Hudubar Masllacin
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na shaikh Salahu Bin Muhammad Albudair
22/10/1439h
YA KU MUSULMAI:
Nisantar zama da masu
sabo da guje musu, da barin farfajiyan
su da kauracewa wuraren su da yanke abokantaka da su da gujewa tafiya
tare da su abu ne da ke nuna hangen
nesan mutum da kuma basirar sa .
Kubuta daga Laila da makwabciyarta *** shi ne kar ka bi ta kwari
daga cikin kauyukanta
Zukata na da rauni shubuhohi na yawan fizga,
fitintinu na tasowa , masu basira suna nisantar majalisan wadanda suke da
cutar zuci, masu bata imani kuma suna
kiyayan abokantaka da fitinannu fandararru daga sunna masu kaucewa duk wasu harka na musulunci da
kama kai da dabi'u irin na musulmai .
Idan ka kasance kai lafiyan ka kalau amma ka yi abokantaka da maara lafiya ka kasance aboki gare shi , to kai ma fa ka
zama mara lafiya .
Duk wanda ya zauna a
majalisan wasu mutane wadda a cikin shi akwai sabo ko bidi'a , to ya wajaba a
gare shi ya musu inkari da hikima tare da daddadan kalma da wa'azi mai kyau da kuma dalili wanda ke
bayyana gaskiya , mai gusar da shubuha,
idan har yana da ikon ya yi inkarin kuma bai yi inkarin ba to ya kasance
zai yi tarayya da su a alhaki,
idan ya gagara kuma yin inkari a gare su
to fa ya wajaba a gare shi da ya bar majalisar tasu , sabo da zaman tare
da cakudaidainiya na haifar da sabo da
kuma koyi da abun , da kuma
kyaliya ga munkari da kuma kauna a zuciya , kuma ta iya yiwuwa
ma fitinar ta fado a kan shi , Amru dan
Kais ya ce ( Kar ka zauna da
ma'abota bata sai zuciyarka ta bata ) Allah madaukakin sarki ya ce : (Alhali
hakika ya saukar a gare ku cikin alkur'ani cewa idan kun ji ayoyin Allah ana
kafirta da ita ana isgili da ita wato kur'ani , to, kada ku zauna tare da
kafiran nan sai sun kutsa cikin wani zancen ba wannan ba , hakika ku yayinnan
in kuka zauna tare da su kamar su kuke a cikin zunubi ) Imamu Addabari ya
ce : (A cikin wannan aya akwai nuni na
bayyane bisa ga hanin zama da ma'abota
bata , na ko wani iri a cikin su
'yan badi'a ne ko fasikai yayin
kutsawan su cikin batar su shaikhul Islam Ibn Taimiyya Allah ya yarda da shi ya
ce : (Baya halarta ga wani da ya halacci majalisan da ake barna bisa son
zabin shi ba tare da wani lalura ba
kamar yanda ya zo a hadisi Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi ya ce (duk wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira to
kada ya zauna a teburin da ake shan giya a kanta ) An daukaka kara zuwa ga Umar dan Abdul'aziz
game da wasu mutane da suke shan giya
sai ya bada umarni da a musu bulala sai a kace da shi lallai a cikin su
akwai mai azumi, sai ya ce ku fara da
shi , ase ba ku ji fadin Allah madaukakin sarki (Alhali hakika ya saukar a
gare ku cikin alkur'ani cewa idan kun ji ayoyin Allah ana kafirta da ita ana
isgili da ita wato kur'ani , to, kada ku zauna tare da kafiran nan sai sun
kutsa cikin wani zancen ba wannan ba , hakika ku yayinnan in kuka zauna tare da
su kamar su kuke a cikin zunubi) Umar dan Abdul-aziz Allah ya yarda da shi ya bayyana
cewa ( masu halartan wurin
sabo kamar masu aikata shi ne)
Sabo da haka ne malamai suke cewa idan aka gayyace shi zuwa ga walima wanda
cikin shi akwai barna kamar shan giya da goge baya halatta da ya je sabo da
Allah madaukakin sarki ya umurce mu da mu hana barna gwargwadon iyawa, duk
wanda ya je bisa zabin shi to hakika ya sabawa Allah da Manzon sa sabo da barin abin
da aka umarce shi da shi na daga kin
inkarin sa da hani game da shi . to idan
ya kasance hakan , to
ina ga wanda zai halarci majalisan shan giya bisa zabin sa ba tare da wata lalura ba kuma bai hana barnan ba kamar yanda Allah ya
umarce shi , to fa ya zama abokin tarayyan fasikai a fasikancin su , to kenan ya zama kamar su .
YA KU MUSULMAI :
Kar ku kara yawan
'yan bidi'a da barna da sabo
daidai da rana guda kar ku
kasance cikin tarun ma'abota fitina da barna .
An karbo daga Abdullahi Dan Abbas Allah
ya kara yarda a gare su cewa wasu mutane
cikin musulmai sun kasance tare da
mushrikai suna kara aukin mushrikai a zamanin Manzon Allah tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi , idan anyi harbi sai kifiya ya samu daya daga cikin su
ya kashe shi ko kuma ya soke shi sai Allah ya saukar da fadin sa ( Lallai wadan da mala'iku ke kashe
su mutane ne da suka zalunci kawunan su
) buhari ne ya fitar da shi .
Duk wanda ya halarci majalisai na barna domin debe kewa da su da farin ciki da aikin
su ko kuma ya yarda da aikin ko ya yi kira zuwa gare su ko ya karfafe su , ko
kuma ya karfafi shafi mai shubuha a yanar gizo da kuma shafuka wadda suke na barna da fasadi
da shafuka masu adawa da addinin
mu da akidar mu da
dabi'unmu da garinmu
ya kuma sanya musu alamar yarda
da karfafa to hakika ya kara aukin su ne
ya zama kuma cikin su .
HUDUBA TA BIYU
YA KU MUSULMAI:
Kar ku bayyana sabo kar
ku halatta abin da Allah ya
haramta kar ku rudu da fatawar masu sakaci da sassautawa da kuma
tsaka-tsakiyan masu da'awan fikihu , masu bada fatawa ba tare da yakini
ba ko kyautatawa ba suna karkata zuwa ga
daya bangare na bata da sunan sauki da
tsaka-tsaki da daidaito .
Duk wanda ya bayyana sabo ya aikata shi a fili to hakika ya fusata
Ubangijin shi kuma ya keta alfarmar shi
kuma ya raina ukubar sa ya cutar da bayin Allah Muminai to ku ji
tsoron Allah ya ma'abota musulunci kar ku rudu da ni'imomi da yalwa kada ku yi amfani da kyauta da aka baku
gurin aikata barna, kada ku bayyana sabo
alhali Allah ya muku ni'ima da rayuwa mai yalwa da abin sha mai kosarwa, ga mutane a kewayen ku suna halin bakar yunwa
na kashe su da kuma mutuwa mai muni .
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق