Hudubar Masallacin Annabi na
shaikh Abdulbari subaiti 11-4- 1439 AH
Hudubar farko
(Tsarki ya tabbata ga wanda yayi tafiyar dare da bawansa da dare daga
Masallaci mai alfarma zuwa masallacin Aksa wanda muka sanya albarka a
gefensa domin mu nuna masa daga Ayoyinmu ) Al'isra 1
Allah na girmama kan shi, kuma yana girmama sha'aninsa sabo da ikonsa da
kudurarsa ga abin da waninsa ba zai iya yi ba, kudurarsa ta bayyana a wannan
tafiya ta ban mamaki, da dauwamammiyar mu'ujiza da ta rikita kwakwale ta kere tunanin masu hankula, sabo da fitanta
daga abin da dan adam ya saba, wato tafiyan dare da aka yi da Manzon Allah.
Daga masallacin kaba Mai Alfarma zuwa Masallacin Aksa a wata tafiya manesaciya, da ya ga ayoyin
Allah masu girma da kuma kasaitan mulkin Ubangiji, sa'annan kuma ya dawo a
cikin wannan daren .
Haka ne sha'anin wata aya
ce mafi girma a cikin ayoyin Annabtaka , kuma
da mu'ujiza mafi daukaka cikinta
akwai hikimomi da hukunce-hukunce, da darusa masu girman fasaha tafiya ce da
Allah ya kebe masoyin shi da ita kuma
zababben shi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, daga Masallaci mai alfarma zuwa Baitil
Makdis gurbin Annabtaka , kuma daya daga cikin masallatayyan alkiblan
musulmai, domin daukaka kuma da girmama matsayin shi, da sabunta azama ga Annabin mu Muhammad da
tabbatar da shi , mu'ujiza ce rayayyiya
daga Ubangiji , ta dauki dan
Adam zuwa ga duniyan sama ta kuma dawo da shi zuwa ga doron kasa
, duniya gaba daya a damkan sa take ,
ba wani abin bautawa da gaskiya sai shi
, ba mu da wani Ubangiji koma bayan shi .
Girman Musulunci na
bayyana a Isra'i da aka yi, kuma lallai shi dinnan Addini ne wanda Allah ya
tattaro dukkan shari'o'i da su ka
gabata a cikin sa, kuma shi ne cikamaki
na dukkan shari'o'i, tafiyar ta dada
kulla dankon 'yan'uwantaka tsakanin
Annabawa , kuma sakon su duka guda daya ne , a duk lokacin da Annabi ya
sauka a sama sai a fiskance su da fadin
su , (maraba da dan'uwa na kwarai kuma Annabi ) Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi ya ce : ( Ni na fi dacewa
a cikin mutane da Isa Dan Maryam a duniya da lahira. Annabawa 'yan uwan
juna ne Uban su daya uwa kowa da na shi, kuma Addininsu guda ne,)
Dukkan Annabawa da sun riski Annabi Muhammad da ya wajaba a gare su da su yi imani da shi, su kuma bi
shi su taimaka mishi, kuma ya zama shi ne jagoran su abin bin su. Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce ga Umar Allah ya yarda da shi
:(Hakika na zo muku da ita fara fat a tsabtace, da musa ya kasance a raye da
ba abin da zai isan mishi sai dai ya bi ni) Abin da ke karfafa wannan shi ne fadin
Allah Madaukakin sarki :(Kuma a
lokacin da Allah ya riki alkawrin Annabawa : lalle ne ban baku wani abu ba daga littafi da hikima ,
sa'annan kuma wani Manzo ya je muku mai
gaskatawa ga abin da yake tare da ku , lalle ne za ku gaskata shi , kuma lalle ne za ku taimake shi ya ce :
''shin kun tabbatar kuma kun riki alkawari na a kan wannan a gare ku suka ce mun tabbatar '' ya ce :'' to ku yi
shaida kuma ni a tare da ku ina daga
masu shaida). Ali Imran 81
Annabawa sun hadu a bayan Annabi
ya limance su sallah a masallacin Aksa sabo da daukakansa da
darajarsa kuma shine mafificin Annabawa
kuma shugabansu kamar yadda ya zo a hadisin Isra'i wanda Annabi yake sifanta
tafiyar da cewa (sai ga Musa ya na
tsaye yana sallah shi mutum ne mai karamin ruwa dunkulalle kamar irin mutanen
kabilar Shanu'a, sai ga Isa dan Maryam shi ma yana tsaye yana sallah wanda ya
fi kama da shi cikin mutane shine Urwa dan Mas'ud Assakafi, sai ga Ibrahim yana
tsaye yana sallah sahibinku ne ya fi kama da shi a cikin mutane – wato yana
nufin kansa- sai na tsaida sallah na limance su)
Wannan kyakkyawan halin na ingiza masu da'awar gaskiya da su yi koyi da
Annabawa amincin Allah ya tabbata a gare su
su hadu akan biyayya da da'a da tsoron Allah su yi watsi da duk wasu
sabuba na sabani da rarrabuwa.
Kudura na ban mamaki da Annabi ya yi amfani da shi na tafiya daga
masallacin ka'aba zuwa masallacin Aksa
ya yi kama da saurin yaduwar musulunci da wanzuwarsa a doron kasa,Addini
ne da zai cika duniya ya keta dukkan iyakoki da kofofi, Musulunci ya yadu a
zamanin farko wanda yana kusa da ace mu'ujiza ne, sai gashi a wannan zamanin
namu ya sake yaduwa don ya gaskata mu'ujiza daga cikin mu'ujizozin Manzon Allah,
wanda yace ga Adiyyu Dan Hatim : (Na rantse da wanda rai na ke hanunsa Allah
zai cika wannan addini har mace ta yi tafiya daga garin Hira har ta je ta yi
dawafi a ka'aba ba tare da wani
makusanci ba). Ya kuma ce :(Lalle Allah ya dunkule kasa ya tattaro min
ita har na ga gabashinta da yammacinta kuma lalle mulkin al'uma ta zai kai duk
inda aka tattaro min na daga gare ta). Ya ce (wannan addini zai isa ga
duk inda dare da wuni ya kai,har ya zama ba wani gida a birni ko kauye sai
musulunci ya shiga da daukakan mai daukaka ko da kaskancin makaskanci,daukaka
ce da Allah zai daukaka musulunci da
musulmai da ita da kuma
kaskanci da zai kaskantar da shirka da masu shirka da ita ).
Manzon Allah ya yi gaskiya domin lallai musulunci a yau shi ne addini ne
da ya fi saurin yaduwa , a tsawon kasa
da fadin ta , tare da shaidar
makiya da kuma rubuce-rubucen su.
Karfin yaduwan
musulunci ya samu ne sakamakon sauki
irin na shari'ar sa da saukakawa ga
hukunce-hukuncen sa, da kuma tsarin sa mai adalci , da yalwar rahamar
sa, wanda ta dulmuye har makiya domin shi
baya aikata aiki na halakarwa ko
zalunci , ko kuma aikin kare –dangi ko
kuma ramuwar gayya,
Allah madaukakin sarki ya ce : ( Ba mu turo ka ba , face rahama ga
talikai ) kuma Allah madaukakin
sarki ya ce : ( Lalle ne wannan
Alkur'ani yana yana shiryarwa ga ( halayen ) wadanda suke mafi daidaita ).
Suratul Isra'I 9
Anyi mi'iraji da Annabi
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi zuwa sammai madaukaka
ya riski wadannan darajoji masu girma sabo da irin
kyawawan halaye da bauta da ke
tattare da shi , sabo da daukaka irin
nata, Ubangiji ya siffanta shi da
ita a wurin mafi daukaka da matsayi mafi
girma , Allah madaukakin sarki ya ce (Tsarki ya tabbata ga wanda ya yi tafiyan dare
da bawan sa . Isra'i Aya 1).
Muna karantawa a
tafiyan isra'i da mi'iraji alaka mai
karfi da ke kulle tsakanin masallacin Haram (Kaba) da wannan masallacin
Annabi da masallacin Aksa , cikin
wannan akwai nuni ga al'uma kan kar ta yi sakaci game da sha'anin masallacin Aksa sabo da matsayin shi da tsarkin shi da
albarkan shi .
Abu Zarri Allah ya kara yarda a
gare shi ya ce : ( na ce ya Manzon Allah ! wani masallacin ne na farkon da aka gina a doron kasa sai ya ce: ''Masallacin Ka'aba sai na ce sai wanne sai ya ce masallacin Aksa
, sai na ce nawa ne ratan da ke
tsakanin su sai ya ce : '' shekaru
arba'in ''.)
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
ya ce : ( Ba a nika gari sai ga masallatayya guda uku Masallacin Ka'aba da
Masallacin Manzon Allah da masallacin
Aksa ) Buhari ne ya rawaito shi.
Masallacin Aksa da tarihin shi da falalan shi yana tada wani
kaimi na hadin kai tsakanin Musulmai ,
kuma yana karfafa dankon 'yan
uwantaka domin bashi kariya da tsarkake
shi daga kazantan shirka da bata . Batun masallacin Aksa
za ta wanzu a zukatan
mabiya wannan Addinin ba wani
abu da zai girgiza kudurin mu kan
haka sabo da musun mai musu ko kagen masu ketare iyaka.
Isra'i da mi'iraji na
koyar da mu cewa gaskiya a bayyane take , kuma za a bata kariya duk yadda
farfagandan masu karya ta
kasaita ko ta yawaita , to karya ginshikin ta na girgiza a kan kanshi
kuma yana da rauni kuma yana da saurin halaka
ginin shi na lalacewa Allah
madaukakin sarki ya ce : (A'a muna jifa da gaskiya a kan karya sai ta darkake ta , sai ga ta halakakka ) Sura
Al-Anbiya Aya na 18
Annabi ya shiga garin Makka kewaye da dakin Ka'aba
akwai gumaka dari uku da sittin (360) sai ya
rinka sukan su da sanda a hanun
shi yana cewa : ( Kuma ka ce gaskiya
ta zo karya ta lalace , lallai karya ta
kasance lalatacciya) . Suratul
Isra'I Aya na 81
Daga cikin mu'ujizozin
Isra'i ; za mu tsinkayi wani darasi mai nauyi da fasaha wanda hakan zai bayyana cikin kasancewan
Allah na tare da bayinsa da taimaka musu da samun kulawansa daga duk wanda ya yi riko da igiyarsa kuma da shiryarwarsa , kasancewa tare da su bangaren kiyayewa da
datarwa da taimako da karfafa da kuma basu
matsayi, wannan shine zai magance cutan masu tsarkin niyya masu ribadi
masu bada kan su don kariya ga musulunci
da musulmai .
Kuma masu dako
da kulla makirci su sani ikon
Allah madaukaki ya kere duk wasu sabuba don ya
bada taimako ga muminai ko da sun kasance 'yan kadan, sai Allah ya bada nasara
ga muminai wadan da suka aminta da alkawarin shi Allah madaukakin sarki ya ce : ( Da yawa kungiya kadan ta rinjayi wata kungiya mai yawa da izinin Allah ,
kuma Allah yana tare da
masu hakuri) sura Al-bakara aya 249 Ya ce: ( To! Lalle ne ,
taimakon Allah yana kusa !) Al-bakara aya 214
Umar Dan Khaddabi yana cewa a wasiyyar sa da ya yi ga Sa'ad Dan Abi wakkas Allah ya yarda da su ( Lallai ku dinnan ba a baku nasara a kan
makiyan ku sakamakon karfin tattali da shiri da
kuke da shi sai dai ana baku
nasara ne a kan su sabo da da'an ku ga Ubangijin ku da kuma sabon su a gare shi,
idan kun yi dai-dai da su a sabo sai su
yi galaba a kan ku da karfin shiri da tattali ) .
To idan kudus da masallacin Aksa abin kulawa ne da muhimmanci ga zukatan musulmai to fa ya wajaba a gare su
kankan da kai zuwa ga Allah da ya kiyaye
shi daga dukkan wata kazantarwa, kuma su yi adu'a ga mutanen Falastin kan tabbatuwa da nasara , Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce : ( Ba wani
musulmi da zai roki Allah madaukakin sarki da wani roko face sai Allah ya amsa
mishi ita, ko ya tunkude mishi wata mummuna kwatankwacin ta , muddin bai roki
wani abu na laifi ba ko yanke zumunci , sai
wani mutum ya ce a cikin mutanen : '' to, indai haka ne za mu yawaita
adu'a'' , sai Annabi ya ce : abin da ke
gun Allah shi ne mafi yawa .)
HUDUBA TA BIYU:
Abubakar siddik yana da wani
maukifi (matsaya) wanda tarihi ya adana, wanda
ke cike da abin lura , mushirikai sun zo wa Abubakar a wayan garin daren isra'I , don su bashi labari cewa abokin shi na raya cewa anyi tafiyan dare
da shi daga Makka zuwa baitil makdis
sannan ya dawo a wannan daren, a zaton su cewa zai karyata sahibin nashi
(Annabi) sai ya fadi kalmarsa mashahuriya
wacce ta zama ka'ida da aka karbo
( in har ya kasance ya fada to hakika ya yi gaskiya).
Mushrikai su kansu sun san cewa a
tarihin shi mutum ne mai gaskiya wanda baya karya kuma
abin gaskatawa ne wanda ba a karyata shi wannan shi ne zurfin gaskatawa daga zuciyan
Abubakar ya samu ne a dalilin imani , a
lokacin da imani yake karkadawa yakini yake girgiza a wannan zamanin
na mu sai a samu wasu daga cikin mutanen
mu wanda za su rika sanya shakku a addini
kuma suna ja da abubuwan da suke tabbatattu a
addini , kuma suna fada da nassoshi na
alkur'ani suna karya ta sunna da hadisan
Manzon Allah su sanya hankulansu su yi amfani da karamin kwakwalwar su , su za su yi hukunci akan nassoshi na kur'ani da hadisi, amma muminai wadan da imani ya zauna a cikin
zukatar su , kuma zuciyan su ta natsu da shi
to, misalin su shi ne fadin Imamu shafi'I Allah ya mishi rahama ( Mun yi imani da Allah da abin da ya zo daga
Allah bisa nufin Allah
kuma munyi imani da Manzon Allah da abin da ya zo daga Manzon Allah , bisa muradin Manzon Allah)
.