Hudubar Juma'a a Masallacin Annabi tare da shaikh Abdulbari
dan Awad Assubaiti 18-8-1439 AH
Allah ya saukar da
littafinsa mai girma don shiryar da Dan-Adam , surorinsa haske ne, ayoyinsa
fayyacewa ne, kuma ruwan marmaro ne da
bai fakewa, mashayan ruwa ne da bai
bushewa, ko gurbacewa, wanda ke cikin damuwa da bakin ciki in ya fiskance shi
zai samu warakarsa cikinsa, haka wanda ke cikin bacin rai in ya koma masa zai
samu abin da zai rarrashe shi a cikinsa
ya bashi annashawa.
Na daga cikin gwalagwalai
masu tsada da ban kaye da ke cikin Alkur'ani akwai suratul ma'uni,
( Bamu labarin wanda
yake karyatawa da ranar sakamako.
Shi ne wanda yake
ingije maraya.
Ba ya kwadaitarwa
bisa ga ciyar da miskini.
To azaba ta tabbata
ga masallatan nan.
Wadan da suke
rabkana ga barin sallarsu.
Wadan da suke riya
kuma suke hana agaji.) Alma'un 1-6
Sura ce mai girma
tsarin gininta ta bayyana auratayya mai karfi da ke tsakani kuduri da halayya,
Wanda ke karyata ranar
sakayya shi ne mai karyata ladan Allah da ukubarsa, kuma ya karyata hisabi,
imani da ranar lahira bai zauna da gindin shi ba a cikin zuciyarsa, mummunar
kuduri na kai ga lalacewan aiki, lalacewan aiki alama ne na lalacewan kuduri.
Me yasa aka sifanta shi
da mai karyata sakayya, sabo da yana karyata addini ne, sabo da a rayuwansa bai
yi wani abu da ke hukunta yana yin addini ba kamar ya tabbatar da haka da
harshensa kuma zuciyarsa ta gaskata,sai dai bai aiwatar da jikinsa ba abin da
addini ya kumsa na halayya da dabi'un
addini ba, da bada hakki na imani da ke kansa ba, da bin tafarkin alkur'ani,
kuma kowa ya sani imani fadi ne da harshe da gaskata wa da zuciya da aiki da
gabbai.
Wanda imaninsa da
hisabi da sakayya ya yi rauni to shi ne mai karyata addini, wanda zuciyarsa
ta kekashe ta dunkule ta bushe, na daga cikin sifarsa yana ingije maraya ya
walakanta shi ya cutar da shi, shi bai iya da imaninsa mai rauni da ya
kyautata rayuwarsa da halinsa, ya
tsoraci mummunar aiki,
To ina kimar addini
idan tasirinsa bai bayyana ba a halaye da dabi'u ba?
To ina hakikanin imani
idan bai sa mutum ya yi laakari da waninsa ba har ya yi mishi alheri ba da
aikata ihsani da ciyar da miskini kai da kwadaitarwa bisa ciyar da miskini, ko
da a ce abin da Allah ya nema a yi abu ne na abin duniya to yin shi alama ne
imani.
Imani da tadawa da
sakayya shi ne zai ja ka zuwa ga
gaskiya, wanda zai dasa fiskantar ayyukan kwarai har ya zama mishi jiki, idan
ya taso a kai, ba zai mishi wahala ba zai tsarkaka ba tare da wani nauyi ba.
Kekashewar zuciya na
kaiwa zuwa ga gafala da karyata addini, maganin haka na cikin hadisin mafificin
halitta,Manzon halitta Annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi, lokacin da wani mutum ya koka mishi
bushewar zuciyarsa sai ya ce: Ka shafa kan maraya ka ciyar da miskini) Albani
ya rawaito cikin sahih Attargib wattarhib.
A fadin Allah : (ba
su kwadaitarwa bisa ga ciyar da miskini) akwai nuni ga cewa musulmi ana so
ya kwadaitar da waninsa wurin yin ihsani, hakan kuma ba zai sauke nauyin da ke
kansa ba aikata alheri ga masu rauni na daga marayu da miskinai gajiyayyu tare
da kiyaye mutuncinsu da yin nesa daga
karya zukatansu, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Magana kyakkyawa da gafara ya
fi alheri kan sadaka da gori ke binta)
Mafi suran ihsani shi
ne taimaka musu da kayan masrufi
da zai taimaka musu don tafiyar da rayuwarsu, da samar musu da hanyoyi na aiki ga zauna gari banza daga cikinsu da
tattala su da shirya su da samar musu da kayan aiki.
(To azaba ta tabbata
ga masallatan nan). Na
daga cikin sifofinsu suna yin salla ne na jeka na yika,ba tare da aikata abin
da sallar ta kumsa ba,ta wofinta daga hakikanin manufarta.rukunanta kuma a tawaye.
Wani mutum ya shiga masallaci ya yi sallah a halin Annabi na zaune a gefe, sai
ya zo yayi mar sallama sai Annabi ya ce: ( Je ka sake sallah don ba salla ka
yi ba.) Bukhari ne ya rawaito.
Wanda ya yi lura da
halin wadanda basu taimakawa marayu kuma basu ciyar da miskini, suna zamba kuma
suna karya, kuma suna saba alkawari, kuma suna zalunci zai samu suna rabkana ga
barin sallarsu.
Duk wanda ya tawaye
sallarsa to sai ya fi tawaye duk wani
abu komabayanta.
Idan ibada ta rasa
ma'anarta sai ta zama kawai motsa jiki
ne da ba karfafan imani ko gyaran hali, sai tasirinta ya raunana a rayuwa,
nassoshin kur'ani da hadisi sun bayyana hikimar shar'anta ibadoji da kuma manufofinta da tasirinta a rayuwar
mutane, kuma wasu makarantu ne na tarbiyya, Allah Madaukakin sarki ya ce : (ka
tsaida sallah don sallah na hana alfahasha da munkari)
Allah ya ce game da
azumi (ya ku wadanda suka yi imani an wajabta muku azumi kamar yadda aka
wajabtawa wadanda suka gaba ce ku ko zaku ji tsoron Allah)
Manzon Allah tsira da
amincin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Duk
wanda bai bar fadin karya ba da aiki da ita to Allah bai da bukatar ya bar abincinsa da abin
shansa) Bukhari ne ya rawaito.
Allah ya ce : Karbi sadaka
daga dukiyoyinsu ka tsarkake su da ita ka kwalle su daga tsatsar zunubai).
Yace game da Hajji :
(Namanta ba ya tarar da Ubangiji ko jininta sai dai tsarkakar niyya ce take
samunsa daga gare ku) Hajj 37
Sallah ita ce karshen
abin da zaa rasa na daga addini, idan ta tawaya to addini gaba daya ya tawaya,
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(za a
kwance igiyar riko na musulunci gaba gaba, a duk lokacin da wata igiya ta kwance
sai mutane su riki wacce ke bi mata, wacce zata fara warwarewa ita ce hukunci
na karshe ko ita ce sallah)
Ingantacce
ne Albani ya rawaito shi cikin Attargib Wattarhib kuma yana da wani hadisi da
zai karfafe shi a matsayin shahid.
Idan an datar da
bawa gurin yaki da musibar rabkanuwa daga barin ibada to suratul Ma'un
zata tunatar da shi game da gyaran zuciyarsa daga riya da fadin Allah (Wadan da suke riya)
wato masu yin riya a cikin sallah da waninta :ta hanyar aikata abu da yin shi
ba don Allah ba,sai don neman yardar mutane, Riya na daga cikin manyan zunubai
na zuciya, yana rusa aiki ya hana shi samun karbuwa a gurin Allah. Na daga cikin
abin da ayar ke nuni gare shi muna fahimtar niyyar da ta cakuda da riya na
sauya aiki nagari ya koma sabo, wanda ma'abocinta ya cancanci bone. Allah
Madaukakin sarki ya ce :
(To azaba ta tabbata
ga masallatan nan.
Wadan da suke
rabkana ga barin sallarsu.
Wadan da suke riya).
Haka nan ne zuciyar da
ta rasa ikhlasi maganar ta ba ta da kimai, ibada ba zata yi wani tasiri ba a
halayenta, kuma ba zaa karbi aikinta ba, ba tsarkaka ga ruhinta.
Na daga cikin mabudi
mafi girma na nasara : a datar da bawa ga jan ragamar sha'awarsa ta riya ya ja
mata linzami, kuma ya mika wuyarsa ga Allah, ya yi ikhlasi a aikinsa, niyyarsa
kuma ya fiskance shi da ita, ya tace ta daga neman wata ganima, ko sha'awa ko
matsayi ko dukiya, ko suna, ko samun matsayi cikin zukatar mutane, ko neman
yabonsu, ko gudun zargi a gare su, Allah Madaukakin sarki na cewa a hadisin
Alkudusi: (ni ne mafi wadatuwa daga abokan tarayya, duk wanda ya yi wani
aiki ya hada ni da wani a ciki to na bar shi abokin tarayyar tasa) Muslim ne ya
rawaito.
Huduba ta biyu
Karshen aya ta wannan
sura na nuni ga muhimmanci halye na gari ga al'uma, ta hana zamewa kankamo,
Allah Madaukakin sarki ya ce : ( kuma suke hana agaji.) wato suna hana bada
aron abin da mutane suke arawa junansu, cikin abin da ba a saba hana wa ba a
al'adance.
Wadannan basu kyautata bautan Ubangijinsu ba, basu kuma
kyautatawa halittunsa ba, ta hanyan bada aron abin da zaa amfana da shi a taimaka da shi, tare da wanzuwar abin a komo da shi ga mai shi, to wadanna n mutanen sun fi kusa da hana bada zakka da abubuwa na
neman kusanci sama da wani abu,
( Bamu labarin wanda
yake karyatawa da ranar sakamako.
Shi ne wanda yake
ingije maraya.
Ba ya kwadaitarwa
bisa ga ciyar da miskini.
To azaba ta tabbata
ga masallatan nan.
Wadan da suke
rabkana ga barin sallarsu.
Wadan da suke riya
kuma suke hana agaji.) Alma'un 1-6
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق