الجمعة، 20 أكتوبر 2017

SON KASA A MUSULUNCI

HUDUBAR JUMA'A  A  MASALLACIN ANNABI  NA SHAIK HUSAINI AL-ASSHAIKH  30-1-1439 AH
HUDUBAR  FARKO
     Na daga cikin abu mafi tsada a gun masu hankali akwai son garin da aka haife su cikinta suka rayu suka ci daga albarkatun da Allah ya sanya cikinta.
Lalle wannan wani abu ne da shariar musulunci ta tabbatar da ita, kuma ta iyakance ta da kulawa da wasu hakkoki da wajibabbu  don kulawa da maslahar addini da duniya gaba daya.
Hakika son kasa da rai abu ne da ke hade kamar yadda kur'ani ya siffanta su, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Kuma da dai lalle mu mun wajabta musu cewa "Ku kashe kanku ko ku fita daga gidajenku" da ba za su aikata shi ba sai kadan daga gare su)
Kuma Allah Madaukakin sarki yace : (Allah ba ya hana ku daga wadan da basu yake ku ba sabo da addini  basu fitar da ku daga gidajen ku ba ga ku kyautata musu ku yi musu adalci.)
 Ibnul Arabi ya na magana kan kissar Musa Amincin Allah ya tabbata a gare shi da komowa  ga iyalansa sai yace : " A dawo wa ga kasa  akwai  wabcewa daga gumurzu da tsallake rijiya da baya da samun kwanciyan hankali.
Batun son kasa da kaunar gida ya sa Annabi ke cewa Makka  yayin kaurarsa  a halin bakin ciki da nuna tsananin kauna :(Abin mamaki da dadin ka (garin Makka) da soyuwarka  gare ni! ba don mutanen garin sun kore ni ba da ba zan zauna a waninka ba.) Tirmizi ne ya rawaito.
Haka kuma yayin da Allah ya nufe shi da kauratowa , ya wayi gari Madina ya zama garinsa wurin rayuwar sa sakonsa ya haskaka garin  sai ya ce : (Ya Allah ka sanya mana kaunar Madina kamar yadda ka sanya kaunar Makka a gare mu ko fiye da haka.)Bukhari ne ya rawaito.
A cikin siffanta zababbun halittu bayan Manzanni  Allah Madaukakin Sarki ya bayyana halin sahabbai da suka yi hijira daga garin Makka zuwa Madina sai ya ce : ( Ku yi mamaki ) Ga matalauta masu hijira wadanda aka fitar daga gidajensu da dukiyoyinsu, suna neman falala daga Allah da yardarsa, kuma suna taimakon Allah da Manzonsa, wadannan su ne masu gaskiya.)
Ya ku Musulmi!
     Na daga cikin ni'ima mafi girma ga bawa samun zaman lafiya a garinsa cikin aminci tare da iyalansa, yana mai bautawa Ubangijinsa, ya na biyayya ga Mahaliccinsa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ("Wanda ya wayi-gari a cikinku da aminci ga ransa, ko a cikin jama'arsa da iyalansa da dukiyarsa, ya wayi-gari da lafiya a cikin jikinsa, ya wayi-gari a wurinsa akwai abincin yininsa, to kamar an hada masa duniya ne gabadayanta".
Ya ku Musulmai ! Lalle son kasa a musulunci na nufin kiyaye mutuncin kasar da kyawawan dabiu da tsarkakan ginshikanta, wato yana nufin taimakekeniya gurin janyo dukkan alheri da gyaran kasa da mutanenta, da tunkude dukkan wata barna da wahala ga kasar da mazaunanta, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Ku ma ku taimaki juna a kan aikin kwarai da takawa).
Lalle son kasa na nufin ko wani daidaiku ya rayu da 'yan uwansa cikin kauna da soyayya da tausayi da jinkai, don amsa kiran Allah madaukaki  (Lalle muminai 'yan uwan juna ne) da kuma fadin Allah mai tsarki (kuma mumunai maza da mumunai mata sashensu majibincin sashe ne , suna umurni  da alheri  kuma suna hani daga abin da ba a so kuma suna tsayar da salla kuma suna bayar da zakka kuma suna da'a ga Allah da manzonsa wadannan Allah zai yi musu rahama .) kuma manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi  ya ce :( Misalin Muminai cikin kaunar juna, da tausayin juna da tausasawa juna, kamar Misalin jiki daya ne. Idan wani sashin jiki babu lafiya sai sauran jikin su kama zazzabi da kasa barci).
Lalle kauna ne da ke sanya wasiya da biyayya da tsoron Allah  da yin nasiha da juna  cikin abin da akwai alheri ga kasa da raya ta. Allah Madaukakin sarki ya ce : ( Lalle mutum na cikin hasara. Sai wadanda suka yi imani kuma suka yi aiki na kwarai kuma suka yi suka yi wa juna wasiyya da bin gaskiya, kuma suka yi wasiya wa juna da yin hakuri)
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Addini nasiha ce, ya fade ta har sau uku, sai muka ce: ga wa nene ya Manzon Allah? Sai yace : Nasiha ga Allah da Manzonsa da littafinsa da jagorin musulmai da sauran jamaa)
Lalle shanin son kasa abu ne da ke sanya bada kariya ga kasar da abubuwan cikinta masu kima, kowa gwargwadon karfinsa da yadda zai iya kuma gwargwadon nauyin da ke kansa.    Zuwa ga wannan ne alkur'ani  ke nu ni a fadin sa Allah mabuwayi da daukaka: ( Sai suka ce mai zai hana mu yi yaki a tafarkin Allah a halin an fitar da mu da 'yayanmu daga gidajenmu ?)
Kuma zuwa gare shi ne fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi     na cewa : ( Duk  wanda aka kashe shi yana kokarin kare dukiyar shi to, shi shahidi ne)
 Wannan shi ne son kasa wanda ke lizimtawa daidaikun al'uman da su shirya  su tari duk wani shirin da zai taba  dukiyar kasa da maslahohinta na addini da na duniya ,  ya kuma sosa amincinta da zaman lafiyanta , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Duk wanda ya ga abin ki , to, ya canza shi da hanunsa , to, idan ba zai iya ba to,  da harshen sa , to, idan bai iya ba  da zuciyar sa ).
 Ba makawa  yana daga cikin abubuwa da aka ki  akwai shirya makirci don taba akidar kasar  da amincin ta  da zaman lafiyanta  ko kuma a taba dukiyanta da albarkatunta ,
son da Musulmi ya ke yiwa kasan sa yana sanya shi ya lizimci kiyaye dukkan wani kadarorin kasar sa da albarkatu kuma ya yi kokari domin samun aminci cikin abubuwan da yake samu kamar yanda ya ke son abubuwa da yake na maslahar kansa, da amfanin sa na karan kansa , :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce  :( Imanin dayanku ba zai cika ba har sai ya so wa dan uwan sa abinda ya so wa kansa )
YA 'YAN UWA MUSULMAI :
Yana daga cikin abinda yake  nuna kauna ga kasa a musulunci  ko wani daidaiku a cikin mutanen ta su kame daga cutar da ita ,  da kuma mazaunanta , ya zo a cikin sunna ingancecciya na daga cikin hakkokin hanya   a  gusar  da  kazanta  daga gare ta, ya zo a hadisai ingantattu daga Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi game da sanya kazanta  a farfajiyan mutane ko kan hanya ko wurin harkokin su,  to Musulmi a na bukatar  da  ya kasance  a cikin garin sa da iyalan sa  kamar yanda Annabi ya yi nusar a fadin sa  :(  Musulmi shi ne wanda musulmai suka kubuta daga sharrin harshen sa  da na hanunsa)
 YA KU MUSULMAI:
      Na daga cikin hakkoki na kasa da mutanen ta  a kan daidaiku,  da su kiyaye daga ha'intar kasan da kuma 'ya'yanta , da kuma ita al'umar kanta , lallai na daga  cikin mafi munin sifa na ha'inci  a kwai ribatar dama da ma'aikata su ke yi da masu matsayi don maslahan kan su , su fifita maslahar kan su akan maslahar al'uma , na daga cikin mafi munin barna akwai barnatar da dukiya , wanda shari'a ta zo da hani mai karfi akan hakan
 Allah madaukakin sarki ya ce :( Duk wanda ya ci gululi zai  je da abinda ya ci na gululin  a ranar kiyama )
 Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Lalle wasu mutane  suna kutsawa a cikin dukiyar Allah ba tare da hakki ba , to, su na da wuta  a ranar alkiyama )
  YA KU MUSULMAI:
 Daga cikin hakkokin kasa a kanmu akwai taimakekeniya tare da  jagorori da Allah ya basu rikon wannan kasa , tare da gudanar da ita kasar,  a  yi gaskiya a gare su a bayyane da boye ,  kuma mu san cewa yi musu biyayya a abin da ba sabon Allah ba wajibi ne daga wajibabbu na shari'a. Kuma mu yi kwadayin hada kayin al'umarta da dunkulewar ta , ko wanne ya zama a shirye yake don kare kasar sa daga dukkan  wani makirci da ake shiryawa kasa , da kuma dukkan hanyoyi  da za su  iya taba amincin ta da kuma amanarta .


HUDUBA TA BIYU
      Tunda  ya tabbata  cewa  son kasa abu ne na dabi'a wacce shari'a ta tabbatar da shi to ta yaya kuma kasar da ta tattaro masallatai biyu masu alfarma a cikin ta da  kuma dakuna masu daraja  lalle wannan shi ne kasa mai tsarki wanda a ka gina ta akan musulunci, a manhajanta da  kuma kundin tsarin mulkin ta bisa  akida na tauhidi ciki da waje , alkalan ta na hukunci na shari'a , kotunan ta  na hukunci da shari'a mai tsarki , gari ne da ma'abotanta sun  rayu a kan sunna da girmamata , da kuma kore bidi'a da 'yan kanzaginta  .
To ya wajaba ga mutanen ta a hali suna samun irin wadannan ni'ima mai yawa da su yi taimakekeniya  bisa ga aminci da zaman lafiya , kuma su yi kwanton  dukkan wani   mai son rusa kasa , ko kuma son mai da dabi'unta irin na yammacin turai musamman a irin wannan  mawuyacin  yanayi , wanda  wata guguwa ke girgiza duniya gaba daya .
Ku kiyaye Allah ya kula ku bisa tabbatuwa cikin aminci, ya kuma bawa garin ku kariya  , daga wadannan fitintinu masu yawa.
 Ku kiyaye dukkan wasu kiraye –kiraye na sharri da barna  da kuma  hanyoyin da zai kawo rarrabuwar kai da raba tsakani .
      Ku kiyaye ya  matasa na wannan gari bisa abin da wannan gari ta saba, na tafiya a kan manhaji na sunna bayyananne tacecce, tsarkakekken da baya ketare iyaka ko wuce gona da iri ,  ba a san shi da wani manhaji ba na bidi'a , ko wani fandararren tunani , na daga cikin abin da zai sabawa  abin da aka gina wannan gari a kai  na kyawawan dabi'u na Musulunci , da halaye na shari'a , da kuma manhaja da mutane suka rayu a kai tsintsiya madaurin ki daya ,kuna masu  taimakekeniya akan dukkan wani alheri , masu haduwa akan  abu mai amfani  ga maslaha ga kasa da kuma bayi , irin taimakekeniya na gaskiya tare da iklasi ga  jagororin ta . Don cimma kyawawan manufofi da ake fata , kuma a tunkude duk barna da ake hasashe, kar ku canza abinda Allah ya ni'imta ku da shi har Allah ya canza muku yanayin ku , kamar yanda Allah madaukakin sarki ya ce  : (  Kuma Allah ya buga misali wata Alkarya ta kasance amintacciya  natsatssiya arzikinta yana je mata a wadace daga ko wani wuri sai ta kafurta da ni'imomin Allah , sabo da haka Allah ya dandana mata tufafin yunwa da tsoro sabo da abin da suka kasance suna sana'antawa ).  
      
                 




ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق