الجمعة، 11 ديسمبر 2020

CUTAR DA MUSULMI

 

ترجمة

خطبة المسجد النبوي للشيخ حسين آل الشيخ

اللغة : الهوسا

المترجم : أمين سعد

التاريخ : 26/4/1442هـ

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI NA SHAIKH HUSAIN AL-ASSHAIKH 26-4-1442AH 11-12-2021AD

 

HUDUBAR FARKO

 

Cutar da halittu   da sabbaba hakan ba tare da hakki ba  na daga cikin hanya mafi hadari ga mutum. Wannan ita ce hanya irin ta shaidanu tana tasowa daga sabani  da gaba da  rikici na kashe juna, tare da rasa ginshiki na rahama  da hali irin na tausayi, da jinkai.

Lalle cutar da bayi dabia ce mara kyau abin zargi ne da  ta tattaro sifofi daban daban  na laifi da abubuwa masu halakarwa.

Lalle sake linzami ga rai ya cutar da wasu  da harshe ne ko a aikace  bai fitowa sai daga masu raunin imani da biye ma son rai, wanda bata da rai mai yawan umarni da mummuna da alfahasha.

To ka kare kanka daga cutar da wani - ya kai musulmi - ka yi wa kanka gargadi daga halaka   zaka kubuta ka rabauta a duniya da lahira Allah Madaukakin Sarki yace :  (Wadannan  da suke cutar da muminai maza da mata ba da abin da suka aikata ba suke jifansu hakika sun lafta karya da zunubi mabayyani ga kansu)

Allah subhanahu yana cewa : ( Wanda ya aikata kuskure karami ko babba sannan ya dorawa wanin sa to hakika ya girba karya da zunubi mabayyani)

   Kuma Manzonmu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayana littafin Ubangijinsa ya fassara shi yayi  bayanin wadannan ayoyi  daki – daki, ta hanya mutawatiri da aka karbo daga gare shi yana mai gargadi mai tsanani da jan hankali mai karfi bisa cutar da wani  da zaluntar su da musu shisshigi da wuce iyaka wajen cutar da su, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :(Musulmi dan uwan musulmi ne ba zai zalunce shi ba ba zai rena shi ba ba zai  tabar da shi ba) Muslim ne ya rawaito.

Kuma ya fitar a hadisin hana zama a kan hanya Annabi  ya bayyana cewa (Na daga cikin hakkin hanya kamewa daga cutarwa)

 ya kai musulmi

ka kiyaye kyawawanka ka kare addininka, ka kame daga cutar da waninka, ka kasance kamar yadda Fudail Bin Iyad yace :(Ba ya halatta a gare ka ka cutar da kare ko alade ba tare da hakki ba, to ina ga halitta mafi daukaka )

Matsanancin hani ya tabbata daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi

Game da cutar da musulmi sai ya ce : (ya tawagan wadanda suka yi imani da harshensu a halin imani bai fantsama cikin zuciyarsu ba, to kar ku cutar da musulmai  kar ku aibata su kada ku bibiyi  al'aurarsu, to lallai wanda ya bibiyi al'aurar dan'uwansa musulmi to Allah zai bibiyi al'aurarsa, kuma duk wanda Allah ya bibiyi al'aurarsa to zai kunyata shi ko da kuwa a tsakiyar gidansa ne ) Tirmizi ne ya rawaito.

Katada yace :(Na hore ku da ku nesaci cutar da mumini domin Allah na kewaye da shi kuma yana iya yin fushi dominsa.)

Ya kai bawan Allah!

Ka kubutar da kanka daga cutarwa , ka hana kanka daga zalunci da ketare iyaka zaka kubuta daga  walakanta da halaka.

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Musulmi shine wanda musulmai suka kubuta daga sharrin harshensa da hanunsa) Buhari ne ya rawaito.

Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira to kada ya cutar da makwabcinsa) Buhari ne ya rawaito. A gun muslim kuma (Ba zai shiga aljanna ba duk wanda makwabcinsa bai aminta da sharrinsa ba)  wato sharinsa da mugayen halinsa.

 

Ya  'yan uwa musulmi

 

A duniyar  yau akwai abin da ake cewa kafofin sadarwa ta sada zumunta,wanda wasu ke amfani da shi wajen cutar da musulmai da suka ga mahukuntansu da malamansu da daidaikunsu. Da al'umominsu  da maganganu na fajirci da yada jita –jita marasa kan gado. To masu yin wannan lalle su tuna cewa : Allah na dakon su a madakata, kuma lalle mizani ya hada da kyawawa da munana  to su kiyaye kada su je ga Ubangijinsu suna halin Muflisai wadanda suka shiga cikin rudani sun yanke tsammani, - muna rokon Allah afuwa da waraka-.

Lalle haramcin cutar da musulmi bai tsaya ga cutar da daidaiku ba, sai dai ya game da cutar da musulmai cikin maslahohinsu da ya shafi kowa da kowa.da abubuwan amfaninsu da ake tarayya kamar kayakin  al'uma mallakin gwamnati, na daga tushe na musulunci akwai (Ba cuta ba cutarwa).

   Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: (ku tsoraci abubuwa biyu masu janyo  tsinuwa : wanda ke bahaya a  hanyar mutane ko inuwar su).Muslim ne ya rawaito.

Dabarani ya fitar  da sanadi hasan daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace ; wanda ya cutar da musulmai a kan hanyar su to tsinuwa ta tabbata a gare shi).


 

Huduba ta biyu

Ya dan uwa musulmi !

Ka sabarwa kanka da kubuta daga cutar da halittu, ka tsarkake ta daga zaluntar wasu a zahiri da badini,  ka sani kubutar da rai daga shirka  da bidiah , da kullin zuci da hasada da kyashi da muzanta musulmai da zaluntansu na daga cikin sabuba na kubuta. Kuma sifa ce daga cikin sifofi na 'yan aljanna . Allah Madaukakin sarki ya ce game da khalilin sa Ibrahim in da ya roki Ubangijinsa game da abin da ya roki Ubangijinsa da shi,( kada ka kunyatar dani ranar da ake tashin mutane) kuma Allah ya ce (Mun fitar da abin da yake cikin kirzansu na daga keta, halin kasancewarsu  "yan uwa, suna kan gadaje suna kallon juna ).

 Hakika hadisai da yawa sun inganta wurin bayyana falalan lafiyan  zuciya  ga musulmai  daga gaba da kiyayya da nufin muzantawa, na daga ciki akwai mutumin na da ya zo daga cikin Ansarawa  wanda Annabi ya yi mar shaida da cewa dan aljanna ne, Abdullahi dan Amru Dan As ya bibiyi wannan mutumin har ya taho ya yi kwanaki uku a gidan mutumin, amma bai ga wani abu na daga kyawawan ayyukan shi ba irin su tsayuwan dare ba, face in ya tashi cikin dare daga makwancinsa sai ya ambaci Allah  yayi kabbara har zuwa ya tashi don sallar Asubahi, bai fadi wani abu ba face alheri, sannan Abdullahi ya bashi labarin abin da Annabi ya fada game da kissarsa, sai mutumin yace da shi game da ayyukansa shi bai yin wani abu face abin da ka gani sai dai ni ba na rike wani musulmi a cikin zuciya ta kuma bana hasada ga wani bisa wani alhairin da Allah ya bashi  saiAbdullahi ya ki cewa lale wanan itace wanda ta kai ka wanan matsayin da ba zamu iya ba.   

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 


 

 


 

 

 

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق