HUDUBAR
JUMA'A NA MASALLACIN ANNABI TSIRA
DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI
NA SHAIKH SALAH AL-BUDAIR NA 25-4-1439 H
HUDUBAR FARKO
Yaku musulmai babu dauwama a
duniya da za a yi fata ko
wanzuwa da za a bida
mutane ba wani abu ba ne face mai tafiya da
kuma dan mai tafiya ***zamani kuma ba wani abu ba ne sai shudewan yini da dare.
Mutuwa kuma ba wani abu ba ne sai abu ne mai sauka kuma makusanci *** rayi kuma ba
wani abu ba ne fa ce abin da ake nesa da haihuwar sa kuma mutuwa
ke kusantowa ga zukata sai ta fita.
Kaito ya mutuwa ba ta da dauke
kafa idan muddar da aka diba ma rayi
ta kai makurar sa*** sa'oi za su mika ka ga wani sashi na daga
lokaci zuwa wani lokaci wanda
babu wani lokaci bayan shi .
Abin mamaki ga saurin ranaku cikin tafiyar su za ta zo ta wuce mu kuma ta zo ta tafi da mu, a ko wani rana akwai buri wanda yana yin nesa, manufansa daga lokaci da ya kusanto .
Ina wanda suka
kasance kafin mu ina su ke *** Ina mutanen da suka
kasance kyawawa kuma masu yin kawa .
Lalle zamani ya biyo ta
kansu ya
karar da wani adadi daga cikin su ***Sa'annan muma yana zuwa kanmu .
Sau da yawa muna ganin mutum mamaci
bayan da ya kasance a raye*** ba
da jimawa ba za a gane mana abin da muka ganewa wasu .
Me ya same mu ne muke amin ta da mutuwa*** kai ka ce ba za mu ganta ta
zo zuwa gare mu ba .
Ya gafalalle ya wanda
ya sha'afa ko kun manta cewa mu 'yan
adam ne kaddara na kewaye da mu kuma mu
dinnan muna cikin tafiya ne, wanda za mu
tafi zuwa kaburbura , mutuwa za ta hada da mu , tashin alkiyama zai
tattaro da mu , to har zuwa yaushe ne za mu wa'azantu mu
daina , to har sai zuwa yaushe ne kunnen ka zai kiyaye fadakarwan mai
fadakarwa , ga
zuciyar ka kuma baya tausasa sabo
da mai zargi .
Ase lokaci bai yi ba da
zuciya za ta ji tsoro *** To kuma ina
kokarin ? a cikin gyangyadi muke ne ko kuma zuciyar ta sandare? To ka farka
dan uwa na kuma ka kiyaye kar ka kwanta .
Kwanciya za ka yi ya
rudadde bayan ga wuta ana kara
kunna ta *** zafin ta ba a kahse shi
haka nan kuma gaushinta baya mutuwa.
Annabi ya kasance amma bai
dauwama ba ga al'umar sa *** Da Allah ya dauwamar da wani halitta kafin
shi , to , da shi ya dauwama .
Mutuwa acikin mu tana da wasu
masu wanda ba sa kuskurewa *** wan da kifiya ta tsere mishi a yau to fa
gobe ba
zata tsere mishi ba .
Allah madaukakin sarki ya ce : ( Kuma ba mu sanya dawwama ga wani mutum ba a gabanin ka . Shin to idan ka mutu to su ne
madauwama ? , ko wani rai mai dandanan mutuwa ne kuma muna
jarraba ku da sharri da alheri domin fitina , kuma zuwa gare mu ake mayar da ku ) AYA 34-35 Al-Anbiya
Ina wadanda muka yi mu'amala
da su na tsawon lokaci muka saba da su,
ina wadanda mu ka karkata zuwa gare su da kauna da tausayawa ,? Sau da yawa mun rintse idanuwan mu( mun yi
kuka ) sabo da masoyanmu, mutum nawa ne masu izza mu ka binne
muka tafi kuma muka bar su sau
da yawa muna binne makusanci mu kwantar da shi
a cikin kabari ba za mu tsaya ba ? shin ko mutuwa na tausayawa mara lafiya daga
cikin mu sabo da raunin halin shi? Shin
ta bar wani mai nema (dan kasuwa)
sabo da 'ya'yan shi? Shin ta
saurarawa ma'aboci iyalai sabo da
iyalan shi ? .
Ya bawan Allah a ko wani rana akwai abun lura bayan abun
lura *** Acikin mutuwa kuma akwai abu mai hani
da ka kasance cikin wan da
suke hanuwa .
Tohar zuwa yaushe? To har zuwa yaushe ? * wai kai yaushe ne za ka ji
gargadi kuma ka ji tsoro.
Zuwa
yaushe ne za ka dena cigaba da dogewa da ruduwa da gafala ***
Sau da yawa haka ne
bacci to yaushe ne ranar farkawa.
Rayuwa ta saraya a wani
lokaci da za ka iya sayan cikin kasa da
sama *** wani irin bata abu mai karewa
za ka saye shi cikin wauta
Ka
saida fushi da yarda *** sannan ka saida aljanna
kuma da wuta .
Yanzu kai masoyi ne ga rayin ka ko kuma makiyi ne gare shi *** to lalle
kai kana jefa ta ga dukkan musibu .
Hakika ka saida ta cikin araha
–ina mai ma bakin ciki*** wanda ta kasance
ba abu ne da yake na tabbas ba a gare ta.
A yau kana aikata abin da ka
keso kuma da abin da ka ke sha'awa *** a gobe kuma za ka mutu kuma a dauke alkaluma .
Mai laifi na zama fasiki ta hanyar aikata babban laifi *** haka nan kuma
idan ya doge a kan kananan laifuka.
Mutum ba zai fita daga imani ba*** sabo da ya aikata manyan laifuka na sabo .
Kuma
ya wajaba a gare shi da ya tuba*** daga
dukkan abin da zai janyo mishi zunubai .
Allah madaukakin sarki ya ce : (
Kuma ku tuba zuwa ga Allah guda daya
, ya ku muminai ko za ku samu babban rabo).
(Lalle Allah na shimfida
hanun shi da da dare don masu laifin wuni su tuba , kuma yana shimfida hanun shi da wuni don masu laifin dare su tuba har rana ta bulla daga
yammacinta ).
Ina neman gafarar Allah
daga zunubi na da barna ta *** lalle ni ko da na kasance ana boye min laifuka
na to fa mai yawan laifi ne
Ba wani sabo da raina za ta janyo
mi ni*** face na samu kai na a tsakanin
haske da duhu .
Hakika ina mamaki bisa gafala
ta da kuma shammata ta*** a halin mutuwa zai kira ni gobe na amsa
Hakika na yi mamaki na tsawon
aminta daga mutuwa ta *** kuma gata zuwa gare ni za ta sadado ta fisge ni.
Na sabawa Allah a wuni na da
dare na *** cikin sabo na saki jiki bone
ya tabbata a gare ni idan har aka
haramta mi n Aljanna Adin .
Kuma bone a gare ni muddin na
shiga wuta kuma bone ya tabbata a gare ni.
Allah madaukakin sarki ya
ce : ( Ka ce ya bayi na wadan da suka
yi barna a kan rayukan su ! kada ku
yanke kauna daga rahamar Allah , lalle Allah na gafar ta zunubai gaba daya
lalle shi mai gafara ne mai jin kai )
HUDUBA NA BIYU
Ya ku musulmai Addini shi ne uwar kudin ku kuma shi ne daukakan hali da makoma.
duk wata karaya addini na gyara ta*** amma karayan
addini ba abin da zai gyara ta.
Dukkan
wasu musibu idan sun bayyana suna da
sauki ko sun ko sun girmama***
sabanin musiban da zai sami mutum a addinin shi.
Ga ruwan fitintinu na ambaliya
yana dukan juna, ga kasa cike da hanyoyi na macizai da kunamu da abubuwa
masu cutarwa a cikin duwatsu na sanda.
Duniya cike take da fitina da
bala'i to ku shirya hakuri don bala'i,
An karbo daga Huzaifa Allah kara yarda a gare shi yace : Ya Manzon
Allah lalle mun kasance muna cikin sharri sai Allah ya tafiyar da shi ya kawo
mana alheri ta hanunka, to shin bayan wannan alherin ko akwai wani sharri? Sai
ya ce : E,sai ya ce to menene shi? Yace wasu fitina kamar yankin duhun dare,
sashi na bin sashe, zasu zo a rikice kamar fiskar shanu,baku fayyace wannan
daga wancan.) Ahmad ne ya rawaito.
(Allah kara yarda a gare shi yace : fitina ba ta cutar da kai muddin ka
san addininka lallai ita fitina idan gaskiya da bata suka rikirkice maka ka
kasa sanin wadda zaka bi to wannan ita
ce fitina ) Ibn Abi Shaiba ne ya fitar da shi
Allah ya kara yarda a gare shi ya ce '' Idan
dayan ku ya so ya san cewa fitina ta same
shi ko bata same shi ba to ya yi dubi :
to in ya kasance abin da ya ke ganin shi a da haram ya koma yanan ganin
shi halal , to, fitina ta same shi, ko
kuma abin da a da yake ganin shi halal ya koma yana ganin shi haram to, nan ma
fitina ta same shi '' Hakim ne ya fito da shi
Ma'ana ra'ayin mutum ya
sanja zuwa son rai da sha'awa .
Malik Dan Anas yana cewa: "
duk lokacin da wani mutum ya zo mana
mafi jayayya yana so mu maida abin da Jibrilu ya zo mana da shi zuwa ga manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi"
.
Yanzu zan zauna a bayan kasusuwa na sun girgiza *** Ahalin mutuwa ta kasance ta
fi kusa zuwa gare ni.
Ina jayayya ga dukkan wani mai
cin karo mai yawan musu *** na sanya
addinin shi ya zamana abin da zai taba mini addini na .
Na bar abin da na sani sabo da ra'ayin wani na
a hali kuma
ilimi na yakini
ba daidai yake da ra'ayin wani
ba.
Ni ban zame mai shiga cikin husuma ba ***
wacce za ta tunkude daga hagu zuwa dama.
Kuma hakika an sunnan ta mana
wasu sunnoni tsayayyu*** Wanda zai sanya lahani ga dukkan wani kofa
ko kuma wani
lokaci.
Gaskiya ta kasance
bata boyuwa *** tana bayyana a goshi
kamar yanda safiya
ke bayyana .
Tafarkin jahamu bai kasance ya zamana
madadi a gare mu ba*** bisa tafarkin
Dan Aminata amintacce .
An karbo daga Abdullahi dan
Dailami ya ce : ( Lallai farkon
tafiyan addini shi ne barin sunna , addini zai tafi sunna bayan sunna ,
kamar yan da igiya ke tafiya gaba bayan
gaba .
Abubakar Siddik Allah ya yarda
da shi ya ce : '' Ban kasance mai barin wani abu da Annabi ya kasance yana
aikatawa ba face sai na yi aiki da
shi , kuma lallai ni ina tsoron na bar wani
abu daga umarnin sa ya zama na karkace ''.
Ku tabbata ya ku bayin Allah akan
littafi da sunna da shari'a
da addini da kuma dabi'u da
halaye kyawawa ku kiyaye masu
batarwa, masu tada fitina , ku kiyaye su kar su fitine ku daga wani sashi na daga abin da Allah ya
saukar a gare ka .
Ya Allah muna rokon ka
tabbatuwa akan al'amari da kuma azama bisa shiriya.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق