Hudubar Masllacin
Annabi 2-Ramadan -1439AH
Hudubar Farko:
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin sarki, muna gode mishi kuma muna neman taimakonsa
, kuma muna neman tsarin Allah daga
sharrin kawunanmu , da munanan ayyukanmu , duk wanda Allah ya shiryar da shi
babu mai batar da shi , duk wan da ya batar kuma babu mai shiryar da shi , na
shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin
tarayya , kuma na shaida Annabi Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa ne, tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa,
Bayan haka ku ji tsoron Allah - ya ku bayin Allah - hakkin tsoronsa, ku
yi riko da igiya mai karfi na musulunci.
Ya ku musulmai!
Ranaku da dararraki na tafiya cikin sauri, shekara na nade watanninsa
daya bayan daya, a cikin haka Masu bauta kuma suna komawa ne ga Allah, ba da jimawa ba
zasu je su riski ayyukansu,
Na daga falalar Allah da karamcinsa ya zaba musu zamuna da lokuta na da'a, ya zabi
wasu ranaku da dararraki da wasu sa'o'I don kara kaimin kwadayin ibada da
kimtsawa, masu munafasa kuma suna tsere gurin ayyukan alheri , a duk lokacin
da jinjirin watan ramadan ya bullo sai ya buso mana wasu kyauta masu albarka,
sai musulmai su fiskance shi zuciyarsu na cike da farinciki da annashawa, zai iya yiwuwa wani sa'a na karbar aiki ya
riski bawa sai ya kai wasu darajoji na
yarda da walwala.
Wata mafi daraja da tsarkaka ta
sauka gare mu,lokaci ne mai girma Allah ya kebance ta da karramawa da daukakawa,sai
ya turo manzonsa a cikinta ya saukar da littafinsa, ya farlanta azumtanta, sa'o'inta na da albarka, duk lokutanta ana
raya su da alheri ne, alheru na bibiyan juna a cikinta, albarka na gamewa a
cikinta, wata ne na ihsani da sadaka zamani ne na neman gafara da kankaran
zunubai, wuninta azumi ne darenta
tsayuwa ake yi, ana raya ta da Alkur'ani, ana bude kofofin Aljanna a cikinta,
ana rufe kofofin wuta,ana daure shaidanu da mari a cikinta, akwai dare a
cikinta da yafi wata dubu alheri, duk
wanda aka hana alherin cikinta to lalle katangagge ne daga samun alheri.
Ramadana fage ne mai yalwa don tsere cikin aikin da'a, kyauta ne na
gyaran zuciya daga dauda da matsaltsalu,wata ne mai karamci ana ribanya ayyuka
a ciki, ana kankare kusakurai a ciki da laifuka, Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce:(salloli biyar da juma;a zuwa wata
juma'a da ramadan zuwa wani ramadan na
kankare abin da ke tsakaninsu muddin an nesaci manyan zunubai) Muslim ne ya
rawaito
A cikin watan ne musulmai ke sauke nauyin daya daga cikin rukunan
musulunci, kuma wani abu ne na bayyane da ke nuna girman wannan addini, da kuma
hada kan musulmai, a nan ne fadin Allah Madaukaki sarki ya ke bayyana (Lalle wannan al'umarku ce guda daya kuma nine
Ubangijinku ku bauta min)
Ribatan lokutan alheri budi ne daga Allah ga wanda ya so daga cikin
bayinsa,a cikin ramadan na ne tushen Ibadoji mafi girma ke gamewa ga salihan bayi.
Salla sadarwa ne tsakanin bawa da Ubangijinsa,ba ta rabuwa da musulmi a
dukkanin rayuwarsa, sallar mutum cikin jam'i farilla ne tana daidai da sallar mutum a gidan
shi da kasuwan shi sau ashirin da bakwai, ya dace da musulmi ya nemi taimako da salla bisa azumin shi ,
kuma ya zama yana da kaso mafi girma na salla a darensa, To (wanda ya yi
tsayuwan dare na ramadana cikin imani da neman lada an gafarta masa abin da ya
gabata na daga zunuban shi) Bukhari da Muslim ne suka rawaito
(Wanda ya yi tsayuwan dare tare da limami har ya tafi to an rubuta
masa tsayuwan dare)Tirmizi ne ya rawaito.
Zakka da sadaka tsarkaka ne ga dukiya da habaka, wadata ne ga zuciya da
tsarkakuwa tasirinta a bayyane yake ga zuciya da dukiya da yara, mai tunkude bala'i mai janyo
yalwa, wanda ya yi kyauta ga
bayin Allah, Allah zai yi mishi kyauta, Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce : Allah
Madaukakin sarki ya ce ya kai dan Adam ! ka ciyar zan ciyar da kai.)Bukhari
da Muslim suka rawaito
Dukkan mutum yana inuwar mutuwarsa ne ranar Alkiyama, to ku yi sadaka da
da dan kadan ne, ka dadawa rai da ita,
ka taimaki maragalihu, (Duk wanda ya
ciyar da mai azumi yana da kwatankwacin ladan shi)
Kuma yana daga cikin koyarwarsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi akwai ciyarwa da kyauta, yana bayar
da kyauta irin kyautan wanda bai tsoron talauci, in ya zo bada kyauta sai ya
yalwata, in ya bada sai yawaita. Ba ya maida mai tambaya, Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ,ba a taba tambayarsa wani abu ba face ya
bada,
Manzon Allah ya fi kyauda a cikin ramadana, ya kasance a cikinsa mai
kyauta kamar iska mai kaiwa ga kowa.
Azumi shi ne ibada mafi girma a wannan wata mai falala, Musulmai na guzurin takawa a
cikinsa, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Ya ku wadanda suka yi imani an
wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabtawa wadanda suka gabace ku ko zaku ji tsoron
Allah)
Ladansa ba iyaka ko kididdiga, Allah ya ce a hadisul kudsi : (Dukkan
aikin dan adam na shi ne sai azumi don
shi nawa ne ni zan saka game da shi)Bukhari da muslim ne suka rawaito.
(Wanda ya yi azumin ramadana cikin imani da neman lada daga Allah an gafarta masa abin da ya gabata na daga
zunubansa)Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Azumi na shamaki tsakanin ma'abocinsa da sharri da zunubai, Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi (Azumi garkuwa ne)Tirmizi ne ya
rawaito
Ba abin da ya fi wani ya
nemi taimako da shi bisa takawa da kiyaye dokokin Allah da nesatan
abubuwan da Allah ya haramta kamar azumi, Ibnul kayyim Allah ya mishi rahama ya ce : ( Amfaninsa ya fi karfin
iyakancewa yana da tasiri na ban
mamaki wurin kiyaye lafiya.)
A lahira zai yi ceto ga ma'abotansa, Manzon Allah tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi ya ce : (Azumi da Alkur'ani suna ceto ga bawa a ranar
Alkiyama sai azumi yace ya Ubangiji na hana shi abinci da sha'awarsa a wuni to ka cece shi don ni,
sai Alkur'ani ya ce : Na hana shi barci da dare to ka bani cetonsa, yace sai a basu cetonsa.Ahmad ne ya rawaito.
Na daga cikin ayyuka na kwarai da ake ribata akwai umra , Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Umra a ramadan na
daidai da hajji)Bukhari da Muslim ne suka rawaito
Kur'ani maganar Allah ne kuma hujjarsa
ne a kan bayinsa, shi ne mabubbuga na hikima, mu'ujiza ce na sakon
manzanci, babu hanya zuwa ga Allah sai ta gun shi, babu tsira gare mu ba tare
da shi ba, haske ne na basira da kuma
gani wanda ya kusance shi zai samu daukaka
wanda yayi riko da shi zai samu buwaya
tilawar sa lada ne da shiriya, bitar sa kuma ilimi ne da tabbatuwa aiki da shi
kariya ne da aminci ilmantar
da shi
da kira zuwa gare shi kambina a kawunan masu biyayya , a
ramadana ana karfafa yawaita karanta
shi da tadabburi da neman iliminsa da kuma ilmantar da shi da aiki da shi da kuma bin koyarwar sa a cikin shi ne ya sauka , Allah madaukakin
sarki ya ce: ( watan ramadana da a ka saukar da alkur'ani a cikin ta shiriya ne ga mutane da bayyanannu na daga shiriya da rarraabewa).Jibrilu
amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana bitan alkur'ani tare da
Annabinmu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sau daya a kowace shekara ,
a shekarar da ya rasu a
cikinta ya yi bita tare da shi sau biyu
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi .
Addu'a ibada ce kuma kusanci
ce , wata ganima ce da ba tare da wahala ba
kuma riba ce wanda babu asara a cikin ta , yana janyo sauki kuma makiyi ne ga dukkan wani
bala'I ba wanda zai halaka muddin yana
adu'a, da shi ne bawa yake riskan burin shi
ya samu bukatar sa , sau da yawa
yakan kusanto da abin da yake nesa kuma sau da yawa yakan saukake abu mai wahala sau da yawa kuma yakan yaye bakin
ciki mafi karbuwan adu'a shi ne wanda
aka yi shi a cikin karshen dare , idan
bawa ya marairaice a gaban Ubangijin shi
, sai Allah ya amsa mishi bukatar
sa , idan rayi ta ji yunwa sai zuciya ta
tausasa ta kwanta mai azumi ba a maida
adu'ar sa har zuwa lokacin buda baki Ibn
Rajab Allah ya mishi rahama ya ce :
( Mai azumi a daren sa da yinin sa yana cikin
ibada ne , ana amsa adu'ar sa a azumin sa haka kuma yayin buda bakin
sa , to shi a wunin sa yana azumi kuma
yana mai hakuri a daren sa kuma mai ciyarwa ne kuma mai godiya )
Wanda ya yi gamon-katar shi ne wanda ya kwankwasa kofar sama, ya sanya
wa kansa a wadannan ranaku da dararraki wani abin adana.
Ambaton Allah ibada ce mai girma mai sauki,duk wanda ya ambaci Allah to
Allah zai ambace shi, bawa idan bai shagaltar da harshensa ba da anbaton Allah
ba to kuwa zai shagaltar da shi da magana mara amfani da na sabo.
Addini muamala ne, mafi cancanta
ihsaninka cikinn halittu shi ne wanda Allah ya gwama hakkinsu da na shi, Iyaye biyu Aljannaka ne kuma wutar
ka ne, su suka fi cancanta ka kyautata musu cikin mutane, Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi,ya
ce : (Hancinsa ya dumbuli kasa ! Hancinsa ya dumbuli kasa! Hancinsa
ya dumbuli kasa! Sai aka ce da shi wane ne? wanda ya riski iyayensa biyu sun
girma ko daya daga cikinsu ko su biyun bai shiga Aljanna ba),Muslim ne ya rawaito.
(zumunci na hade ne da Al'arshi ne tana cewa ya Allah duk wanda ya
sada ni ka sada misi, wanda ya yanke min ka yanke mishi)Bukhari da Muslim ne
suka rawaito.
(wanda zai burge shi da a yalwata mishi a arzikinsa, a jinkirta masa a bayansa to ya sada
zumuncinsa) Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Na daga cikin cikan daa a kiyaye
su daga dukkan abin da zai tawaye su ko ya warware su
Mai azumi ya fi tsananin son ya kiyaye ibadarsa da azuminsa daga abin da
zai keta alfarmansa ko ya bata shi, Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce : ( a ranar da dayanku yake azumi to kada yayi batsa, kada ya yi hayaniya, idan wani ya
zage shi ko ya nemi fada da shi, to yace
ni mutum ne, mai azumi ne ) Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Na daga cikin koyarwar magabata Allah ya musu rahama idan sun yi azumi
sai su zauna a masllaci sai su ce : Mu kiyaye azuminmu kar mu ci naman wani,
Ahmad Allah ya mishi rahama ya ce : Ya dace ga mai azumi da ya bibiyi azuminsa
ya bashi kulawa tun daga harshensa kada
ya yi musu, ya dace ga mai azumi idan ya yi azumi ya kiyaye jinsa da ganinsa da harshen sa da dukkan gabbansa , kada ya sanya ranar azumin sa
kamar ranar shan ruwan sa ,
Bayan haka ya ku musulmai :
To lallai biyayya bata kasancewa
cikakkiya kuma bata tsayawa akan
kwabrinta da kuma gun da ya dace sai
tare da kauna wanda za ta kai ma'abocinta zuwa ga ikilasi da gaskiya
wanda ke haifar da kekkewar bin sunna , aiki baya kasancewa na kusanci
har sai tushen shi da ma'ingizan shi ya
kasance imani ne ba al'ada ba da son rai , ba kuma neman suna ko yi don riya
ba kuma har sai ya kasance manufar
sa shi ne neman lada gun Allah da kuma
yardar sa idan imani ya hadu da neman
lada a aiki to nan ne karbuwa yake tabbatuwa da kuma gafara .
INA NEMAN TSARIN ALLAH DAGA SHAIDAN ABIN
JEFEWA
(Ku yi gaggawa zuwa ga gafara daga Ubangijin ku da aljanna da
fadinta sammai da kassai antanajeta ga masu tsoron Allah ).
Allah ya sa mini albarka ni da ku a cikin al'kur'ani mai girma
HUDUBA TA BIYU
Dukkan yabo da godiya sun tabbata
ga Allah bisa ga kyautatawan sa
godiya ta tabbata a gare shi bisa ga datarwansa da
kuma baiwarsa na shaida babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya ina mai girmama sha'anin sa , kuma na shaida Annabinmu Muhahammadu bawan
sa ne kuma Manzon sa ne tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabban shi da aminci
tabbatacce mai kari .
YA KU MUSULMAI :
Duniya za ta kare da jin dadin ta da kuma bakin cikin ta shekaru za su
kare da tsawon su da gajertan su kowa ya je ya hadu da Ubangijin su to a
wannan lokacin ne fa dukiya ba zai yi amfani ba ko 'ya'ya face wanda ya zo wa
Allah da zuciya lafiyayyiya , to ku fiskanci watan ku da tuba na
gaskiya , kuma ku kulla azama bisa ga
ribatanta da kuma raya lokutan ta da biyayya , rayuwan duniya ba wani abu ba ne
face wasu numfashi kididdigaggu da kuma
ajali iyakantacce , ku ribaci lokuta masu daraja ku sani
kuma ku yi fata kuma ku yi bushara
, hasararru su ne wadanda suka riski ramadana ba a gafarta musu ba ,
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Hancin shi ya dongwali kasa duk mutumin da ramadana ya
shiga har ya fita kafin a gafarta masa ) Tirmizi ne ya rawaito
(Duk wanda bai bar fadin karya
ba da kuma aiki da shi to ba ruwan Allah da ya bar abin cin sha da ruwan shan
sa ) Bukhari da Muslim suka rawaito .
Mafi girman abin da zai gyara zuciya shi ne ambaton Allah da kuma
lizimtar alkur'ani mai girma, da tsayuwan dare,
da zama da mutanen kwari .
Sannan ku sani ; lallai Allah ya umarce ku da salati da aminci ga
Annabin sa ………
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق