الجمعة، 23 مارس 2018

KABARI MASAUKIN FARKO NE NA LAHIRA


Hudubar juma'a  na Masllacin Annabi na Shaikh Abdulbari Subaiti 6/7/1439 AH
Hudubar Farko:
Tafiyan Mutum a wannan rayuwa   masaukanta na sabunta , marhalolinta na jujjuyawa , yana rayuwa ne na wasu matakai a cikin mahaifiyar sa  sannan da wasu matakai a doron kasa , da wasu matakan kuma a cikin kasa har zuwa a tashe shi.
          Wannan tafiyan tana da tsawo a zahirinta  sai dai tana da saurin gushewa ,  kuma  tana da saurin karewa da tafiya,  to ita duniya ba gidan zama ba ne ga rayayye, mai hankali zai tuna irin jujjuyawa da take da shi  da saurin karewan shekaru,  sai ya ratsa jikin   zuciyan shi ta  tausasa .
           Masaukin da baya  yiwuwa ga ko wani matafiyi sai ya sauka gare shi  wata rana shi ne kabari   , kuma lallai  ya isa abin wa'azi a  gare shi , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya  ce : (Lallai kabari na da wata matsa  wanda da a ce dayan mu zai kubuta daga gareta  da  Sa'ad Dan Ma'azu ya kubuta daga gare ta ).
      An karbo  daga Amirul muminina  Usman Dan Affan  Allah ya kara yarda a gare shi ya kasance idan ya tsaya a wurin kabari  sai ya yi ta kuka har gemun shi ya jika da hawaye , sai a ka ce da shi  kana tuna aljanna da wuta amma ba ka kuka amma in ka tsaya a wurin kabari sai ka yi kuka    , sai ya ce na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa  : ( Kabari shi ne farkon masaukan lahira  idan mutum ya tsira daga gare shi to abin da zai biyo baya ya fi sauki  a gare shi, idan kuma bai tsira ba to abin da zai biyo baya ya fi tsanani a gare shi ).
                  Yana daga cikin rukunnan imani da ranar lahira akwai kudurtawa da hakikanin imani da kabari , imani da ni'iman kabari ga ma'abota da'a da kuma   azabar kabari ga  wadan da suka cancanta ma'abota sabo  da fajirci,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Badon kada ku ki binne mamatan ku ba da na roki Allah ya jiyar da ku daga azabar kabari na daga abin da na ke ji ).
Ziyaran kabari don daukan izina da wa'azantuwa sunna ce kuma kusanci ne, wanda ya ziyarci kabari zai tuna wadannan matattu wadanda kakaninsa ne da iyayensa, sai ya sakankance cewa zai mutu a binne shi kamarsu, kuma zaa tambaye shi a kabarinsa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( ku ziyarci makabarta zai tunatar da ku lahira).
                      Idan an binne mutum a kabarin shi  iyalan shi da dukiyan shi suka bada baya farkon maziyartan shi su ne mala'iku guda  biyu su mishi jarabawa,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (  Lallai idan an sanya mamaci a kabarinsa zai ji sautin takalman su lokacin da suke bada baya   idan ya kasance mumini ne sai salla ta kasance ta kansa azumi ta kasance ta damansa , zakka kuma ta hagunsa,  zai  kasance ayukan  da yake aikatawa na alheri  na daga sadaka da salla da ma'arufi da kyautatawa mutane a ta kafan sa , sai a zo ta kansa sai salla ta ce tanan ba gun shiga zai a je  ta daman sa sai azumi ya ce ta guna ba mashiga  sai a zo ta hagun sa sai zakka ta ce  ba wani mashiga ta guna  sai a zo ta bangaren kafafuwan sa  sai ayukan alkairi   na daga sadaka da  ihsani da kyautatawa mutane  su ce ba mashiga ta guna  sai  a ce da shi zauuna , sai ya zauna  sai a suranta mishi rana tana kusan faduwa  sai a ce da shi ko ka ga wannan  da ke fiskantar ku me za kace  game da shi  me za ka shaida kuma game da shi ? sai ya ce ku barni na yi salla , sai a ce da shi, ai za ka yi amma bamu labarin a bin da muka tambaye ka game da shi ,  ka ga mutumin nan da ke ta fiskar ka me za ka ce game da shi kuma wacce shaida za ka masa? Sai yace : Muhammad, ne, kuma na shaida shi           Manzon Allah ne, kuma yazo da gaskiya daga Allah  ,  sai a ce da shi : akan haka ka rayu, kuma a kan haka ka mutu , kuma a kan haka za a tashe ka in Allah ya yarda , sai a bude mishi kofofi n Aljanna  sai a ce da shi  nan ne masaukin ka a cikinta da abinda Allah ya tattala maka a ciki  sai ya kara jin kaimi da farin ciki  , sa'annan sai a bude mishi kofofin wuta  sai a ce da shi ka ga wannan  shi ne masaukin ka da abin da Allah ya tattala maka a ciki da ka saba mishi , sai ya kara kaimi da farin ciki  sannan sai a buda mishi a kabarin shi   zira'i  saba'in  a haskaka mishi ciki  a maida jikin shi kamar yanda aka fare shi , sai a sanya ruhinsa a cikin wani iska mai dadi  wato wani tsuntsu ne ke shawagi akan itaciyar aljanna  wannan shi ne fadin Allah madaukakin sarki  ( Allah yana tabbatar da   wadan da suka yi imani da magana tabbatacciya  a cikin rayuwar duniya   da cikin lahira kuma Allah yana batar da azzalumai ).      Lallai kafuri  in anzo ta fiskan shi ba za a samu komai ba , in anzo ta daman shi ba za a samu komai ba in anzo ta hagun shi ba za a samu komai ba sai a zo ta kafafuwan shi ba za a samu komai ba  sai a ce da shi zauna sai   ya  zauna  cikin tsoro  da firgici, sai a ce da shi  ba ka  ga wancan mutumin da ya kasance a cikin ku ba me za ka ce game da shi kuma wacce shaida za ka  yi akansa , sai ya ce wani mutumi?  Ba zai ma gane sunan shi ba  sai a ce da shi Muhammad      sai ya ce ban sani ba  na ji dai mutane suna cewa wani magana sai ni ma na fada  kamar yanda suka  ce, sai a ce da shi  a haka ka rayu kuma ahaka ka mutu kuma akan haka za a tada  in sha Allahu, sai a bude mishi kofa daga   cikin kofofin wuta sai a ce da shi wannan ne masaukin ka na daga wuta  da abin da Allah ya tanada maka na daga cikinta ,   sai ya kara bakin ciki da hasara  , sannan a bude mishi kofa daga cikin kofofin Aljanna   ace da shi, wannan masaukin ka ne a cikin ta da abin da Allah ya tattala maka  da ka mishi biyayya,  sai ya kara bakin ciki da hasara  sai kabarin shi  ya kuntata a gare shi  har  kasusuwan hakarkarin shi su shiga junan su.
               Wannan ita ce rayuwa ta kunci wanda Allah ya ambata ( To lallai ne rayuwa mai kunci ta tabbata  a gare shi ,  kuma muna tayar da shi a ranar kiyama yana makaho ) Dabarani ne ya rawaito da Ibn Hibban a sahihin sa .
       Mai hankali  zai shirya ne kafin mutuwa ya kimtsa wa kabarinsa don kansa,  ya raya ta, ta hanyar ayuka na kwarai  da imani  don ya kasance yana da dausayi daga cikin dausayin Aljanna Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Yana daga cikin abin da zai riski mumini   bayan mutuwan na daga aikin shi da kyawawan aikin sa ,    ilimi da ya ilmantar kuma  ya  yada shi   ,  da Da na kwarai da ya barshi , da Alkur'ani da ya gadar da shi ko masallaci da ya gina ,  ko kuma gida da ya gina na 'yan tafarki , ko korama  da ya buda ya gudana , ko sadaka da ya fitar daga dukiyar shi ,  a halin yana mai lafiya yana raye  zai riske shi  bayan mutuwar sa .'
     Wanda ke yawan  tuna mutuwa  zai raya kabarin sa da kyawawan ayuka, domin ya sani bisa yakini , lallai shi ya sani idan ya wayi gari ba zai yi yammaci ba  , idan kuma ya yi yammaci  ba zai jira wayan gari ba  sai ya yi gaggawa zuwa ga ibada kafin a yi shamaki tsakanin shi da ita , ga Amr  dan As  yana ganin mamaci an binne shi sai yayi sauri ya tafi masallaci ya yi salla raka'a biyu, sai aka ce da shi me ya sa ka yi haka ?,  sai ya ce makabarta ta tuna min fadin Allah ( Sai aka yi   shamaki  tsakanin su da abin da suke sha'awa  ).
     Sai na sha'awi salla kafin a yi shamaki tsakani na da ita , wanda yake son aboki a kabari wanda zai debe mishi kewa, ya haskaka mishi kabarin shi  ya tafiyar mishi da kadaici to ya riki Alkur'ani .
     Yana daga cikin sabuba na tsira   daga fitinan kabari da azabar sa, dauwama akan karanta suratul mulk, da aiki da abin da ta hukunta .  An  karbo daga Dan Mas'ud Allah ya yarda da shi ya ce :  (Za a zo wa mutum a cikin kabarinsa sai a zo  ga kafansa sai kafofin sa  su ce :   ba ku da wata dama ko kofa ta fuskar mu ya kasance yana tsayuwa da mu  ya karanta suratul mulk sannan sai a zo ta kirjin sa ko ta cikin sa ,  sai ya ce  ba ku da wata dama ta bangare  na a kan shi ya kasance da ni yake karanta suratul mulk  sannan a zo ta kasan sa sai ya ce  baku da wata kofa  akan shi game da ni ya kasance da ni yake karanta suratul mulk  ,  sai ya ce : ita ce  mai hani, tana hani  daga azaban kabari  tana cikin attaura suratul mulk   wanda ya karanta ta a dare to hakika ya yawaita kuma  tsawaita )  Hakim ne ya rawaito shi a mustadrak ya ce ingantacce ne amma(Bukhari da Muslim) basu fitar da shi ba  Albani  ya  inganta shi  
                 Istigfari ga muminai da musu adu'a zai tabbatar da al'amarin ka a kabari yayin tambaya  , Manzon Allah tsira  da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance in ya binne mamaci  sai ya tsaya gaba gare shi sai ya ce ku nemawa dan uwan ku gafara  kuma ku roka mishi tabbatuwa domin   yanzu za a tambaye shi  , mutanen kwarai na raya  kaburburan su ne ta hanyar lazimtar adu'o'i a ko wace salla, suna  neman tsari  daga fitinan  kabari , Annabi ya kasance yana adu'a Ya Allah ina neman tsarin ka daga azaban kabari da azabar wuta ,  da fitinar rayuwa da ta mutuwa,  da fitinan  masihuddajjal).

      HUDUBA NA BIYU
Musulmi mai hankali yana kiyaye wa daga guraren fitina da halaka,wanda ke lalata al'umarsa kuma ya fitine shi a kabarinsa, na daga ciki akwai yada karerayi da sadar da su, ya zo a hadisin Isra'i da Mi'iraji mai tsawo Jibrilu ya ce da Manzon Allah ( amma shi  mutumin da ka zo mi shi ana keta mukamukin sa  zuwa keyan sa ,  da hancin sa zuwa keyan sa da idanuwan sa  zuwa keyan sa , to lallai mutum ne yana wayan gari daga gidansa sai ya yi karyan da za ta bazu a duniya  ,  yana daga ciki kuma akwai cin riba da halatta shi    ya zo a hadisin isra'i da mi'i raji , amma mutumin da ka zo mi shi  yana iyo a korama yana hadiye duwatsu to  lallai shi maciyin riba  ne )  .
    Yana daga ciki mutumin da yake bacci ya bar sallan farilla da me kauracewa kur'ani , to a cikin hadisin isra'i da mi'iraji ( Amma mutumin da ka zo mishi yana dandaka kansa da dutse shi ne mutumin da yake daukan kur'ani ya yi watsi da shi , ya yi bacci kuma daga sallan farilla).
Yana daga cikin sabuba na azaban kabari yawo a tsakanin mutane da annamimanci da yin sake wurin tsarki , manzon Allah ya wuce wasu kaburbura  guda biyu sai ya ce :( Lallai su dinnan ana azabtar da su ne kuma ba akan wani abu mai girma ba ake azabtar da su, amma dayan su ya kasance ba ya tsarkaka daga fitsari, shi kuma dayan yana yawo da annamimanci).Sahihul Jami'i:  Albani.      
   

السبت، 17 مارس 2018

GARGADI A KAN ZUNUBAI DA SABON ALLAH


Hudubar Juma'a na Masallacin Annabi na shaikh Abdullah Dan Abdurrahman Al-Buaijan 21-6-1439 AH.

HUDUBAR FARKO :
  Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin sarki,  muna gode mishi kuma muna neman taimakonsa ,  kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu , da munanan ayyukanmu , duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi , duk wan da ya batar kuma babu mai shiryar da shi , na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya , kuma na shaida Annabi Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa ne, Allah ya turo shi don rahama ga  talikai, sai ya buda zukata, ya haskaka hankula da shi, ya buda makantattun idanuwa da shi, da kuraman kunnuwa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa  da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa har zuwa ranar sakayya .
Bayan haka :
Lalle da'a ita ce bin Allah sau da kafa  da biyayya ga Manzo, sabo kuma shi ne sabawa Allah da kirkiran bidio'i, mafi sharrin al'amura ita ce bidi'a da fararrun al'amura, da laifuka da abin da aka ki, mafi muninsu shine  sha'awe –sha'awe da shubuhohi.
Ku bi Allah cikin umarninsa , ku hanu game da abin da ya hane ku ya tsawatar,(ya ku wadanda suka yi imani ku bi Allah da takawa, a kan hakkin binsa da takawa, kuma kada ku mutu face kuna musulmai)
Ya ku bayin Allah!
Lalle Allah ya halicci mutum ya ba shi kyautan hankali da harshe,ya bashi sharia ya sanar da shi bayani, ya turo manzanni da hujjoji ya saukar da littafi da mizani, ya kaddara mutuwa da rayuwa, don ya gwada ku ya ga wanda ya fi kyan aiki .
Ya halicci mutum don ya mishi biyayya da zai haifar da yardarsa, ya hane shi ga  saba mishi da zai haifar da fushinsa, (To wanda ya aikata wani aiki gwargwadon nauyin zarra na alheri zai gan shi. kuma wanda aikatagwargwadon nauyin zarra na sharri zai gan shi ).
Ya sanya duniya gida na aiki da jarrabawa, ya rubuta mata karewa, gidan lahira kuma gidan hisabi da sakayya,ya rubuta mata dauwama da wanzuwa,(To wanda ya yi aiki na kwarai don kansa,wanda ya munana don kansa)
Ya tattalawa masu takawa  gidajen Aljanna, koramai na gudana daga karkashinsu,suna madauwama a cikinta har abada. Cikinta akwai abin da ido bai taba gani ba, kunne bai taba ji ba, bai kuma taba fadowa ga zuciyan wani dan 'adam ba, ya tanada, ya tanadawa kafurai wutan jahannama, ba ta ragewa kuma ba ta bari, mai nacewa ga jiki ce da kuna, suna masu zama a cikinta na wasu zamuna, ba su dandanar wani sani sanyi ko abin sha, face tafasasshen ruwa da rubabben jini, sakamako mai dacewa.
Kowani rai mai dandanar mutuwa ne, kuma ana cika muku ladanku ne a ranar Alkiyama, to wanda aka nesantar daga barin wuta kuma aka shigar da shi Aljanna to lalle ne ya tsira, kuma rayuwar duniya bata zama ba face jin dadin rudi.) Ali – Imran 185
Ya ku bayin Allah !
Lalle dan'adam ana jarraba shi da sha'awa da shubuhohi, yana tunkuduwa cikin jin dadi da hutu, ana jarabta shi da zunubai, da munanan laifuka, hakika makiyansa sun yi hayan masa da abokan fadansa, shaidan abokin tafiyansa ne kuma makiyinsa ne, makiyyinsa ne mai tsananin jayayya, ga rai mai yawan umarni da mummuna, kuma tana cikin jiki, ga gabbai masu musu ne kuma shaidu.
Hakika shaidan ya yi rantsuwa  ( sai ya ce :To ina rantsuwa  da buwayarka sai na batar da su gaba daya. Face bayinka tsarkakku daga gare su )Sad 82
Ya kuma bamu labari game da rai sai ya ce :    (Lalle rai mai yawan umarni ne da mummuna)Yusuf  52
Game da gabbai sai yace : ( A ranar da harsunansu zasu yi shaida akansu da hannayensu da kafafuwansu da abin da suka kasance suna aikatawa) Annur :24
(kuma suka cewa fatunsu don me kuka yi shaida akanmu? Suka ce Allah wanda ke sanya ko wani abu yayi furuci shi ne ya sanya mu mu yi furuci kuma shi ne ya halitta ku can da farko kuma zuwa gare shi za ake mayar da ku. Baku kasance kuna sani ba a boye cewa jin ku zai yi shaida a kan ku kuma ganinku zai yi,kuma fatunku zasu yi, kuma amma kun yi zaton Allah bai san abubuwa masu yawa daga abin da ku ke aikatawa ba,)
To shaidan na ingizawa zuwa ga sabo da laifuka masu halakarwa, rayi na umarni da munana da abin da aka ki, gabbai shaidu ne masu tabbatarwa, mai wayo shi ne wanda  ya yi wa kansa hisabi ya mata linzami don kar ya auka ga zunubai.
Ya ku musulmi!
Lalle aikata zunubai  da laifuka akwai cutuwa da kuma barna a ciki da ke haifar da fushin Allah da ukubarsa, da azabarsa, kuma yana janyo  saukar azabarsa da bala'insa. (kuma da yawa daga alkarya wadda ta yi tsaurin kai daga barin umarnin Ubangijinta da Manzanninsa, sai muka yi mata hisabi,hisabi mai tsanani, kuma muka azabtar da ita, azaba abar kyama. Sa'annan ta dandana masifar al'amarinta , kuma karshen al'amarinta ya kasance hasara. Allah ya musu tattalin wata azaba mai tsanani, sabo da haka ku bi Allah da takawa ya ma'abota hankula ).Dalak 8 -9.
To abin da ke faruwa ga musulmai na fitintunu da musibu  masu radadi da jarabawa da tsadan kaya da mulka irin na makiya, da fari da fako,da cututtuka da yunwa da bala'i  ba wani abu ya haifar da shi ba face sabon Allah da laifuka da zunubai, da abin ki.
Hakika Allah ya buga misali ga mai lura ya koro ayoyi ko akwai mai wa'azantuwa, ya bayyana  cewa zunubai da laifuka na daga mafi girman sabuba na gushewar ni'ima da saukar azaba, sai Allah ya ce :(kuma Allah ya buga misali, wata Alkariya ta kasance amintacciya natsatsiya  arzikinta yana je mata a wadace daga kowane wuri,sai ta kafurta da ni'imomin Allah sabo da haka Allah ya dandana mata tufafin yunwa da tsoro, sabo da abin da suka kasance suna sana'antawa, ). Annahl 112
To Abin mamaki ga  walakancin halitta a gun Allah Mabuwayi idan an saba umarninsa.
Ya ku bayin Allah!
Lalle hadarin sabo na girmama kuma ukubanta na kasaita da musibanta  idan aka wayi gari mutane sun saba da ita suna bayyana ta a fili jama'a na fito na fito da Allah, kuma dukkan al'uma na samun kubuta daga sabo banda masu bayyanawa, mutane ba za su halaka ba sai an basu hanzari akansu.
Ya ku bayin Allah!
Lalle bayyana sabo wani nau'i ne na watsi da hakkin Allah da bushewar  ido gare shi, da ja da mumunai da kara yawan masu sabo,da  kuma isar shi gurbin   sabon ne zuwa  ga wani,
Kuma da zamewa sababi na janyo su gare shi da kwadaitar da su, da kuma kasancewa  sababin sanya zunubai ga wanda bai yi inkari ba(hani ba). Duk wanda aka jarabce shi da wasu sabo to ya boye da boyewar da Allah ya mishi, kuma ya tuba zuwa ga Allah tuba na gaskiya.
Ya ku Musulmai!
 Lalle dogewa a kan zunubai  da sake jiki cikin aikin sabo, da dulmuya cikin laifuka da murna da su,da bushewan ido cikinta, da aminta daga makarkashiyar  Allah,da rena laifuka, abu ne da ke shelanta gafala da janyo fushin Allah, kuma sababi ne na tabewa da halaka, An karbo daga  Abdullahi dan Mas'ud Allah kara yarda a gare shi, yace : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : ku kiyayi rena kananan laifuka, domin su ne ke taruwa  akan mutum har su halaka shi, lalle Annabi ya buga misali game da su yace kamar mutane ne suka sauka jeji sai lokacin dafa abincin su ya yi, sai mutum ya je ya kawo kirya, wani mutum ma ya dauko kirya,har suka hada taru mai yawa, sai suka hura wuta suka dafa abinda suka jefa a  ciki). Ahmad ne.
Musiba na girmama  ga mai laifin idan ya ga kananan zunubai abin renawa an kididdige su,sun habaka ,sai ya firgita ya  ce :(Kaitonmu mene ga wannan littafi ba ya barin karama kuma ba ya barin babba face ya kididdige ta,to kuma suka sami abin da suka aikata halarce, kuma ubangijinka ba ya zaluntar kowa.)
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya  sun tabbata ga Allah da yake gafarta zunubai, ya suturce aibi, ya yaye bakin- ciki, yana shinfida hannayensa da dare ga masu laifin wuni don su su tuba,kuma yana shimfida hannayensa da rana ga masu laifin dare don su tuba su koma.
Ya ku bayin Allah! Ku ji tsoron Allah kada ku aikata zunubai kada ku rena shaninsu,  ku kankantar da su, ba abin da ya fi a gare ku, ku hadu da Allah da shi kamar karancin laifuka.
Ya jama'ar musulmi!
Lalle hadarin zunubai na kanzaga kuma yana tada hankali,bala'inta da musibanta  na girmama na tsoratarwa, idan ta zama abu sananne mutane suka  tabbatar da ita, baa umarni da kyakkyawa ko hani ga mummuna,  Allah Madaukakin sarki ya ce : An la'ani wadanda suka kafirta daga  banu Isra'ila, akan harshen Dauda da Isa da maryam, wannan kuwa sabo da sabawar da suka yi ne, kuma sun kasance suna ta'adi.sun kasance ba su hana juna daga abin ki, wanda suka aikata,hakika abin da suka kasance suna aikatawa ya munana.)
An karbo daga Abi bakra Allah ya kara yarda a gare shi ya ce ;Manzon Allah tsira da amincin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Lalle mutane idan sun ga munkari basu canja ba to suna kusa da Allah ya game su da azaba daga gare shi.).
Umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna na daga cikin dabia ta al'umar Muhammadu, kuma aminci ne daga saukar bala'i, kuma katanguwa daga  kaidin makiya da wawaye ,Allah Madaukakin sarki ya ce: Ku kasance, Allah ya yi umarni da shi ya kwadaitai a inda ya ce.(A cikinku a samu wata al'uma suna kira zuwa ga Alheri suna umarni da kyakkawa , suna hani da mummu ,  to lalle wadannan sune masu rabauta)
Ya Al'umar Muhammada ku yi umarni da kyakkya wa , ku hana munkari, Duk wanda , ya ga abinki to ya canza shi da hanunsa, idan ba zai iya ba to ya sanja shi da hannunsa,in ba zai iya ba da harshensa, idan bai iya ba da zuciyarsa, idan bai iya ba da zuciyarsa, wannan shine mafi raunin imani)
Ya ku bayin Allah!
Lalle ku din nan abin tambaya  ne  game da gidajenku da abin da aka ba ku kiwo,to ku ji tsoron Allah cikin 'ya'yanku da matayenku, ku sanar da su shariar Allah, kuma ku hana su fadawa ga abin da Allah ya haramta, ku tarbiyantar da su bisa halaye masu kyau da kyakkyawan dabiu, domin lalle zaa tambaye ku game da su gobe gaba ga Allah, kuma zasu zama shaidu akan ku, kuma zaa rubuta shaidar su kuma zaa tambaye su, a ranar da mai laifi zai yi fatan a fanshe shi daga azabar wannan rana da 'ya'yanan sa, da matarsa da dan'uwansa,  da danginsa da suke tattara shi,da wanda ke cikin duniya duka gaba daya sa'annan fansar ta sirar da shi.
Ku kula da abin da aka baku kiwo, kuma  (kada ku yaudari Allah, da Manzonsa, kuma ku yaudari amanoninku, alhali kuwa kuna sane. Kuma ku sani cew abin sani kawai dukiyoyinku da 'ya'yanku wata fitina ce, kuma lalle ne Allah a wurinsa akwai lada mai girma).
Ba wani mutum da Allah zai bashi kiwon wani abin kiwo,  ya zama ya zambace su, face Allah ya haramta Aljanna a gare shi.
Wanda ya yi kokari wurin gyaran mutanen gidansa, ya tsaida shariar Allah  a cikin abin da aka bashi kiwo,ya dasa musu imani a cikin zukatansu, zai kasance yana da lada kwatankwacin aikin da suka yi, ba tare da an tawaye wani abu na daga ladansu ba.
Ya tabbata daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce : (Idan dan'adam ya rasu ayyukansa zasu katse sai guda uku daga ciki akwai :Da na kwarai da  ya ke mishi adu'a ).
Ya jama'ar musulmai!
Lalle koyi da yammaci ya fadada, ya kutsa gidaje, da na'urori da hanyoyin sadarwa, sun rusa kyawawan halaye sun bata dabiu na kwarai , an wayi gari abin ki (MUNKARI) a jiya ya zama  shine  abin so (MA"ARUFI), abin da ya ke ma'arufi ne a jiya an wayi gari ana sifanta shi da ci-baya da rashi wayewa da fandarewa.
Abu Mas'ud Al'ansari ya shiga wa Huzaifa sai ya ce : ka mana wasiyya ya Baban Abdullahi, sai Huzaifa ya ce : Ase yakini bai zo ma ba? Sai yace : E ya zo, da buwayar Ubangiji na, sai yace : ka sani Bata hakikanin bata shine ka zama abin da ka ke ganinsa  a jiya mara kyau ya zama abu mai kyau, haka kuma abu da jiya ka ke gani mai kyau  to yau ya zama mara kyau , to na hore ka da juyawa,  addinin Allah daya ne.)           
  To ya ku bayin Allah ku riki sunna, Ina muku gargadi da fararrun abubuwa , domin dukkan fararren abu bidi'a ne, kuma dukkan bidi'a bata ne, kuma dukkan bata na wuta.
Ya Allah ka nuna mana gaskiya gaskiya ce ka bamu ikon bin ta, ka nuna mana karya karya ce ka ba mu ikon guje mata.
Ya Allah ka sanya mana son imani , ka kawata shi a zukatanmu, ka sa mu tsani kafurci da fasikanci da sabo,ka sanya mu cikin shiryayyu.
Ya Allah ka daukaka musulunci da musulmai,ka taimaki bayinka masu kadaita ka,
Allah ka sanya wannan gari cikin aminci da natsuwa, da sauran garuruwan musulmai,
Ya Allah ka kasance tare da masu rauni a garin suriya mai ruwa da itatuwa, ya Allah ka kare jininsu, ka suturce al'aurarsu, ka amintar da su daga tsoro.  Ya Allah ka musanya musu tsoron su da aminci, bayan rauninsu Allah ka basu nasara.
Ya Allah an zalunce su ka taimake su, ya Allah ka taimake su akan wanda ya zalunce su,
Ya Mai karfi  ya Mabuwayi.   


الجمعة، 23 فبراير 2018

KUNYA ALHERI NE DUKA


Hudubar Masallacin Annabi  na shaikh AbdulMuhsin Alkasim  7-6-1439AH
HUDUBAR FARKO :
  Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin sarki  muna gode mishi kuma muna neman taimakonsa , muna neman gafarar sa  , kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu , da munanan ayyukanmu , duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi , duk wan da ya batar kuma babu mai shiryar da shi , na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya , kuma na shaida Annabi Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa  da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa .
Bayan haka

Ku ji tsoron Allah - ya ku bayin Allah – ku yi riko da igiya mai karfi na musulunci .
Mabudin bautawa Allah da sirrin bauta masa na ga sanin sunayen Allah ne da sifofinsa.to sunayensa  Madaukaki duk kyawawa ne, sifofinsa duk Madaukaka ne.  Yana da  wata sifa ta bauta na musamman ga dukkan suna da sifa  tsarki ya tabbata a gare shi , yana daga cikin  abin da ke haifar da shi  da kuma abin da ya kumsa,  Allah yana son sunayensa da sifofinsa kuma  yana son bayyana alamomin su ga halittunsa , sai ya umarci bayinsa da su roke shi da su,  Allah Madaukakin sarki ya ce: (Kuma  Allah yana da sunaye masu kyau , sai ku roke shi da   su ). Kuma mafi soyuwan halitta zuwa ga Allah  shi ne wanda ya siffantu da sifofin da Allah ke kauna ,  wanda ya bautawa Allah da sifofin shi zai kusantu  zuwa ga rahamarsa , wanda ya kiyaye sunayen sa  zai saukar da shi a aljannarsa  daga cikin sunayen Allah   akwai ALHAYIYU wato mai kunya  kuma daga cikin sifofin sa akwai kunya ,  kuma Allah ya siffanta kan shi da ita   sai ya ce : (Lallai ne Allah ba ya jin kunyar ya bayyana wani misali,  kowane iri ne, sauro da  abin da yake  bisa gare shi ) .
  Manzon sa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ambace shi sai ya ce :( Lallai Allah mabuwayi da daukaka  mai kunya ne , kuma marufin asiri ne  yana son kunya da  suturcewa ) Abu Dauda ne ya rawaito .   Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( Lallai Ubangijin ku mai girma da daukaka Makunyaci ne, kuma mai karamci ne , yana jin kunyar bawansa  idan ya daga hannayensa biyu zuwa gare shi ya dawo da su haka banza ).Abu Dauda ne ya rawaito shi
             Ibn Alkayyim Allah ya mishi rahama ya ce : '' Kunyan Ubangiji Madaukakin sarki ga bawansa, abu ne da fahimta ba zai riske shi ba , hankali kuma ba zai gano yadda yake ba, domin shi wani kunya ne na karamci  da kyautatawa  da kuma kyauta da daukaka ''.
             Mafi girman kyawawan halaye cikin halittu kuma mafi daukakansu da kuma mafi girma a daraja da kima kuma mafi  yawan amfani; shi ne kunya , wata dabi'a ce  wadda ke sa  abar duk wani munanan dabi'u  kuma yana hana yin sakaci  a cikin hakkin  ma'abocin hakki , tushen sa da asalin  maddarsa daga rayuwa ne ,  kuma bisa iya gorgodon rayuwar zuciya  iya kasancewar kunaya a cikin ta  a duk lokacin da zuciya  ta fi rayuwa , sai kunya ta fi cika a cikinta   da karfi  kunya bata  gushe ba  al'amarin ta tabbatacciya ce , kuma amfani da  ita  wajibi ne tun  zamanin Annabawan  farko ,  kuma ba wani  Annabi face   ya kirayi al'umar sa zuwa gare ta kuma an turo shi da ita  ba a goge ta ba cikin abubuwan da a ka goge na shari'o'insu , kuma  ba a canza ta ba cikin abubuwan da ake canzawa , sabo da wannan al'amari  da ya bayyana karara  na daidai ne  an sanshi  kuma  falalar shi ya bayyana  dukkan hankula sun yi taraiyya bisa ga kyanta , duk wanda wannan ya kasance shi ne sifansa  bai  halatta a goge shi ko a canza shi ba, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Lallai yana daga cikin  abin da mutane suka riska  na maganan Annabawa  shi ne idan baka ji kunya ba ka aikata abin da ka ga dama ) Buhari ne ya rawaito
      Mafificin halittu ya siffantu da ita kuma Allah ya kyautata yabo ga ma'abotanta   to kuma mala'iku ma sun siffantu  da ita  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata  gare shi ya ce game da Usman : ( Ase ba zan ji kunyar mutumin da mala'iku suke jin kunyar sa ba ), Muslim ne ya rawaito  , Annabawa an san su a cikin mutanen su da haka,   halittu za su nemi ceto ranar alkiyama da Adamu da Nuhu Alaihimassalam , sai ko wannen su ya tuna zunuban shi sai ya ji kunya )  Musa amincin Allah ya tabbata a gare shi makunyaci ne , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce : ( Lallai Musa  ya kasance  mutum ne makunyaci  mai yawan suturcewa  ba a ganin wani abu na daga fatar jikin shi sabo da irin kunyar sa ), Buhari ne ya rawaito
      Annabinmu Muhammadu  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana da kaso mafi tsoka na daga kunya,  sabo da haka yakan  yi jirwayi da kamar wanka,  baya yin karara,   akan gane  kunyar sa daga fuskarsa,  Abu Sa'id Al khudri ya ce:  '' Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ( Ya kasance   mafi tsananin kunya  fiye da budurwar  da take cikin haudajin ta , kuma ya kasance idan ya tsani wani abu mukan gane a fuskar sa) Buhari da Muslim ne suka rawaito  shi 
       Ya kai ya komo a daren mi'iraji  tsakanin Musa da Ubangijinsa yana rokon a sassauta game da sha'anin sallah har zuwa lokacin da ya ce : " ( Hakika na ji kunyar Ubangiji na ") ,  a yayin da ya shiga da Zainab 'yar Jahash,  an kira mutane   don hakan, sai suka ci abinci suka fita  sai ya rage wasu mutane uku suna ta hira a dakin  sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ji kunyar ya ce  mu su wani abu ,  sai ya fita ya bar su  a dakin, sai Allah Mabuwayi da daukaka ya saukar da : (Ya ku wadanda suka yi imani kada ku shiga gidajen Annabi  face fa idan anyi izini a gare ku zuwa ga wani abinci ,   ba da kun tsaya jiran nunar sa ba , kuma amma idan  an kira ku, to , ku shiga   sa'annan idan kun ci, to ku watse , kuma ba da kun tsaya kuna masu hira da wani labari ba ,  lallai wannan  yana cutar da Annanbi,  to yana jin kunyar ku , alhali kuwa Allah baya jin kunya daga gaskiya) Ahzab 53  Buhari da Muslim ne suka rawaito
            Kuma Usman Allah ya yarda da shi ya zama abin buga  misali a  akunya cikin sahabbai,  watarana  ya shigo ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  sai  Manzon Allah ya zauna ya daidaita tufafin shi   sai aka tambaye shi game da haka sai ya ce : ( Lallai Usman mutum ne makunyaci  na ji tsoron kada na mishi izini a wannan yanayi ya ki isowa zuwa gare ni , cikin bukatar sa ) Muslim ne ya rawaito .
         Mace an halicce ta bisa kunya  , kuma kunya ce adon ta  kuma kariya ne a gare ta da aminci   Aisha Allah ya kara yarda a gare ta ta ce " Ya Manzon Allah  ai ita budurwa tana jin kunya sai ya ce yardan ta –da auren - ai shi ne yin shurun ta  " Buhari ne ya rawaito
      'yar ma'abocin madyana  tazo  kunya na lullube da ita ta suturce fiskanta da hanunnta da kuma tufafin ta Allah madaukakin sarki ya ce : ( Dayan su sai ta zo tana tafiya bisa kunya  sai tace lalle mahaifi na na kiranka don ya saka maka abin da ka yi na shayar da mu)   .Kuma Aisha uwar muminai  Allah ya yarda da ita,  kunya ya kaita da ta suturce kanta  a cikin dakinta sabo da Umar  Allah ya yarda da shi   bayan an binne shi ( a  dakin ta ) Allah ya kara yarda  a gare ta, ta ce: "Na  kasance ina shiga  daki na   wanda aka binne  Manzon Allah a cikinsa da mahaifi na sai na cire tufafi na,  sai na ce ai wannan mijina ne, wannan kuma mahaifina  ne , to amma a lokacin da aka binne Umar tare da su   to wallahi ban shiga dakin ba face sai ina daure da tufafi na  a jiki na sabo da kunyar umar  )Ahmad ne ya rawaito .
          Kuma ga wata mace da ta yi hakuri bisa jarabawa   amma bata yarda da cire rigar kunya  ba , sai sakayyar ta  ya kasance aljanna :  Abdullahi Dan Abbas Allah ya kara yarda a gare su shi da mahaifin shi ya ce ga  Ada Dan Abi Rabah  Allah ya mishi rahama ya ce : " Ase   ba zan nuna maka mata 'yar aljanna ba ? sai na ce e;  sai ya ce : " wannan bakar matar  ta zo ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  sai ta ce : "   Lallai ni  ina da cutar  farfadiya  har nakan  yaye daga tufafi na,  to ka roka min Allah  ya raba ni da ita,  sai ya ce in kin so ki yi hakuri kina da aljanna  in kuma kin so in roka miki Allah ya baki lafiya " sai ta ce : "zan  yi hakuri,  sai dai nakan yi tsiraici , to ka rokamini  Allah kada na rinka yin tsiraici  sai ya roka mata Allah" ) Buhari da Muslim ne suka rawaito
       Kuma tana cikin dabi'u masu daraja wanda har mutanen jahiliyya ma sun wanzu a kan ta, Abu Sufyan Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : " a yayin nan da Hiraklu ya tambaye shi game da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,  kuma a lokacin yana kafurci : (Wallahi ba don kunya ba a wannan ranar kar mutane na su taba kama ni da karya a wannan ranar da na yi mishi karya , a lokacin da ya tambaye ni game da  shi, amma sai dai na ji kunya kar a same ni da karya sai na fada mishi  gaskiya).
      Da kunya ne a ke samun walwala   a riski kuma sabubanta, dukkan  ta alheri ne  , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Kunya alheri ne dukanta  ko kuma ya  ce  kunya  dukkan ta alheri ne )Muslim ne ya rawaito
      Karshen ma'abocinta alheri ne    har abada  kuma ba zai hadu da nadama ba har abada   , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  yana cewa : ( Kunya bata kawo wani abu sai alheri). Muslim ne ya rawaito
      Ibn Kayyim Allah ya mishi rahama ya ce :" kunya wani sinadari ne na rayuwar zuciya kuma ita ce tushen dukkan alheri ,  rasa ta kuma rasa alheri ne gaba dayan shi  )
Yana daga cikin mafi girman alherin da ke cikin ta akwai sabarwa rayi  da kyawawan dabi'u da kuma nisantar munanan dabi'u , idan kunayar mutum ta tsananta sai a kare mutuncin sa kuma sai a binne laifukansa a kuma yada kyawawansa.
          Yana daga cikin  akidar ahlussunna waljama'a ; cewa imani fadi ne  da kudiri da aiki,  kunya wani yanki ne daga gare shi   Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata  a gare shi ya ce:( Imani yanki ne sittin da dori kuma kunya wani yanki ne na imani )    Buhari da Muslim ne suka rawaito shi .
 Ibn Hibban Allah ya mishi rahama ya ce :"kunya  na daga cikin imani kuma mumini na aljanna, ba za a  zare kunya daga wani ba face an zare imanin shi  ".
       Manzon Allah ya wuce wani mutum yana zargin dan uwansa game da  kunya, yana cewa : " Lallai kai kana jin kunya  har kamar yana cewa  da shi  ya kai ma yana cutar da kai , sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( kyale shi, lallai  kunya na daga cikin imani) . Buhari da muslim ne suka rawaito
      Ba ukubar da Allah zai yi ga zuciya da tafi a kwashe kunya daga gare ta, Ibn Umar Allah ya kara musu yarda  ya ce : " Lallai kunya da imani an hada su tare  idan an dauke dayan su sai a dauke dayan ma "  .
       Kunya da'a ce da ke janyo wasu biyayya  da za su kai  ma'abocinta zuwa ga tsentseni wanda kuma ya barta to zai aikata abin da yake kishiyan haka , Umar Allah  ya kara yarda a gare shi ya ce: " wanda kunyar sa ta karanta to tsentseninsa zai karanta, wanda tsantsenin sa ya karanta zuciyar sa ta mutu.
       Kunya na daga cikin abu mafi girma da ke  shiga tsakanin mutum  da  aikata sabo , makunyaci na  katse ayyukan sabo da kunya kamar yanda imani ke katse sabo,  idan an tube kunya daga bawa to sai ya zama ba abin da  ya rage da zai hana shi aikata munanan abubuwa   da kuma halaye marasa kyau,  sai ya zama kamar bai da imani,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( Idan  mutum bai ji kunya ba to ya aikata abin da ya so). Buhari  ne ya rawaito
                  Ibn Abdulbar Allah ya mishi rahama ya ce : " Duk wanda bai da kunyan da zai katange shi daga abin da Allah ya haramta , to daya ne a gare shi aikata aikin karamin zunubi da babba,   a cikin hadisin akwai gargadi da narkon azaba game da karancin  kunya "
 Zunubai na raunana kunya daga bawa har ma ya tafi gaba daya daga gare shi ,  ya zamana ba zai dame shi ba don mutane sun san halin shi ko suka gane abin da ya ke aikatawa , kai hakika ma yakan bada labari bisa halin shi da munanan  ayukan shi .
                 A kunya akwai ado da kawa ga ma'abocinta   Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Batsa baya shiga cikin komai sai ya bata shi kunya kuma baya shiga cikin komai sai ya kawata shi – wato ya adonta shi )  Tirmizi ne ya rawaito shi
                  Kunya na kira zuwa ga izzar rayi da kare ta , ba zai tambayi mutane wani abu ba ko da ya bukaci hakan , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Ba miskini shi ne wanda ya ke kai komo a kan loma daya ko biyu ba, sai dai miskini shi ne wanda ba yi da wadata kuma yana kunya, ko kuma baya tambayan mutane bisa naciya ) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
                Kunya kamar wani adireshi ne na kyakkyawan dabi'a da ladabi.  Annabi  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tambaya : ( Game da itaciyar da take kama da musulmi , sai Ibn Umar Allah ya yarda da su ya ce : ( sai ya fado a zuciya ta cewa bishiyar dabino ne sai na ga Abubakar da Umar ba su yi magana ba, sai   na ji nauyin  na yi magana. a wani lafazin kuma ya ce : " sai na ji kunya ) Buhari da muslim ne suka rawaito .
         Mutum ana sakanya mishi da irin aikin da ya yi,  na daga cikin amfanin kunya da kyakkyawan sakayyan ta Allah na  jin kunyan  ma'abotanta  , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: ( Amma dayan sai ya ji kunya sai Allah ya ji kunyar sa ) Buhari da Muslim ne suka rawaito 
           Tushen kunya kuma shi ne a ji kunyar Allah madaukaki, ta yanda kar ya gan ka  a inda  ya hane ka,  kar ya rasa ka kuma a in da ya umarce ka ,    Allah ne ya fi cancanta da a ji kunyar sa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: ( Ku ji kunyar Allah cancantar kunyar sa) Tirmizi ne ya rawaito  
    Kunyar  Allah shi ne Allah ya jefa wani haske a zuciya da zai sa ya rinka ganin Allah gaba gare shi lokacin da yake shi kadai ko a cikin jama'a,  jin kunyan Allah  na tabbatuwa ne  ta hanyar tsinkayar baiwar sa da girman ni'imominsa tare da halarto da laifuka na rayi tare da gazawanta , kuma da sanin cewa yana tsinkayan abin da yake na  sirri da wanda ya fi boyuwa: ((Allah) Ya san yaudarar idanu da abin da kiraza ke boyewa) sura Al-Gafir aya 19  Allah madukakin sarki ya ce : (  Suna neman boyewa daga mutane  kuma ba sa neman boyewa daga Allah  alhali kuwa shi yana tare da su ).
 Idan bawa ya san cewa Allah madaukakin sarki yana kallon shi ;  kuma cewa  yana   gaban idon sa ne kuma yana jin sa  kuma  ya kasance mai jin kunya to sai ya ji kunyar kada ya kutsa zuwa ga  abin da zai fusata  shi  tare da mutum akwai mala'ikun  da ba sa rabuwa da shi yana daga cikin karrama su ka ji kunyar su (  Lalle ne a kanku  hakika akwai  matsara . masu daraja marubuta . Suna sanin abin da kuke aikatawa )  .
      Ibnul  Kayyim  Allah ya mishi rahama ya ce : " Ai ku  ji kunyan wadannan matsara din ku karrama su   ku ga kimar su   , ku ji nauyin su ganku  kuna aikata abin da ku ke jin kunyar wasun ku su ga kuna aikatawa ". 
            Jin kunyan mutane yana haifar da mutunci da kyawawan dabi'u  kai ko da ma a ce  mutum musulmi   bai samu wani Abu daga dan uwan shi ba sai kunyar  sa da zai hana shi aikata  sabo to ya isar mishi, wannan wani  alheri ne da zai taimakawa ma'abocin shi bisa jin kunyar Allah , to duk wanda baya kunyar mutane  to baya kunyar Allah , haka kuma duk wanda   ya zauna da ma'abota kunya , kunyar shi za ta sabunta   .
         Wanda ya fi dacewa mutum ya girmama shi ne kansa , duk mutumin da ya aikata wani aiki a sirrace  wanda ake jin kunyar aikata shi a  bayyane to bai kimanta kan sa ba,  wanda ya ji kunyar mutane bai ji kunyar kansa ba  to kansa ta fi walakantuwa a gunshi fiye da wanin shi  wanda ya ji kunyan wani kuma ya ji kunyar kansa bai ji kunyar Allah ba to baisan Ubangijin sa ba,  wanda  kunya ya lullube masa tufafin shi to mutane ba za su ga aibin shi ba.
   Bayan haka ya ku Musulmai   to musulunci addini ne na kyawawan halaye da  kyawawan dabi'u , ya tattaro daga halayya mafi kyansu   da sifofi kuma mafi daukakan su  ba wani alheri face ya yi umarni da shi , ba wani sharri kuma face ya yi gargadi game da shi,  to wajibi ne gare mu muyi riko da shi  kuma muyi alfahari da shi  kuma mu kira  mutane zuwa ga shi , jin kunyar Allah shi ne ta hanyar bin umarninsa  da kuma nisantar saba mishi .
       INA NEMAN TSARIN ALLAH DAGA SHARRIN  SHAIDAN  ABIN  JEFEWA
(Kuma wane ne ya fi  kyau ga addini daga wanda  ya sallama fuskar sa ga Allah alhali kuwa yana mai kyautatawa kuma ya bi akidar Ibrahim yana mai karkata ga gaskiya )
 Allah ya sa mini albarka ni da ku cikin alkur'ani mai girma,  kuma Allah ya amfane ni da ku da abinda yake cikin sa na daga ayoyi da ambato mai hikima , ina fadin wannan magana tawa kuma ina mai neman gafarar  Allah  da ni da ku da dukkan musulmai  daga dukkan zunubai ku nemi  gafarar shi lallai shi mai gafara ne mai jin kai
 HUDUBA TA BIYU 
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa kyautatawan sa  , godiya ta tabbata a gare shi bisa  datarwar sa da baiwarsa na shaida  ba abin bautawa da gaskiya  sai Allah shi kadai yake bashi da  abokin tarayya   muna mai girmama sha 'anin sa,  na shaida Annabinmu Muhammad bawan sa ne kuma mManzon sa ne tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan sa da sahabbansa  da aminci tabbatacce mai yawa ,
 Ya ku Musulmai   :
  Kunyan da yake abin yabawa a maganan Annabi  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ita ce   wannan dabi'ar  da ke sanya mutum ya aikata kyakkyawan abu ya bar mummuna amma rauni da gazawa, Wanda ke sa gajartawa a wani abu na daga hakkokin Allah, ko hakkokin bayinsa,wannan ba su da alaka da kunya a wani abu, in ya hana ma'abocinsa wani alheri to bai zama abin a yaba ba. Aisha Allah ya kara yarda a gare ta ta ce : (Madalla da matayen Ansar kunya bai hana su neman fahimtar addininsu ba) Muslim ne ya rawaito.
Babu kunya cikin neman sanin addini, wanda ya bar ilimi don kunya to zai zauna cikin jahilci har abada ya hana kansa alheri.
Mujahid Allah ya masa rahama ya ce :  ( Mai kunya ko Mai girman kai ba zai samu ilimi ba)
Kuma ku sani Allah na umartanku da salati da aminci ga Annabinsa    
           ( lalle Allah da malaikunsa suna salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce.)  
               
  










































السبت، 10 فبراير 2018

TARBIYANTARWA DA KAUNA

Hudubar Masallacin Annabi  na shaikh Abdulbari subaiti 23-5- 1439 AH
Hudubar farko
Musulunci na raya tashi da nauyin mas'uliyya a cikin zuciyar musulmi: mafi girman mas'uliyya shine kula da yara da tarbiyantar da su bisa turba da ginshiki na  addini da kyawawan halaye, wanda addini ne mabubbuga na duk wasu halaye na mutunci, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( Dukkan ku Makiyaya ne, kuma zaa tambayi kowannenku abin da aka ba shi kiwo) Bukhari ne ya rawaito.
Idan tarbiya ta yi rauni zaa wayi gari  damuwar wanda  ake tarbiyantarwa  da tunanin shi  kawai  yadda zai kashe  yunwarsa  da kosar da sha'awarsa, yana tafiya duk inda zai kai shi ga holewa da morewa na jin dadin rayuwa. Allah Madaukakin sarki ya ce : (Lalle ne Allah na shigar da wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan  kwarai a gidajen Aljanna, kogunan ruwa na gudana  daga karkashinsu, kuma wadanda suka kafirta, suna jin dan dadi (a duniya)  kuma suna ci kamar yadda dabbobi ke ci, kuma wuta ita ce mazauni a gare su.) Muhammad:12
Abin da ya fi karfin tasiri a tarbiya ita ce zuciya, idan ta gyaru to sauran jiki ya gyaru, to idan ya lalace to sauran jiki ma ya baci, (Domin lalle ne idanun basu makanta, amma zukata wadanda ke a cikin kiraza su ke makanta.)   Al-Hajj 46
     Idan zuciya ta gyaru ta yi kyau sai hankula su nuna su kuma rayuwa ta haskaka jiki, gabbai kuma su rusuna, Allah Madaukaki ya ce : ( shin lokaci bai yi ba ga wadanda suka yi imani  zukatansu su yi tawalui ga ambaton Allah da abin da ya sauka daga gaskiya.) Al-Hadid:16
Lalle ba makawa kauna  wani tushe ne mai asali daga koyarwar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, shi ne zancen  ruhi kuma sako ne daga zuciya zuwa zuciya, gurin tarbiyya da gyara. Kuma hakika Allah ya kimtsa zukatan iyaye biyu bisa son 'ya'ya da suke bawa tarbiya, Usama Dan Zaid na cewa Manzon Allah ya kasance yana dauka na ya zaunar da ni akan cinyarsa ya kuma zaunar da Hasan kan daya cinyar sai ya game su sannan ya ce : (ya Allah ka tausaya musu ni ma ina tausaya musu) Bukhari ya rawaito, a wata riwayar : (ya Allah lalle ni ina son su to ya Allah  ka so su) Tirmizi ne ya rawaito da isnadi ingantacce.
Na daga cikin alamomin tarbiyantarwa na bayyane  da kauna akwai sumbatar yara da manna su a jiki, Manzon Allah ya sumbaci Hasan a tare da shi akwai Akra Bin Al-Habis zaune sai yace :Ina da yara goma amma ban taba sumbatarsu ba sai Manzon Allah ya ce : (Duk wanda ba ya tausayawa to ba zaa tausaya masa ba,Tirmizi ne ya rawaito da isnadi ingantacce,
Manzon Allah ya kasance yana cikin huduba ga sahabbansa sai ga Hasan da Husaini sun zo suna sanye da tufafi jajaye suna tafiya suna faduwa, sai Annabi ya sauka daga kan minbari ya daga su ya dora su kan hannayensa,sannan ya ce Allah ya yi gaskiya (Dukiyoyinku da 'ya'yanku fitina dai ne) na  kalli yarannan biyu kanana suna tafiya suna faduwa sai na gaza hakuri na yanke zance na na daga su. Tirmizi da Nasa'I ne suka rawaito da isnadi ingantacce.
Manzon Allah ya kasance yana raha da yara kuma yana musu tawali'u, tare da la'akari da abin da ya kebance su, yace da dayansu (kai mai kunnuwa biyu.) Nasa'I ne ya rawaito da isnadi ingantacce. Yana cewa ga wani yaron kuma :( Ya Baban Umair menene labarin kanarin ka)?Bukhari da Muslim ne suka rawaito.       
 Kada iyaye biyu su manta cewa na daga cikin abu mafi girma da amfani  da tasiri a hanyoyi na tarbiya da kauna a aikace akwai lazimtar  adu'a ta shiryuwa da datarwa da gyaruwa da kariya ga wanda ake tarbiyantarwa, to bayin Mai rahama cewa suke yi a aduarsu : (Ya Ubangijinmu ! ka bamu sanyin idanu daga matanmu da zuriyarmu) Al-Furkan 74
Ga Annabi Zakariyya yana cewa : (sai ka ba ni wani mataimaki daga wajenka, ya gaje ni kuma ya yi gado daga gidan yakubu, kuma ka sanya shi yardajje ya Ubangiji!) Maryam 5-6
Ga Annabi Ibrahim yana cewa :  (Ya Ubangiji ka ba ni (abokin zama) daga salihan mutane)Assaffat 100 (Ya Ubangiji ka sanya ni mai tsayar da sallah  kuma daga zuriyyata).Ibrahim :40
Amma yi musu mummunar adu'a hani ya zo kan hakan, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :(kada ku yi mummunar adu'a a kanku, kuma kada ku yi mummunar adu'a ga  'ya'yanku, kuma kada ku yi mummunar adu'a ga dukiyarku, domin kar ku yi muwafaka da lokacin amsawa  sai a amsa muku) Muslim ne ya rawaito
Abin nkoyi mai kyau wani tushe ne na tarbiya, kuma haske ne na tsarkaka, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Ka ce: idan kun kasance kuna son Allah to ku bi ni, Allah ya so ku, kuma ya gafarta muku zunubanku, kuma Allah Mai gafara ne Mai jin kai).Al-Imran :31
 Kuma abu ne da bai buya cewa kwaikwayo da koyi na da tasirin da ya fi fadi da karatu da  sauraro,
Sabo da muhimmancin koyi ne ma da hadarin da ke tattare da shi Allah ya ke cewa :(Ya ku wadanda  suka yi imani! Don me ku ke fadin abin da ba ku aikatawa? Ya girma ga zama abin kyama a wurin Allah. Ku fadi abin da ba ku aikatawa). Assaf : 2-3  
Kauna na wanzuwa da karfafuwa da dawwama har a lokacin zamewa (kuskure) da gajartawa, wannan ita ce koyarwar Manzon Allah , hakika wani mutum ya zo mishi sai ya ce: ya Manzon Allah na halaka ! sai ya ce : (Me ke gare ka?) sai ya ce : na aukawa mata ta a halin ina azumi, sai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :(Ko kana da wuyaye da za ka 'yanta? Sai ya ce : A'a. sai yace :(To za ka iya yin azumin wata biyu a jere?) sai yace :A'a. sai ya ce :(To zaka iya samun ciyar da miskinai sittin ?) sai ya ce :A'a). sai manzon Allah ya dan zauna jim kadan muna halin haka sai i aka  kawo wa Annabi  kwando  a cikin shi akwai dabino, kwando wata tasa ce ta awu   sai ya ce ina mai tambaya? Sai yace : Ga ni sai Manzon Allah ya ce karbi wannan ka yi sadaka  da shi, sai ya ce : ga wanda ya fi ni talauci ya Manzon Allah? To na rantse da Allah! ai duk  kewayen madina a tsakanin duwatsunta biyu ba mutan gidan da  suka  kai iyalan gida na  bukata.sai Annabi yayi dariya har fikarsa suka bayyana sai yace : ka ciyar da shi ga iyalanka).Bukhari ne ya rawaito.
A yanayi na kauna mai tarbiyantarwa ba zai shakala yin amfani da hikima da kyakkyawan fadakarwa da tausasa zance, da saukin hali, tare da nesatan amfani da karfi da suka da walakantarwa,  Allah Madaukakin sarki ya ce: (Ka yi kira  zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima da wa'azi mai kyau, kuma ka yi jayayya da su da magana wadda take mafi kyau.)ANNAHL -125
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : Lalle Allah Mai sauki ne,kuma yana son saukakawa, kuma ta hanyar sauki ya kan bada abin da bai bada shi ta hanyar karfi ko waninsa.) Muslim ne ya rawaito.
Ya ce da balaraben kauyen da ya yi fitsari a masallaci: (ku kyale shi, ku kwarara bokitin ruwa ko guga guda a kan fitsarin  nashi abin sani kawai an turo ku ne kuna masu sauki baa turo ku kuna masu tsanani ba).Bukhari ne ya rawaito.
Kamar yadda girmama wadda ake tarbiyantarwa da yi mishi maraba da nuna haba-haba da shi, koyarwa ne na Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. A'isha Allah kara yarda a gare ta ta ce : Fadima ta fiskanto tana tafiya, tafiyarta irin na Annabi sai Annabi yace : (Maraba da 'ya ta )sannan ya zaunar da ita a damansa ko hagunsa) Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Jiki na da gudumawa da yake bada wa gurin tarbiyyantarwa da kauna; kamar murmushi da fara'a ta gaskiya, da shafa irin na shauki, da kalmomin kwantar da hankali, da tausayawa irin na zuci.
Mai bada tarbiya ba zai yi sakaci da dama da ya samu ba na halrtowar hankali zuwa gare shi face ya dasa kyawawan dabiu ba tare da kankantar da hankalin yaro ba ko renarwa.
An karbo daga Abdullahi dan Abbas Allah kara yarda a gare shi da mahaifin shi yace : wata rana na kasance a bayan Annabi sai ya ce: ya kai yaro zan sanar da kai wasu kalmomi: ka kiyaye Allah zai kiyaye ka,ka kiyaye Allah za ka same shi a gaba gare ka)Tirmizi ne ya rawaito da isnadi ingantacce.
Tarbiyantarwa da kauna na bukatar yanayi  da iyalai zasu game su dukule,su so juna , ta inda zasu samu farinciki da  walwala su yi wasa da bai sabawa shariar wannan addini ba, Aisha Allah kara yarda a gare ta tana cewa :Na kasance a wata tafiya tare da Annabi  sai muka yi tsere  da shi sai na yi galaba a kan shi,da kafafuwa ta,a yayin da na yi jiki muka sake tsere da shi sai ya yi galaba a kai na, sai ya ce : (To da wannan ni ma na rama wancan galaba da aka yi a kai na.)Abu Dawuda ya rawaito da isnadi ingantacce.
An karbo daga gare –Allah kara yarda a gare ta- ta tace: (na ga Manzon Allah a kofar daki na ga habashawa suna wasa a masallaci Annabi ya kare ni da mayafinsa ina kallon wasar tasu.)Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Tarbiyantarwa da kauna na bukatar kulawa da adalci wajen bayyana kauna ga yara, sai ya fadada  so da ya ke musu ya game su  gabadayansu ba tare da wariya ba,
Yayin da Annabi yusuf ya yi mafarki (lalle ne ni na ga taurari goma sha daya, da rana da wata na gan su suna masu sujada a gare ni) sai mahaifinsa Annabi  Yakub  -Amincin Allah ya tabbata a gare shi - ya ce da shi : (ya karamin da na! kada ka labarta mafarkinka ga 'yan uwanka har su kulla maka wani  kaidi,  lalle shaidan ga mutum makiyi ne  bayyananne.) yusuf 4 &5
Manzon Allah ya ki ya shaida kyautar da wani mahaifi ya bawa daya daga cikin 'ya'yansa yace : (Ni ba zan yi shaida na zalunci ba). Bukhari ne ya rawaito.
Tarbiyantarwa ta hanyar kauna da kosar da zukata da sosa mata inda ya ke mata kaikayi shiryarwa ne na Annabi kuma bukata ce aka halicci mutum a kanta,kuma ya fi karfi ta bangaren  'ya'ya mata Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Wanda aka jarabce shi   da wani abu na daga wannan 'ya'ya  matan , sai ya kyautata musu to za su kasance  kariya a gare shi daga wuta) buhari da muslim ne suka rawaito  lafazin na Buhari ne ,  : kyautatawa ga 'ya'ya mata ta hanyar koyar da su da  tada su akan kamun  kai, da nesantar da su daga abin da Allah ya haramta , na daga tsiraici da bayyana jiki   .
                 Da dora yara maza a tafarki tsayayya  na aiki mai amfani , da kuma  shirye-shirye na aikin alheri wanda zai daga manufar su  ya kuma  kare su daga fadawa  cikin abubuwa marasa muhimmanci  da yawon banza.
       Yana daga cikin abin da ke warware tarbiyantarwa da kauna ; akwai shagwabantar  da yara  ta hanyar amsa musu duk  abin da suka nema  da abubuwan  kwadaye-kwadayen  su da kuma yin sakaci ta bangaren ladabtar da su da gyara musu kusakuran su : to jajarcewa wani lokaci yana cikin kauna ,: musgunawa uwa a gaban 'ya'ya yana toshe kofar soyayya  amma bayyana zunubai da fandarewa da iyaye za su yi a gaban 'ya'yan su to hanya ne mai rusa tarbiya Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (  ya isa zunubi ga mutum da ya sarayar da  wanda yake ciyarwa ) Abu Dauda da Ahmad suka rawaito da isnadi ingantacce  .
           HUDUBA TA BIYU
Hakika hanyoyin tasiri na zamani sun habaka , kuma sun haifar da wani sanje- sanje na tushe  a tunani da fahimta da dabi'u, har a ka wayi gari suna  gogayya  da  gudumawar da iyaye suke bayarwa na tarbiyan 'ya'yayen su ,: to  a nan ne muhimmancin tarbiyantarwa  da kauna zata bayyana, da kuma bashi mafaka  da kuma  gina gada mai karfi na aminci  da sabunta salo,  da shuka kyawawan dabi'u da zaburantar da himmar kafafen ilmantarwa da tarbiyantarwa , don tashi da sakonnin su   wurin kiyaye   madosan al'uma da fatanta nan gaba , da kuma kiyaye arzikin kasa , ta hanyar bada kariya ga ginshiki na addini da kuma dabi'u  da bada kulawa ga matasa ,  da kuma  abin da suke burin zama nan gaba  da kuma kiyaye radadin su da damuwan su .
Allah Madaukakin sarki ya ce : ( Ya ku wadan da suka yi imani ku karewa kan ku da iyalan ku wata  wuta makamashinta  mutane da duwatsu ne.