsarki ya tabbata a gare Ni da na riki da,) Buhari ne ya rawaito. A hadisin Abu Huraira :Amma zaginsa gare Ni cewarsa : Allah ya riki da  Alhali kuwa Nine Allah tilo Assamad bai haifa ba kuma ba a haife shi ba, bai da wanda yake kininSa,
Wannan yayi nuni da fadinsu ya fi muni a kan masu bautan gumaka. shirka Allah ba ya gafarta shi sai da tuba Allah  Madaukakin sarki ya ce :( lalle wanda ya ke hada Allah da wani to hakika Allah ya haramta Aljanna a gare shi kuma babu wasu mataimaka ga azzalumai )
Na daga cikin abin da ya ke sauya fidra kuma ya bata ta akwai zunubai da aikata sabo Allah bai halaka alumman da su ka gabace mu ba face sabo da lalacewan fidransu da kuma ketare iyakansu daga umarnin Allah mabuwayi da daukaka Allah bai tsiratar da muminai ba da su ke tare da su face da gyaruwan fidrarsu Allah madaukakin sarki ya ce (sai muka tsiratar da wadanda suka yi imani sun kasance kuma suna jin tsoron Allah) ga wannan aya akwai abin lura cikin halaka mutanen ludu gaba dayansu ba wanda ya tsira daga cikin su ko da mutun daya saboda lalacewan fidran su da kuma juyawanta suna aikata alfahasha mai mummuna ba wanda ya tsira sai ludu amincin Allah su tabbata a gare shi da 'ya'yansa mata biyu
Sabo yana lalata fidra ta fiskan abin lura shi ne ko wani Annabi da Allah ya halaka alummarsa wasu sashi sun yi imani da shi sai Allah ya tsiratar da su daga shi amma mutanen ludu hakika sabo ya lalata musu fidrar su sai aka yi musu mafi tsananin ukuba a doron kasa
Na daga cikin abin da ya ke lalata fidra akwai yin zina domin yana da tasiri wurin kazanta zuciya, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (mai zina ba zai yi zina ba a yayin da ya ke zina a halin yana mumini, Barawo ba zai yi sata ba a yayin da ya ke sata a halin yana mumini  mai shan giya ba zai sha giya ba ayayin da ya ke shan giya a halin yana mumini ) Buhari da Muslim ne suka rawaito daga Abi Huraira
  Ibnu mas'ud Alla ya kara yarda a gare shi ya ce: "An hada zina tare da shirka" yana nufin fadin Allah Madaukakin sarki (mazinaci ba zai aura ba face mazinaciya ko mushrika )
To fa giya ita ce ummul kaba'isi wato uwar kazanta Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (ku nisaci ummul kaba'isi) Ibnu Hibban ne ya rawaito da baihaki daga hadisin usman Allah ya kara yarda a gare shi manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (giya matattara ce ta laifi) saboda tana rusa fidra ta lalata gudanarwa da hankali, kayan maye da miyagun kwayoyi su suka fi tsananin lalata fidra da hankali kuma su suka fi hatsari ga alumma, to giya illan ta kan iya zame wa kebabbiya ga mai shanta, kuma yana katangewa daga jin alkura'ani wanda shi ne sababin dukkan alheri, kuma yana kai ma'abocin shi zuwa ga ukuba.
 Na daga cikin abin da ya ke lalata fidra akwai zaluncin bayi ga junan su, rushewar duniya na ga zaluntar bayi sashin su ga sashe,   Allah madaukakin satrki ya ce (kuma wadancan alkaryu mun halaka su a lokacin da suka yi zalunci kuma muka sanya lokacin alkawarin ga halaka su)
Ya kai mutum rabautar ka da gyaruwarka da farincikinka da daidaituwan al'amuranka gaba dayansu da gadanka ga Aljanna mai ni'ima da tsirar ka daga azaban jahima na ga kiyaye daidaitacciyar fidira ta hanyar riko da wannan sharia ta musulunci mikakkiya, Allah Madaukakin satrki ya ce (kuma lalle wannan ne tafarki na yana madaidaici sai ku bi shi kuma kada ku bi wasu hanyoyi su rarraba ku daga barin hanya ta, wannan ne Allah ya muku wasiyya da shi ko za ku ji tsoron Allah)
 Allah ya sanya mini albarka ni da ku a Alkur'ani mai girma ya kuma amfane ni da ku da abin da ke cikinsa na ayoyi da ambato mai hikima.

Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai Mai karfi, Majibincin masu tsoron Allah, ina kyautata yabo ga Ubangiji na kuma ina gode masa bisa ga ni'imominSa da ba mai iya kididdige su sai shi, muna gode masa irin godiyar masu shukura, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya,  Allan mutanen farko da na karshe, kuma na shaida Annabinmu kuma shugabammu Muhammdu bawansa ne kuma ManzonSa ne mai gaskiya amintacce Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka bisa ga bawanka kuma Manzon ka muhammad da iyalansa da sahabbansa da wanda suka bi su da kyautatawa zuwa ranan sakayya, bayan haka ku ji soron Allah madaukaki cancancin soron shi ku kiyaye saba wa shari'arsa ba wanda zai rabauta cikin wanda su ka saba mishi. 
Ya ku bayin Allah ku kyautatawa kanku ta hanyar daidaituwa kan tafarki, hakika Allah ya kyautata muku da shiriya da nau'ka na karama ya kai mutun : ka tsarkake ranka daga kazantaccen abubuwa ka tsarkaketa ta hanyan amsa kira da karban abinda Ubangijinka ke kiran ka zuwa gare shi Allah Madukakin sarki ya ce (ku amsa wa Ubangijinku tun gabanin wani yini ya zo ba bu makawa gare shi daga Allah ba ku da wata mafaka a ranan nan kuma ba ku iya yin wani musu )
Idan ka amsa ya kai mutun ga umarni to za ka tashi da shi idan ka amsa kira ga hani kuma to za ka nesace shi, to hakika matsayinka zai daukaka a wurin Ubangijinka kuma ka karrama  kanka ka gode wa ni'man fidra wacce ta ke ita ce mafi girman ni'ma. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Lalle Allah na daga darajan wasu mutane da wannan Alkur'ani, kuma ya kan yi kasa da wasu dalilin shi)
da kuma abin da al ummu su ka canja wanda ta wofanta daga fidrar Allah ba su amsa kiran Manzanninsu ba sai su ka walakanta a wurin Allah kuma za su auka cikin tozarci da kuma hasara ) Allah madaukakin sarki ya ce:( saboda haka ko wannen su mun kama shi da laifinsa daga cikin su akwai wanda muka aika iskar tsakuwa akan sa kuma daga cikin su akwai wanda tsawa ta kama kuma daga cikin su akwai wanda muka birkice kasa da shi , kuma daga cikinsu akwai wanda muka nutsar, baya yiwuwa ga Allah ya zalunce su , amma sun kasan ce kan su su ke zalunta )

Ya ku bayin Allah! lallai Allah da mala'ikunsa suna salati ga Annabi, ya ku wadanda su ka yi imani ku yi salati gare shi da aminci tabbatacce .      

الأحد، 15 ديسمبر 2019

SURAR DA KE BAYANIN DALILAN TSIRA DAGA HASARA


Hudubar Masallacin Annabi na shaikh Ahmad Bin Dalib 16-4-1441Ah/13-12-2019
Hudubar farko
Allah yana fadi a cikin littafinSa mai girma, kuma shi ne mafi gaskiyar masu magana. (Ina rantsuwa da zamani. Lalle mutum na cikin hasara. Face wadanda suka yi imani kuma suka yi aiki na kwarai kuma suka yi wasiyya ga juna da gaskiya kuma suka yi wasiyya da hakuri.)
Allah ya yi rantsuwa da Asr wato zamani ko kuma wani yanki na shi, wato lokacin yammaci, shi aka yi rantsuwa da shi kan cewa lalle jinsi na mutum na cikin hasara, to kowa duk wanda ya kasance haka to makomarsa gidan halaka tir da matabbata, sai Allah ya toge daga cikin hasararrun wadanda suka siffatu da sifofin nan guda hudu da ayoyi bayyanannu suka nuna:
Sifa ta farko ita ce  a fadinSa: "Face wadanda suka yi imani" Imani kuma asalin shi da kamalarsa bai samuwa sai da ilimi.
Sifa ta biyu ita ce  a fadinSa:" kuma suka yi aiki na kwarai" shi aiki na kwarai shi ne wanda aka yi shi don Allah kuma bisa koyarwar Manzon Allah.
 Sifa ta uku ita ce  a fadinSa Madaukakin ambato :" : "kuma suka yi wasiyya ga juna da gaskiya" Hakikaninta kira zuwa ga Allah.
Sifa ta hudu ita ce  a fadinSa Tabaraka wata'ala : " kuma suka yi wasiyya da hakuri." Wato suka Siffatu da wannan sifa mai kubutarwa daga hasara.
Duk wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, kuma ya yarda musulunci shine addini, kuma ya yarda Muhammad  a matsayin Annabi kuma Manzo, ya san abin da Allah ya ke kauna, ya fahimci manufa na wahayin Allah, ya yi aiki na kwarai don Allah, ya tsarkake shi daga shirka, da bidia abin munantarwa, ya maida kansa kamili ta hanyar ilimi mai amfani da aiki na kwarai, sannan ya yi kokari wurin maida waninsa ma kamili ta hanyar kiransa zuwa ga gaskiyan da ya samu, ya yi wasiyya kuma ya nemi a mar nasiha da abin da zaa tambayi kowa a kabarinsa na sanin Allah da sanin Manzonsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da sanin addinin musulunci, sani da ke tare da dalilanta na  daga littafin Allah  da sunnan Manzonsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da kuma abin da aka karbo daga sahabbai da limamai na addini  masu shiryarwa. Kuma ya yi hakuri bisa imani da aiki na kwarai, da kuma kira zuwa ga Allah Mabuwayi da daukaka yana yin shi a aikace da neman sani da ilmantarwa, da kuma hakuri bisa abin da ke faruwa na cutarwa ga duk wanda ya  riki tafarkin Annabawa, to hakika wallahi ya tsira da hasara na rantse da Ubangijin zamani.
Sabo da cika na wannan sura mai girma tare da gajarcinta wajen bayanin abin da zaa umarci mutane don su tsira su rabauta Abu Abdullahi Imam Al shafi'i Allah ya jikan shi ya ke cewa: "Wannan sura da Allah bai saukar da wata hujja ba ga bayinSa sai ita to ta ishe su."
Ai da ta ishe su wajen tsaida musu hujja sabo da wajabcin riko da umarnin Allah na sharia, ta hanyar gaskata wahayi na Allah, da bin umarninSa da nesatan haninSa,da kudurta abin da Allah Mai tsarki  ya halatta.
Allah sa min Albarka ni da ku.

Huduba ta biyu
Allah Madaukakin sarki yana cewa  (ka sani cewa ba abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma ka nemi gafarar zunubinka da na muminai maza da muminai mata Allah ya sa majuyarku da mazauninku).
 Sufyan Bin Uyaina  Allah ya masa rahama ya ce : "sai ya fara da ilimi kafi fadi da aiki,"  dukkan shiriya na cikin sanin ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, Addinin gaskiya gabadayansa ya kunshi neman gafara ne gurin Allah da tuba zuwa gare shi furuci da aiki,
Allah Mabuwayi da Dauka yana cewa  (Suna so su bice hasken Allah da bakunansu alhali kuwa Allah Mai kammala haskenSa ne ko da kafurai sun ki.shi ne wanda ya turo ManzonSa da shiriya da Addinin gaskiya don ya daukaka shi akan dukkan addinai ko da mushrikai sun ki)

الأربعاء، 11 ديسمبر 2019

HUNTURU LOKACIN KAKA NE NA MUMINI


Hudubar Masallacin Annabi na shaikh Abdullah Bin    Abdurrahman Albuaijan 9-4-1441AH/6-12-2019AC
Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah masanin gaibi Mai suturce aibi mai yaye bakinciki Mai yafe zunubai Mai tsinkayan dukkan sirri da ke zukata, muna gode masa kuma muna neman taimakonSa muna neman gafararSa muna kuma tuba zuwa gare shi.
Muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu, muna riko da shi (Allah) a dukkan al'amuranmu da yanayinmu.
Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake ba shi da abokin tarayya.
Kuma na shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, ya isar da sako kuma ya sauke amana.ya yi nasiha ga al'uma ya yi jahadi don Allah cancancin jahadi har mutuwa ta zo masa. Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalanSa da sahabbanSa baki daya.
Bayan haka,
Mafi alherin zance shine maganar Allah, mafi alherin shiriya shi ne koyarwar Annabi Muhammad, mafi sharrin al'amura shine fararrunsu, kuma dukkan bid'ah bata ce, kuma dukkan bata na wuta.
Ya ku bayin Allah ku ji tsoron Allah cikin umarninsa ku hanu daga abin da ya yi hani a kai ya kuma tsawatar. (ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah cancancin tsoronSa kada ku mutu face kuna musulmi)
 Ya ku bayin Allah!
Lallai ga karewan kwanaki akwai abin lura, ga abin da ya shude kuma a kwai tunatarwa da izina (Allah na juya dare da wuni, lalle ga hakan  akwai abin lura ga ma'abota basira).  
Ranaku da watanni da lokutan shekara, da shekaru na shudewa suna bin junan su, burace – burace da ajali na karewa, wasu al'uman na riskan wasu,  (Duk wanda ke kanta zai kare sai fiskar Ubangijinka ma'aboci daukaka da karamci zai wanzu).
 Ya ku jama'ar Musulmai!
 Hakika lokacin hunturu ya fiskanto ku, sanyinsa mai gargadi ne, Allah ya yiwa jahannama izini da ta numfasa a cikinsa, An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi yace :Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( wuta ta koka zuwa ga Ubangijinta sai ta ce :" sashi na ya ci sashi, sai Allah ya sanya mata numfasawa biyu :numfasawa daya a lokacin hunturu,dayan kuma a lokacin bazara, shi numfasawarta na lokacin hunturu to shine jaura, na lokacin bazara kuma shine wannan iska mai tururi)Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
An rawaito daga Umar dan khaddabi cewa idan hunturu ya zo sai ya bibiyi talakawansa sai ya rubuta zuwa gare su : "Lalle hunturu ya zo kuma shi makiyi ne to ku masa shiri na daga fatu da hoffofi da safanni, ku riki fatu a matsayin riga 'yar ciki da ta waje, domin sanyi makiyi ne mai saurin shiga (jiki) mai dadewa bai fita ba".
  To ku bibiyi bayin Allah -masu rauni- ku taimaka musu bisa sanyin hunturu, ku bibiye su don basu abinci da tufafi da mayafi, ku nemi ladan su gurin Allah a ranar gamuwa, (Duk abin da ku ke ciyarwa na alheri to don kan ku ne, ba wani abu da za ku ciyar face don neman yardar  Allah, ba wani abu da zaku ciyar na alheri face an cika muku shi, a halin ku ba zaa zalunce ku ba.)


Ya ku bayin Allah!
Ku yi lura da wadannan zamuna da lokutan shekara da abin da ke cikinsu na maslahohi da hikimomi, da ace zamanin gaba daya lokaci guda ne cikin lokutan shekara da wasu maslahohin an rasa su wato na sauran fasalin, kamar da dukkan shekara bazara ce to da an rasa amfani da maslahohin hunturu, haka ma in da kaka ne gaba dayansa ko   damina  dukaninsa.
Abin mamaki ta yaya zaa sabawa Ubangiji***
                     Ko ta yaya wani mai korewa zai kore shi*
Cikin komai akwai alama tasa***
                    Da ke nuni cewa shi kadai ne*

Ya ku jama'ar Musulmai!
Hunturu ya fiskanto, to maraba da ganimar masu bautan Allah, da kuma kaka ta muminai, dare na tsawaita cikin shi sai su samu rabon su na barci, sannan hakarkarinsu na yin nesa daga makwanci, don su yi tsayuwan dare, wuninsa mai sanyi na gajarta don ya saukake musu wahalar azumi.
Allah Madaukakin sarki ya ce : (lallai masu tsoron Allah suna cikin lambuna da maremari. Suna masu dibar abin da Ubangijinsu ya ba su, lallai su sun kasance masu kyautatawa a gabanin haka(a duniya). Sun kasance a lokaci kadan na dare suke yin barci. Kuma a lokutan asuba suna ta yin istigfari.)
Lokacin Hunturu -Ya ku bayin Allah! - Lokaci ne na kaka ga muminai, suna kiwo cikin gonakan da'a ga Allah. Suna shakatawa a fagage na ibadoji zukatansu na walwawa cikin dausayin kusantar Ubangiji, an samu saukin wahala da gajiya, azumin bai gajiyar da su, ko dare ya kuntata gare su ga barcinsu ko tsayuwansu na  dare.
An rawaito daga Amir dan Mas'ud Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :"Azumi cikin hunturu wata ganima ce na ruwan sanyi)Ahmad da Tirmizi ne suka rawaito.
Abdullahi dan salam ya ce :A yayin da Annabi ya zo garin Madina mutane sun yi cacarindo zuwa gare shi, Sai na shigo cikin mutane don na gan shi, a yayin da na samu ganin fiskar shi sai na tabbatar wannan fiskar ba na makaryaci ba ne,farkon maganar da ya fara da ita ya ce  : (ya ku mutane ku yada sallama ku ciyar da abinci, ku sada zumunci, ku yi salla a halin mutane suna barci za ku shiga Aljannar Ubangijinku da aminci).Ahmad da Tirmizi ne suka rawaito,kuma ya inganta shi.
Yayin da mutuwa ta zo wa Mu'az Bin Jabal sai ya ce ga kuyangarsa : "kaiton ki shin gari ya waye? Sai tace : a'a, sai ya kyale ta zuwa bayan wani dan lokaci sai ya ce: ki duba, da ta duba sai tace ; "e"  sai ya ce : Ina neman tsarin Allah daga safiyar da za ta kai zuwa ga wuta, sannan sai yace : Maraba da mutuwa, maraba da bakon da yazo ana halin talauci, duk wanda ya yi nadama ba zai rabauta ba, Allah ka san ba wai ina bukatar zama a duniya ba ne sabo da tona sabbin rami na koramai ba, ko dashen itatuwa ba, sai dai ina son zama ne don na dage da kokari a daren hunturu mai tsawo, da kuma fiskantar kishin garji a lokacin tsananin zafi, da kuma gogayya da malamai a sahun halkan ambaton Allah."

Ya ku bayin Allah!
A lokacin hunturu ne dare ke tsawaita wuni ke gajarta, Hakika Allah ya sanya dare sutura, ya sanya barci kuma hutu, wuni kuma don neman abin rayuwa.
(Allah ne wanda ya sanya muku dare domin ku natsu a cikinsa, da rana mai ganarwa, lalle Allah hakika Ma'abocin falala ne a kan mutane, kuma amma mafi yawan mutane ba su godewa.)
 Hakika dimantan kwana ba barci wata cuta ce mai tafiyar da nashadi, mai kashe jiki,  mai hana neman arziki da aiki, kuma yana banzatar da lokuta, kuma yana shagaltarwa daga da'a, kuma ya sabawa sunna.
Allah Madaukakin sarki ya ce :(kuma na daga cikin ayoyinSa barcinku a cikin dare da wuni, da neman ku ga falalarSa, lalle a cikin wannan akwai ayoyi ga mutane masu saurarawa.)
 Annabi ya kasance yana kin barci kafinta da zance bayanta –wato sallar lisha-
Ina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan abin jefewa. (kuma shi ne wanda ya sanya muku dare ya zama tufa, da barci ya zama hutawa, da yini ya zama lokacin tashi).
Allah ya sa min albarka ni da ku a cikin Alkur'ani.

Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa datarwarSa da kyautatawarSa, tsira da amincin Allah su tabbata ga Muhammad Mai kira zuwa ga yardarSa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalanSa da sahabbansa, da 'yan uwansa.
Ya jama'ar Musulmai!
Lalle ba abin da musulunci ya bari a halin rayuwa , ya yi la'akari da sanjawar zamani da lokuta sai ya shar'anta hukunce –hukunce na azima da sauki a yayin larura.
Na daga cikin abin da Allah ya ke daga darajoji da shi, ya kuma kankare kusakurai da laifuka akwai gaggautawa zuwa ga tsarki, wanda sharadi ne na ibadoji, kuma rabi ne na imani, kuma sharadi ne na salla wanda yake rukuni ne na musulunci. To dagewa  da jurewa da hakuri ga abin da aka ki, da bauta ta hanyan amfani da ruwa a lokacin sanyi a hunturu, na cikin masu kankare zunubai, An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :"Ase ba zan nusar da ku ga abin da Allah ke goge zunubai da shi ba, kuma ya daga darajoji da shi? Su ka ce : E ya Manzon Allah,sai yace : Yalwata alwala a halin ba a so, da yawan taku zuwa ga masallatayya, da jiran salla bayan idar da salla: Wancannin ku shi ne Ribadi )Muslim ne ya rawaito.

Ya ku bayin Allah
Na daga cikin sauki irin na shari'a da hikima na musulunci da rangwami da saukakawa mutane a yayin wahala mai bijirowa, da cutuwa da ake tsammani  (kuma bai sanya muku wani abu na kunci ba a addini)
  Duk wani abu mai wahala na janyo  saukakawa, (kuma Allah bai dora wa rai sai abin da ya ba shi, Allah zai sanya sauki bayan tsanani.
   Musulunci ya shar'anta sauki  yayin kunci da whala  da larura, na daga ciki akwai mara lafiya,
Kai har ma mai laifiyan idan ya  tsoracewa kansa, amfani da ruwa to an shar'anta masa taimama da kasa, kamar yadda a ka shar'anta wa wanda ya ji ciwo da ya yi shafa kan abin da ya rufe ciwon ko ma a kan maganin.

  An karbo daga Jabir Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Mun fita a wata tafiya  sai dutse ya samu wani mutum ya mishi rotse a kai, sai ya yi mafarki sai ya tambayi mutanensa sai yace : ko ina da sauki ko zan iya na yi taimama? Sai suka ce ba ka da wani sauki tunda za ka iya amfani da ruwa, sai ya yi wanka sai ya mutu. Yayin da suka zo gun Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare sai aka bashi labarin hakan sai ya ce:  sun kashe shi Allah ya kashe su, me ya sa ba za su tambaya ba idan basu sani ba, ba komai ba ne maganin jahilci sai tambaya. Ai daya yi taimama kawai da ya isan masa ya matse ko ya daure ciwon nasa da tsumma, sai ya shafa kan ciwo ya kuma wanke sauran jikin nasa )
An karbo daga Amru dan As  Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Na yi mafarki a dare mai dari a yakin zatus salasil, sai na tausayawa kai na na yi taimama don in nayi wanka zan halaka.sai na yi (jagorancin ) salla ga mutane na sallar asuba, sai su ka ambaci hakan ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai yace : ya Amru ka yi limanci wa mutanenka a halin kana janaba? Sai na gaya mishi abin da ya hana ni wanka nace ni na ji fadin Allah da ya ke cewa : (kuma kada ku jefa kan ku ga halaka lalle Allah ya kasance mai tausayi ne a gare ku),sai Manzon Allah ya yi dariya bai ce komai ba. Abu Dauda ya rawaito Albani kuma ya inganta shi.
   

الجمعة، 29 نوفمبر 2019

HUKUNCIN SHAFA A KAN HUFFI A MUSULUNCI


Hudubar Masllacin Annabi na shaikh Muhammad Salah Al-budair 2-4-1441AH/29-11-2019AC

Hudubar farko
Ya ku musulmai!
Ku ji tsoron Allah, duk wanda ya ji tsoron Allah Matsayinsa zai daukaka har ya haura nisan taurari ya taka tsanin da zai kai shi kololuwa.(ku ji tsoron Allah zai ilmantar da ku,kuma Allah Masani ne ga dukkan komai).
 Fikihu guzuri ne na mai bautan Allah, kuma taimako ne ga mai neman shiriya. duk wanda fikihunsa ya karanta to aikinsa zai munana,  jahilcinsa kuma ya halaka shi  , idan hunturu ya zo  mutane sukan yi amfani da  huffi  da safa   da  mayafi  da abin dumama jiki .
Shafa akan huffi guda biyu abu ne da ya halatta ba mai musun haka sai dan bidi'a, mai sabawa jama'ar musulmai da malaman fikihu da hadisi.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya kasance yana shafa akan huffi, ya tabbata shafa akan safa daga wasu sashi na daga sahabbai Allah ya kara yarda a gare su .
 Halaccin shafa  a kan huffi biyu sauki ne  da kuma dadadawa da yalwatawa da  saukakawa   a cikin shari'a   sabo da bukatuwar  sanya shi   sannan kuma   za a hadu da wahala wurin  yawan cire shi.
Wanda ya ke son shafa a kan huffi to ya wajaba ya nemi sanin hukunce- hukuncensa  da  sanin tsawon  mudda (lokaci) da sifarsa da sharudan halaccinsa, da abin da ke warware shi  da hukuncinsa idan ya warware  da wanin haka na daga matsaloli .

YA KU MUSULMAI:
Huffi abu ne da aka sana'anta shi daga fata  ana ambaton shi  da huffi ne sabo da  rashin nauyinsa  ko kuma  kamar yadda  wasu suka ce '' sabo da hukunci ya yi sauki na in an sanya shi a yi shafa a madadin wankewa, ''
Amma ita safa aba ce da ke rufe kafa wanda aka sana'anta ta daga auduga ko gashi ko jawazkar gashi, ko kyalle, wanda aka fi sani a yau da Shurrab.
.
 An shardanta su zama suna da tsarki kuma sun suturce dukkan kafofi biyu da idon sawu, kuma su zama suna da kauri basu bayyana jiki, to idan huffi ya zama mai bayyana jiki, kuma danshin shafan da aka yi yana jika kafa, kuma yana bayyana launin fata, to bai halatta a yi shafa a kansa. idan ya kasance ba shara-shara ba ne kaurinsa bai barin ruwa ya jika kafa to ya halatta a yi shafa a kansa, a daya daga cikin zantuka biyu na malamai.
Kuma an shardanta ya sanya su bayan ya yi cikakken tsarki na ruwa, idan ya yi shafa akansu ba tare da yana da dahara cikakkiya na ruwa ba kafin sa su to alolarsa da sallarsa basu inganta ba.
Idan ya wanke daya daga cikin kafafuwarsa sa'anan ya sanya safa sannan ya wanke daya kafar kuma ya sanya ta cikin huffi ko safa to baya halatta ya shafa akanta a zance mafi inganci cikin maganganu biyu na malamai sabo da hadisin Abu bakrata -Allah ya kara yarda a gare shi-  ya zo cikin shi (Idan yayi tsarki sai ya sanya huffinsa biyu, to ya yi shafa a kansu) to harafin  Fa a hadidisin yana hukunta bin juna take hade da jerantawa : sabo da haka ya wajaba ya kammala tsarkinsa ya kuma kammala alolarsa ya kuma gama wanke kafafuwansa biyu sa'annan sai ya shigar da su cikin huffinsa biyu ko safarsa biyu.
Mazaunin gida na iya shafa akan hufi tsawon wuni da dare, matafiyi kuma zai iya shafa bisa huffi har tsawon kwanaki uku dare da wuninsu.
Muddar shafan na fara wa ne tun daga shafar farko bayan ya yi karamin hadasi a zance mafi inganci cikin maganganu biyu na malamai,
To zai yi ta shafa a kan su tun daga shafan farko bayan hadasi karami har zuwa misalin wannan lokaci na  washegari idan mazaunin gida ne. in kuma matafiyi ne to har zuwa kwatankwacin wannan lokaci na rana ta hudu.
Umar dan khaddabi Allah ya kara yarda a gare shi yace: zai shafa a kan su har zuwa kwatankwacin wannan sa'a  na wuninsa da darensa) Abdurrazak ya fitar da shi.
To idan Muddar ta kare to dahararsa ta warware a gun wasu malaman fikihu, wasu kuma suka ce: a'a, alolarsa bata warware ba ko da kuwa lokacin shafa ya kare ne a halin yana cikin salla to zai karasa sallarsa don karewar mudda baa sanya ta cikin masu warware alola, amma maganar farko ta fi zamewa Ahwad iyakantacciya don fita daga sabani ga sallar. Kiyayewa da yin taka tsantsan shi ya fi dacewa bisa a rasa tabbacin sharadi na inganci.
Idan ya yi hadasi bayan karewar muddar to ba zai yi shafa a kansu ba har sai ya cire su, ya yi cikakken tsarki sannan ya sa su.
Zai iya shafa cikin muddar muddin ba janaba ya yi ba, to idan ya yi janaba ta hanyar jima'i ko mafarki ko waninsu, to ba zai yi shafa akan su ba har sai ya wanke dukkan jikinsa, har da kafafuwarsa biyu, An karbo daga Safwan bin Assal Allah ya kara yarda a gare shi yace: (Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana umartanmu in mun kasance muna halin tafiya da kada mu cire huffinmu har tsawon kwanaki uku da dararrakinsu, sai dai don janaba, ba bahaya ko fitsari ko barci ba.
     Idan yayi shakku bisa muddar shafan to ba zai shafa ba tare da shakku, sabo da rashin tabbacin sharadin halaccin shafar.
  A duk lokacin da ya cire huffinsa biyu ko safanninsa biyu, ko kuma ya cire huffin daya daga cikin kafafuwa biyu to shafarsa ta warware alolarsa kuma ta baci, wanke kafafuwarsa ba zai isar masa ba da ya ci gaba da shafa a kansu, sai dai ya wajaba a gare shi ya sabonta tsarki na ruwa kafin ya halatta a gare shi ya yi shafa a kansu a   zance mafi inganci cikin maganganu biyu na malamai.
Don kiyayewa da iyakancewa ga salla, sabo da kuma mustahabbi ne fita daga sabani.

Ya ku masallata masu tsarki!
Idan har a huffi ko safa akwai huji ko yagewa ko kecewa wanda bigere na farilla ke bayyana to in har ya yi girma sosai to ba ya halatta a yi shafa a kansa sai in ya kasnce kadan ne. idan kecewar daga saman idon sawu ne to haka ba zai cutar da shi ba.
Abin da ya ke wajibi shine shafa a saman huffi ba kasansa ba, ko dunduniyarsa ko kwabrinsa ba,
Sifar shafar ita ce : ya dora jikakkun hannayensa yana mai bude yatsun hannayensa bisa yatsun kafarsa sai ya tafiyar da su tun daga saman  tsintsiyar kafar  har ya isa ga makyangyamarsa, ba sunna ba ne ya shafa kasansa ko dunduniyarsa ko kwabrinsa, a zance mafi inganci sabo da hadisin Aliyu Allah ya kara yarda a gare shi yace:(Da a ce addini ra'ayi ne da shafa kasan huffi shi ya fi dacewa a kan shafa samansa, hakika na ga Manzon Allah yana shafa bisa saman huffinsa) Abu Dawuda ne ya rawaito.
    Wanda ya bar shafar saman huffi to alolarsa bata inganta da ijma'in malamai, kuma ko da ya yi salla to sallar ta baci.
Wani mai waka ya ce : Mai barin shafan sama (huffi)  ka bata ,   zai yi shafa ne gaba daya dama akan dama hagu akan hagu  wasu suka ce :- sunna ne a gabatar  da dama .
       Imamu Ahmad  Allah ya mishi rahama ya ce:-
( Duk yanda ka yi ya halatta  da hanu daya ko hannaye biyu).
Ba mustahabbi ba ne maimaita  shafa  sabo da rashin zuwan hakan , ba a shafa akan huffi mai najasa .
     Ya ku masallata matsarkaka : wanda ya kasance matafiyi ya kuma fara shafan a muddar halin tafiya, ya yi shafa  kasa da  wuni da dare  sa'annan ya dawo garin  shi   zai cika wuni da dare.  idan ya yi shafan a halin tafiya wuni da dare  zuwa sama sa'annan ya dawo garin su zai cire safar sa biyu bisa wajabci, sabo da karewar lokacin shafa  da isowar sa zuwa garinsa, to idan kuma mazaunin gida ya yi shafa sai ya yi tafiya  kafin karewar muddar shafar  to sai ya cika shafa irin na matafiyi.
 ya ku masallata matsarkaka:
 Idan ya yi alola da ruwa cikakken alola sannan ya sanya safa  ba tare da yayi hadasi ba har ya sake dora wani safan daban  akan shi   to ya halatta yayi shafa akan safan saman ,  idan ya yi shafa akan safan saman sa'annan ya cire shi to alwalan sa ya baci .
   Idan ya yi alola cikakken alola da ruwa sannan ya sanya safansa , sannan ya yi hadasi sai kuma ya sanya safa a sama bayan yayi hadasin  to  baya halatta a gare shi ya yi shafa akan na saman,  sabo da ya sanya shi ne a halin bai da  tsarki , wato yana mai hadasi   to idan ya shigar da hanunsa   kasan safan saman   to ya halatta,  idan ya sanya safa a halin yana mai tsarki  na ruwa cikakke  sannan ya yi hadasi   ya kuma shafa akan shi  sa'annan ya sanya wani safan akan shi   to baya halatta yayi shafan akan  na saman  sabo da  ya sanya shi ne a halin yana da tsarki na shafa ba tsarki na ruwa ba.  wanda ya sanya safa a halin yana da tsarki na ruwa cikakke  sannan ya sanya  takalmin sau-ciki  mai tsawo a kan shi  ko but ko kambas, wanda duk sun rufe idon sawu, to zai iya shafa a kan su, idan ya cire  takalmin sau-ciki  mai tsawo  ko but ko kambas, bayan ya yi shafa a kan su to alolarsa ta baci.
 Idan ya sanya takalmi wato sau ciki wanda bai suturce idon sawu ba, to shafa a kanta ba zai isar mishi ba.
Idan a kasan akwai safa da ta rufe idon sawu kuma ya sanya ta da takalmin kafin ya yi hadasi zai shafa bisa takalmin da abin da ya bayyana na safanni biyu, saman gurin da ake wankewa ya kuma yi salla a cikinsu gaba daya, to idan ya cire takalman to alolarsa ta baci, sallarsa kuma bata inganta ba da safa kadai sabo da shafa ya ta'allaka da su.
 Allah ya sanya ni da ku cikin wadanda suke bautawa Allah bisa ilimi da basira.
Ina fadin abin da ku ke ji, ina nema mana gafaran Allah kuma ku nemi gafararsa, madallah da da rabauta irin na masu neman gafara.

Huduba ta biyu
Ya ku musulmai!
Ya wajaba ga mai salla ya rika bibiyar safarsa don tana da saurin yin wari, to a duk lokacin da safa ta yi wari ko doyi  to ya wajaba ya cire ta don kar ta cutar da mai salla ko musulmi da warinta.
Ko mutanen da sukan yi karin magana da warinta inda suka ce (ya fi wari a kan warin safa).sun yi zambo da shi sai dayan su yace :
Ibnu Umair ya yi yakin da ya bar suna  na yabo irin warin safa ketacciya.
Wani kuma ya ce :
Ki yi yabo a gare ni da abin da ki ka sani domin ni * ina yabon ki kamar yadda ake yiwa iskar safa.

Ya ku musulmai !
Muna nasiha da fadi da ya fi iyakancewa ga salla a babin shafa bisa huffi, idan ba wasu nassoshi na yanke ko bayyane, in har ba kunci  ko wahala mai tsanani da ke wajabta sauki wurin amfani da  Ahwad din sannan kuma in wurin amfani da Ahwad din akwai karin bauta da lada.
Hakika malaman fikihu sun nassanta cewa fita daga sabni abu ne mustahabbi.
Hakika Annabi ya yi amfani da Ihtiyadi  kuma ya yi hukunci da shi a waki'i da ya shahara
Na daga ciki akwai abin da Buhari da Muslim suka rawaito daga Anas dan Malik Allah ya kara yarda a gare shi yace:(Annabi ya wuce ga wani dabino ya fado sai yace : (Ba don ina tsoron kar ya zama cikin na sadaka ba da na ci shi).
  . Muna kira ga musulmi da zuciyarsa ta bude ta karbi sabani a irin wadannan mas'aloli, to in ba haka ba sai su zama sababi na sabani da kauracewa juna da fada da kiyayya da yankewa juna,   
. Ya ku musulmai ! ku godewa Allah bisa ni'imarsa mai yawa da falalarSa mai yawan zuba, ku tuna yadda mutane su ke tafiya huntaye ba takalma suna rasa abin jin dumi suna barci bisa duwatsu da safa, sannan kun wayi gari a bayan su kuna rayuwa mai yalwa.da gurin noma mai yawan alheri da 'ya'yan itace nunannu masu ganye, ku godewa Allah bisa yalwan falaloli da ni'imomi, to mai biyayya mai godiya yana ci gaba ne cikin falala da habaka da albarka, kuma mai sabo mai gujewa Allah na tafiya ne zuwa ga walakanci da talauci da halaka.
Ku yi salati da aminci ga Ahmad.