Hudubar Masallacin
Annabi na shaikh AbdulMuhsin Alkasim 7-6-1439AH
HUDUBAR FARKO :
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin
sarki muna gode mishi kuma muna neman
taimakonsa , muna neman gafarar sa ,
kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu , da munanan ayyukanmu ,
duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi , duk wan da ya batar
kuma babu mai shiryar da shi , na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah
shi kadai yake bashi da abokin tarayya , kuma na shaida Annabi Muhammadu
bawansa ne kuma Manzonsa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da
iyalansa da sahabbansa da aminci
tabbatacce mai yawa .
Bayan haka
Ku ji tsoron Allah - ya ku bayin Allah – ku yi riko da igiya mai karfi
na musulunci .
Mabudin bautawa Allah da sirrin bauta masa na ga sanin sunayen Allah ne
da sifofinsa.to sunayensa Madaukaki duk
kyawawa ne, sifofinsa duk Madaukaka ne. Yana da
wata sifa ta bauta na musamman ga dukkan suna da sifa tsarki ya tabbata a gare shi , yana daga cikin abin da ke haifar da shi da kuma abin da ya kumsa, Allah yana son sunayensa da sifofinsa
kuma yana son bayyana alamomin su ga
halittunsa , sai ya umarci bayinsa da su roke shi da su, Allah Madaukakin sarki ya ce: (Kuma Allah yana da sunaye masu kyau , sai ku
roke shi da su ). Kuma mafi soyuwan halitta zuwa ga
Allah shi ne wanda ya siffantu da
sifofin da Allah ke kauna , wanda ya
bautawa Allah da sifofin shi zai kusantu
zuwa ga rahamarsa , wanda ya kiyaye sunayen sa zai saukar da shi a aljannarsa daga cikin sunayen Allah akwai ALHAYIYU wato mai
kunya kuma daga cikin sifofin sa akwai
kunya , kuma Allah ya siffanta kan shi
da ita sai ya ce : (Lallai ne Allah
ba ya jin kunyar ya bayyana wani misali,
kowane iri ne, sauro da abin da
yake bisa gare shi ) .
Manzon sa tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi ya ambace shi sai
ya ce :( Lallai Allah mabuwayi da daukaka
mai kunya ne , kuma marufin asiri ne
yana son kunya da suturcewa ) Abu
Dauda ne ya rawaito . Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce :( Lallai Ubangijin ku mai girma da daukaka Makunyaci
ne, kuma mai karamci ne , yana jin kunyar bawansa idan ya daga hannayensa biyu zuwa gare shi ya
dawo da su haka banza ).Abu Dauda ne ya rawaito shi
Ibn Alkayyim Allah ya mishi rahama ya ce :
'' Kunyan Ubangiji Madaukakin sarki ga bawansa, abu ne da fahimta ba zai riske
shi ba , hankali kuma ba zai gano yadda yake ba, domin shi wani kunya ne na
karamci da kyautatawa da kuma kyauta da daukaka ''.
Mafi girman kyawawan halaye cikin halittu
kuma mafi daukakansu da kuma mafi girma a daraja da kima kuma mafi yawan amfani; shi ne kunya , wata
dabi'a ce wadda ke sa abar duk wani munanan dabi'u kuma yana hana yin sakaci a cikin hakkin ma'abocin hakki , tushen sa da asalin maddarsa daga rayuwa ne , kuma bisa iya gorgodon rayuwar zuciya iya kasancewar kunaya a cikin ta a duk lokacin da zuciya ta fi rayuwa , sai kunya ta fi cika a
cikinta da karfi kunya bata
gushe ba al'amarin ta tabbatacciya
ce , kuma amfani da ita wajibi ne tun
zamanin Annabawan farko , kuma ba wani
Annabi face ya kirayi al'umar sa
zuwa gare ta kuma an turo shi da ita ba
a goge ta ba cikin abubuwan da a ka goge na shari'o'insu , kuma ba a canza ta ba cikin abubuwan da ake
canzawa , sabo da wannan al'amari da ya
bayyana karara na daidai ne an sanshi
kuma falalar shi ya bayyana dukkan hankula sun yi taraiyya bisa ga kyanta
, duk wanda wannan ya kasance shi ne sifansa
bai halatta a goge shi ko a canza
shi ba, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Lallai
yana daga cikin abin da mutane suka
riska na maganan Annabawa shi ne idan baka ji kunya ba ka aikata abin
da ka ga dama ) Buhari ne ya rawaito
Mafificin halittu ya siffantu da ita kuma
Allah ya kyautata yabo ga ma'abotanta to kuma mala'iku ma sun siffantu da ita
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata gare shi ya ce game da Usman : ( Ase ba
zan ji kunyar mutumin da mala'iku suke jin kunyar sa ba ), Muslim ne ya
rawaito , Annabawa an san su a cikin
mutanen su da haka, halittu za su nemi ceto ranar alkiyama da
Adamu da Nuhu Alaihimassalam , sai ko wannen su ya tuna zunuban shi sai ya ji
kunya ) Musa amincin Allah ya tabbata a
gare shi makunyaci ne , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi ya ce : ( Lallai Musa ya kasance
mutum ne makunyaci mai yawan
suturcewa ba a ganin wani abu na daga
fatar jikin shi sabo da irin kunyar sa ), Buhari ne ya rawaito
Annabinmu Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
yana da kaso mafi tsoka na daga kunya,
sabo da haka yakan yi jirwayi da
kamar wanka, baya yin karara, akan gane
kunyar sa daga fuskarsa, Abu Sa'id
Al khudri ya ce: '' Manzon Allah tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi (
Ya kasance mafi tsananin kunya fiye da budurwar da take cikin haudajin ta , kuma ya kasance
idan ya tsani wani abu mukan gane a fuskar sa) Buhari da Muslim ne suka
rawaito shi
Ya kai ya komo a
daren mi'iraji tsakanin Musa da Ubangijinsa
yana rokon a sassauta game da sha'anin sallah har zuwa lokacin da ya ce :
" ( Hakika na ji kunyar Ubangiji na ") , a yayin da ya shiga da Zainab 'yar Jahash, an kira mutane don hakan, sai suka ci abinci suka fita sai ya rage wasu mutane uku suna ta hira a
dakin sai Annabi tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi ya ji kunyar ya ce
mu su wani abu , sai ya fita ya
bar su a dakin, sai Allah Mabuwayi da
daukaka ya saukar da : (Ya ku wadanda suka yi imani kada ku shiga gidajen
Annabi face fa idan anyi izini a gare ku
zuwa ga wani abinci , ba da kun tsaya
jiran nunar sa ba , kuma amma idan an
kira ku, to , ku shiga sa'annan idan
kun ci, to ku watse , kuma ba da kun tsaya kuna masu hira da wani labari ba
, lallai wannan yana cutar da Annanbi, to yana jin kunyar ku , alhali kuwa Allah
baya jin kunya daga gaskiya) Ahzab 53 Buhari da Muslim ne suka rawaito
Kuma Usman
Allah ya yarda da shi ya zama abin buga
misali a akunya cikin sahabbai, watarana
ya shigo ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai
Manzon Allah ya zauna ya daidaita tufafin shi sai aka tambaye shi game da haka sai ya ce :
( Lallai Usman mutum ne makunyaci na
ji tsoron kada na mishi izini a wannan yanayi ya ki isowa zuwa gare ni , cikin
bukatar sa ) Muslim ne ya rawaito .
Mace an halicce ta bisa
kunya , kuma kunya ce adon ta kuma kariya ne a gare ta da aminci Aisha Allah ya kara yarda a gare ta ta ce
" Ya Manzon Allah ai ita budurwa
tana jin kunya sai ya ce yardan ta –da auren - ai shi ne yin shurun ta " Buhari ne ya rawaito
'yar ma'abocin madyana tazo
kunya na lullube da ita ta suturce fiskanta da hanunnta da kuma tufafin
ta Allah madaukakin sarki ya ce : ( Dayan su sai ta zo tana tafiya bisa
kunya sai tace lalle mahaifi na na
kiranka don ya saka maka abin da ka yi na shayar da mu) .Kuma Aisha uwar muminai Allah ya yarda da ita, kunya ya kaita da ta suturce kanta a cikin dakinta sabo da Umar Allah ya yarda da shi bayan an binne shi ( a dakin ta ) Allah ya kara yarda a gare ta, ta ce: "Na kasance ina shiga daki na
wanda aka binne Manzon Allah a
cikinsa da mahaifi na sai na cire tufafi na,
sai na ce ai wannan mijina ne, wannan kuma mahaifina ne , to amma a lokacin da aka binne Umar tare
da su to wallahi ban shiga dakin ba
face sai ina daure da tufafi na a jiki
na sabo da kunyar umar )Ahmad ne ya
rawaito .
Kuma ga wata mace da ta yi hakuri bisa
jarabawa amma bata yarda da cire rigar
kunya ba , sai sakayyar ta ya kasance aljanna : Abdullahi Dan Abbas Allah ya kara yarda a
gare su shi da mahaifin shi ya ce ga Ada
Dan Abi Rabah Allah ya mishi rahama ya
ce : " Ase ba zan nuna maka
mata 'yar aljanna ba ? sai na ce e; sai
ya ce : " wannan bakar matar ta zo
ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai ta ce : " Lallai ni
ina da cutar farfadiya har nakan
yaye daga tufafi na, to ka roka
min Allah ya raba ni da ita, sai ya ce in kin so ki yi hakuri kina da
aljanna in kuma kin so in roka miki
Allah ya baki lafiya " sai ta ce : "zan yi hakuri,
sai dai nakan yi tsiraici , to ka rokamini Allah kada na rinka yin tsiraici sai ya roka mata Allah" ) Buhari da
Muslim ne suka rawaito
Kuma tana cikin
dabi'u masu daraja wanda har mutanen jahiliyya ma sun wanzu a kan ta, Abu
Sufyan Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : " a yayin nan da Hiraklu
ya tambaye shi game da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma a lokacin yana kafurci : (Wallahi ba
don kunya ba a wannan ranar kar mutane na su taba kama ni da karya a wannan
ranar da na yi mishi karya , a lokacin da ya tambaye ni game da shi, amma sai dai na ji kunya kar a same ni da
karya sai na fada mishi gaskiya).
Da kunya ne a ke samun walwala a riski kuma sabubanta, dukkan ta alheri ne
, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (
Kunya alheri ne dukanta ko kuma ya ce
kunya dukkan ta alheri ne )Muslim
ne ya rawaito
Karshen ma'abocinta alheri
ne har abada kuma ba zai hadu da nadama ba har abada ,
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa : ( Kunya bata kawo wani abu sai
alheri). Muslim ne ya rawaito
Ibn Kayyim Allah ya
mishi rahama ya ce :" kunya wani sinadari ne na rayuwar zuciya kuma ita
ce tushen dukkan alheri , rasa ta kuma
rasa alheri ne gaba dayan shi )
Yana daga cikin mafi girman alherin da ke cikin ta akwai sabarwa
rayi da kyawawan dabi'u da kuma nisantar
munanan dabi'u , idan kunayar mutum ta tsananta sai a kare mutuncin sa kuma sai
a binne laifukansa a kuma yada kyawawansa.
Yana daga cikin akidar ahlussunna waljama'a ; cewa imani fadi
ne da kudiri da aiki, kunya wani yanki ne daga gare shi Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce:( Imani
yanki ne sittin da dori kuma kunya wani yanki ne na imani ) Buhari da Muslim ne suka rawaito shi .
Ibn Hibban Allah ya mishi
rahama ya ce :"kunya na daga cikin
imani kuma mumini na aljanna, ba za a
zare kunya daga wani ba face an zare imanin shi ".
Manzon Allah ya wuce wani mutum yana zargin
dan uwansa game da kunya, yana cewa :
" Lallai kai kana jin kunya har
kamar yana cewa da shi ya kai ma yana cutar da kai , sai Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( kyale shi,
lallai kunya na daga cikin imani) .
Buhari da muslim ne suka rawaito
Ba ukubar da Allah zai yi ga zuciya da tafi a
kwashe kunya daga gare ta, Ibn Umar Allah ya kara musu yarda ya ce : " Lallai kunya da imani an
hada su tare idan an dauke dayan su sai
a dauke dayan ma " .
Kunya da'a ce da ke janyo wasu
biyayya da za su kai ma'abocinta zuwa ga tsentseni wanda kuma ya
barta to zai aikata abin da yake kishiyan haka , Umar Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: " wanda kunyar
sa ta karanta to tsentseninsa zai karanta, wanda tsantsenin sa ya karanta
zuciyar sa ta mutu.
Kunya na daga cikin abu mafi girma da ke shiga tsakanin mutum da
aikata sabo , makunyaci na katse
ayyukan sabo da kunya kamar yanda imani ke katse sabo, idan an tube kunya daga bawa to sai ya zama
ba abin da ya rage da zai hana shi
aikata munanan abubuwa da kuma halaye
marasa kyau, sai ya zama kamar bai da
imani, Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce :( Idan
mutum bai ji kunya ba to ya aikata abin da ya so). Buhari ne ya rawaito
Ibn
Abdulbar Allah ya mishi rahama ya ce : " Duk wanda bai da kunyan da zai
katange shi daga abin da Allah ya haramta , to daya ne a gare shi aikata aikin
karamin zunubi da babba, a cikin
hadisin akwai gargadi da narkon azaba game da karancin kunya "
Zunubai na raunana kunya daga
bawa har ma ya tafi gaba daya daga gare shi ,
ya zamana ba zai dame shi ba don mutane sun san halin shi ko suka gane
abin da ya ke aikatawa , kai hakika ma yakan bada labari bisa halin shi da
munanan ayukan shi .
A kunya akwai ado
da kawa ga ma'abocinta Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Batsa baya shiga
cikin komai sai ya bata shi kunya kuma baya shiga cikin komai sai ya kawata shi
– wato ya adonta shi ) Tirmizi ne ya
rawaito shi
Kunya na kira zuwa ga izzar rayi
da kare ta , ba zai tambayi mutane wani abu ba ko da ya bukaci hakan , Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Ba miskini shi
ne wanda ya ke kai komo a kan loma daya ko biyu ba, sai dai miskini shi ne
wanda ba yi da wadata kuma yana kunya, ko kuma baya tambayan mutane bisa naciya
) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Kunya kamar
wani adireshi ne na kyakkyawan dabi'a da ladabi. Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi ya tambaya : ( Game da itaciyar da take kama da musulmi , sai Ibn Umar
Allah ya yarda da su ya ce : ( sai ya fado a zuciya ta cewa bishiyar dabino ne
sai na ga Abubakar da Umar ba su yi magana ba, sai na ji nauyin
na yi magana. a wani lafazin kuma ya ce : " sai na ji kunya )
Buhari da muslim ne suka rawaito .
Mutum ana sakanya mishi da irin aikin da ya yi, na daga cikin amfanin kunya da kyakkyawan
sakayyan ta Allah na jin kunyan ma'abotanta
, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: ( Amma
dayan sai ya ji kunya sai Allah ya ji kunyar sa ) Buhari da Muslim ne suka
rawaito
Tushen kunya kuma shi
ne a ji kunyar Allah madaukaki, ta yanda kar ya gan ka a inda
ya hane ka, kar ya rasa ka kuma a
in da ya umarce ka , Allah
ne ya fi cancanta da a ji kunyar sa Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce: ( Ku ji kunyar Allah cancantar kunyar sa) Tirmizi
ne ya rawaito
Kunyar Allah shi ne Allah ya jefa wani haske a zuciya
da zai sa ya rinka ganin Allah gaba gare shi lokacin da yake shi kadai ko a
cikin jama'a, jin kunyan Allah na tabbatuwa ne ta hanyar tsinkayar baiwar sa da girman
ni'imominsa tare da halarto da laifuka na rayi tare da gazawanta , kuma da
sanin cewa yana tsinkayan abin da yake na
sirri da wanda ya fi boyuwa: ((Allah) Ya san yaudarar idanu da abin
da kiraza ke boyewa) sura Al-Gafir aya 19
Allah madukakin sarki ya ce : ( Suna
neman boyewa daga mutane kuma ba sa
neman boyewa daga Allah alhali kuwa shi
yana tare da su ).
Idan bawa ya san cewa
Allah madaukakin sarki yana kallon shi ;
kuma cewa yana gaban
idon sa ne kuma yana jin sa kuma ya kasance mai jin kunya to sai ya ji kunyar
kada ya kutsa zuwa ga abin da zai fusata
shi
tare da mutum akwai mala'ikun da
ba sa rabuwa da shi yana daga cikin karrama su ka ji kunyar su ( Lalle ne a kanku hakika akwai
matsara . masu daraja marubuta . Suna sanin abin da kuke aikatawa ) .
Ibnul Kayyim
Allah ya mishi rahama ya ce : " Ai ku ji kunyan wadannan matsara din ku karrama
su ku ga kimar su , ku ji nauyin su ganku kuna aikata abin da ku ke jin kunyar wasun ku
su ga kuna aikatawa ".
Jin kunyan mutane yana
haifar da mutunci da kyawawan dabi'u kai
ko da ma a ce mutum musulmi bai samu wani Abu daga dan uwan shi ba sai
kunyar sa da zai hana shi aikata sabo to ya isar mishi, wannan wani alheri ne da zai taimakawa ma'abocin shi bisa
jin kunyar Allah , to duk wanda baya kunyar mutane to baya kunyar Allah , haka kuma duk
wanda ya zauna da ma'abota kunya ,
kunyar shi za ta sabunta .
Wanda ya fi dacewa mutum
ya girmama shi ne kansa , duk mutumin da ya aikata wani aiki a sirrace wanda ake jin kunyar aikata shi a bayyane to bai kimanta kan sa ba, wanda ya ji kunyar mutane bai ji kunyar kansa
ba to kansa ta fi walakantuwa a gunshi
fiye da wanin shi wanda ya ji kunyan
wani kuma ya ji kunyar kansa bai ji kunyar Allah ba to baisan Ubangijin sa ba, wanda
kunya ya lullube masa tufafin shi to mutane ba za su ga aibin shi ba.
Bayan haka ya ku
Musulmai to musulunci addini ne na
kyawawan halaye da kyawawan dabi'u , ya
tattaro daga halayya mafi kyansu da sifofi kuma mafi daukakan su ba wani alheri face ya yi umarni da shi , ba
wani sharri kuma face ya yi gargadi game da shi, to wajibi ne gare mu muyi riko da shi kuma muyi alfahari da shi kuma mu kira
mutane zuwa ga shi , jin kunyar Allah shi ne ta hanyar bin
umarninsa da kuma nisantar saba mishi .
INA NEMAN TSARIN ALLAH
DAGA SHARRIN SHAIDAN ABIN
JEFEWA
(Kuma wane ne ya fi kyau ga
addini daga wanda ya sallama fuskar sa
ga Allah alhali kuwa yana mai kyautatawa kuma ya bi akidar Ibrahim yana mai
karkata ga gaskiya )
Allah ya sa mini albarka ni da ku
cikin alkur'ani mai girma, kuma Allah ya
amfane ni da ku da abinda yake cikin sa na daga ayoyi da ambato mai hikima ,
ina fadin wannan magana tawa kuma ina mai neman gafarar Allah
da ni da ku da dukkan musulmai
daga dukkan zunubai ku nemi
gafarar shi lallai shi mai gafara ne mai jin kai
HUDUBA TA BIYU
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa kyautatawan sa , godiya ta tabbata a gare shi bisa datarwar sa da baiwarsa na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya muna
mai girmama sha 'anin sa, na shaida
Annabinmu Muhammad bawan sa ne kuma mManzon sa ne tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi da iyalan sa da sahabbansa
da aminci tabbatacce mai yawa ,
Ya ku Musulmai :
Kunyan da yake abin yabawa a maganan
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi ita ce wannan dabi'ar da ke sanya mutum ya aikata kyakkyawan abu ya
bar mummuna amma rauni da gazawa, Wanda ke sa gajartawa a wani abu na daga
hakkokin Allah, ko hakkokin bayinsa,wannan ba su da alaka da kunya a wani abu,
in ya hana ma'abocinsa wani alheri to bai zama abin a yaba ba. Aisha Allah ya
kara yarda a gare ta ta ce : (Madalla da matayen Ansar kunya bai hana su
neman fahimtar addininsu ba) Muslim ne ya rawaito.
Babu kunya cikin neman sanin addini, wanda ya bar ilimi don kunya to zai
zauna cikin jahilci har abada ya hana kansa alheri.
Mujahid Allah ya masa rahama ya ce :
( Mai kunya ko Mai girman kai ba zai samu ilimi ba)
Kuma ku sani Allah na umartanku da salati da aminci ga Annabinsa
( lalle
Allah da malaikunsa suna salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati
a gare shi da aminci tabbatacce.)
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق