الجمعة، 17 نوفمبر 2017

BURI A RAYUWA

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI NA SHAIK ABDULBARI   ATHUBAITI NA 28- 2 1439.
     HUDUBAR FARKO :
BAYAN HAKA:
Allah  madaukakin sarki  ya hore wannan duniya mai fadi ya sanya ta  farfajiya na burace-buracen Dan adam wanda ba sa yankewa, mutane  wasu a cikinta  na gajarta buri wasu kuma na tsawaitawa  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :  ( Da dan adam ya kasance yana da kwari na dabino da ya yi fatan ya sake samun wani  kamar sa   sa'annan kuma ya sake samun  wani kamar sa har ma ya yi fatan ya  zama yana da  kwarurruka,   ba abin da yake cika cikin Dan adam sai turbaya )  Ibn Hibbana ya rawaito shi a sahihin shi.
                   Dukkan wani buri da ake fatan aikata aikin alheri  abun yabo ne, duk wani buri kuma da ake ja da abin da Allah ya kaddara  ko kuma  ayi fatan samun abin da ba zai yiwu ba to wannan abin zargi ne ,   shi buri yana nuni ne da irin abin da mutum ke dauke da shi a zuciyar sa  , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce  : (  Kuma rayi yana buri  kuma yakan yi sha'awa).   Akwai wanda yake wulgawa da burin sa  zuwa ga  izza da daukaka   wani kuma  kan jefa burin sa zuwa ga cikin rami .
                   Ma'abota himma  da azama  suna fadada burin su  kuma su kawata rayuwan su da shi  ga Umar Dan Khaddabi  yana zaune cikin  mutanen shi wata  rana sai ya ce da su  kowa ya fadi burinsa ,  sai wani mutumi ya ce : '' ina burin ace  wannan gidan gaba daya a cike da zinari na ciyar da shi a tafarkin   Allah   ''   ,  sai  ya sake cewa:   '' kowa ya fadi burinsa'' sai wani mutumi ya sake cewa : '' ina fata a ce wannan gidan  a cike yake da lu'u-lu'u  , da Zubarjadi ,  da Jauhari na ciyar da shi a tafarkin Allah kuma na  yi sadaka da shi ,  sannan sai Umar ya ce  : '' ku fadi burinku ''  sai suka ce :  '' to, kai me kake gani ya Amiral muminin ''  sai Umar ya ce : ''  Ina fata  da ace wannan gidan a cike yake da mazaje  irin su Abu Ubaida Dan Jarrah  da Mu'azu Dan Jabal da Salim  Maula Abi Huzaifa  da  Huzaifatu Dan Yaman .
                      Kyakkyawan buri na daga cikin kofofi ne na lada mai girma , Abu Kabshata Al anmari ya rawaito daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata  a gare shi cewa  ya  ambaci wasu mazaje guda hudu:  (  Mutumin da Allah ya bashi dukiya da ilimi yana aiki da  ilimin sa  a cikin dukiyar sa yana ciyar da ita  bisa hakkin ta , da kuma mutumin da Allah ya bashi ilimi bai bashi dukiya ba ,  to, sai yana cewa ina ma da ina da irin wannan  ( dukiyar) sai na yi aiki da ita kamar yanda  yake aiki da shi    Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : '' Duk ladan su iri daya ne da kuma mutumin da Allah ya bashi dukiya amma bai bashi ilimi ba sai yana ta kwamacala a cikin dukiyar tasa  yana ciyar da ita ba a cikin hakkinta ba , da kuma mutumin da Allah bai bashi ilimi ba bai bashi dukiya ba  to amma yana cewa ina ma da ina da irin dukiyar da wane yake da shi    na yi irin aikin da yake yi da shi  ,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce : ''  Dukan su biyu suna daidai a alhaki '').  Ibn Maja ne ya  rawaito shi.
             Burace-burace shi kadan shi ba yi da kima matukar bai hadu da aiki na kwarai ba tare kuma da kyakkyawar niyya na gaskiya  , da kuma bin koyarwan Annabi  tare  da kuma juriya   Allah  madaukakin sarki ya ce : (  Ku yi gaggawa zuwa ga neman gafara daga  Ubangijin ku) shi burace-burace wani nau'I ne na addu'a wanda ke tabbatuwa idan an amsa shi,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (  Idan dayan ku zai yi adu'a  to, ya roka da babban masaki , domin Ubangijin shi  yake tambaya) Haithami ya rawaito
Albani ya ce marawaita hadisan amintattu ne kuma marawata ne na sahihi.
        Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (  idan dayan ku zai yi buri to, ya yi dubi zuwa ga abin da zai burata  ,  domin bai sani ba me za a rubuta mishi na daga burin nasa   . Ahmad ne ya  rawaito  da isnadi ingantacce .
     Kamar yan da mai hankali ba zai yi fatan   fitintinu ba ko haduwa da makiya , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce  : (   kar ku yi fatan haduwa da makiya , ku roki Allah  samun sauki  idan kun hadu da su to ku yi hakuri ).
            Mus'ab da Urwa da Abdullahi dan Zubair da Abdullahi dan Umar suka hadu a Hijir ,  sai suka ce kowa ya ambaci burinsa , sai Abdullahi dan Zubair ya ce  ni buri na in samu kalifanci , Urwa kuma ya ce : '' ni kuwa buri na a dauki ilimi daga gare ni , shi kuma Mus'ab sai ya ce na ga na rike Mulkin iraki na hada tsakanin Aisha 'yar Dalha da sukaina 'yar Husain , shi kuma Abdullahi Dan Umar ya ce ni kuma buri na in samu gafara , dukkan su kuma sai suka samu abin da suka nema,  ta iya yiwuwa Ibn Umar din ma an gafarta mishi .
       Umar dan Abdul'aziz Allah ya mishi  rahama  ya kasance yana da himma madaukakiya  wanda kuma ya cimmata da falalan Allah  , ana kuma fatan dayan ma ya cimmata   yana cewa ina da rayi mai yawan shauki ya yi shaukin Fadimatu 'yar Abdulmalik  kuma na aure ta,  na yi shaukin zama gwamna kuma na zama,  na yi shaukin kalifanci(shugaban kasa)  kuma na riske ta , kuma na bukaci Aljanna kuma ina  fatan na same ta in Allah mai girma da daukaka ya so.''
       Musulunci na kira zuwa ga yin fatan alheri da yada fata nagari da rayuwa, ba ya kira zuwa ga mutuwa da abu mara kyau, bai dacewa da shi munanan fata da neman mutuwa ko da fitinu sun tsananta, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Kada dayanku ya yi fatan mutuwa sakamakon wani cuta da ya same shi, in har ba makawa sai ya yi to ya ce : Ya Allah ka raya ni muddin rayuwar  ta kasance alheri a gare ni, kuma ka kashe ni idan mutuwa ta fi alheri gare ni) Buhari da Muslim ne suka rawaito.           
         Yin fata nagari na nuni ne ga kyautata zaton bawa  ga Ubangijinsa, ya zo cikin Hadisin Kudsi  : ''  Ni ina gun da bawa na ya zace ni, to , ya zaci  duk abin da ya so game da ni '' ibn Hibbana ya rawaito shi   a sahihin sa .  Wato ni  ina da ikon  na aikata da bawa na  duk abin da ya zaci zan aikata da shi . To idan bawa ya kyautata zato ga Ubangijin sa , sai hakan ya juyo  cikin  Burin sa sai ya zame madaukaki  a kima da kuma manufa .
            Mai hankali  yana saka burace –buracen sa ne tare da ,  jin ni'imar Allah a gare shi ba tare da ya yi hasada ga 'yan uwan sa ba , ko fatan abin hanun su ba  . Allah madaukakin sarki ya ce :   (kuma kada ku yi burin abin da Allah ya fifita shashenku da shi a kan sashe.)
Musulmi na da masaniyar cewa cin ma buri na hanun Allah ne shi kadansa, sabo da haka ba zai yi raki ko yayi bakin ciki ba sabo da rasa cin ma burinsa da ya ke fata ba,  Alheri na cikin zabin Allah   da kuma godiyan bawa ga Ubangijin sa a ko wani hali Allah madaukakin sarki ya ce :  (Akwai fatar  cewa ku ki wani abu alhali  shi ne mafi alheri   a gare ku kuma akwai fatar cewa kuna son wani abu alhali kuwa shi ne mafi sharri a gare ku ,  kuma   Allah ne  yake sani kuma ku ba ku sani ba ) .
          Iblisu shi ne tushen burace-burace mara kan gado , kuma ya yi alkawarin  ya nitsar da bayin Allah cikin kogin burace –burace na karya  na  jin dadin gaggawa ( duniya ) da kuma sa'ada mara tabbas  kamar yanda yake kawatawa dan Adam mummunan aikin shi sai ya gan shi kyakkyawa  Allah madaukakin sarki ya ce : ( Kuma wanda ya riki shaidan majibinci baicin Allah , to , hakika ya yi hasara bayyananniya yana yi musu alkawari  kuma yana sanya musu guri alhali  shaidan baya yi musu wa'adin komai face  rudi .)
                               Idan burace-buracen mutum ya gajarta bisa ga kyala-kyalan duniya,  ya zama babu na lahira  to hakika ya kauce hanya ya bar tafarki mikakke  Allah madaukakin sarki ya ce : (  wanda  ya kasance yana nufin duniya     sai mu gaggauta abin da muka ga  dama ga wanda muka ga dama  a cikin ta sannan mu sanya jahannama gare shi   a lahira  ya shige shi abin zargi , abin korewa.  wanda yake nufin lahira da aikin sa  ya yi kokari ya aikata aiki irin nata   a gare ta alhali shi yana mai bada gaskiya ga Ubangiji ,  to, wadancannin ka  aikin su ya kasance abin godewa) .
                                   Wanda burace-buracen sa ke nitso a kogin mafarkai yana fadake ko yana bacci ba tare da wani aiki ba, ya kewaye jikin sa da kasala , to ba zai tsinkaya ba sai kawalwainiya, an karbo daga Anas Dan Malik Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce   : (  Mai wayo shi ne wan da ya yi wa  kan sa hisabi ya yi kuma aiki domin bayan mutuwa ,  shi kuma gajiyayye shi ne wanda ransa ya bi abin da ya ke so ya yi kuma gurace-gurace  a wurin  Allah ).
                        Wanda ya bi hanyoyin da aka haramta domin cimma burace-buracen sa ta  hanyar komawa  zuwa ga matsafa ,  ko 'yan  siddabaru , to hakika ya zalunci kansa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Duk wanda ya je wurin boka ko matsafi ya yarda da abinda ya ce to, hakika ya kafurce da abin da aka saukarwa  Muhammadu ). Dabarani ne ya rawaito Ibn Hajar kuma ya hassana isnadin sa.
                  HUDUBA TA BIYU
A  cikin kaburbura wanda ake fara rayuwan barzaku  akan samu gurace-gurace masu tsananin kunci  , burin mumini a kabarin sa shi ne kiyama ta tsaya , sabo da irin abin da ya ke gani kuma yake sauraro  na daga ni'ima da farin ciki ,  amma  kafuri burin sa kada alkiyama ta tsaya sabo da abin da yake gani da daga azaba mai tsanani .
         Mamaci na fatan sake dawowa duniya  don riskan abin da ya tsere mishi na daga da'a  ya samu ya yi sallah ko da raka'a biyu  ne  Annabi ya wuce wani kabari sai ya ce : ( Wane ne ma'aboci wannan kabari ? sai suka ce wane ne , sai ya ce  : '' raka'a biyu ya fi soyuwa ga wannan  (mutumin kabarin ) akan duk sauran abin duniya) .    
        Matattu na  fatan komowa  duniya domin su yi sadaka  kuma su ambaci Allah  ko da da tasbihi guda ne , ko  da hailala guda ne ,  Allah madaukakin sarki ya ce : (  KU CIYAR DAGA ABIN DA MUKA AZURTA MUKU  TUN GABANIN MUTUWA BA TA ZO MUKU BA YA FARA CEWA UBANGIJINA DON ME BA KA JINKIRTA MINI BA  ZUWA AJALI MAKUSANCI IN YI SADAKA DA ZAKKA , DON NA KASANCE DAGA CIKIN  SALIHAI ) .
Burin  mai radadi wanda ba makawa daga gare su  , shi ne kiran hasara   ga 'yan wuta ranar alkiyama don shi kafuri mai sabo  a yayin da ya karbi littafin shi da hanun  hagu , kuma ya ga makomarsa  sai ya yi fatan ina ma da ya  kasance turbaya  Allah  madaukakin sarki ya  ce : (  wancannin ka shi ne rana ta gaskiya   wanda ya ga dama  zai riki komawa zuwa ga Ubangijin sa  .   Lalle ne mu mun yi mu ku gargadin azaba makusanciya  ranar da mutum ke dubi zuwa ga abin da hannayen sa suka aikata , kuma kafuri ya ce kaito na da dai na zama turbaya  ).
                   Mafi daukakan matsayi  a tafiya na buri shi ne abin da 'yan aljanna za su samu   na ni'iman burace-burace ,  kuma Ubangijin su mai kyauta yana  mai kyauta a gare su kuma yana musu kari da karamcin sa,  mafi karancin guri da ma'abota sa'ada shi ne wanda zai shiga aljanna  a karshe ,  ta kammala kuma ta adonta a gare shi sai Ubangiji ya ce mishi fadi burin ka  sai bawan ya yi ta buri , har iya kurewar burin sa sai Allah ya ce wa bawan na shi an baka abinda ka burata da kwatankwacin shi guda goma tare da shi.
       Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (  Idan 'yan aljanna sun shiga aljanna sai Allah madukakin sarki ya ce shin ko kuna sha'awan  wani abu na muku kari sai su ce ya Ubangijin mu shin  yanzu akwai  abun da  ya fi alherin fiye da  abinda ka bamu  sai ya ce e, yarda na ya fi  girma ).  
          TA TIKE
         
     


ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق