Hudubar juma'a na
Masallacin Annabi tare da sheikh Salah
bin Muhammad Albudair 20-7-1439 AH.
Hudubar farko:
Ya ku Musulmai ! Ajali
na kusantowa, Burace –burace na karewa, duk wani tsani ya yanke, lokacin tafiya
da kaura ya zo, ya raba mutum da iyalai da sadawa da su,
Ba na ganin akwai
abin da zai sha gaqban mutuwa ya tsallake ta, *
Mutuwa ta katse jin dadi ga mawadaci
da talaka.
Ka yi dubi ga duniya
da idon mai ban kwana, *
Domin
hakika tafiyar ta kusa lokacin ban kwana ya yi.
Lallai Masoyi abin
fizgewa ne daga masoyansa, *
Mai gadi ko mai tsaro bai
hana mutuwa.
Ta yaya zai yi farin
ciki da duniya da jin dadin cikinta?*
mutumin da ana kidanya masa lafuzansa da numfashinsa.
Dukkan wata gida
–wata rana-abar rushewa ce *
Komin dadewarta bisa ginshikinta.
Ya ku musulmai!
Yayin da duniya ta
kasance gida ce ta fitintinu da jarabawa to mutum zai dandani wahalar neman
abin rayuwa ,da gwagwarmaya da bala'i da cututtuka da nau'uka na musibu, da cin
karo da abubuwa masu hanun riga, da kawatarwa irin na shaidan, da ma'abota
barna.
Mai kyauta da karamci
Mai jinkai,Mai girma ya yi kira ga bayinsa muminai zuwa ga Aljannarsa gidan karamcinsa gidan aminci da ni'ima, kubutacciya daga
bakin ciki da bacin rai, wanda babu matsaltsalu da tashin hankali da bala'I,(kuma
Allah na kira zuwa gidan aminci)
Idan duniya ta ma
kunci gabadayanta *** ka zama baka da wani masauki sananne.
To ka yi gaggauto
zuwa ga Jannatu Adnin domin ita dinnan
*** Masaukan mu ne na farko kuma cikinta akwai shemomi
sai dai fursunonin
yaki ne na Magauda (Makiya) abin mamaki ya jama'a *** shin ko za mu koma gidajenmu mu samu
aminci?
Gida ce da ni'imarta
bai karewa , bai halakewa,gidan da akwai
dukkan alheri cikinta har da kari, an tanade ta an kusanto da ita an kawata ta domin
karramawa ga masu tsoron Allah, ba su jin tsoron wani abu a ciki na bakin ciki
ko hayaniya da gajiya,ba su tsoron talauci ko bashi a cikinta,ko fitarwa ko
katsewa ko karewa ba. (Ba zaa fitar da su daga cikinta ba).
Duk wanda ya shiga
Aljanna ba zai samu wata damuwa ba, tufafinsa ba zai ridddige ya tsufa ba,haka
samartansa ba zai tsufa ba, mai yekuwa zai kira su : (lalle za ku samu lafiya a cikinta ba za ku yi rashin lafiya
ba har abada, kuma ku rayu ba za ku mutu ba har abada, kuma ku zama matasa
ba za ku tsufa ba har abada, lalle kuma za ku samu ni'ima ba za ku samu wata
damuwa ba har abada, sai a ce : Ya ku 'yan Aljanna ku dawwama ba mutuwa har
abada, ya ku 'yan wuta ! ku dawwama ba mutuwa,
a cikin Aljanna akwai abin da ido bai taba gani ba, kunne bai taba ji
ba,zuciyar dan Adam bai taba hararo shi ba,).
(Mala'iku na shiga
musu ta kowace kofa, Amincin Allah ya tabbata a gare ku sabo da hakurin da ku
ka yi, madalla da gida mai kyakkyawan karshe).
Allah Mai girma!!
Mala'iku na shigo musu,!! Mala'iku su zo musu,Mala'iku su gaishe su, Mala'iku na taya su murna!!
(To amincin Allah ya
tabbata a gare ku, kun ji dadi, ku shige ta kuna masu dawwama.)
Abin mamaki da girman
wannan kusancin da girmamawa a gidan aminci.
Lalle Allah Madaukakin
sarki zai ce ga 'yan Aljanna, :(
ya ku 'yan Aljanna ! sai su ce : Mun amsa kirarka kuma mun rusuna, sai yace :
ko kun gamsu? Sai su ce : ta yaya ba
za mu gamsu ba bayan ka bamu abin da baka baiwa wani ba daga cikin halittunka,sai
yace : zan baku abin da ya fi haka.sai su ce Ya Ubangiji me ne ne ya fi
hakan?, Sai yace : zan sanya yarda ta a gare ku bayan haka ba zan yi fushi
da ku ba har abada).
(Kuma yardar Allah
ya fi girma)
Ya fi girma bisa
Aljannar da koramanta ya fi girma akan benayenta da tufafinta da guzurinta.
Amma ganin Allah a
Aljanna shi ne abin da masu jan damara su ke jan damara akan shi, masu yin
munafasa da rige –rige ke tsere a kan shi, ya hana shi ga wadanda aka musu
shamaki da Ubangijinsu, kuma aka kore su daga kofarsa, Allah Madaukakin
sarki ya ce :(Wasu fiskoki a wannan rana suna mani'imta ne. masu dubi zuwa ga Ubangijinsu) Al kiyama 21-22
An karbo daga Abu
Musa Allah kara yarda a gare shi yace : Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce : Gonakai guda biyu na azurfa kwanukansu da abin da ke
cikin su,da gonakai biyu na zinari
kwanukansu da abin da ke cikinsu, ba wani abu da yake tsanin mutanen da
su ga Ubangijinsu mai tsarki da daukaka
face rigar girmame –girmame a fiskarsa
cikin Aljannar Adni) Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
An karbo daga
Suhaibu daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, daga Annabi
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :: Idan 'yan Aljanna sun
shiga Aljanna Allah Madaukakin sarki zai ce : Ko kuna son wani abu na kara
muku? Sai su ce : Allah ba ka haskaka fusakanmu ba ka shigar da mu Aljanna ba
kuma ka tseratar da mu daga wuta? Yace sai ya yaye hijabin sai su ji dadin da ba a taba basu wani abu da ya fi soyuwa a gare
su ba kamar ganin Ubangijinsu ba
Mabuwayi da Daukaka).Muslim ne ya rawaito.
Ibnul Kayyim Allah ya
mishi rahama ya ce : To wannan kenan in
ka tambayi ranar kari daga Mabuwayi Abin
godiya, da ganin fiskarsa tsarkakakka daga misali ko kamanci, kamar yadda kake
ganin rana lokacin azahar, da kuma wata a daren sha hudu, kamar yadda aka karbo
daga mai gaskiya abin gaskatawa,ta hanyoyi
masu dumbin yawa, hakan na nan cikin sahihai da sunann da musnadai, na
daga riwayar Jarir da Suhaibu da Anas da Abu Huraira da Abu Musa da Abu Sa'id ,
Ka saurari ranar da mai kira zai yi kira ? Ya 'yan Aljanna Ubangijinku zai nemi ziyartarku,, to ku zo , don
ziyartarshi, sai su ce : mun ji mun bi,sai
su taso zuwa ga ziyara suna gaggautowa har lokacin da suka isa kwarinmai fadi wanda aka sanya musu magama, suka hadu a
can ba wani guda da mai kiran ya bari, Ubangiji Allah sai ya yi umarni da a
kafa masa kujerar sarautarsa, sai aka kafa, su kuma aka kafa musu minbarai na haske, da minbarai na lu'ulu'u, da
minbarai na zubarjadi, da minbarai na zinari da minbarai na azurfa, mafi karancin
daraja a cikinsu ya zauna,- duk da ba wani makaskanci cikinsu- bisa wata
turbaya na almiski, kuma basu ganin nan kan kujera sun fi su samu kyauta,
Har zuwa lokacin da
kowa ya natsu a mazauninsa hankali ya kwanta, sai mai kira ya yi kira,: ya 'yan
Aljanna lalle kuna da wani alkawari a
gurin Allah da yake so ya cika muku! Sai su ce : Mene ne shi? Ase ba an haskaka
fisakanmu ba,a ka nauyaya mizaninmu ba, aka shigar da mu Aljanna ba, aka
nesatar da mu daga wuta ba? Suna cikin haka sai wani haske ya bayyana wanda Aljanna ta haskaka da shi, sai suka
daga kawunansu, sai ga Aljabbaru (kasaitacce) Girmansa ta kasaita,
sunayensa sun tsarkaka, ya fuskanto su daga ta samansu,yace : (ya 'yan
Aljanna amincin Allah ya tabbata a gare ku) Ba a amsa wannan gaisuwar da
sama da fadin cewa : ya Allah kai ne aminci, daga gun ka aminci ya ke, albarka
ta tabbata a gare ka,ya Ma'abocin girma da karamci,sai Ubangiji ya yi tajalli
a gare su(Ya bayyana) Albarka da daukaka sun tabbata a gare shi, ya musu
dariya yace : Ya 'yan Aljanna ! sai
ya zama farkon abin da zasu ji daga gare shi shine : Ina bayi na da suka yi min
biyayya a fake bisa halin ba su ganni ba? To wannan ne ranar kari , sai su yi
tarayya a kalma guda: Mun yarda to ka
yarda da mu, sai ya ce ya 'yan Aljanna in da ban yarda da ku ba da ba zan
saukar da ku a Aljanna ta ba. Sai yace :
wannan ne ranar kari ku roke ni! Sai duk su yi tarayya a kan kalma guda: ka
nuna mana fuskar ka mu yi dubi zuwa gare shi, sai Ubangiji Allah Madaukakin sarki ya yaye shamaki, Daukaka
ya tabbata a gare shi, sai ya yi tajalli a gare su, sai ya lullube su da haskensa,
sai su manta da duk wata ni'ima da su ka taba gani, badon Allah ya hukunta ba
za su kone ba da sun kone, ba wani da zai rage a wannan majlisar har sai
ubangiji ya mar lacca kai tsaye, har ma ya ce ya wane ko kana tuna ranar kaza
ka aikata kaza da kaza,? Yana tunatar da shi wasu sashi na ha'ince –ha'incen da
ya yi a duniya, sai ya ce ya Ubangiji ba ka yafe mini ba? Sai yace ai da gafara
tawa ce ka kai wannan matsayin taka da ka ke kai.
Allah Mai girma! Abin
mamaki da girman irin wannan ni'imar,
abin mamaki da irin wannan karramawar, zasu ga Ubangijinsu a Aljanna, za su ga Allah Ma'abocin girma da kyau da
kamala, za su ga abin bautan da sun dade suna bauta masa, suna mishi tasbihi,da
halala da kabbarori, suka yi mishi
sujada kuma suka girmama shi.
Wani irin dadi ne da
jin dadi, wace irin ni'ima ce, wani irin rayuwa ce wani irin walwala ce,wani
irin zabi ne, zasu ga Allah wanda duniya
bata yi dadi ba sai da ambatonsa,lahira ma bata yi dadi ba sai da
yafiyarsa, haka ma Aljanna ma bata yi dadi ba sai da kallo zuwa gare shi, wayyo
kwadayinmu zuwa gare shi, wayyo shaukinmu zuwa ga gidan ni'ima, wacce a cikinta
masu kadaita Ubangiji zasu , zai yi tajalli a gare su ya bayyana, kuma yayi
dariya agare su,ya fiskanta zuwa gare su, kuma yana bayyana ga 'yan Aljanna a
kowace juma'a, cikin wata turbaya na Alkafur sai su kasance kusa da shi
gwargwadon gaggawar su zuwa Juma'a a duniya,ba su kara dubi zuwa ga Ubangijinsu
sai hakan ya kara musu karama.
Zaka ga fiskar
Ubangiji madalla da fiska da ke cike da
kauna da daukaka.
Ya ku bayin Allah!
Wannan dadin labari ina
ga dadin ganin?
Ya Allah muna rokon ka
dadin dubi zuwa fiskar ka, da kwadayin haduwa da kai, ba cikin wata cuta ko
cutarwa ba, ko wata fitina mai cutarwa ba.
Huduba ta biyu
Ya ku musulmai !
Ku kimtsa kayanku ku
gaggauta morar rayuwarku ku ribaci
lokacin ku, to me ke baya ni'ima da jin dadi da kawar rayuwa da walwalarta face
mutuwa da kare wa da rididdigewa,
Mutuwa kofa ce kuma
dukkan mutane zasu shige ta
Me zan ji bayan
wannan kofar me ke cikin gidan?
Gidan Aljanna ne na
dawwama muddin ka yi aiki da abin da zai
yardar da Allah
In ka gaarta sai
wuta, sune gidaje biyu mutane basu da wasu gidan in ba su ba.
To ka duba wa kanka
wanne zaka zaba.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق