السبت، 17 مارس 2018

GARGADI A KAN ZUNUBAI DA SABON ALLAH


Hudubar Juma'a na Masallacin Annabi na shaikh Abdullah Dan Abdurrahman Al-Buaijan 21-6-1439 AH.

HUDUBAR FARKO :
  Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin sarki,  muna gode mishi kuma muna neman taimakonsa ,  kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu , da munanan ayyukanmu , duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi , duk wan da ya batar kuma babu mai shiryar da shi , na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya , kuma na shaida Annabi Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa ne, Allah ya turo shi don rahama ga  talikai, sai ya buda zukata, ya haskaka hankula da shi, ya buda makantattun idanuwa da shi, da kuraman kunnuwa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa  da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa har zuwa ranar sakayya .
Bayan haka :
Lalle da'a ita ce bin Allah sau da kafa  da biyayya ga Manzo, sabo kuma shi ne sabawa Allah da kirkiran bidio'i, mafi sharrin al'amura ita ce bidi'a da fararrun al'amura, da laifuka da abin da aka ki, mafi muninsu shine  sha'awe –sha'awe da shubuhohi.
Ku bi Allah cikin umarninsa , ku hanu game da abin da ya hane ku ya tsawatar,(ya ku wadanda suka yi imani ku bi Allah da takawa, a kan hakkin binsa da takawa, kuma kada ku mutu face kuna musulmai)
Ya ku bayin Allah!
Lalle Allah ya halicci mutum ya ba shi kyautan hankali da harshe,ya bashi sharia ya sanar da shi bayani, ya turo manzanni da hujjoji ya saukar da littafi da mizani, ya kaddara mutuwa da rayuwa, don ya gwada ku ya ga wanda ya fi kyan aiki .
Ya halicci mutum don ya mishi biyayya da zai haifar da yardarsa, ya hane shi ga  saba mishi da zai haifar da fushinsa, (To wanda ya aikata wani aiki gwargwadon nauyin zarra na alheri zai gan shi. kuma wanda aikatagwargwadon nauyin zarra na sharri zai gan shi ).
Ya sanya duniya gida na aiki da jarrabawa, ya rubuta mata karewa, gidan lahira kuma gidan hisabi da sakayya,ya rubuta mata dauwama da wanzuwa,(To wanda ya yi aiki na kwarai don kansa,wanda ya munana don kansa)
Ya tattalawa masu takawa  gidajen Aljanna, koramai na gudana daga karkashinsu,suna madauwama a cikinta har abada. Cikinta akwai abin da ido bai taba gani ba, kunne bai taba ji ba, bai kuma taba fadowa ga zuciyan wani dan 'adam ba, ya tanada, ya tanadawa kafurai wutan jahannama, ba ta ragewa kuma ba ta bari, mai nacewa ga jiki ce da kuna, suna masu zama a cikinta na wasu zamuna, ba su dandanar wani sani sanyi ko abin sha, face tafasasshen ruwa da rubabben jini, sakamako mai dacewa.
Kowani rai mai dandanar mutuwa ne, kuma ana cika muku ladanku ne a ranar Alkiyama, to wanda aka nesantar daga barin wuta kuma aka shigar da shi Aljanna to lalle ne ya tsira, kuma rayuwar duniya bata zama ba face jin dadin rudi.) Ali – Imran 185
Ya ku bayin Allah !
Lalle dan'adam ana jarraba shi da sha'awa da shubuhohi, yana tunkuduwa cikin jin dadi da hutu, ana jarabta shi da zunubai, da munanan laifuka, hakika makiyansa sun yi hayan masa da abokan fadansa, shaidan abokin tafiyansa ne kuma makiyinsa ne, makiyyinsa ne mai tsananin jayayya, ga rai mai yawan umarni da mummuna, kuma tana cikin jiki, ga gabbai masu musu ne kuma shaidu.
Hakika shaidan ya yi rantsuwa  ( sai ya ce :To ina rantsuwa  da buwayarka sai na batar da su gaba daya. Face bayinka tsarkakku daga gare su )Sad 82
Ya kuma bamu labari game da rai sai ya ce :    (Lalle rai mai yawan umarni ne da mummuna)Yusuf  52
Game da gabbai sai yace : ( A ranar da harsunansu zasu yi shaida akansu da hannayensu da kafafuwansu da abin da suka kasance suna aikatawa) Annur :24
(kuma suka cewa fatunsu don me kuka yi shaida akanmu? Suka ce Allah wanda ke sanya ko wani abu yayi furuci shi ne ya sanya mu mu yi furuci kuma shi ne ya halitta ku can da farko kuma zuwa gare shi za ake mayar da ku. Baku kasance kuna sani ba a boye cewa jin ku zai yi shaida a kan ku kuma ganinku zai yi,kuma fatunku zasu yi, kuma amma kun yi zaton Allah bai san abubuwa masu yawa daga abin da ku ke aikatawa ba,)
To shaidan na ingizawa zuwa ga sabo da laifuka masu halakarwa, rayi na umarni da munana da abin da aka ki, gabbai shaidu ne masu tabbatarwa, mai wayo shi ne wanda  ya yi wa kansa hisabi ya mata linzami don kar ya auka ga zunubai.
Ya ku musulmi!
Lalle aikata zunubai  da laifuka akwai cutuwa da kuma barna a ciki da ke haifar da fushin Allah da ukubarsa, da azabarsa, kuma yana janyo  saukar azabarsa da bala'insa. (kuma da yawa daga alkarya wadda ta yi tsaurin kai daga barin umarnin Ubangijinta da Manzanninsa, sai muka yi mata hisabi,hisabi mai tsanani, kuma muka azabtar da ita, azaba abar kyama. Sa'annan ta dandana masifar al'amarinta , kuma karshen al'amarinta ya kasance hasara. Allah ya musu tattalin wata azaba mai tsanani, sabo da haka ku bi Allah da takawa ya ma'abota hankula ).Dalak 8 -9.
To abin da ke faruwa ga musulmai na fitintunu da musibu  masu radadi da jarabawa da tsadan kaya da mulka irin na makiya, da fari da fako,da cututtuka da yunwa da bala'i  ba wani abu ya haifar da shi ba face sabon Allah da laifuka da zunubai, da abin ki.
Hakika Allah ya buga misali ga mai lura ya koro ayoyi ko akwai mai wa'azantuwa, ya bayyana  cewa zunubai da laifuka na daga mafi girman sabuba na gushewar ni'ima da saukar azaba, sai Allah ya ce :(kuma Allah ya buga misali, wata Alkariya ta kasance amintacciya natsatsiya  arzikinta yana je mata a wadace daga kowane wuri,sai ta kafurta da ni'imomin Allah sabo da haka Allah ya dandana mata tufafin yunwa da tsoro, sabo da abin da suka kasance suna sana'antawa, ). Annahl 112
To Abin mamaki ga  walakancin halitta a gun Allah Mabuwayi idan an saba umarninsa.
Ya ku bayin Allah!
Lalle hadarin sabo na girmama kuma ukubanta na kasaita da musibanta  idan aka wayi gari mutane sun saba da ita suna bayyana ta a fili jama'a na fito na fito da Allah, kuma dukkan al'uma na samun kubuta daga sabo banda masu bayyanawa, mutane ba za su halaka ba sai an basu hanzari akansu.
Ya ku bayin Allah!
Lalle bayyana sabo wani nau'i ne na watsi da hakkin Allah da bushewar  ido gare shi, da ja da mumunai da kara yawan masu sabo,da  kuma isar shi gurbin   sabon ne zuwa  ga wani,
Kuma da zamewa sababi na janyo su gare shi da kwadaitar da su, da kuma kasancewa  sababin sanya zunubai ga wanda bai yi inkari ba(hani ba). Duk wanda aka jarabce shi da wasu sabo to ya boye da boyewar da Allah ya mishi, kuma ya tuba zuwa ga Allah tuba na gaskiya.
Ya ku Musulmai!
 Lalle dogewa a kan zunubai  da sake jiki cikin aikin sabo, da dulmuya cikin laifuka da murna da su,da bushewan ido cikinta, da aminta daga makarkashiyar  Allah,da rena laifuka, abu ne da ke shelanta gafala da janyo fushin Allah, kuma sababi ne na tabewa da halaka, An karbo daga  Abdullahi dan Mas'ud Allah kara yarda a gare shi, yace : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : ku kiyayi rena kananan laifuka, domin su ne ke taruwa  akan mutum har su halaka shi, lalle Annabi ya buga misali game da su yace kamar mutane ne suka sauka jeji sai lokacin dafa abincin su ya yi, sai mutum ya je ya kawo kirya, wani mutum ma ya dauko kirya,har suka hada taru mai yawa, sai suka hura wuta suka dafa abinda suka jefa a  ciki). Ahmad ne.
Musiba na girmama  ga mai laifin idan ya ga kananan zunubai abin renawa an kididdige su,sun habaka ,sai ya firgita ya  ce :(Kaitonmu mene ga wannan littafi ba ya barin karama kuma ba ya barin babba face ya kididdige ta,to kuma suka sami abin da suka aikata halarce, kuma ubangijinka ba ya zaluntar kowa.)
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya  sun tabbata ga Allah da yake gafarta zunubai, ya suturce aibi, ya yaye bakin- ciki, yana shinfida hannayensa da dare ga masu laifin wuni don su su tuba,kuma yana shimfida hannayensa da rana ga masu laifin dare don su tuba su koma.
Ya ku bayin Allah! Ku ji tsoron Allah kada ku aikata zunubai kada ku rena shaninsu,  ku kankantar da su, ba abin da ya fi a gare ku, ku hadu da Allah da shi kamar karancin laifuka.
Ya jama'ar musulmi!
Lalle hadarin zunubai na kanzaga kuma yana tada hankali,bala'inta da musibanta  na girmama na tsoratarwa, idan ta zama abu sananne mutane suka  tabbatar da ita, baa umarni da kyakkyawa ko hani ga mummuna,  Allah Madaukakin sarki ya ce : An la'ani wadanda suka kafirta daga  banu Isra'ila, akan harshen Dauda da Isa da maryam, wannan kuwa sabo da sabawar da suka yi ne, kuma sun kasance suna ta'adi.sun kasance ba su hana juna daga abin ki, wanda suka aikata,hakika abin da suka kasance suna aikatawa ya munana.)
An karbo daga Abi bakra Allah ya kara yarda a gare shi ya ce ;Manzon Allah tsira da amincin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Lalle mutane idan sun ga munkari basu canja ba to suna kusa da Allah ya game su da azaba daga gare shi.).
Umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna na daga cikin dabia ta al'umar Muhammadu, kuma aminci ne daga saukar bala'i, kuma katanguwa daga  kaidin makiya da wawaye ,Allah Madaukakin sarki ya ce: Ku kasance, Allah ya yi umarni da shi ya kwadaitai a inda ya ce.(A cikinku a samu wata al'uma suna kira zuwa ga Alheri suna umarni da kyakkawa , suna hani da mummu ,  to lalle wadannan sune masu rabauta)
Ya Al'umar Muhammada ku yi umarni da kyakkya wa , ku hana munkari, Duk wanda , ya ga abinki to ya canza shi da hanunsa, idan ba zai iya ba to ya sanja shi da hannunsa,in ba zai iya ba da harshensa, idan bai iya ba da zuciyarsa, idan bai iya ba da zuciyarsa, wannan shine mafi raunin imani)
Ya ku bayin Allah!
Lalle ku din nan abin tambaya  ne  game da gidajenku da abin da aka ba ku kiwo,to ku ji tsoron Allah cikin 'ya'yanku da matayenku, ku sanar da su shariar Allah, kuma ku hana su fadawa ga abin da Allah ya haramta, ku tarbiyantar da su bisa halaye masu kyau da kyakkyawan dabiu, domin lalle zaa tambaye ku game da su gobe gaba ga Allah, kuma zasu zama shaidu akan ku, kuma zaa rubuta shaidar su kuma zaa tambaye su, a ranar da mai laifi zai yi fatan a fanshe shi daga azabar wannan rana da 'ya'yanan sa, da matarsa da dan'uwansa,  da danginsa da suke tattara shi,da wanda ke cikin duniya duka gaba daya sa'annan fansar ta sirar da shi.
Ku kula da abin da aka baku kiwo, kuma  (kada ku yaudari Allah, da Manzonsa, kuma ku yaudari amanoninku, alhali kuwa kuna sane. Kuma ku sani cew abin sani kawai dukiyoyinku da 'ya'yanku wata fitina ce, kuma lalle ne Allah a wurinsa akwai lada mai girma).
Ba wani mutum da Allah zai bashi kiwon wani abin kiwo,  ya zama ya zambace su, face Allah ya haramta Aljanna a gare shi.
Wanda ya yi kokari wurin gyaran mutanen gidansa, ya tsaida shariar Allah  a cikin abin da aka bashi kiwo,ya dasa musu imani a cikin zukatansu, zai kasance yana da lada kwatankwacin aikin da suka yi, ba tare da an tawaye wani abu na daga ladansu ba.
Ya tabbata daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce : (Idan dan'adam ya rasu ayyukansa zasu katse sai guda uku daga ciki akwai :Da na kwarai da  ya ke mishi adu'a ).
Ya jama'ar musulmai!
Lalle koyi da yammaci ya fadada, ya kutsa gidaje, da na'urori da hanyoyin sadarwa, sun rusa kyawawan halaye sun bata dabiu na kwarai , an wayi gari abin ki (MUNKARI) a jiya ya zama  shine  abin so (MA"ARUFI), abin da ya ke ma'arufi ne a jiya an wayi gari ana sifanta shi da ci-baya da rashi wayewa da fandarewa.
Abu Mas'ud Al'ansari ya shiga wa Huzaifa sai ya ce : ka mana wasiyya ya Baban Abdullahi, sai Huzaifa ya ce : Ase yakini bai zo ma ba? Sai yace : E ya zo, da buwayar Ubangiji na, sai yace : ka sani Bata hakikanin bata shine ka zama abin da ka ke ganinsa  a jiya mara kyau ya zama abu mai kyau, haka kuma abu da jiya ka ke gani mai kyau  to yau ya zama mara kyau , to na hore ka da juyawa,  addinin Allah daya ne.)           
  To ya ku bayin Allah ku riki sunna, Ina muku gargadi da fararrun abubuwa , domin dukkan fararren abu bidi'a ne, kuma dukkan bidi'a bata ne, kuma dukkan bata na wuta.
Ya Allah ka nuna mana gaskiya gaskiya ce ka bamu ikon bin ta, ka nuna mana karya karya ce ka ba mu ikon guje mata.
Ya Allah ka sanya mana son imani , ka kawata shi a zukatanmu, ka sa mu tsani kafurci da fasikanci da sabo,ka sanya mu cikin shiryayyu.
Ya Allah ka daukaka musulunci da musulmai,ka taimaki bayinka masu kadaita ka,
Allah ka sanya wannan gari cikin aminci da natsuwa, da sauran garuruwan musulmai,
Ya Allah ka kasance tare da masu rauni a garin suriya mai ruwa da itatuwa, ya Allah ka kare jininsu, ka suturce al'aurarsu, ka amintar da su daga tsoro.  Ya Allah ka musanya musu tsoron su da aminci, bayan rauninsu Allah ka basu nasara.
Ya Allah an zalunce su ka taimake su, ya Allah ka taimake su akan wanda ya zalunce su,
Ya Mai karfi  ya Mabuwayi.   


ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق