الجمعة، 20 أبريل 2018

sha'aban wata ne na kimtsawa don ramadan


Hudubar juma'a  na Masallacin Annabi tare da sheikh Abdullah Bin Abdurrahman Albu'aijan 4-8-1439AH
Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, wanda ya sanya jinjirin – wata  lokuta ne ga mutane da kuma sanin kidayan  zamani, shekaru da watanni , ya sanya dare da wuni  mayau ga wanda ya ke  nufin ya wa'azantu ko ya ke nufin  godiyar    ni'imar  Ubangiji  , na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya , ya sanya rana ya zama mai tsananin haske da wata kuma mai haske   na shaida Annabi Muhammadu bawan sa ne kuma Manzon sa ne  , ya turo shi da shiriya da addini na gaskiya , yana mai albishir da gargadi kuma mai kira  zuwa ga Allah da izinin shi da fitila mai haskakawa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabban shi da aminci tabbatacce mai yawa .
            Bayan haka :
 Lallai zance mafi gaskiya shi ne littafin Allah , mafi kyan koyarwa shi ne koyarwar Annabi  mafi sharrin al'amura shi ne fararrun ta , kuma dukkan fararrun abu bidi'a ne  kuma dukkan bidi'a bata ne  kuma dukkan bata na wuta .
        Bayin Allah :
Ina muku wasiyya da ni kai na da tsoron Allah  mabuwayi da daukaka, domin ita ce wasiyyar mutanen farko  da na karshe  ( Hakika mun yi wasiyya ga wadan da aka bawa littafi  kafin ku da ma ku kanku da ku ji tsoron Allah ).
YA JAMA'AR MUSULMI:
Lallai  Allah na da  wasu yanki na  rahama  to ,  ku yi kokari ku same su  da wasu zamuna na alheri  to ku yi kokari ku same su  da kuma lokuta masu falala ku yi kwadayin riskan su, ga su sun  fiskanto  ku,  to ku fiskance su  ga su sun sauka gare ku to ku ribace su  domin su dinnan wasu lokuta ne kadan  da za su zo su wuce kamar kyabtawan ido,  kaito ga sarayar da rayuwa ga mutumin da  ya sarayar da ita, madalla  kuma da  wanda ya ribace ta  ya yi nasara da ita (Shi ne wanda ya sanya dare da rana mayau ga wanda  yake nufin  ya wa'azantu ko yake nufin godiyar ni'imar Ubangiji ).
                     Rajabu ya shude  to me  ka kaddamar a cikin shi  *** Ga kuma watan   sha'abanu mai albrka   
Ya kaiton wanda ya sarayar da lokuta bisa jahilci *** da alfarmar ta  ka farka  ka kuma kiyaye  albarkoki 
To da sannu  za ka rabu da jin dadi  cikin karfi *** mutuwa kuma  zai sanya ka a kana ki   ka bar gidan ka
Ka yi kokari  ka tuba daga kusakurai ***tuba irin na mai iklasi kuma ka sanya  abun riska
Bisa neman kubuta daga wutar jahima *** mafi alkairi ga ma'abota laifuka shi ne wanda ya yi kokari ya gyara.
YA KU BAYIN ALLAH
Hakika watan sha'abana ya sauka a gare ku, kuma yana cikin lokuta na da'a  da kuma lokuta masu falala,  ana neman alheri a cikin shi  ana daga ayyuka a cikin shi  da ayuka na kusanci , an karbo da Usama Dan Zaid Allah ya kara yarda a gare su da baban shi  ya ce : '' na ce ya  Manzon Allah  ban gan ka kana azumtar wani  wata daga cikin watanni ba kamar yanda  kake azumtar sha'aban''. Sai Manzon Allah ya ce  (Wannan wata ne da mutane ke gafala daga gare shi,  wanda ke tsakanin rajab da ramadana  shi ne watan da ake daga ayyuka a cikin shi  zuwa ga Ubangijin talikai , ina so  kuma a daga ayyuka na  ina mai azumi , an karbo daga Aisha Allah ya kara yarda a gare ta  ce : Manzon Allah ya kasance yana azumi har mu ce ba zai sha ruwa ba , kuma yana shan ruwa har mu ce ba zai yi azumi ba  ban ga Annabi ya cika azumin wani wata ba  sai ramadana  ban ganshi kuma yana yawaita azumi ba kamar yanda yake yawaitawa a sha'aban .
YA KU BAYIN ALLAH
Lalle watan sha'aban fage ne na kimtsawa da shiryawa don fiskantar ramadan, to shi rai na bukatar maimaci da a bi da shi mataki bayan mataki, da shimfida har ya saba da shi, haurawa zuwa sama na bukatar matakala da tsani, rayi kan kwace, jiki kan gaji  kuma mutum ya kosa daga ibada   sabo da ba abi da shi mataki -mataki ba sai ya rasa jin dadin ta  kuma ya rinka haduwa da tsananin ta , ta iya yiwuwa ma ya yanke daga  gare ta  ya kasa cigaba da ita  sai alheri mai yawa ya tsere mishi .
               Ya yin da sha'aban ya kasance  mukaddima  ne ga  ramadan  to ya dace ga musulmi ya dage a cikin ta  irin kokarin da zai yi a ramadan , matsayin azumin sha'abana ga ramadan kamar matsayin sunnonin farilla ne  ga  sallan farilla , azumtar shi na daga cikin shiri ne da kwadayi bisa ga  ramadana daya daga cikin rukunnan musulunci   kuma azumi  na  daga cikin ibadoji  da ake  neman kusanci da shi  da kuma  da'a  da ibada mafi girma,  an karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : '' Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: ''Allah madaukakin sarki ya ce : ( Dukkan aikin dan adam na shi ne sai azumi  lallai shi nawa ne kuma ni zan sakanya game da shi ).
          (Kuma azumi garkuwa ne  idan dayan ku na azumi  kada ya yi fasikanci   kada ya yi batsa  kada ya yi hayaniya   in wani ya zage shi  ko ya yi fada da shi ya ce ni mutum ne mai azumi .( Na  rantse da wanda ran muhammadu ke hanunsa   warin bakin mai azumi ya fi kamshi a wurin Allah a kan turaren almiski),  ( mai azumi na da farin ciki biyu ; farin ciki yayin shan ruwarsa da kuma  farin ciki yayin  haduwa da Ubangijinsa) .
   YA JAMA'AR  MUSULMI:
Kofofin alheri a bude suke, kuma Allah baya sarayar da ladan wanda ya kyautata aiki  ,ga aiyuka na da'a da suke saki waiwai  ba a kayyade su da zamani ko wuri ba,  nau'ukan ayyukan da'a   suna da yawa  kuma suna fin junan su  gwargwadon lokaci  sai dai  ba wasu ibadoji na da'a da aka kebance  su da watan  sha'aban  sai dai wata ne da ake daukaka ayukan shekara a cikin ta  kamar yanda ake daukaka ayukan mako     a litinin da alhamis  ya dace mutum ya yi kwadayin  ya cika ta , sabo da haka ne Manzon Allah yake  son  azumtar shi , kamar yanda ya ke son azumtar litinin da alhamis .
    Ya jama'ar Musulmi :
Lallai gafala wata cuta ce mai wuyan magani  kuma  abu ne na laifi wanda yake mai zunubi  yana  yanke sila tsakanin bawa da Ubangijin shi ba zai rinka jin wani laifin shi  ba   ko ya yanke daga  alhakin shi ba ,  ba zai tuba daga zunubin shi  ba  ba zai yi wani ma'arufi ba ko ya yi hani ga wani munkari ba   lokutan alheri na ta wuce shi da lokutan falala  alhali yana cikin bacci na gafala  baya farkawa  yana gani baya lura ana mishi wa'azi baya wa'azantuwa ana fadakar da shi baya fadakuwa  hakika Manzon Allah ya kwadaitar game da  azumin sha'aban sabo da gafalan da yawa daga cikin mutane game da shi  sai ya ce  : (  Wancan wani wata ne da mutane suke gafala game da shi  yana tsakanin rajab da ramadana ).
         Ya mai yiwa kan shi nasiha ka gajarta buri  kuma ka farka daga gafalan ka  ka yi shiri don hisabi  kafin zuwan ajali .
      Ina neman tsarin Allah daga shaidan  abin jefewa 
(Ka tsare kanka tare da wadan da suke bautawa Ubangijin su  safiya da maraice suna nufin  fuskan Allah da ibada  ta su  kada ka juyar da idanunka da barin abokantaka ta su , kana nufin kawar duniya   kada ka bi wadan da muka rafkanar da zuciyar sa da barin ambatonmu  ya bi son zuciyar sa  a cikin shirka  al'amarin sa ya kasance faifayi )
Allah ya sa mini albarka ni da ku  a cikin alku'ani
HUDUBA TA BIYU
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah , yabon da ya dace da daukakar sa  tsira da amincin Allah su tabbata  bisa ga  zababbe cikin Manzannin sa da Annabawan sa  da iyalan sa da sahabban sa  da mabiyan sa da masoyan sa   .
YA KU BAYIN ALLAH :
 Lallai Allah  bai halicci mutum ba  ya kara mishi a tsawon rayuwa face don ya yi kokari wajen yi mishi da'a kuma ya nesanci saba mishi Allah madaukakin sarki ya ce :(Ban halicci mutum da aljani ba sai don su bauta mini)  Hakika Allah ya fifita wasu sashi na lokuta ya kwaranya musu sauki  da albarkatu da alheri mai busowa, ya shar'anta wasu hukunce-hukunce da ayyuka da kuma da'a, kuma ya yi wa bayin sa izini da su nemi  alheri a cikinta, to ku nemi alheri a dukkan zamaninku,kuma ku kutsa don karbar rahamar Allah, lalle Allah Mabuwayi da daukaka,na da wani yanki na rahamarsa da ke samun wanda ya so da ita daga cikin bayinsa.
Ya Al'uma masu kadaita Allah!
Ku kiyaye akidarku   ku rike ta da  hakwaran cin tuwo   domin ita ce tushen tsiran ku,  ku yi riko da addinin ku da littafin ku da shiryarwan Annabin ku
 YA JAMA'AR MUSULMI :
 Lallai Shaidan makiyi ne a gare ku to,  ku rike shi makiyi  domin shi dinnan yana iya kokarin shi a lokutan alheri da falala don ya batar da mutane daga shiriya ya yi shamaki tsakanin su da yanki na rahama da gafara ya katange su daga da'an Ubangijin su kuma ya sanya alheri mai yawa ya tsere musu  , sai ya batar da wasu sashi na daga  mutane ta hanyar shubuhohi  kamar yanda yake batar da wasu sashi na su ta hanyar   sha'awe –sha'awe  , sai ya fitini wasu mutane ta hanyar bidi'o'i da fararrun abubuwa   ya sarayar musu  da dama na lokutan alheri  ta hanyar bidi'o'i da sha'awe-sha'awe.
 TO YA JAMA'AR MUSULMAI :
(Hakika kuna da abin koyi mai kyau daga Manzon Allah   ga wanda ya kasance yana fatan Allah da ranar lahira )
(kuma duk wanda ya yi wani aiki wanda ba umarnin mu a ciki to an maida mishi )
To ku yi riko da sunna to fa dukkan fararren abu bidi'a ne dukkan bidi'a bata ne kuma   dukkan bata na wuta.
YA KU BAYIN ALLAH :
Duk wanda yake da ramuwa na ramadana a kansa to ya gaggauta azumtar shi  kafin shigowar ramadana  domin lokacin ya matse,  to, wajibi ne ga dukkan musulmi ya gaggauta biya  , ku yi tsere wurin ayukan alheri  ku gaggauta wurin da'a ku yi gaggawa zuwa ga gafara daga Ubangijin ku  da aljanna fadint ya kai kasa da sammai .
                YA KU BAYIN ALLAH
Hakika lallai Allah ya saukar a gare ku mafi daraja cikin littatafai ya kuma aiko muku da mafi daraja cikin manzanni ya cika muku addini kuma ya yarda da shi a gare ku  ya bayyana shi akan dukkan addinai , ya cika ni'ima  sai ya ce :  (A yau na cika muku addininku kuma na cika muku ni'imata a gare ku , na yarda a gare da musulunci a matsayin  addini)
 Hakika mun yarda da Allah shi ne Ubangiji da musulunci shi ne addini  kuma Muhammadu shi ne Annabi kuma Manzo ,
 muna rokon Allah da ya tabbatar da mu da tabbataccen zance  a rayuwan duniya  da kuma lahira , kuma ya  nisantar da fitina daga gare mu na bayyane da na boye ,  kuma ya azurta mu da riko da sunna  kuma ya tunkude mana gafala da tabewa kuma ya datar da mu  a sha'abana kuma ya riskar da mu da ramadana.
 ya  Allah ka daukaka musulunci ga musulmai  

       
      


ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق