الجمعة، 1 ديسمبر 2017

NI"IMAR RUWA GA AL"UMA

HUDUBAR  MASALLACIN ANNANBI  TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI NA SHAIK ABDULMUHSIN AL-KASIMI NA 13- 3-1439 AH
 HUDUBAR FARKO :
  Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki  muna gode mishi kuma muna neman taimakon sa , muna neman gafarar sa  , kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunan mu , da munanan ayyukan mu , duk wanda Allah ya shiryar da shi ba bu mai batar da shi , duk wan da ya batar kuma babu mai shiryar da shi , na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya , kuma na shaida Annabi Muhammadu bawan sa ne kuma Manzon sa ne tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan sa  da sahabban sa da aminci tabbatacce mai yawa .
 BAYAN HAKA :
Ku ji tsoron Allah -ya ku bayin Allah- hakkin tsoron sa   da tsoron Allah ne ake haskaka basira da zukata  kuma ake kankare kusakurai  da zunubai ,.
    YA KU MUSULMAI:
Allah mai tausayi ne ga bayinsa , yana tausaya musu ta inda ba su sani ba,  yana sanya musu sababi na maslahohin su ta inda ba su zata ba ,  lalle shi mai kyautatawa ne kuma mai rahama  ne   mai kyauta kuma mai karamci,  ya yalwata ni'imomin shi a gare mu na bayyane da na boye,  Allah madaukakin sarki ya ce : ( kuma idan kun kidaya ni'imar Allah ba ku iya lissafa ta )
Akwai  wata   ni'ima mutane basu isa su wadatu ga barin ta ba a ko wani hali, Allah ya sanya ta  dalilai ne na tabbatar da rububiyyar sa  Allah madaukakin sarki ya ce : (  Shin kuma ba su gani ba , cewa lalle mu muna kora ruwa zuwa ga kasa  kekasasshiya  sa'annan mu fitar game da shi wata shuka  , wadda dabbobin su , da su kansu ke ci  daga gare ta  ? ashe fa ba su gani ba ? )
                        Allah ya gagari bayin shi da su kawo kwatankwacin ta  (  Shin    kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha  shin ku ne kuke saukar da shi daga girgije  ko kuwa  mu ne masu saukarwa ? Da mun so da mun mayar da shi ruwan zartsi to don me ba ku godewa ) , gaibi ne, ba wanda ya san lokacin shi na tabbas da gwrgodon shi da amfanin shi sai Allah  , Allah madaukakin sarki ya ce : ( Lalle Allah a wurin sa ne kawai sanin sa'a  yake , kuma yana saukar da girgije  kuma yana sanin abin da yake a cikin mahaifannai).
 yana daga cikin  hujjoji na tabbatar da uluhiyyar Allah   da cancantar shi da a bauta mishi shi kadan shi , akwai saukar da ruwa daga sama  Allah madaukakin sarki ya ce :(  kuma ya saukar da ruwa daga sama  sa'annan ya fitar da abinci  daga 'ya'yan itace game da shi  )  .
                    Kuma shi din yana daya daga cikin dalilai na fitarwa daga kabari da tadawa,  Allah madaukakin sarki ya ce:( Kuma akwai daga ayoyin sa  cewa lalle kai kana ganin kasa kekasasshiya , to, idan mun saukar da ruwa a kanta sai ta girgiza kuma ta kumbura, lalle wannan da ya raya ta hakika , mai rayar da matattu ne, lalle shi mai ikon yi ne akan ko wani abu ) da shi ne Allah ya ke rahama yake kuma azabtarwa ,  Allah madaukakin sarki ya ce:( kuma da sun tsayu sosai akan hanya da lalle mun shayar da su daga ruwa mai yawa) . 
         Ruwa daukaka ne kuma da girma da izza  ne, kuma al'arshin mai rahama yana kan ruwa, Allah madaukakin sarki ya ce : ( Al'arshin sa ya kasance a kan ruwa )  yana daga cikin ni'imomin Allah masu yawa  wanda Allah ya yi shi  har ga wadanda suka gabace mu  ni'ima da shi  , wanda ya gode daga cikin su Allah sai ya kara mishi, wanda kuma ya butulce  mishi sai Allah ya azabtar da shi , Allah madakakin sarki ya ce : ( Shin ba su gani ba  da yawa muka halakar da wani karni daga gabanin su , mun mallaka musu, a cikin kasa abin da  ba mu mallaka muku ba , kuma muka saki  sama akan su tana ta zuba ).
            Sabo da kasancewar sa ni'ima   mai girma , Allah ya turo gaba gare shi abin da  ke albishir da zuwan shi Allah madaukakin sarki ya ce : ( kuma shi ne ya aiko mana  iskokin bushara  gaba ga rahamar sa  )  yana daga cikin rahamar Allah ga bayin sa  ya jefa  farin ciki da annashuwa ga zukatan su ,  dalilin dubin su  zuwa ga abin da  suke kallo na daga ni'imomin shi  abin sabontarwa ,  yana daga cikin abin da  yake sanya walwala  ga zukata jin dadin da suke yi na saukar ruwan sama  bisa kasa  Allah madaukakin sarki ya ce : (  Kuma shi ne  ke saukar da girgije (ruwa) a bayan sun yanke kauna  kuma  yana watsa rahamar sa   alhali kuwa shi ne majibinci mai godiya) .
          Kuma kasa na farin ciki da gabatowan sa , sai  ta girgigiza  kuma ta kumburo  ta fitar da adon ta  Allah madaukakin sarki ya ce : ( Sa'annan idan muka saukar da ruwa  akan ta sai ta girgiza kuma ta kumbura , kuma ta tsirar  da tsiri daga ko  wani nau'I mai ban sha'awa)  da shi ne kasa ke rayuwa bayan mutuwar ta , Allah madaukakin sarki  ya ce : (  kuma muna saukar da ruwa daga sama  sai mu raya kasa da shi bayan mutuwar ta )   .
           Kuma halittu suna bishara ga  junan su da gabatoawan shi Allah madaukakin sarki ya ce : ( Sa'annan   idan Allah ya sami wadan da ya so daga bayin sa sai  ga su  suna bishara da shi )  kuma yana cikin sabuba na yardan Allah ga bawa in ya gode mishi game da ita ,               Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (  Lalle Allah na yarda game da bawa da ya ci abinci ya gode mi shi game da shi ko ya sha abin sha sai  ya gode mishi sabo da ta  )  MUSLIM NE YA RAWAITO .
        Ruwa  jinsin shi guda ne tare da babbancin lokuta da kuma wurare, Allah ya halicce shi ba launi  ya samar da shi ba tare da dandano ba  kuma ya saukar da shi ba tare da wari ba ,  abu ne mai dadi da yake shiga cikin ciki mai karfi  yana zuwa ya cike  kwarurruka  ya haura duwatsu , halitta ne mai girma  idan ya sauka a matsayin azaba babu mai yaye shi sai Allah , Allah madaukakin sarki ya ce : ( Zan tattara zuwa ga wani dutse ya tare ni daga ruwan  ,(NUHU ) ya ce : babu mai tsarewa a yau daga umarnin Allah face wanda ya yiwa rahama ,  sai taguwar ruwa ta shamakace a tsakanin su  sai  ya kasance daga wadanda aka nutsar).
          Amfaninsa ba shi kididdiguwa mai yawan tsarki ne ga gardi ga dadi mai taimakawa Allah madaukakin sarki ya ce :   (kuma  Muka saukar daga sama ruwa mai yawan  tsarki )  yana tsarkake jiki  da zukata, Allah Madaukakin Sarki ya ce : (  Alokacin da Allah ya ke rufe ku da gyanngyadi    domin aminci daga gare shi kuma yana saukar da ruwa daga sama a kan ku domin ya tsarkake ku da shi  kuma ya tafiyar da kazantar shaidan  daga barin ku) .
        Allah ya halicce shi da albarka  to sai ga 'yan kwayoyi kadan   kasa na rayuwa da su da wanda suke cikinta  Allah ya ce : (Kuma   Muka saukar da ruwa  daga sama mai albarka), da shi ne Allah ya ke tsirar da dukkan shuke-shuke  Allah madaukakin sarki ya ce : (   Sa'annan muka fitar game da shi daga dukkan 'ya'yan itace   )  Allah ya sanya shi mai kankara ne ga zunubai da kusakurai a cikin alola Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (  Idan bawa musulmi ya yi alola – ko mumini ya wanke fiskan sa  sai ya fita daga fiskarsa  dukkan kusakuran da ya kalla da idanuwan nasa tare da digon ruwan ko tare da digon karshe na ruwan, to idan ya wanke  hannayen sa sai ya fita daga hannayen nasa dukkan kusakuran da hannayen nasa suka aika ta  tare da  ruwan , ko tare da digon karshe na ruwan -  to idan ya wanke kafafuwan sa   sai  dukkan kusakuran da yayi tafiya da wannan kafan zuwa gare ta  ya fita tare da ruwan – ko tare da digon karshe na ruwan-  har ya fita tsarkakake daga  zunubai  ) MUSLIM NE YA RAWAITO
           Saukan sa zuwa doron kasa  bisa gwargwado  ya ke , ana kidanya adadin digon, Allah madaukakin sarki ya ce : (    Muka saukar da ruwa daga sama bisa gwargwado)  karin sa daga gwargwadon sa wani azaba, ne  aya mai ban mamaki  ana kiyayeshi  acikin kasa kuma yana da taskoki acikinta ba wanda yasansu sai Allah, Allah madaukakin sarki yace: ( shin baka gani bane Allah  ya saukar da ruwa daga sama  sa'an nan ya gudanar dashi yana mare mari acikin kasa ),wani sashin na fita daga dutse Allah madaukakin sarki yace( kuma lallai ne daga duwatsu ,hakika akwai abin da maremari suke bubbuga daga gareshi kuma lallai ne daga garesu hakika akwai abin da yake tsatsagewa har ruwa ya fita daga gareshi )mai muujiza idan ya sauka a doron kasa, kasa keka sassa sai ya canza launinta zuwa ga abin kallo mai ban kaye, Allah madaukakin sarki yace : (Ashe ba ka gani ba lalle ne  Allah ya saukar da ruwa daga sama sai kasa ta wayi gari koriya ? lalle Allah mai tausayawa ne mai kididdigewa )
Halittan Allah  da ya yi ga ruwan sama a matakansa alamari ne na ban mamaki Allah madaukakin sarki ya ce (Allah ne wanda ke aika iskoki sai su motsar da giragizai  sa'annan ya shin fida shi a cikin sama yadda ya ke so kuma ya sanyashi wani babbake sannan ka ga ruwa na fita daga tsakaninsa ,sa'annan idan Allah ya sami wadan da ya so daga bayinsa sai gashi suna bushara da shi .)
Na daga cikin cikan ni'mar Allah a gare mu bayan saukarsa kiyaye shi a kasa bayan saukarsa, Allah Madaukakin Sarki ya ce : (sa'annan muka saukar da ruwa daga sama sa'annan muka shayar da ku shi, kuma baku zama masu taskacewa a gare shi ba.)
Ni'ma ce makusanciyar riska mai saukin samuwa, idan bayi sun sabawa  Ubangijin su sai ya nesatar da su daga gare ta, Allah Madaukakin sarki ya ce : (ka ce ko kun gani idan ruwanku ya wayi gari fakakke to wane ne zai zo muku da ruwa wani mai bubbuga).
Kamar yadda wannan take ni'ima ce – to wannan iska mai taushi da  kananan digo wanda ake ni'imta bayi da shi to ta na iya sauyawa da umarnin Allah zuwa ga azaba, Allah ya halaka wasu mutane da wannan ruwa sabo da juyawa Allah baya da suka yi, shi ne farkon azabar da aka yi wa wata al'uma, Allah Madaukakin sarki ya ce :(Mutanen Nuhu sun karyata a gabaninsu ,sai suka karyata BawanMu ,kuma suka ce, Shi mahaukaci ne " kuma aka tsawace shi)(Saboda haka ya kira ubangijinsa (ya ce),lalle ni an rinjayeni sai ka yi taimako)
(sai muka bude kofofin sama da ruwa mai zuba ) (kuma muka bubbugar da kasa ta zama idanun ruwa sannan ruwa ya hadu akan wani umarni da aka riga aka kaddara shi. Kuma muka dauke Nuhu akan jirgi na alluna da kusoshi. Tana gudana a cikin kiyayewarmu domin sakamako ga wanda aka yi wa kafircin).Alkamar 9-14
Fir'auna ya yi girman kai ga musa ya mishi alfahari da ruwa sai ya ce : (Ashe mulkin Masar ba a gare ni ya ke ba , kuma wadannan kogunan  suna gudana daga karkashi na?) Zukhruf 51
Sai Allah ya halaka shi sakamakon girman kai da ya yi, ya sanya shi abin lura ga mutane,
Allah Madaukakin sarki ya ce : (Har a lokacin da nutsewa ta riske shi yace : Na yi imani cewa Hakika babu abin bautawa face wannan da banu Isra'ila suka yi imani da shi kuma kuma ni ina daga Musulmai). Yunus 90
 Ya kasance malalin Arimi (Dam) ga mutanen  Saba'i ya yin da suka kafurcewa ni'imar Allah sai Allah ya kekketa su da shi kekketawa, Allah Madaukakin sarki ya ce :(sai suka bijire saboda haka muka saki malalin arimi(dam) a kansu, kuma muka musanya musu gonakinsu biyu da wadansu gonaki biyu masu 'ya'yan itace kadan : Talakiya da goruba da wani abu na magarya kadan ). Saba'I 16.
Hakika Allah ya sanya shi nasara ga muminai a yakin badar, Allah Madaukakin sarki ya yace : (A lokacin da Allah ya ke rufe ku da gyangyadi  domin aminci daga gare shi , kuma yana saukar da ruwa daga sama a kanku, domin ya  tsarkake ku da shi, kuma ya tafiyar da kazantar shaidan daga barinku, kuma domin ya daure akan zukatanku, kuma ya tabbatar da kafafu da shi.) Anfal 11
Kuma shi yana daga cikin ni'imomin da idanuwa ke jin dadi da shi a cikin aljanna mai ni'ima.
Allah Madaukakin sarki ya ce : (A cikin ta akwai wadansu koguna na ruwa ba mai sakewa ba).
Kuma 'yan wuta suna neman agaji da shi  Allah Madaukakin sarki ya ce : (Kuma abokan wuta suka kirayi abokan Aljanna cewa , ku zubo a kanmu daga ruwa ko kuwa daga abin da Allah ya azurta ku, su ce : lalle ne Allah ya haramta su a kan kafurai) Araf 50
Bayan haka ya ku Musulmai!
To ruwa na daga cikin ayoyin Allah da ke wajabta imani, Allah Madaukakin sarki yace : (Kuma muka sanya dukkan komi mai rai daga ruwa shin ba za su yi imani ba? ) Anbiya' 30
Aya ce mai ban kaye ba wani da ke ja cewa daga Allah ne, ba kuma wanda  ke samar da shi koma bayansa. Allah Madaukakin sarki yace : ( Kuma lalle idan ka tambaye su wane ne ya saukar da ruwa daga sama har ya rayar da kasa,game da shi a bayan mutuwar ta lalle suna cewa, Allah ne).
Kuma wani ni'ima ce  mai girma daga Allah,tana tare da mu a kowani wuri da  lokaci, to ya wajaba a gare mu mu yi godiya game da ita, da tunani  cikin sha'aninta , da biyayya ga Mahaliccinta, kuma kada mu rudu da falalar da Allah ya mana da ita, kar mu yi barna a cikinta, kuma ya dace mu rike ta abin taimako don raya lahirar mu.
Ina neman tsarin Allah daga shaidan abin jefewa.
(sai nace ku nemi gafara daga Ubangijinku  lalle ne shi ya kasance mai  gafara ne, ya sako girgijen sama akan ku da ruwa mai bubbuga).
Allah ya sanya mini albarka ni da ku a cikin Alkur'ani Mai girma.
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa kyautatawarsa , da godiya bisa datarwarsa da baiwarsa, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah ina mai girmama sha'aninsa, na shaida Annabinmu Muhammad bawansa ne kuma Manzo sa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbansa, da aminci tabbatace mai yawa,
Ya ku musulmai !
Allah Mai azurta bayinsa ne mai biyayyansu da fajirinsu, (Ba wata dabba  a cikin kasa face ga Allah arzikinta ya ke)Hud 6
Kuma arzikin  Ubangiji yana sauka ne da biyayya a gare shi, da tuba zuwa a gare shi, Allah Madaukakin sarki ya ce :   (Kuma da lalle mutanen Alkaryu sun yi imani suka yi takawa da mun bude Albarkoki a kansu daga sama da kasa)
Kuma godiya na kiyaye ni'ima yana shelanta  karinta Allah Madaukakin sarki ya ce : (Kuma a lokacin da Ubangijinku ya sanar, lalle ne idan kun gode,hakika ina kara muku, kuma lalle ne idan kun kafirta, hakika azaba ta tabbas mai tsanani ce) Ibrahim  7
Sannan ku sani Allah ya umarce ku da salati da aminci ga Annabin sa ….)   

  

   

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق