Hudubar Masallacin Annabi na
shaikh Abdulbari subaiti 23-5- 1439 AH
Hudubar farko
Musulunci na raya tashi da nauyin mas'uliyya a cikin zuciyar musulmi:
mafi girman mas'uliyya shine kula da yara da tarbiyantar da su bisa turba da
ginshiki na addini da kyawawan halaye,
wanda addini ne mabubbuga na duk wasu halaye na mutunci, Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( Dukkan ku Makiyaya ne, kuma zaa
tambayi kowannenku abin da aka ba shi kiwo) Bukhari ne ya rawaito.
Idan tarbiya ta yi rauni zaa wayi gari
damuwar wanda ake tarbiyantarwa da tunanin shi kawai yadda zai kashe yunwarsa
da kosar da sha'awarsa, yana tafiya duk inda zai kai shi ga holewa da
morewa na jin dadin rayuwa. Allah Madaukakin sarki ya ce : (Lalle ne Allah
na shigar da wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan kwarai a gidajen Aljanna, kogunan ruwa na
gudana daga karkashinsu, kuma wadanda
suka kafirta, suna jin dan dadi (a duniya)
kuma suna ci kamar yadda dabbobi ke ci, kuma wuta ita ce mazauni a gare
su.) Muhammad:12
Abin da ya fi karfin tasiri a tarbiya ita ce zuciya, idan ta gyaru to
sauran jiki ya gyaru, to idan ya lalace to sauran jiki ma ya baci, (Domin
lalle ne idanun basu makanta, amma zukata wadanda ke a cikin kiraza su ke
makanta.) Al-Hajj 46
Idan zuciya ta gyaru ta yi kyau sai hankula
su nuna su kuma rayuwa ta haskaka jiki, gabbai kuma su rusuna, Allah Madaukaki
ya ce : ( shin lokaci bai yi ba ga wadanda suka yi imani zukatansu su yi tawalui ga ambaton Allah da
abin da ya sauka daga gaskiya.) Al-Hadid:16
Lalle ba makawa kauna wani tushe
ne mai asali daga koyarwar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,
shi ne zancen ruhi kuma sako ne daga
zuciya zuwa zuciya, gurin tarbiyya da gyara. Kuma hakika Allah ya kimtsa
zukatan iyaye biyu bisa son 'ya'ya da suke bawa tarbiya, Usama Dan Zaid na cewa
Manzon Allah ya kasance yana dauka na ya zaunar da ni akan cinyarsa ya kuma
zaunar da Hasan kan daya cinyar sai ya game su sannan ya ce : (ya Allah ka
tausaya musu ni ma ina tausaya musu) Bukhari ya rawaito, a wata riwayar : (ya
Allah lalle ni ina son su to ya Allah ka
so su) Tirmizi ne ya rawaito da isnadi ingantacce.
Na daga cikin alamomin tarbiyantarwa na bayyane da kauna akwai sumbatar yara da manna su a
jiki, Manzon Allah ya sumbaci Hasan a tare da shi akwai Akra Bin Al-Habis
zaune sai yace :Ina da yara goma amma ban taba sumbatarsu ba sai Manzon Allah
ya ce : (Duk wanda ba ya tausayawa to ba zaa tausaya masa ba,Tirmizi ne ya
rawaito da isnadi ingantacce,
Manzon Allah ya kasance yana cikin huduba ga sahabbansa sai ga Hasan da
Husaini sun zo suna sanye da tufafi jajaye suna tafiya suna faduwa, sai Annabi
ya sauka daga kan minbari ya daga su ya dora su kan hannayensa,sannan ya ce
Allah ya yi gaskiya (Dukiyoyinku da 'ya'yanku fitina dai ne) na kalli yarannan biyu kanana suna tafiya suna
faduwa sai na gaza hakuri na yanke zance na na daga su. Tirmizi da Nasa'I ne
suka rawaito da isnadi ingantacce.
Manzon Allah ya kasance yana raha da yara kuma yana musu tawali'u, tare
da la'akari da abin da ya kebance su, yace da dayansu (kai mai kunnuwa
biyu.) Nasa'I ne ya rawaito da isnadi ingantacce. Yana cewa ga wani yaron kuma
:( Ya Baban Umair menene labarin kanarin ka)?Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Kada iyaye biyu su manta cewa na
daga cikin abu mafi girma da amfani da
tasiri a hanyoyi na tarbiya da kauna a aikace akwai lazimtar adu'a ta shiryuwa da datarwa da gyaruwa da
kariya ga wanda ake tarbiyantarwa, to bayin Mai rahama cewa suke yi a aduarsu :
(Ya Ubangijinmu ! ka bamu sanyin idanu daga matanmu da zuriyarmu) Al-Furkan
74
Ga Annabi Zakariyya yana cewa : (sai ka ba ni wani mataimaki daga
wajenka, ya gaje ni kuma ya yi gado daga gidan yakubu, kuma ka sanya shi
yardajje ya Ubangiji!) Maryam 5-6
Ga Annabi Ibrahim yana cewa : (Ya Ubangiji ka ba ni (abokin zama) daga
salihan mutane)Assaffat 100 (Ya Ubangiji ka sanya ni mai tsayar da sallah kuma daga zuriyyata).Ibrahim :40
Amma yi musu mummunar adu'a hani ya zo kan hakan, Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi yace :(kada ku yi mummunar adu'a a kanku,
kuma kada ku yi mummunar adu'a ga 'ya'yanku, kuma kada ku yi mummunar adu'a ga
dukiyarku, domin kar ku yi muwafaka da lokacin amsawa sai a amsa muku) Muslim ne ya rawaito
Abin nkoyi mai kyau wani tushe ne na tarbiya, kuma haske ne na tsarkaka,
Allah Madaukakin sarki ya ce : (Ka ce: idan kun kasance kuna son Allah to ku
bi ni, Allah ya so ku, kuma ya gafarta muku zunubanku, kuma Allah Mai gafara ne
Mai jin kai).Al-Imran :31
Kuma abu ne da bai buya
cewa kwaikwayo da koyi na da tasirin da ya fi fadi da karatu da sauraro,
Sabo da muhimmancin koyi ne ma da hadarin da ke tattare da shi Allah ya
ke cewa :(Ya ku wadanda suka yi
imani! Don me ku ke fadin abin da ba ku aikatawa? Ya girma ga zama abin kyama a
wurin Allah. Ku fadi abin da ba ku aikatawa). Assaf : 2-3
Kauna na wanzuwa da karfafuwa da dawwama har a lokacin zamewa (kuskure)
da gajartawa, wannan ita ce koyarwar Manzon Allah , hakika wani mutum ya zo
mishi sai ya ce: ya Manzon Allah na halaka ! sai ya ce : (Me ke gare ka?)
sai ya ce : na aukawa mata ta a halin ina azumi, sai manzon Allah tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :(Ko kana da wuyaye da za ka
'yanta? Sai ya ce : A'a. sai yace :(To za ka iya yin azumin wata biyu a jere?)
sai yace :A'a. sai ya ce :(To zaka iya samun ciyar da miskinai sittin ?) sai ya
ce :A'a). sai manzon Allah ya dan zauna jim kadan muna halin haka sai i aka kawo wa Annabi kwando
a cikin shi akwai dabino, kwando wata tasa ce ta awu sai ya ce ina mai tambaya? Sai yace : Ga ni
sai Manzon Allah ya ce karbi wannan ka yi sadaka da shi, sai ya ce : ga wanda ya fi ni talauci
ya Manzon Allah? To na rantse da Allah! ai duk kewayen madina a tsakanin duwatsunta biyu ba mutan
gidan da suka kai iyalan gida na bukata.sai Annabi yayi dariya har fikarsa suka
bayyana sai yace : ka ciyar da shi ga iyalanka).Bukhari ne ya rawaito.
A yanayi na kauna mai tarbiyantarwa ba zai shakala yin amfani da hikima
da kyakkyawan fadakarwa da tausasa zance, da saukin hali, tare da nesatan
amfani da karfi da suka da walakantarwa, Allah Madaukakin sarki ya ce: (Ka yi
kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da
hikima da wa'azi mai kyau, kuma ka yi jayayya da su da magana wadda take mafi
kyau.)ANNAHL -125
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :
Lalle Allah Mai sauki ne,kuma yana son saukakawa, kuma ta hanyar sauki ya kan
bada abin da bai bada shi ta hanyar karfi ko waninsa.) Muslim ne ya rawaito.
Ya ce da balaraben kauyen da ya yi fitsari a masallaci: (ku kyale
shi, ku kwarara bokitin ruwa ko guga guda a kan fitsarin nashi abin sani kawai an turo ku ne kuna masu
sauki baa turo ku kuna masu tsanani ba).Bukhari ne ya rawaito.
Kamar yadda girmama wadda ake tarbiyantarwa da yi mishi maraba da nuna
haba-haba da shi, koyarwa ne na Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi. A'isha Allah kara yarda a gare ta ta ce : Fadima ta fiskanto tana
tafiya, tafiyarta irin na Annabi sai Annabi yace : (Maraba da 'ya ta )sannan ya
zaunar da ita a damansa ko hagunsa) Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Jiki na da gudumawa da yake bada wa gurin tarbiyyantarwa da kauna; kamar
murmushi da fara'a ta gaskiya, da shafa irin na shauki, da kalmomin kwantar da
hankali, da tausayawa irin na zuci.
Mai bada tarbiya ba zai yi sakaci da dama da ya samu ba na halrtowar
hankali zuwa gare shi face ya dasa kyawawan dabiu ba tare da kankantar da
hankalin yaro ba ko renarwa.
An karbo daga Abdullahi dan Abbas Allah kara yarda a gare shi da
mahaifin shi yace : wata rana na kasance a bayan Annabi sai ya ce: ya kai yaro
zan sanar da kai wasu kalmomi: ka kiyaye Allah zai kiyaye ka,ka kiyaye Allah za
ka same shi a gaba gare ka)Tirmizi ne ya rawaito da isnadi ingantacce.
Tarbiyantarwa da kauna na bukatar yanayi
da iyalai zasu game su dukule,su so juna , ta inda zasu samu farinciki
da walwala su yi wasa da bai
sabawa shariar wannan addini ba, Aisha Allah kara yarda a gare ta tana cewa
:Na kasance a wata tafiya tare da Annabi
sai muka yi tsere da shi sai na
yi galaba a kan shi,da kafafuwa ta,a yayin da na yi jiki muka sake tsere da shi
sai ya yi galaba a kai na, sai ya ce : (To da wannan ni ma na rama wancan
galaba da aka yi a kai na.)Abu Dawuda ya rawaito da isnadi ingantacce.
An karbo daga gare –Allah kara yarda a gare ta- ta tace: (na ga
Manzon Allah a kofar daki na ga habashawa suna wasa a masallaci Annabi ya kare
ni da mayafinsa ina kallon wasar tasu.)Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Tarbiyantarwa da kauna na bukatar kulawa da adalci wajen bayyana kauna
ga yara, sai ya fadada so da ya ke musu
ya game su gabadayansu ba tare da wariya
ba,
Yayin da Annabi yusuf ya yi mafarki (lalle ne ni na ga taurari goma
sha daya, da rana da wata na gan su suna masu sujada a gare ni) sai
mahaifinsa Annabi Yakub -Amincin Allah ya tabbata a gare shi - ya ce
da shi : (ya karamin da na! kada ka labarta mafarkinka ga 'yan uwanka har su
kulla maka wani kaidi, lalle shaidan ga mutum makiyi ne bayyananne.) yusuf 4 &5
Manzon Allah ya ki ya shaida kyautar da wani mahaifi ya bawa daya
daga cikin 'ya'yansa yace : (Ni ba zan yi shaida na zalunci ba). Bukhari
ne ya rawaito.
Tarbiyantarwa ta hanyar kauna da kosar da zukata da sosa mata inda ya ke
mata kaikayi shiryarwa ne na Annabi kuma bukata ce aka halicci mutum a kanta,kuma
ya fi karfi ta bangaren 'ya'ya mata Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Wanda aka jarabce
shi da wani abu na daga wannan
'ya'ya matan , sai ya kyautata musu to
za su kasance kariya a gare shi daga
wuta) buhari da muslim ne suka rawaito
lafazin na Buhari ne , :
kyautatawa ga 'ya'ya mata ta hanyar koyar da su da tada su akan kamun kai, da nesantar da su daga abin da Allah ya
haramta , na daga tsiraici da bayyana jiki
.
Da dora yara maza
a tafarki tsayayya na aiki mai amfani ,
da kuma shirye-shirye na aikin alheri
wanda zai daga manufar su ya kuma kare su daga fadawa cikin abubuwa marasa muhimmanci da yawon banza.
Yana daga cikin abin da ke
warware tarbiyantarwa da kauna ; akwai shagwabantar da yara
ta hanyar amsa musu duk abin da
suka nema da abubuwan kwadaye-kwadayen su da kuma yin sakaci ta bangaren ladabtar da
su da gyara musu kusakuran su : to jajarcewa wani lokaci yana cikin kauna ,:
musgunawa uwa a gaban 'ya'ya yana toshe kofar soyayya amma bayyana zunubai da fandarewa da iyaye za
su yi a gaban 'ya'yan su to hanya ne mai rusa tarbiya Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( ya isa zunubi ga mutum da ya sarayar da wanda yake ciyarwa ) Abu Dauda da Ahmad suka
rawaito da isnadi ingantacce .
HUDUBA TA BIYU
Hakika hanyoyin tasiri na zamani sun habaka , kuma sun haifar da wani
sanje- sanje na tushe a tunani da
fahimta da dabi'u, har a ka wayi gari suna gogayya da
gudumawar da iyaye suke bayarwa na tarbiyan 'ya'yayen su ,: to a nan ne muhimmancin tarbiyantarwa da kauna zata bayyana, da kuma bashi
mafaka da kuma gina gada mai karfi na aminci da sabunta salo, da shuka kyawawan dabi'u da zaburantar da
himmar kafafen ilmantarwa da tarbiyantarwa , don tashi da sakonnin su wurin kiyaye madosan al'uma da fatanta nan gaba , da kuma
kiyaye arzikin kasa , ta hanyar bada kariya ga ginshiki na addini da kuma
dabi'u da bada kulawa ga matasa , da kuma
abin da suke burin zama nan gaba
da kuma kiyaye radadin su da damuwan su .
Allah Madaukakin sarki ya ce : ( Ya ku wadan da suka yi imani ku
karewa kan ku da iyalan ku wata wuta
makamashinta mutane da duwatsu ne.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق