Hudubar Masallacin Annabi na
shaikh Husain Al- Asshaikh 27-3- 1439 AH
Batu mai girma na cikin zuciyar kowani Musulmi : shine batun Masallacin Aksa Kiblar farko na Musulmai
kuma masallaci mai daraja na uku, kuma gurin da aka yi ISRA'I (Tafiyan dare )
da Shugaban Halittu.
shine batu mafi muhimmanci a yanzu wanda ba zai gushe ba daga zuciyar kowani musulmi daidaiku da al'uma, a duk yadda
kalu bale ke fiskantar musulmai , da duk yadda musulmai suka samu kansu a ciki
na fitintinu.
Kudus da abin da kasarta ta kumsa na masallacin Aksa batu ne na akida a
gurin musulmai, kuma RIBADI ne mai
zurfin tarihi ba za a manta shi ba a a kowani yanayi ko a goge shi
daga kundin Musulunci, sabo da wani
Alami ne daga cikin alamomi na musulmai
, kuma ginshiki ne daga ginshikanta da ba a sauya su, kuma guri ne mai tsarki
daga cikin gurare masu alfarma a musulunci.
Ta yaya zai yiwu bayan ga littafin Ubangijinmu na tunatar da mu safiya
da maraice da fadinsa Mai tsarki (Tsarki ya tabbata ga wanda yayi tafiyar
dare da bawansa da dare daga Masallaci mai alfarma zuwa masallacin Aksa wanda
muka sanya albarka a gefensa domin mu nuna masa daga Ayoyinmu lalle ne
shi shi ne Mai ji Mai gani ) Al'isra 1
Masallacin Aksa daya ne daga cikin Masallatayya guda uku ne da ba ya
halatta a nika gari zuwa ga wasu sai
zuwa gare su da sunan neman kusanci ga Allah da neman kari daga falalansa kamar yadda hadisai suka zo daga Manzon Allah
tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi.
Kasar baitul Makdis nan ne kasar da za a hada halittu a tada su a ranar
alkiyama , An karbo daga Maimuna baiwar Annabi ta ce : Ba mu labari game da
baitul Makdis sai ya ce : (kasa ce na tattarowa da tadawa ).Ibnu Maja ya
rawaito shi da isnadi Ingantacce.
Baitul Makdis na da matsayi mai girma a musulunci da falala na musamman,
an karbo daga Abu Zarri Allah kara yarda a gare shi ya ce : (Muna tattaunawa
a gaban Manzon Allah ko wanne ya fi falala Masallacin Annabi ko Masallacin
Baitul Makdis, sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya
ce : (Salla guda a Masallaci na ya fi salloli hudu a cikin shi kuma madalla
da Masallaci, Yana dab da ya kasance
mutum ya zama bai da abinda ya kai
igiyar dokinsa na daga kasa wanda zaa ga Baitul Makdis daga can hakan ya fi mishi duniya da abin da ke
cikinta) Hakim ne ya rawaito ya inganta shi Kuma Imam Azzahabi ya mara
mishi baya wurin ingantawar.
Na daga cikin falalolin shi a musulunci shi ne gurin da aka yi tafiyar
dare da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi kuma daga nan
ne aka tafi sama da shi,
An karbo daga Anas Dan Malik Allah ya kara mishi yarda cewa Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : An kawo min Alburak
wata dabba ce fara mai tsawo ya fi jaki bai kai alfadari ba, yana sanya kofoton
sa iya makuran ganinsa, ya ce Na hau shi har na zo baitul Makdis, sai ya ce sai
na daure shi a tirken da Annabawa ke daure wa. Yace sai na shiga Masallaci na
yi raka'a biyu a cikinsa, sai na fita sai Jibrilu ya zo min da kwano daya na
giya daya kuma na nono sai na zami nono, sai Jibrilu ya ce ka zabi FIDIRA (Musulunci) sai ya haura da mu zuwa sama.) Muslim ne
ya ya rawaito.
Na daga cikin falalolin shi akwai hadisin Abdullahi Dan Amr Dan
As daga Annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Yayin da Sulaiman dan Dawud ya kammala
gina Baitul Makdis sai ya roki Allah abu uku; hukuncin da zai yi daidai da hukuncin sa, da
mulkin da ba wanda ya dace ya samu irin shi a bayan sa , kada kuma wani ya zo wannan masallacin da ba
abin da ya nufa sai salla a cikin shi face ya
fita daga zunuban shi kamar ranar da
mahaifiyar shi ta haife shi ) , sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi ya ce : - Amma biyun hakika an
bashi su ina fatan an bashi na uku)
Nasa'i ya rawaito shi da Ibn Maja Albani ya inganta shi .
'YAN UWA A MUSULUNCI :
Kuma Baitul
makdis da Masallacin Aksa na da falaloli masu girma a Musulunci
wanda ya sanya malaman musulunci
tun a karnoni da suka shude ,
sukan ware su da talifi daban-daban masu bin juna da rubutu daya bayan
daya , game da falalan shi da girman hakkin shi , hakika
dunbin malamai na wannan al'umma
sun yi rubutu takanas akan shi:
Daga cikin su akwai Baha'uddin Ibn Asakir a cikin littafin shi (
Aljami'ulmustakasa fi fada'ilil masjidi
aksa ) . Daga cikin su akwai
Aminuddin Ibn Hibatillah asshafi'I a
littafinsa (Kitabul Uns fi Fada'ilil Kudus), a cikinsu
akwai Burhanuddin Alfazari a
littafin sa ( Ba'isul nufus ila ziyaratilkudus almaharus) daga cikin su akwai Shihabuddin Ahmad Dan Muhammad Almakadisi
a littafin shi ( Musirulgaram ila ziyaratil kudus wa sham ) , daga cikin su akwai Alhussainul Husaini a littafin shi (
Alraudulmugris fi fada'ilu baitilmakadis ) daga cikin su akwai Ibnul jauzi
a cikin littafin sa ( Fada'ilul kudus ) daga cikin su akwai suyudi a cikin littafin sa ( Ithafu Al'akhissa bi
fada'ili Almasjidil aksa) .
Da wannan ne
ya sa musulmai gaba dayan su ba za su
yarda su tabbatar da duk wani mataki da
zai taba batun kudus da Masallacin Aksa ba abu ne da yake mai tsarki a musulunci baya halatta da kowani irin hali
a taba shi kai sai dai ma irin wannan
tasarrufin , ba abin da zai karawa musulmai sai tsayuwa da jajarcewa da dogewa
bisa ga neman hakkokin su tabbatattu
wanda ya yi daidai da
ginshikai tabbatattu don tantance gaskiya da
tsawatarwa ga zalunci , da kuma
yiwa wanda a ka zalunta adalci, kamar
yanda shari'o'i na sammai da dokokin kasa da kasa suka tabbatatar .
Kai duniya ma gaba
daya a yau , yana daukan duk wani mataki irin wannan
abu ne da yake na keta dokokin da aka yi tarayya a kai na kasa da kasa,
na cewa kudus birnin tarayya ne
na musulunci , kuma gu ne mai tsarki daga cikin tsarkakan gurare na musulmai .
Lalle batutuwa na al'uma ba a yin nasara ta hanyar
huduba kawatacciya ko kalmomi masu
amsa amo ba , ba yi da wani
amfani ya- ma'abota musulunci na nuna
bakin ciki da bacin rai , ko
kuma daga abubuwa na nuna Allah wadarai da yawaita jerin gwano a titi
don bayyana manufa , sau nawa hakan ya
faru da musulmai , da suka yi haka abin ya zo ya wuce ba a cimma manufa ba tare da hakan
bai wuce ya zama wani abu na maida martani irin wanda ba zai tunkude
zalunci ba ko ya kauda cuta ba , kuma ba zai hana tokobin mai ketare iyaka ba
ko ketan mai keta ba, to fa lalle mu
sani ba makawa sai an ko ma ga Allah mai girma da daukaka komawa na gaskiya , tare da kankan da kai da ikhlasi zuwa ga Allah mai girma da kasaita tabaraka wata ala .
Al'uma tana samun nasara
ne kawai idan ta taimaki al'uma ciki da waje ,
tana mai amsa kira a waki'I, a
duk lokacin da al'uma ta kasance mai riko da addinin Allah tana mai girmama umarnin shi da shari'an
shi tana tunkuduwa a
harkokin ta daga addini na
gaskiya wan da batun Masjidul Aksa ya tsayu a kai, to, a
wannan lokacin ne za a samu waraka da
kuma nasara tabbatacce , sa kuma samu
mafita mai amfani , Allah madaukakin sarki ya ce : ( Idan kun taimaki Allah(
wato addinin sa) zai taimake ku ( akan magautan ku ) Muhammad 7 .
YA JAMA'AR MUSULMAI:
Duk ranar da
tsoratarwa na kur'ani da sunna ke galaba a kan zuciya , sannan hujjoji na waki'i suka gaskata haka a
fagage na rayuwa da lokutan ta , to
musulmai ba za su taba fadawa cikin rauni ba , da walakanci ba, kuma wani abu da zai same su na kaskanci
da walakanci , Allah madaukakin
sarki ya ce : ( Kuma kada ku yi rauni
kuma kada ku yi bakin ciki alhali kuwa, ku ne mafiya daukaka idan kun kasance
masu imani ) Ali Imrana 139
Hakika lokaci ya yi ga musulmai
musamman ga 'yan uwa da suke FALASDIN a
halin suna tinkaran kalubale mai hadari
, wanda ta shafi amincin al'iumman su
gaba daya , da su hadu a kan da'a da tsoron Allah , kuma su yi sulhu bisa ga
maslahohi na addini da lahira kuma su hadu don kauda duk wani abin da zai kawo sabani da rarrabuwa a tsakanin su, su fita daga
dabar gaba zuwa ga farfajiya ta 'yan uwantaka , su fita
daga wutan kiyayya , zuwa ga haske na zuciya
su kuma fita daga juyawa juna baya da
rarrabuwar kawuna , zuwa ga yafiya da hadin kai , su yi watsi da
kungiyanci da bangaranci , su gudo zuwa ga ruhi na 'yan uwantaka na musulunci
, da kauna na imani A llah madaukakin sarki ya ce : ( Kuma ku yi da'a ga Allah da Manzon sa , kuma
kada ku yi jayayya har ku raunana , kuma karfin ku ya tafi, kuma ku yi hakuri
lalle ne Allah yana tare da masu hakuri ) Anfal 46
A duk lokacin da musulmai suka tabbatar
da cikakken sako na musulunci a waki'in su ba tare da sun
tawaye ba kuma suka hakimantar da shi hakimantarwa
cikakke gamamme , kuma suka yi aiki da
shi ciki da waje , kuma suka rayu da
musulunci don musulunci, to Allah ba zai tozartar da aikin su ba duk yadda
wahala ta kai wahala , ba za su taba
ganin duhu ba a kan hanyar su ta tafiya
da kuma mafita duk yanda musiba ta yi girma muddin
akan tafarki na musulunci suke tafiya
, kuma suna masu bin hukunce
–hukuncen shi , kuma suna masu koyi da riko
da sunnan Annabi, Allah madaukakin sarki ya ce : ( Lalle ne Allah yana bada kariya ga wadanda suka yi imani ,) Hajj
38 .
Amma fa muddin al'uma
ta kasance ta dauwama wutan sha'awe-sha'awe na haramun na kadawa
, ya yi awun gaba da ita , abubuwa na shagaltarwa na bata na
fisganta taguwar son rai na fandarewa
da shubuhohi na dibanta to a wannan
lokacin za ta tinkari ambaliyar fitintinu da jarabawowi da nau'uka na bala'o'I masu yawa , Allah
madaukakin sarki ya ce : ( Kuma abin da ya same ku na wata masifa to, game da abin da hannayen ku suka sana'an
ta ne , kuma ( Allah) yana yafewa (
wadan su laifuffuka ) masu yawa) Shura
30 .
Allah madaukakin sarki ya ce game da yakin uhud : ( Shin kuma a lokacin da wata masifa hakika ta
same ku, alhali kuwa kun samar da biyun
ta kunce : ( daga ina wannan yake ka ce
daga wurin rayukan ku ya ke ) lalle ne Allah akan dukkan komai mai ikon yi
ne) Ali Imran 165.
YA
KU JAMA'AR MUSULMAI :
Ba makawa al'uma ta sakankance da wasu martabobi na
yakini dukkan su ba za su tsiratar da
ita daga matsatsi da ta shiga ba ko kuma ta kawar da ita daga yanayi da ta
shiga ba na bakin ciki face musulunci na gaskiya akan akida na tauhidi tacecce
da bin sunna ingantacce , wanda yake shi
ne tafarki na dai-dai a littafi da sunna bisa fahimtar magabata na al'uma to wannan shi ne tushe na asali kuma shi ne
ginshiki mai karfi na samun daukaka da
jagoranci , da kuma samun taimako da daukaka Allah madaukakin sarki yana cewa : ( Wadan da sukayi imani
kuma basu gauraya imanin su da zalunci ba wadan nan suna da suna da aminci kuma su ne shiryayyu) .
An'am 82
Alkawari ne na
tabbas kuma labari ne na gaskiya (
Kuma ya kasance tabbatacce, taimakon Muminai wajibi ne a kan mu) ARRUM 47
( Rinjaye ga Allah ya
ke kuma da manzon sa kuma da
muminai kuma amma munafukai ba su sani
ba ). Munafikun 8 ( Hakika muminai sun rabauta ) muaminun 1
YA KU JAMA'AR
MUSULMAI:
Lallai wajibi ne ga
dukkan musulmai bisa sabanin matsayin
su su tsaya bisa batu mai tushe wato batun masallacin Aksa da kuma Baitul makdis
da kasar FALASDIN su tsaya
tsayuwan daka a irin mahanga na musulunci
ba wanin sa ba ta hanyar hadin kai mai tasiri , da
kyakkyawan motsi wanda zai kai ga
samar da da mai ido da cimma
manufofi Allah madaukakin sarki ya ce :
( Kuma ka ce ku yi aiki sa'annan
Allah zai ga ayukan ku da Manzon sa da
muminai ) Tauba 105 .
Ba makawa sai an yi
amfani da basira mai karfi da cikakkiyar hikima wanda da ita ne al'umar musulmi za su iya
tinkarar kalubale daban-daban kuma ko
wani iri wanda zai yi daidai da hadin
kai da kuma da'iran taimakekeniya da
karfafan juna , da taimakon juna ba
rikici ko fada ko zage-zage , ko neman wani laifi da wannan ne za a toshe zaluncin masu zalunci
al'uma ta kai ga nasara mai karfi .
Ba makawa sai anyi dubi
bisa batu na al'uma da dubi wanda yake
akwai hangen nesa a ciki, wanda zai
tashi daga motsi na zahiri zuwa ga
bigire mai tasiri da kuma ayyuka da aka auna su wanda za su kai ga rinjayi cikin jerin gwanon hada karfi da karfe da kyakkyawan tsari don a kai ga matsaya na
gaskiya wanda ya taso daga tuta na
addinin musulunci mai hikima , , da kuma abin da shari'ar shugaban Annabawa da
Manzanni ta kebanta da shi, wanda ita ce za ta iya jan ragamar duniya gaba
daya zuwa ga wayewa da aminci da walwala
da hadin kai da zaman lafiya .
Dole ne al'uma ta
tafi akan kokari gurin hada karfi da
karfe don fiskantar kalubale da salo da ya dace da kuma
tattaunawa mai kaiwa ga manufa
nesa daga salo na cece ku ce da kuma kalmomi na bangaranci da ife-ife da ta'assubanci ko agender
na wata kasa , to wadan nan wasu
abubuwa ne da ba za su haifar da wani abu ga al'uma ba sai sharri da
bala'I Allah madaukakin sarki ya ce : ( Sai
( al'umar) suka yayyanke al'amarin su a
tsakanin su guntu-guntu kowace kungiya
suna masu farin ciki da abin da yake a gare su ) Muaminun 53 .
Ba makawa wurin amsa kiran fadin Allah madaukakin sarki ( Lalle ne wannan
ita ce al'ummar ku , ta zama al'umma guda kuma ni ne Ubangijin ku sai ku bauta
mini )
HUDUBA TA BIYU
Kasar haramaini masu
mulkin su kuma da talakawan su a ko yaushe suna tsaye tsayin daka wurin bada kariya ga dukkan batutuwa na musulunci
da kuma na larabci musamman batun FALASDINU , to matsayan wannan kasar da
mahukuntan ta game da batun
FALASDINU abu ne da yake tabbatacce ba
za su girgiza ko su sauka daga kanta ba
batu ne dake cikin abu mafi muhimmanci
da suke iya kokarin su ta fiskoki
daban-daban , musamman bangarorin da
suka shafi bangarorin tattalin arziki da
na siyasa.
A zamanin mai hidimawa
masallatayya biyu masu alfarma sarki Salman
duniya ta shaida ba da kulawa da
cigaba da wannan tafiya karkashin
kulawan mai girma Allah ya kara kiyaye shi
sabo da la'akari da yayi da ita batu ne na musulunci kafin ta zama batu ne na larabawa , wannan kasan tana ganin wani nauyi ne da ke
kanta kuma tana bautawa Ubangijinta da
shi , kuma tana samun daukaka da ita da kuma hukuncin sakon ta na musulunci da matsayinta a duniyance , sabo da haka
ba wani gurbi na neman kari ga duk wani mai kin gaskiya bisa ga kokarin wannan kasa haka kuma da mai musanta hakan , da kuma 'yan sashi-fadi , da kuma mai kawo shakku cikin
jinsin mu (na larabawa) bisa ga
kokarin da wannan kasa take tashi da shi
, to, ya wajaba a gare su da su ji tsoron Allah su sani cewa duk wani dauki ba dadi da ake yi don taba wannan kasa mai alfarma to lalle fa suka ne ga fadar
musulunci da kuma suka ga wadanda suke
rike da tutar bada kariya a gare shi , to, yin haka kamar wata tawaga ne da suna yaudarar kawunan su kuma suna makirtar al'umar su .
Allah madaukakin sarki ya ce
: ( Suna yaudarayya da Allah da wadan da suka yi imani alhali ba su yaudarar
kowa face kansu , kuma basu sakankancewa
) Bakara 9.
Kuma su sani wannan kasan tana tafiya ne
a kan tsari na musulunci wanda ba
ya bukatan kari sabo da yabon mai
yabo ko kuma jafa'i
sabo da farfagandan makiya masu fatan sharri ga kasan, Allah na sane kuma yana ganin nufin su.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق