الأربعاء، 23 ديسمبر 2020

SHI NE ALLAH

 

خطبة الشيخ  أحمد الطالب

المترجم : أمين سعد

اللغة : الهوسا

التاريخ : 4-5-1442هـ

 

 

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI NA SHAIKH AHMAD –ADDALIB

4-5-1442AH 18-12-2020AD

 

HUDUBAR FARKO

Dukkan yabo  da godiya sun tabbata ga Allah  muna gode masa kuma muna neman taimkonSa kuma muna neman gafararSa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da munanan  ayukanmu duk wanda Allah y shiryar da shi babu mai batar da shi  kuma duk wanda ya batar da shi babu mai shiryar da shi .

Kuma na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah  shi  kadai yake bashi da abokin tarayya , kuma na shiada Annabi Muhammadu bawansa ne kum ManzonSa ne , kuma zababbenSa ne cikin halittunSa , kuma badadayinSa ne,  ya isar da sako kuma ya bada amana  ya yi nasiha wa al'uma  ya yaye bakin ciki ya yi jahadi don Allah cancancin jahadi ,  har mutuwa ta zo mi shi ,tsira da amincin Allah su tabbata agare shi  da iyalan gidansa tsarkaka  da kuma matayen sa  uwayen muminai da  sahabbansa  masu hasken hannaye  da kuma wanda ya bisu da kyautatawa zuwa ranar sakayya .

 BAYAN HAKA:

Lallai mafi gaskiyan zance shi ne littafin Allah , mafi alherin shiriya shi ne shiryarwan Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi , mafi sharrin al'amura kuma su ne fararrun ta , kuma  dukkan fararrun abu bidi'a ne dukkan bidi'a bata ne, dukkan bata na wuta .

Ya ku Muminai:

Lallai Allah ya kira ku ne da suna na imani ,  kuma ya kira ku da ku ji tsoronSa kuma ya umarce ku da ku yiwa kanku hisabi kafin  a yi muku hisabi, dubi zuwa ga  abin da kuka tanada mata kafin komawa , ya muku gargadi game da manta ta, da kuma  radadin hasarar ta  ya sanar da ku fifikon hali da za a shiga a ranar  komawa gare shi  , da girmar tasirin alkur'ani da an saukar da shi ga duwatsu , ya kuma sanar da ku da kamalar sunayenSa masu daraja da kaye .

 Shi ne Allah wanda  zukata  take bauta mi shi bisa kauna da  rusunawa  da tsoro,  da tsammani da kushu'i , da fata da kuma firgici .

Shi ne Mai gaskiya duk  abin da ke koma bayan shi bata ne, kuma mai gushewa, ba abin bautawa da gaskiya  sai shi, gani bai  iyakance shi,  tunani baya  riskan shi, sutura baya mishi shamaki, sirri baya boyuwa gare shi, da izinin shi ne falaki ya ke juyawa mai kewayawa, da hukuncinSa da hikimarSa dare kan saba da wuni..

Ma'aboci rahama mai yalwa mai dorewa, ya daidaita bisa mafi yalwan halittunSa.Da  mafi kyaun sunayen sa da mafi yalwan sifofinSa, (Mai rahama , Ya daidaita  a kan Al'arshi. Abin da ya ke a cikin sammai Nasa ne, da abin da ya ke  a cikin kasa  da abin da yake a tsakaninsu  da abin da ke karkashin  turbaya .

Kuma  idan  ka bayyana da  magana, to, lalle Shi, Yana sanin  asiri da mafi  boyuwa . Allah babu abin bautawa  face  Shi . Yana da sunaye  mafiya  kyau.)

RahamarSa ta yalwaci halittu wurin samarwa da tattalawa da taimakawa  da shiryarwa  da zabarsa ga waliyyanSa, halin shiryarwa da kuma datarwa  da tattalawa  har  ya kaisu ga matabbatar rahamarSa da ni'imar aljannarSa,  mulki mai zartuwa na iko a duniya da aikinSa ne da umarninSa , mamallakin sarakuna da abin da aka mallaka da malakuti da falakoki , yana bada mulki ga wanda ya so ya kwace ga wanda ya so ,  ya daukaka wanda ya so ya kaskantar da wanda ya so,  alheri na hanunSa, kuma shi yana da iko ga dukkan komai.

(UmarninSa, idan Ya yi nufin wani abu , sai Ya ce masa kawai, ''Ka kasance,'' sai yana kasancewa (kamar yadda Yake nufi).

Ya tsarkaka daga dukkan tawaya sabo da kamala , ya kubuta daga dukkan aibi  sabo da kyau ,  ya tsarkake abin da ya so sabo da albarka da daukakawa, ya amintar da wanda ya so bisa ga wanda ya so sabo da daukakawa da kaskantarwa.

 (makoma), shine amincin masu tsoro, kuma mafakan masu yankewa don ibada , ba aminci  Ya yi imani na da fadinSa cewa shine gaskiya Mai kasaita, kuma muminai sun yi imani da  shi bisa dadin rai a fadi da aiki, saura halittu kuma suna da'a  bisa tilas  a karshe ba zaman lafiya sai daga gare shi kuma zuwa gare shi,  rinjayin iko a ilimi da umarni  da shaidawa da karfin mulki  da amfanarwa da cutarwa  a sirrace da a bayysane duka na shi ne .

Ya buwaya bisa ga halittunSa wanda tsarki ya tabbata a gare shi  a karfi da kudura da galaba  da hani .

Ya karya  garkuwan halittu bisa umarninSa da haninSa a shari'a da kaddara  da karfin mulki , ya karya garkuwan su  ta karaya da talauci , da tsanani da cuta ,  bisa jin dadi da wadatarwa  da gamsarwa  da kuma saukakewa da taimakawa.

Shi ya fi komai girma da daukaka da daraja da sha'ani  da zati da sifa  da ayyuka  da iko, to ko wani abu kasa da shi ya ke karami ne abin renarwa  ya tsarkaka daga dukkan wani abokin tarayya , kuma ya daukaka ba wani abu kwatankwacinSa shi mai ji ne kuma  mai gani , ya yi halitta daga babu  sai ya bayyana  shi  ya halicci iska sai ya sanya mishi wuri  ya suranta a mahaifa sai ya rarrabe , ya kadaita da sunaye , wanda suka kai kololuwa wurin kyawu a lafazi da ma'ana  , ko wani abu ya yi tasbihi a gare shi  yana mai tsarkake shi  da dukkan harshe .

Allah ya buwaya daga makamanci  ko kini, ko kishiya da majibinci da mataimaki. Ya kyautata halitta a hukunci da hikima, shine Al hakku  kuma maganarSa gaskiya ce, hukuncinSa adalci ne alkalancinSa ne  mai rabewa (kat), babu kusakurai ko zamewa, ba wani abu da zai fita daga iliminSa na aiki ne ko fadi, Shi Mai hikima ne gwani.(Ya ku wadan da suka yi imani  ku ji tsoron Allah kuma rai ya dubi abin da ya gabatar domin gobe , kuma ku bi Allah da takawa . Lalle Allah  Mai kididdigewa ne ga  abin da  kuke aikatawa.

Kuma kada  ku kasance  kamar wadanda suka  manta  Allah,  Shi  kuma Ya mantar  da su rayukansu . Wadannan  su ne fasikai .

'Yan wuta da 'yan aljanna basu daidaita , 'yan aljanna su ne masu babban rabo.

 Da mun saukar wannan Alkur'ani akan dutse , da lallai ka ga dutsen yana mai tawali'u mai tsatssagewa sabo da tsoron Allah, kuma wadancan misalai muna bayyana su ne ga mutane da fatan za su yi tunani .

(Wanda ya saukar da Alkur'ani) Shi ne Allah wanda babu wani abin bautawa face shi masanin fake da bayyane , shi ne mai rahama mai jin kai .

Shi ne Allah wanda babu abin bautawa  face shi Mai mulki mai tsarki , aminci , Mai amintarwa Mai tsarewa Mabuwayi Mai tilastawa  Mai kamun kai , tsarki ya tabbata a gare shi daga abin da suke yi na shirki da shi.

Shi ne Allah mai halitta mai ginawa  Mai surantawa Yana da sunaye masu kyau , abin da ke a cikin sammai da kasa suna tsarkake shi, kuma shi ne mabuwayi  Mai hikima ).

Allah ya sa mini albarka ni da ku a cikin Alkur'ani mai girma , ya amfane ni da ku da abin da ke cikin shi na daga ayoyi da ambato mai hikima, ina fadin wannan maganar tawa  ina neman gafarar Allah wa ni kai na da ku da sauran musulmai daga dukkan zunubai , kuma ku nemi gafararSa , lallai shi mai gafara ne mai jin kai .

HUDUBA TA BIYU

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah  wanda ya isa, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi zababbe  da iyalansa da sahabbansan , da wanda suka bi sawunsu .

Bayan haka:

To ku ji tsoron Allah ya ku bayin Allah , lallai mafi alherin guzuri shi ne tsoron Allah, kuma ku yi riko da igiya mai karfi na musulunci .

Ku yi salati da aminci…. Ya ku bayin Allah  karshe da kuma adu'a.

 

       

 

 

  

     

   

 


 


 

 


 

 

 


 

 


 

 


 

 


 

 


 

 


 

 


 

 


 

 

 

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق