الجمعة، 23 مارس 2018

KABARI MASAUKIN FARKO NE NA LAHIRA


Hudubar juma'a  na Masllacin Annabi na Shaikh Abdulbari Subaiti 6/7/1439 AH
Hudubar Farko:
Tafiyan Mutum a wannan rayuwa   masaukanta na sabunta , marhalolinta na jujjuyawa , yana rayuwa ne na wasu matakai a cikin mahaifiyar sa  sannan da wasu matakai a doron kasa , da wasu matakan kuma a cikin kasa har zuwa a tashe shi.
          Wannan tafiyan tana da tsawo a zahirinta  sai dai tana da saurin gushewa ,  kuma  tana da saurin karewa da tafiya,  to ita duniya ba gidan zama ba ne ga rayayye, mai hankali zai tuna irin jujjuyawa da take da shi  da saurin karewan shekaru,  sai ya ratsa jikin   zuciyan shi ta  tausasa .
           Masaukin da baya  yiwuwa ga ko wani matafiyi sai ya sauka gare shi  wata rana shi ne kabari   , kuma lallai  ya isa abin wa'azi a  gare shi , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya  ce : (Lallai kabari na da wata matsa  wanda da a ce dayan mu zai kubuta daga gareta  da  Sa'ad Dan Ma'azu ya kubuta daga gare ta ).
      An karbo  daga Amirul muminina  Usman Dan Affan  Allah ya kara yarda a gare shi ya kasance idan ya tsaya a wurin kabari  sai ya yi ta kuka har gemun shi ya jika da hawaye , sai a ka ce da shi  kana tuna aljanna da wuta amma ba ka kuka amma in ka tsaya a wurin kabari sai ka yi kuka    , sai ya ce na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa  : ( Kabari shi ne farkon masaukan lahira  idan mutum ya tsira daga gare shi to abin da zai biyo baya ya fi sauki  a gare shi, idan kuma bai tsira ba to abin da zai biyo baya ya fi tsanani a gare shi ).
                  Yana daga cikin rukunnan imani da ranar lahira akwai kudurtawa da hakikanin imani da kabari , imani da ni'iman kabari ga ma'abota da'a da kuma   azabar kabari ga  wadan da suka cancanta ma'abota sabo  da fajirci,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Badon kada ku ki binne mamatan ku ba da na roki Allah ya jiyar da ku daga azabar kabari na daga abin da na ke ji ).
Ziyaran kabari don daukan izina da wa'azantuwa sunna ce kuma kusanci ne, wanda ya ziyarci kabari zai tuna wadannan matattu wadanda kakaninsa ne da iyayensa, sai ya sakankance cewa zai mutu a binne shi kamarsu, kuma zaa tambaye shi a kabarinsa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( ku ziyarci makabarta zai tunatar da ku lahira).
                      Idan an binne mutum a kabarin shi  iyalan shi da dukiyan shi suka bada baya farkon maziyartan shi su ne mala'iku guda  biyu su mishi jarabawa,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (  Lallai idan an sanya mamaci a kabarinsa zai ji sautin takalman su lokacin da suke bada baya   idan ya kasance mumini ne sai salla ta kasance ta kansa azumi ta kasance ta damansa , zakka kuma ta hagunsa,  zai  kasance ayukan  da yake aikatawa na alheri  na daga sadaka da salla da ma'arufi da kyautatawa mutane a ta kafan sa , sai a zo ta kansa sai salla ta ce tanan ba gun shiga zai a je  ta daman sa sai azumi ya ce ta guna ba mashiga  sai a zo ta hagun sa sai zakka ta ce  ba wani mashiga ta guna  sai a zo ta bangaren kafafuwan sa  sai ayukan alkairi   na daga sadaka da  ihsani da kyautatawa mutane  su ce ba mashiga ta guna  sai  a ce da shi zauuna , sai ya zauna  sai a suranta mishi rana tana kusan faduwa  sai a ce da shi ko ka ga wannan  da ke fiskantar ku me za kace  game da shi  me za ka shaida kuma game da shi ? sai ya ce ku barni na yi salla , sai a ce da shi, ai za ka yi amma bamu labarin a bin da muka tambaye ka game da shi ,  ka ga mutumin nan da ke ta fiskar ka me za ka ce game da shi kuma wacce shaida za ka masa? Sai yace : Muhammad, ne, kuma na shaida shi           Manzon Allah ne, kuma yazo da gaskiya daga Allah  ,  sai a ce da shi : akan haka ka rayu, kuma a kan haka ka mutu , kuma a kan haka za a tashe ka in Allah ya yarda , sai a bude mishi kofofi n Aljanna  sai a ce da shi  nan ne masaukin ka a cikinta da abinda Allah ya tattala maka a ciki  sai ya kara jin kaimi da farin ciki  , sa'annan sai a bude mishi kofofin wuta  sai a ce da shi ka ga wannan  shi ne masaukin ka da abin da Allah ya tattala maka a ciki da ka saba mishi , sai ya kara kaimi da farin ciki  sannan sai a buda mishi a kabarin shi   zira'i  saba'in  a haskaka mishi ciki  a maida jikin shi kamar yanda aka fare shi , sai a sanya ruhinsa a cikin wani iska mai dadi  wato wani tsuntsu ne ke shawagi akan itaciyar aljanna  wannan shi ne fadin Allah madaukakin sarki  ( Allah yana tabbatar da   wadan da suka yi imani da magana tabbatacciya  a cikin rayuwar duniya   da cikin lahira kuma Allah yana batar da azzalumai ).      Lallai kafuri  in anzo ta fiskan shi ba za a samu komai ba , in anzo ta daman shi ba za a samu komai ba in anzo ta hagun shi ba za a samu komai ba sai a zo ta kafafuwan shi ba za a samu komai ba  sai a ce da shi zauna sai   ya  zauna  cikin tsoro  da firgici, sai a ce da shi  ba ka  ga wancan mutumin da ya kasance a cikin ku ba me za ka ce game da shi kuma wacce shaida za ka  yi akansa , sai ya ce wani mutumi?  Ba zai ma gane sunan shi ba  sai a ce da shi Muhammad      sai ya ce ban sani ba  na ji dai mutane suna cewa wani magana sai ni ma na fada  kamar yanda suka  ce, sai a ce da shi  a haka ka rayu kuma ahaka ka mutu kuma akan haka za a tada  in sha Allahu, sai a bude mishi kofa daga   cikin kofofin wuta sai a ce da shi wannan ne masaukin ka na daga wuta  da abin da Allah ya tanada maka na daga cikinta ,   sai ya kara bakin ciki da hasara  , sannan a bude mishi kofa daga cikin kofofin Aljanna   ace da shi, wannan masaukin ka ne a cikin ta da abin da Allah ya tattala maka  da ka mishi biyayya,  sai ya kara bakin ciki da hasara  sai kabarin shi  ya kuntata a gare shi  har  kasusuwan hakarkarin shi su shiga junan su.
               Wannan ita ce rayuwa ta kunci wanda Allah ya ambata ( To lallai ne rayuwa mai kunci ta tabbata  a gare shi ,  kuma muna tayar da shi a ranar kiyama yana makaho ) Dabarani ne ya rawaito da Ibn Hibban a sahihin sa .
       Mai hankali  zai shirya ne kafin mutuwa ya kimtsa wa kabarinsa don kansa,  ya raya ta, ta hanyar ayuka na kwarai  da imani  don ya kasance yana da dausayi daga cikin dausayin Aljanna Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Yana daga cikin abin da zai riski mumini   bayan mutuwan na daga aikin shi da kyawawan aikin sa ,    ilimi da ya ilmantar kuma  ya  yada shi   ,  da Da na kwarai da ya barshi , da Alkur'ani da ya gadar da shi ko masallaci da ya gina ,  ko kuma gida da ya gina na 'yan tafarki , ko korama  da ya buda ya gudana , ko sadaka da ya fitar daga dukiyar shi ,  a halin yana mai lafiya yana raye  zai riske shi  bayan mutuwar sa .'
     Wanda ke yawan  tuna mutuwa  zai raya kabarin sa da kyawawan ayuka, domin ya sani bisa yakini , lallai shi ya sani idan ya wayi gari ba zai yi yammaci ba  , idan kuma ya yi yammaci  ba zai jira wayan gari ba  sai ya yi gaggawa zuwa ga ibada kafin a yi shamaki tsakanin shi da ita , ga Amr  dan As  yana ganin mamaci an binne shi sai yayi sauri ya tafi masallaci ya yi salla raka'a biyu, sai aka ce da shi me ya sa ka yi haka ?,  sai ya ce makabarta ta tuna min fadin Allah ( Sai aka yi   shamaki  tsakanin su da abin da suke sha'awa  ).
     Sai na sha'awi salla kafin a yi shamaki tsakani na da ita , wanda yake son aboki a kabari wanda zai debe mishi kewa, ya haskaka mishi kabarin shi  ya tafiyar mishi da kadaici to ya riki Alkur'ani .
     Yana daga cikin sabuba na tsira   daga fitinan kabari da azabar sa, dauwama akan karanta suratul mulk, da aiki da abin da ta hukunta .  An  karbo daga Dan Mas'ud Allah ya yarda da shi ya ce :  (Za a zo wa mutum a cikin kabarinsa sai a zo  ga kafansa sai kafofin sa  su ce :   ba ku da wata dama ko kofa ta fuskar mu ya kasance yana tsayuwa da mu  ya karanta suratul mulk sannan sai a zo ta kirjin sa ko ta cikin sa ,  sai ya ce  ba ku da wata dama ta bangare  na a kan shi ya kasance da ni yake karanta suratul mulk  sannan a zo ta kasan sa sai ya ce  baku da wata kofa  akan shi game da ni ya kasance da ni yake karanta suratul mulk  ,  sai ya ce : ita ce  mai hani, tana hani  daga azaban kabari  tana cikin attaura suratul mulk   wanda ya karanta ta a dare to hakika ya yawaita kuma  tsawaita )  Hakim ne ya rawaito shi a mustadrak ya ce ingantacce ne amma(Bukhari da Muslim) basu fitar da shi ba  Albani  ya  inganta shi  
                 Istigfari ga muminai da musu adu'a zai tabbatar da al'amarin ka a kabari yayin tambaya  , Manzon Allah tsira  da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance in ya binne mamaci  sai ya tsaya gaba gare shi sai ya ce ku nemawa dan uwan ku gafara  kuma ku roka mishi tabbatuwa domin   yanzu za a tambaye shi  , mutanen kwarai na raya  kaburburan su ne ta hanyar lazimtar adu'o'i a ko wace salla, suna  neman tsari  daga fitinan  kabari , Annabi ya kasance yana adu'a Ya Allah ina neman tsarin ka daga azaban kabari da azabar wuta ,  da fitinar rayuwa da ta mutuwa,  da fitinan  masihuddajjal).

      HUDUBA NA BIYU
Musulmi mai hankali yana kiyaye wa daga guraren fitina da halaka,wanda ke lalata al'umarsa kuma ya fitine shi a kabarinsa, na daga ciki akwai yada karerayi da sadar da su, ya zo a hadisin Isra'i da Mi'iraji mai tsawo Jibrilu ya ce da Manzon Allah ( amma shi  mutumin da ka zo mi shi ana keta mukamukin sa  zuwa keyan sa ,  da hancin sa zuwa keyan sa da idanuwan sa  zuwa keyan sa , to lallai mutum ne yana wayan gari daga gidansa sai ya yi karyan da za ta bazu a duniya  ,  yana daga ciki kuma akwai cin riba da halatta shi    ya zo a hadisin isra'i da mi'i raji , amma mutumin da ka zo mi shi  yana iyo a korama yana hadiye duwatsu to  lallai shi maciyin riba  ne )  .
    Yana daga ciki mutumin da yake bacci ya bar sallan farilla da me kauracewa kur'ani , to a cikin hadisin isra'i da mi'iraji ( Amma mutumin da ka zo mishi yana dandaka kansa da dutse shi ne mutumin da yake daukan kur'ani ya yi watsi da shi , ya yi bacci kuma daga sallan farilla).
Yana daga cikin sabuba na azaban kabari yawo a tsakanin mutane da annamimanci da yin sake wurin tsarki , manzon Allah ya wuce wasu kaburbura  guda biyu sai ya ce :( Lallai su dinnan ana azabtar da su ne kuma ba akan wani abu mai girma ba ake azabtar da su, amma dayan su ya kasance ba ya tsarkaka daga fitsari, shi kuma dayan yana yawo da annamimanci).Sahihul Jami'i:  Albani.      
   

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق