الجمعة، 26 يناير 2018

NEMAN ILIMI DA LADUBARSA

Hudubar Juma'a na Masallacin Annabi na shaikh Abdullah Dan Abdurrahman Al-Buaijan 9-5-1439 AH.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, wanda ya ilmantar da alkalami, ya sanar da mutum abin da bai sani ba,ina kyautata yabo a gare shi  bisa ni'imominsa,ina kuma  gode mishi bisa abin da ya mana na falaloli da karamci.
Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bai da abokin tarayya, na shaida Annabi Muhammad shine cikamakin Annabawansa da Manzanninsa, Allah ya zabe shi a kan sauran al'umu, ya turo shi don tausayawa ga talikai zuwa ga larabawa da ajamawa, ya isar da sako, ya sauke amana ya yi jahadi a tafarkin Allah hakkin jahadi har mutuwa ta zo mishi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,da iyalan shi da sahabbansa da duk wanda ya bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakayya.
Bayan haka, Lalle Alkur'ani shine zance mafi kyau, Addini a wurin Allah shine Musulunci,mafi alherin shiryarwa shine shiryarwar Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ( Ya ku mutane ! ku bautawa Allah Ubangijin ku da takawa ,  kuma ku ji tsoron wani yini, ranar da wani mahaifi baya sakawa dansa  da komai ko wani da ya sakawa mahaifin sa da komai  lallai wa'adin Allah gaskiya ne  , sabo da haka kada rayuwar duniya ta rude ku  kuma kada marudin nan ya rude ku  game da Allah ) .
    YA KU BAYIN ALLAH !
Hakika Allah ya zabi dan adam  domin ya sanya shi kalifa a doron kasa  ya bashi ilimi  wanda yana ta'alluki ne da aiki da kuma daukaka  , ya kuma bashi hankali  wanda ya ta'allaka ne da takalifi  Allah Madaukakin sarki  ya ce : (  kuma a lokacin da Ubangijinka ya ce ga mala'iku  lallai ne ni mai sanya wani halifa ne a cikin kasa:  suka ce,  ashe za ka sanya a cikin ta wanda zai yi barna  kuma ya zubar da jini  alhali kuwa mu muna yi maka tasbihi game da gode maka , kuma muna tsarkakewa  gare ka  ya ce : lallai ne ni  na san abin da ba ku sani ba )
      Sannan ya bayyana cewa ilimin nan yana ta'allake ne da falala da daukaka sai ya ce :
 ( Kuma ya sanar da Adam sunaye dukkan su sa'annan kuma ya gitta su a kan mala'iku sa'annan ya ce :  to ku gaya mini sunayen wadannan idan kun kasance masu gaskiya)
 suka ce  tsarki ya tabbata a gare ka ! ba bu sani a gare mu face abin da ka sanar da mu , lallai ne kai, kai ne masani mai hikima .  Ya ce : ya Adam ! ka gaya musu sunayen su  : '' to alokacin da ya gaya musu sunayen su , (Allah) ya ce :  ashe ban ce muku  ba lallai ni ina sane da gaibin sammai da kasa ( kuma ina sane da abin da kuke bayyanawa da abin da kuka kasance kuna aikatawa)
        Sai Allah ya fifita mutum bisa da yawa daga cikin halittun sa  a dalilin ni'ima ta ilimi da hankali ,  ya kuma dora taklifi a kan haka .
        YA JAMA'AR MUSULMI!
Dalibai maza da mata za su fiskanci sabon fasali na karatu a wannan  ranaku,  to madalla da wanda ya dage ya yi kokari  ya ja damara cikin aikin alheri to zai samu sa'ada , to lallai  ilimi shi ne ginshikin addini  kuma da shi ne mutum zai san addinin shi  kuma da shi ne  mutum zai iya sanin yadda zai yiwa Ubangijin shi da'a ,  kuma farkon  umarnin da mala'ika jibrilu ya zo da shi  daga wurin Allah zuwa  ga Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  shi ne ;  umarni da neman ilimi  , kuma farkon ayan da ta sauka a Alkur'ani shi ne;  ( yi karatu).
    An karbo daga Aisha  , Allah ya kara yarda a gare ta  ta ce : (  Farkon abin da   aka   fara wahayi wa Manzon Allah shi ne mafarki  na gaskiya  a cikin bacci , ya kasance baya ganin wani abu a cikin bacci  face abin ya bayyana kamar hasken  safiya  sannan sai aka kwadaitar a gare shi yin khalwa , ya kasance yakan tafi kogon hira ya kebanta yana ta bauta a ciki na wasu dararraki  masu adadi  kafin ya dawo zuwa ga iyalan shi ya sake samun guzuri  , har zuwa lokacin da gaskiya ta  zo mishi , mala'ika Jibrilu ya sauka a gare shi a halin yana kogon hira sai mala'ika ya zo mishi sai ya ce :  yi karatu , ya ce : ( ni ba mai karatu ba ne ) sai ya ce : sai ya kama ni ya matse ni  har na ji wahala sannan ya  sake ni  sai ya ce yi karatu :  sai na ce: ( ni ba mai karatu ba ne )  sai ya sake kama ni ya matse ni a karo na biyu har na ji ba dadi sannan ya sake ni , sai ya ce yi karatu : sai na ce : ( ni ba mai karatu ba ne) sai ya kama ni ya matse ni a karo na uku har na ji jiki , sannan ya sake ni sai ya ce : yi karatu da sunan Ubangijin ka  wanda ya yi halitta, ya halitta mutum daga  gudan jini,  ka yi karatu  kuma Ubangijinka shi ne mafi karamci ,  wanda ya sanar da (mutum ) game da alkalami  ya sanar da mutum abin da bai sani ba ).
       Ya ku bayin Allah hakika  Alkur'ani ya kwadaitar bisa ga neman ilimi, Allah bai umarci  Annabin shi ba da ya roke shi karin wani abu ba sai  ilimi , ( kuma ka ce ya Ubangiji ka kara min ilimi )
       Kuma ya koda matsayi irin na malamai  sai ya ce :  ( Malamai kawai ke tsoron Allah a cikin bayin sa).
        Kuma Allah ya hada su da kansa da mala'ikunsa cikin shaidawa  da  kadaitakarsa,  Allah madaukakin sarki ya ce : ( Allah ya shaida cewa : Lalle ne babu abin bautawa face  shi , kuma mala'iku  da ma'abuta ilmi sun shaida ,  Yana tsaye  da adalci , babu abin bautawa  face shi , mabuwayi , mai hikima ).
Kuma Allah ya yi nuni bisa kimansu sai ya ce: ( Ka  ce  ashe , wadanda suka sani , suna daidaita  da wadanda ba su sani ba ?).       
Kuma ya yi umarni da komawa gare su yace :(To ku tambayi ma'abota ilimi in kun kasance baku sani ba).
Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya kwadaitar game da shi ya bayyana cewa alama ne na alheri (Wanda Allah ya nufe shi da  alheri zai fahimtar da shi addini).
  Yace : (Wanda ya kama hanya ta neman ilimi Allah zai saukake mishi hanya ta shiga Aljanna)
To ku bawa ilimi wani kaso na daga lokutanku,kuma ku kwadaitar da yaranku bisa kokari da jajarcewa wajen nemansa.domin shi ne hanya mafi dacewa ta tarbiya, kuma mafi tabbatuwar  yakini  wurin tsarkake zuciya.kuma ya fi kawo amintuwa daga fitintinu, kuma yake kawo tabbatuwa  da tsayuwa yayin  jarabawa, yafi kawo hakuri yayin musiba,kuma yana cikin kyawawa mafi daraja da aikin lada mafi girma na neman kusanci ga Allah, da samun daraja mafi daukaka.
Ya ku Musulmai!
Duk wanda Allah ya nufe shi da alheri zai sanar da shi addini, mafi alheri cikinku a lokacin jahiliyya sune mafi alherinku a lokacin musulunci in sun yi ilimi,kuma malamai sune magada Annabawa.
Shagaltuwa da ilimi na cikin Bakiyatussalihat da sadaka mai gudana bayan mutuwa,  da  samun lada mai dorewa bayan wafati,
An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : Idan mutum ya rasu ayyukansa zasu katse sai guda uku: Sadaka mai gudana, ko ilimi da ake amfana da shi, ko da na kwarai da yake mishi adu'a)
Sai dai fa ilimi na bukatar hakuri da lokaci da kokari da juriya, da bada kai,  gwargwadon wahalar  da aka sha gwargwadon yadda zaa  cinma manufa,da biyan bukata.
Neman ilimi na bukatar ikhlasi a niyya da azama ta gaskiya, da tsarkake zuciya,  da tsiraituwa daga duk  abin da zai kawo cikas ko kashe jiki,  to lalle duk wanda ya riki filo aboki ba shi ba riskan matsayi (Yaro bata dare ka yi suna).
(kuma Ba ya kasancewa ga muminai su fita zuwa yaki gaba daya. Saboda haka don mene ne wata jama'a daga kowane bangare daga gare su ba ta fita (zuwa neman ilimi ba) domin su nemi ilimi ga fahimtar addini kuma domin su yi gargadi ga mutanensu idan sun koma zuwa gare su, tsammaninsu, suna yin sauna? ).
Mai neman ilimi na bukatar laduba na shari'a a cikin nemansa  har ya zama abin koyi abin buga misali mai kyau, kuma ya zama ahali na karbar wannan sako, kuma cikin adilai na wannan Al'uma.
 Ya inganta daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, (wadanda zasu karbi wannan ilimi cikin mamaya sune adilan cikinsu, suna kore karkatarwar masu ketare iyaka da da'awar mabarnata da tawilin jahilai).
Bayan haka ya ku bayin Allah! dukkan ilmuka masu amfani an shar'anta nemansu, sawa'un tushensu Alkur'ani ne da sunna: kamar ilimin addini, na akida da tafsiri da hadisi da fikihu da wasunsu, ko tushensu ya samu asali ne daga sanin yau da kullum (Gogewa da gwaji) da dubi ga duniya da rayuwa kamar ilimin likitanci ko ilimin da ke nazari kan haske da sauti ko (kimiyya da fasaha), da waninsu.
, to duk wanda ya kyautata niyyarsa wajen nemansu ina fatan fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : (Wanda ya kama hanya ta neman ilimi Allah zai saukake mishi hanya ta shiga Aljanna) ya game da shi.
Ina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan abin jefewa
Shine wanda ya aika a cikin mabiya  al'adu wani Manzo daga gare  su yana karanta ayoyinsa a gare su kuma yana tsarkake su, kuma yana sanar da su littafin da hikimar sa ko da yake sun  kasance daga gabaninsa suna cikin bata bayyananna . Da wadansu mutane daga  gare su, basu ida riskuwa da su ba.alhali kuwa shine Mabuwayi Maihikima.
 
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, godiyar da ta dace da daukakarsa, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake bai da abokin tarayya, cikin girmansa da kamalarsa, na shaida Annabi Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,da iyalan shi da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa, har zuwa ranar sakayya.
Ya ku bayin Allah!
Lalle ilimi na da jakunkuna da ke adana shi, da masu tsaro da ke bada kariya a gare shi, da mazaje da ke daukanshi da shehunai da ke mishi hidima, ta hanyarsu ne yake tafiya ya yadu a duniya da kokarinsu.
Ya ku al'uma!
Lalle malami yana wakiltar Annabawa ne a ayyukansu na tarbiyantarwa da ilmantarwa, ya ke tashi da hidima don samar da al'uma masu tasowa nan gaba,kuma ya dasawa yara masu tasowa na wannan al'uma iri na kyakkyawan rayuwa da walwala na duniya da lahira,to lalle ya dace da a girmama shi a kimanta shi kuma ya dace da a mutunta shi, haka kuma a dauke kai game da kananan laifukansu a yafe masa kurakuransa.
Ya ku Malamai da masu bada tarbiya maza da mata.
Ku kasance abin koyi mai kyau ku siffantu da ilimi da ladubansa, to ku manya ne a idon dalibanku, daliban na sha'awan kwaikwayon ku da koyi da ku, to ku zama abin koyi nagari don Allah ku zame abin koyi nakwarai, idan kun bayyana musu kyan gaskiya to ku kasance cikin masu gaskiya, idan kun umarce su da hakuri to ku  zama cikin masu hakuri,
Fara da kanka ka hanu daga zalunci irin na rai   ***
idan ka hanu to kai ne mai hikima
To a nan ne zaa karbi abin da ka ke fadi a yi koyi * **
da ilimi daga gare ka, ilmantarwan ya yi amfani
Kar ka yi hani ga wani hali kuma ka aikata irin shi***
Babban laifi ne a gare ka in ka yi haka.
Ya ku Malamai!
Nauyin da ke kanku na da girma, amanar da ke wuyanku babba ce. 'ya'yan wannan al'uma amana ne a kan ku, kuma an bada ajiyar wannan al'uma a hannunku, abin da ake hanga na gabanta ya taallaka ne da nauyin da ke kanku. Ku ji tsoron Allah game da kiwon da aka baku, ku ji tsoron Allah game da kiwon da aka baku! (Dukkan ku masu kiwo ne kuma abin tambaya ne bisa kiwon da aka baku,).
To in kun kyautata to kun kyautatawa kanku ne, kuma haka ake zata muku,to kuwa kuna da falala mai girma a gurin Allah, in kun muzguna to kun muzgunawa kanku da al'umarku ne.
Ya ku dalibai zababbu 'ya'ya ga malamai masu biyayya!
Ku kasa kunnuwanku  ku saurara, wannan zance ne da ya kebance ku, daga mai tausaya muku kuma masoyinku:
Lalle girmama malami da kimanta shi ladabi ne na sharia kuma halaye ne na wajibi, kuma nasara ne na ilimi da na tarbiyya. A tafiyar Annabin Allah Musa da khidr Amincin Allah ya tabbata a gare su a kwai abin lura da wa'azi  da tunatarwa,
(yace shin ba zan bi ka ba don ka sanar da ni daga abin da aka sanar da kai na shiriya?). sai malamin ya maida mishi amsa da : (Lalle ne kai ba za ka iya yin hakuri tare da ni ba, kuma ya ya za ka yi hakuri da abin da baka kewaye sani da shi ba ga jarrabawa ).sai musa ya zanta mishi cewa ya san hakkin malami da wahala irin na neman ilimi,  (yace : zaka same ni in Allah ya so mai hakuri, kuma ba zan saba maka ba ga wani umarni).
Lalle falalar malami na da girma, kokarinsa da kyautarsa hakki ne da ba zaa saka masa ba sai da alheri, to na hore ku da ku kiyaye kar ku musu rashin ladabi, domin alama ce ta lalacewar tarbiya, da fandarewan dabiu, da hali mara fasali,  ba mai yarda da shi sai dan iska.
Kuna da abin koyi  mai kyau daga magabata, ga Rabi'u almajirin imamusshafi'I Allah ya jikansu da rahama, yana cewa : Ban iya bushewan ido ba na sha ruwa a gaban Imamusshafi'i yana kallo na sabo da kwarjininsa.
Ku girmama malamanku, kowa ku san matsayin shi, ku bawa kowani mai hakki hakkinsa, Allah ya datar da ku, ya azurta ku da ilimi mai amfani, da aiki na gari.
Ya Allah ka daukaka musulunci da musulmai.             


            

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق