ترجمة خطبة المسجد النبوي
الخطيب الشيخ عبد الباري الثبيتي
المترجم : أمين سعد
اللغة : الهوسا
Hudubar
Masallacin Annabi Na shaikh Abdul bari Bin Awad
Assubaiti
19/4/1442AH
4/12/2020Ac
Hudubar
Farko
Da sunan
Allah da godiya a gare shi nake farawa, tsira da amincin Allah su tabbata ga
Manzon Allah, Shiyarwar Manzon Allah shi ne mabubbuga na alheri, kuma da haske
ne mai fantsama da kuma hasken rayuwa : yana tare da kai har a lokacin zamewa
da kuskurewa, Buhari ya rawaito daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi
daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : lalle wani bawa ya aikata zunubi ko kuma yace ya yi wani
zunubi,sai ya ce : ya Ubangiji na yi laifi ko kuma na aikata laifi, ko na
aikata wani to ka gafarta mini, sai Ubangijinsa ya ce : ase bawa na ya san yana
da Ubangiji yana gafarta zunubai kuma ya yi damka sabo da shi? na gafarta wa
bawa na, sannan ya zauna na wani lokaci da Allah ya so sai ya sake aikata
zunubi ko ya yi laifi sai ya ce ya Ubangiji na yi zunubi ko na aikata wani
laifi to ka gafarta shi, sai ya ce : bawa na ya san yana da Ubangiji yana
gafarta zunubi kuma yana damka da shi? na gafartawa bawa na, sai ya zauna na
wani lokaci da Allah ya so sai ya sake
aikata zunubi ko ya yi laifi sai ya ce ya Ubangiji na yi zunubi ko na aikata
wani laifi to ka gafarta shi a gare ni. Sai yace :Bawa na ya san yana da
Ubangiji da yana gafarta zunubi kuma yana damka da shi? Na gafartawa bawa na
har sau uku, to ya aikata abin da ya so,)
Wannan hadisi
yana hakaito halin bawa game da zunubi da tsarin musulunci wurin gyara halin
masu laifi- dukkan mu masu laifi ne – yana bude kofar fatan alheri da kofa ta
alhini kamar yadda ake surantawa kowani mai laifi rahamar Allah da ta yalwaci
dukkan komai da kyautarSa ga masoyanSa, da tausayinSa ga bayinSa.
Wannan hadisi
na farawa ne da fadinsa (Lalle bawa ya yi
zunubi) musulunci
na lura da yanayin rayi irin na mutum, wacce ta ke aukawa cikin zunubai, kuma
kafa ta zame da ita bisa mantuwa ko wata shubuha ko sha'awa, a dalilin fizga
irin na shaidan da batarwarsa: An karbo daga Abu
Said daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, lalle iblis ya
ce da Ubangijinsa Mabuwayi da Daukaka, na rantse da buwayarka da daukakarka
bazan gushe ba ina batar da bani adama muddin rai na gangan jikinsu, sai UbangijinSa
Mabuwayi da daukaka ya ce :Na rantse da buwaya ta da Daukaka ta ba zan gushe ba
ina gafarta musu muddin suka nemi gafara ta.). Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce : na rantse da wanda raina ke hanun shi, ba
don kuna laifi ba da Allah ya tafiyar da ku sai ya zo da wasu mutane suna laifi
kuma suna neman gafara sai ya gafarta musu.)
(lalle wani bawa ya aikata zunubi sai yace ya Ubangiji na
yi laifi) mutum ya yi ikirari da zunubinsa wannan wani jarumta ne,
da nuna ya san lalle ya yi kuskure wannan kankan da kai ne da rusunawa, wannan
shine matakin farko na gyaran zuciya da ladabtar da ita, Allah Madaukakin Sarki
ya ce : (wasu sun yi furuci da laifukansu sun
cakuda ayyuka na kwarai da wani mummuna, ana fatan Allah ya yafe musu lalle
Allah Mai gafara ne Mai jinkai)
A cikin fadin
Manzon Allah ga Aisha Allah ya kara yarda a gare ta (Lalle idan bawa ya yi furuci da zunubansa ya kuma tuba sai Allah ya
karbi tubansa)
Musulmi na
furuci da zunubansa a duniya ya tabbatar da su a lahira, to idan ya aikata haka
sai a gafarta masa zunubansa da izinin Ubangijinsa, An karbo daga Abdullahi dan
Umar Allah ya kara yarda a gare su, yace na ji Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi yace : (Lalle Allah
na kusanto da mumini sai ya dora kariyarSa ya suturce shi. Shin ka san zunubi
kaza? Shin ka san zunubi kaza? Sai ya
ce : e ya Ubangiji, har zuwa lokacin da ya tabbatar da zunubansa ya fahimci
cewa ya halaka, sai Allah ya ce na suturtata a gare ka a duniya to a yau na
yafe ma ita, sai a bashi littafin shi na kyawawan ayyukansa).
furuci da zunubai
yana da lokacinsa idan ya wuce to sai ukubar zunubai ta sauka gare shi, Allah Madaukakin
Sarki ya ce game da 'yan wuta wadanda
basu yi furuci da gajartawansu ba sai bayan sun dandani azabar wuta: (sai suka yi furuci da zunubansu to nesa ga 'yan wutar sa'ira).
Musulunci
ya nusar da musulmi zuwa ga ikirari da furuci da zunubai sai dai ya yi gargadi
game da tonon asiri da yada kuskurensa bayan Allah ya suturce shi, Manzon Allah
tsira da amincin Allah tsira da amincin Allah tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi yace : (Dukkan al'uma ta na samun
waraka sai masu bayyana sabo, na daga cikin bayyana sabo mutum ya yi wani aiki
da dare bayan Allah ya suturta shi, sai ya ce ya wane na aikata kaza da kaza a
halin ya kwanaUbangijinsa na suturta shi, sai ya wayi gari yana yaye suturawar Allah
a gare shi.)
Na daga
cikin falalan Allah a gare mu suturtawan
aibi da kiyaye anbato tsakanin halittu. Wani mutum yace ga daya daga cikin magabata : ya ya ka wayi gari? Sai yace : tsakanin
ni'imomi biyu, ban sani ba wanne ta fi wani zunubai da Allah Mabuwayi da
Daukaka ya suturta ta ba wani da zai iya aiba ta ni da su, da kauna da Allah ya
jefa cikin zukatan bayi guri na ba zai iya riska ba, Bawa yana cewa na yi laifi
ga raina na disan kunya sabo da ya saka da kyauta mai kyau bisa sabo mummuna, zuciyarsa na
fito da radadi sabo da nauyin zunubai da tsananin tsoron Allah, wannan
yanayi da
Wannan wani Abu ne Mai ratsa jiki da
yanayi na ruhi da ke rayye wanda hakan na karfafan imani kuma ya kan janyo rahamar Ubangiji Mai rahama.
Komowa zuwa ga Allah bayan zunubi wata
kyauta ce daga Allah kuma raya makunnin
shiriya ne bayan duhun sabo, Allah Madaukakin Sarki yace:
: ( Lallai
wadanda suka ji tsoron Allah Idan wani yanki NA shaidan ya shafe su sai su tuna
sai ga shi suna gani irin na basira).
Sau dayawa wani zunubin kan haifar da
rayayyen zuciya ga ma'abocin shi da kankan da kai da rusunawa da kuma fiskantar
Allah da gaggawa wurin aikin alheri ,
sau dayawa sabo kan haifar da tuba ga
ma'abocinsa , tuba irin wanda ke daga
matsayinsa ya gyara halayensa , kuma ya
kara imanin sa , kuma ya gyara rayuwarsa .
Ya zo a sunna ingantacce cewa wani sahabi ya aikata wani
zunubi mai girma sannan ya tuba bayansa , tuban da
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce game da
ita (Hakika ya yi
tuban da da za a kasa ta tsakanin al'uma
da ta ishe su ).
Ya zo a hadisi (Ya Ubangiji na aikata zunubi ka gafarta mini ), (Wanene ke gafarta zunubi
face Allah ):- shi ne wanda tsarki ya tabbata a gare shi ya
ke cewa (Ka labartawa bayina lallai ni dinnan mai
gafara ne mai jin kai ) kuma
mai cewa wanda ya aikata wani mummuna ko ya zalunci
kansa to, zai samu Allah mai gafara kuma mai rahama) . Ya zo a
hadisil kudusi .
(Ya ku bayi
na lallai ku kun kasance kuna kusakurai
a cikin dare da yini , kuma ni ina
gafarta zunubai gaba daya to ku nemi
gafara na , sai in gafarta mu ku). Ya zo a cikin hadisi (Ya Ubangiji na
na yi zunubi to ka gafarta mini ). To istigfari tarihi ne na
Annabawa, kuma abin nanatawa ne a bakin salihai, kuma shi dinnan magani ne na cututtuka ; yana gyaran
rayi , ya tsarkake ta kuma ya
shigar da kyawawa , shi ne hasken da yake
zuwa ga zunubai sai ya halaka ta ya zo
ga zukata marasa lafiya sai ya ingantata, ya zo ga rayuka masu nauyi sakamakon
zunubai sai ya mikar da shi, ya sanya rayuwa
ta zama ado, rayi kuma ya zamana mai
sheki Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Kuma ku nemi
gafarar Ubangijin ku kuma ku tuba zuwa gare shi , zai jiyar da ku dadi, jin dadi mai kyau zuwa wani lokaci abin ambato,
kuma ya bawa ko wani ma'aboci falala falalarsa ) Manzon Allah tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:- (Lallai
ni ina neman gafara zuwa ga Allah kuma in tuba zuwa gare shi sama da sau saba'in a wuni ) ya zo a hadisi
sai Ubangijin shi ya ce :- ( Ase bawa na
ya san yana da Ubangiji mai gafarta zunubai , ? kuma yana damka da shi ? to na
gafartawa bawana ) (na gafartawa bawa na) :- Kalmace da take kamar wani magani na yanke wurin waraka bisa ga zukata masu tsoro , da kwarara
natsuwa a cikin zukata masu tsoro; kalma
ce da Allah ke tabbatar da tsarkin jiki
da ita, da kawar zuciya
da walwala a rayuwa , kuma ta goge zunubanka ta yaye zuciya kuma ta saukake alhaki wanda bayanka ke dauke da shi .
(Na
gafartawa bawana ).Fa'ida ne wanda ya san Ubangijin shi zai fiskance shi, ya ji tsoron mahaliccin shi kuma zubowan
hawaye kamar tsani ne zuwa gare shi .
(Na gafartawa bawa na ) Kalma ce da ke wasa himma na muminai kuma ta karfafi
azamar masu zunubai , ta hanyar gaggawa zuwa ga neman gafara da ribatar dama ,
da neman mafaka a wurin Allah , to zunubbai , suna da mai rahama kuma mai jin
kai zai goge ta , da Allah mai tausayi da zai gafarta musu .
Wanda ya gafala daga neman gafara bayan
aikata sabo , ko kuma bai haura don nemanta ba to lallai ya wajaba ya tada idanuwan sa daga
gyangyadin da yake yi kuma ya rinka
bibiyan imaninsa , wannan alamace na
mutuwar jin bawa na aikata sabo, Allah Madaukakin sarki ya ce :- (kar ku kasance kamar wadanda
suka manta da Allah sai ya mantar da su kawunansu, wadannan sune
fasika).
Mafi girman zunubai shine bawa ya
manta cewa shi yana cikin mantuwa wannan
shi ne tarun bala'i , kuma wannan ita ce asara
mai mummunan karshe Allah ya yi gargadi ga wanda ya zalunci kansa
ya bijirewa istigfari, sai yace : ( Ase ba za su tuba
zuwa ga Allah bakuma su nemi gafararSa lalle Allah Mai gafara ne kuma Mai
jinkai)
(Allah
yace :Na gafartawa bawana sau uku ya
aikata abin da ya so).fadinSa (ya aikata abin da ya so) ba ya nufin umarni ne da ya aikata sabo
ba, sai dai ana nufin tun da ya kasance haka a ko yaushe ya yi zunubi zai tuba
to zunubin ba zai cutar da shi ba bayan tuba, sabo da tuba na goge abin da ke kafinta,
sai dai mutum ya kiyaye daga aikata sabo, sabo da yana da yakini bisa ga sabo
amma bai da yakini bisa ga gafara, kuma
zain iya rasa dacen tuba.
Kiyayewa daga zunubai wajibi ne ,; sau dayawa zunubi kan
lalata zuciya ya fusata Ubangiji , kuma
ya bakanta hanya , kuma yakan sa saukar da ukuba a doron kasa, a debe albarkan ,
a kazanta fidira a rarraba dangi .
Yin
ko inkula da sabo dabi'a ne abin zargi, wofantar da halin mai zunubi abu ne mai yanke kauna
da cire tsammani , Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Ka
ce ya ku bayi na wanda suka yi barna bisa kawunan su kar ku
yanke kauna daga rahamar Allah , lallai Allah yana gafarta zunubai gaba daya ,
lallai shi mai gafara ne mai jin kai).
HUDUBA TA BIYU
Na daga cikin hakurin Allah jinkirtawa mai laifi har ya tuba , idan ya
koma kuma ya tuba Allah sai ya karbi tubansa , Allah baya gajiya sai dai ku ku
gaji ; ya zo a hadisi , cewa:- Shugaban istigfari shi ne ; bawa ya ce :- (Ya Allah kai ne Ubangiji na ba abin bautawa da gaskiya
sai kai , ka halicce ni kuma ni bawanka ne , kuma ina bisa alkawarinka mai
karfi da alkawarinka , iya- iyawa na, ina neman tsarinka bisa ga sharrin abin
da na aikata , ina komowa a gare ka da ni'imominKa da ke gare ni , kuma ina
komowa gare ka da zunubi na –wato yana furuci da shi to, ka gafarta min lallai
ba mai gafarta zunubai sai kai .
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق