الجمعة، 23 أكتوبر 2020

WASIYOYIN ALLAH GA ANNABAWA DA SAURAN HALITTU

 

 

 

ترجمة الخطبة

اسم المترجم :أمين سعد عبد الله

اللغة : الهوسا

التاريخ : 15-2-1442هـ

 

Hudubar jumma'a na masallacin Annabi na shaik Ahmad Bin Dalib 15-2-1442 Ah / 2-10-2020

 

Hudubar farko

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah muna gode masa kuma muna neman taimakonSa da gafararSa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi, kuma duk wanda ya batar babu mai shiryar da shi. Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, na kuma shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma manzonSa ne. tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da aminci tabbatacce.

(Ya ku wadanda suka bada gaskiya ku ji tsoron Allah cancancin tsoronSa kada ku mutu face kuna musulmai)

(ya ku mutane ku ji tsoron Allah wanda ya halitta ku daga rai guda kuma ya halitta matarsa daga gare shi ya yada daga gare su mazaje masu yawa da mata, ku ji tsoron Allah da ku ke roko da (sunan) shi. Da zumunci, lalle Allah ya kasance mai tsaro ne a kan ku.)

(ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah ku fadi zance na daidai. zai gyara muku ayyukan ku kuma ya gafarta muku zunubanku, duk wanda ya ke yi wa Allah biyayya da ManzonSa to ya rabauta rabauta mai girma.)

(Ka  ce : '' in karanta  abin da Ubangiji ku  ya haramta .'' wajibi ne akan  ku  kada ku yi shirkin kome da shi.  Kuma ga  mahaifa  biyu  ku (kyautata  mu su) kyautatawa  kuma kada ku kashe diyan ku sabo da talauci , mu ne muke    azurtaku  ku da su kuma kada ku kusanci abubuwan alfasha  abin da ya bayyana  daga gare  ta da abin da ya boyu kada ku kashe rai wanda Allah ya haramta  face  da haki wannan ne (Allah) ya yi muku wasiyya da shi tsammaninku kuna hankalta.

Kada ku kusanci dukiyar maraya  face  da wadda  take ita ce mafi kyau  har ya kai ga karfin  sa  kuma ku cika mudu da sikeli  da adalci  ba mu kallafa wa  rai face  iyawarsa   kuma idan kun fadi magana to ku yi adalci , kuma ko da ya kasance ma'abocin zumunta ne  kuma da alkawarin Allah ku cika , wannan ne ya  mu ku wasiyya da shi  ,  tsammanin ku kuna  tunawa .

Kuma lalle wannan ne  tafarki Na yana madaidaici sai ku bi shi  kuma kada ku bi wasu hanyoyi ,  su rarraba da ku  daga barin hanyaTa , wannan ne Allah ya yi muku wasiyya da shi tsammanin ku kuna yin takawa 

Sa'annan  kuma  mun baiwa Musa littafi yana cikakke  bisa ga wanda ya kyautata (hukuncin Allah ) da rarrabewa  daki –daki  ga ko wani abu , da shiriya da rahama  tsammanin su  suna yin imani da haduwa da Ubangijin su .

Kuma wannan littafi ne  mun saukar da shi mai albarka ne sai ku bi shi  kuma ku yi takawa , tsammanin ku ana jin-kanku .

 Domin kada ku ce abin sani kawai , an saukar da littafi akan kungiya biyu daga gabaninmu , kuma lalle  ne mu mun kasance daga karatun su hakika gafilai .

 Ko kuwa ku ce ''  da dai lalle mu ansaukar da littafi akan mu hakika da mun kasance mafiya shiryuwa daga gare su , to lalle ne ne wata hujja bayyananniya daga Ubangijinku ta zo mu ku  da shiriya da rahama .

To wane ne mafi zalunci  daga wanda ya karyata game da ayoyin Allah  kuma  ya hinjire daga barin su za mu sakawa wadanda suke hinjirewa daga barin ayoyin mu  da mugunyar azaba saboda  abin da suka kasance suna yi na hinjirewa.

Shin suna jiran (wani abu) face  dai mala'iku  su je mu su , ko kuwa Ubangijinka ya je . A ranar da sashin ayoyin Ubangijinka  ya ke zuwa , imanin rai  wanda bai kasance ya yi imani ba a gabanin ,  ko kuwa  ya yi  tsiwirwirin wani alheri  baya amfanan sa  ka ce :- '' Ku  yi jira lalle  ne mu masu jira ne .

Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bamu labari,  labari na gaskiya yana halin  mai isar da sako kuma yana  mai gaskatawa , (Lalle Allah ya umarci Yahya dan Zakariyya da kalmomi guda  biyar  da ya yi aiki da su kuma da ya umarci banu isra'ila  da  su yi aiki da su, kuma lalle shi dinnan ya kusa da ya jinkirta su  sai ysa ce :- ''Isa  lalle Allah ya umarce  ka da kalmomi guda biyar don ka yi aiki da su  kuma ka  umarci banu Isra'ila da su yi aiki da su  ko dai ka umaarce su ko kuma ni na umarce su  sai yahya ya ce ina tsoron kar ka rigani tashi da su  da sai Allah ya kisfe  ni ko ya  azabtar da ni   sai ya tara banu Isra'ila a Baitul-Makdis, sai masallaci ya cika  suka zauna akan tudu, sai ya ce lalle Allah ya umurce ni da kalmomi guda biyar , da na yi aiki da su kuma na umarce ku kuma ku yi aiki da su : - na farkon su shi ne ku bautawa Allah kada ku hada wani da shi , lalle misalin wanda ya yi shirka da Allah kamar misalin mutum ne da ya sayi bawa daga kudin sa shi kadai na azurfa ko zinari,sai ya ce : wannan gida na ne kuma wannan aiki na ne,to kana yin aiki ka kawo min, to sai ya kasance yana yin aikin kuma yana kaiwa wanin maigidansa, a cikin ku wa zai yarda da bawansa da ya kasance kamar wannan? Kuma lalle Allah ya umarce ku da sallah to idan kuna sallah banda waiwaye, a cin sallah, Allah  na kafa ganinSa ga idon bawansa a cikin sallarsa  muddin bai waiga ba, kuma na umarce ku da azumi, kuma lalle misalin haka shi ne misalin mutumin da ke cikin jama'a tare da shi akwai jaka a ciki akwai turaren almiski, dukkan su yana burge su ko kuma kamshinsa na burge kowannen su,  Warin bakin mai azumi  ya fi kamshi  a wurin Allah fiye da turaren almiski,  kuma na umarce ku da sadaka , lalle misalin haka kamar mutum ne da makiya suka kamashi  suka sa mishi ankwa a hanu zuwa wuyan sa  , suka kuma gabatar da shi don sare wuyan sa , sai ya ce :- '' ni zan fanshe shi daga gare ku  da abu kadan da mai yawa sai ya fanshi kanshi daga gare su ,  kuma na umarce ku da  ku ambaci Allah, misalin haka ; kamar misalin mutum ne da ya fita  makiya suka  bishi a bayan shi da sauri  har sai da ya kai wani katanga mai karfi  sai ya boye kanshi  daga gare su  to haka nan ne bawa wanda baya kare kansa daga shaidan sai da ambaton Allah .)

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:- (Nima ina umurtan ku da abubuwa guda biyar Allah ya umurce ni da su  ji  da bi , da  jahadi da hijira  da kuma jama'a  domin duk wanda ya kauracewa jama'a gwargwadon  taki  to hakika ya kwance kulli na  musulunci  daga wuyansa  sai dai idan ya dawo , wanda ya yi da'awa irin da'awan jahiliyya to hakika lalle shi yana cikin makamashi na jahannama   sai wani mutum ya ce ya  Manzon Allah  ko da ya yi salla ya yi azumi? Sai ya ce ''e, ko da ya yi salla ya yi azumi''  ku yi kira da kiran Allah wanda ya ambace ku da musulmai  muminai .)

Ya ku bayin Allah:

Wannan shi ne gaskiyan zance kuma shi ne mafi alherin shiryarwa

(Wadancannin ka su ne wadan da Allah ya shiryar da su , to, ka yi koyi da shiryarwar su , ka ce ba zan tambaye ku wani lada ba   , shi ba wani abu ba ne sai tunatarwa  ga talikai ).

Ku ji tsoron Allah gwargwadon iyawan ku .

Ku yi aiki da abin da aka yi muku wahayi  daga Ubangijin ku  za ku rabauta kuma  ku yi nasara.

Kuma ku nemi  gafaran  Ubangijinku , ku tuba zuwa gare, lalle shi ya kasance ga masu komowa gare shi mai yawan gafara.


 

Huduba ta biyu

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Muhammadu da iyalansa da sahabbansa baki daya da wanda ya bi su da kyautatawa zuwa ranar sakayya.

(Ya ku wanda suka yi imani ku ji tsoron Ubangijin ku  ku tsoraci wata rana  wanda mahaifi ba zai fanshi dansa ba  , ko da ya fanshi mahaifin sa da wani abu ba , lalle alkawarin Allah  gaskiya ne  kada  rayuwar duniya ta rude ku  kada wani mai  rudi  ya rude ku daga barin Allah ).

Annabi ya bayyana abin da ke kulla kaskanci da abin da ke kawo hasken daukaka  idan kunyi  cinikayya da riba ku ka riki jelan  shanu  kuka yarda da shuki kuka bar jahadi  Allah zai sallada muku  kaskanci , sannan ba zai cire shi ba har sai kun komo addinin ku  .

Bayan haka

Ya ku mutane:

Ku yi salati da aminci  ga wanda ambatonSo ke dadada zukata       

         

      

 


 

 


 

 

 


 

 


 

 


 

 


 

 


 

 


 

 


 

 


 

 

 

DUNIYA HIKIMOMI DA HUKUNCE HUKUNCE

 

ترجمة الخطبة بالمسجد النبوي

اسم المترجم :أمين سعد

اللغة : الهوسا

التاريخ 22-2-1442هـ

Hudubar juma'a  na  masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na Shaikh Aliyu Bin Abdurrahman Alhuzaifi 22-2-1442Ah

Hudubar farko:

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin kasa da sammai,mai daga darajoji,ya yi umarni da biyayya sabo da abin da ke ciki na alheri da albarka, ya yi hani daga abubuwan da aka haramta, sabo da abin da ke cikin su na shu'umci da sharri da halaka.

          Ina kyautata yabo ga Ubamgiji na kuma ina gode mishi bisa ni'imominSa da ba mai iyakance su sai Shi, wadanda muka sani da wadanda bamu sani ba, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, ya dayanta da sunaye kyawawa da sifofi mafi kamala, na shaida Annabinmu kuma shugabanmu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, mafi alherin halittu wanda aka karfafe shi da mu'ujizozi Ya Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka bisa ga bawanKa kuma ManzonKa Muhammad da iyalansa da sahabbansa masu tsere zuwa ga alheri, Bayan haka.    

To ku ji tsoron Allah ta hanyan kusantan shi, ku kusanta zuwa gare shi da abinda zai yardar da shi da kauracewa abinda zai fusata shi ,kuma ya cutar da shi, abin mamaki da kyakkyawan karshe irin na masu tsoron Allah, abun mamaki da munin karshe na masu sabawa Allah mabarnata, to ku kasance daga cikin wadanda suka bi tafarkin tsira kar ku kasance daga cikin wadanda suka bi hanyoyi na masu sabo, Allah madaukakin sarki ya ce (duk wanda yayiwa Allah da'a da Manzon Sa to wadannan suna tare da wadanda Allah ya yi ni'ima a gare su na daga annabawa da siddikai da shuhada'ada salihan bayi madalla da abokan zama irin wadannan) (wannan falala ne daga Allah kuma Allah ya isa masani) kuma Allah Madaukakin sarki ya ce:( Duk wanda ya ke sabawa Allah da manzonSa to lallai yanada wutan jahannama yana dawwama a ciki har abada)

Ya ku musulmai:

Lallai Allah ya halicci wannan duniya kuma ya sanya abubuwan da duk mukallafi ke bukata a ciki na daga arziki ne da jin dadi ne da kawa da dukiya ne da dabbobi  da waninsu , kuma ya saukake wannan  duniya ga halittu ya horar da su duka gaba daya domin maslahohin halittu da amfanin su da kuma tashi tsayuwan rayuwansu zuwa ga lokaci abin ambato a wurin Allah wanda ba mai iya tsallake shi, Allah Subhanahu wa Ta'ala ya ke cewa (shi ne wanda ya sanya muku doron kasa a kaskance to ku yi tafiya a yankin ta ku ci daaga arzikin Sa kuma zuwa gare shi za a tashe ku), Allah Madaukakin sarki ya ce (ba mu halicci sammai da kasa ba da abunda ke tsakanin su face da gaskiya kuma da wani ajali a ambato wadanda suka kafurce suna masu kauda kai daga abunda aka musu gargadi) Allah Subhanahu wa ta'ala ya ke cewa:(dabbobin gida ya halicce su ne don ku a ciki akwai dif'un da kuma abun amfani daga ciki kuke ci kuma kunada kawa a ciki lokacinda kuke yammaci da kuma lokacin da kuke safiya) (kuma tsana daukan abubuwanku masu nauyi zuwa ga wasu garurruwa wanda baza ku iya ba sai da wahalan rayi, lallai ubangijin ku mai tausayi ne mai jin kai) (dawakai kuma da alfadura da jakuna don ku hausu kuma da ado , yana halittan abinda baku sani ba)  Allah Subhanahu wa ta'ala ya ke cewa (kuma ya horar a gare ku abunda ke cikin sammai da abunda ke cikin kasa domin gaba daya daga gare shi , lallai a cikin haka akwai a'ayoyi ga mutane da su ke tinani), Allah Mai tsarki ya ke cewa (Allah ya sanya a gare ku daga kawunan ku mataye, ya sanya muku kuma daga matayen ku 'ya'ya da kuma jikoki, kuma ya azurta ku daga dadada, shin da bata za su yi imani kuma su kafurcewa ni'imomin Allah?).

Allah Subhanahu wa Ta'ala ya ke cewa:(in za ku kidanya ni'imomin Allah ba za ku iya iyakance su ba), Allah ya halicci wannan duniyan cikin kamalarSa da kyansa da kuma cikansa sosai da abubuwa da suke na tsaida rayuwa dukkanin su yayi ne ga wanda suke doron kasa da kuma yawan abubuwan amfaninsa da kuma nau'ukan su da kuma horewan shi da sabuba na wanzuwan rayuwa da kuma habakan ta ,Ubangijinmu ya bamu labari Mabuwayi da daukaka cewa bai halicci wannan duniyan ba don wasa, kuma bai barsu haka ba kuma bai yishi haka banza ba, Allah mai tsarki ya ke cewa:(ban halicci sama da kasa ba da abunda ke tsakanin su da sunan wasa) (da a ce mun so mu rike shi wasa da mun rike shi daga gare mu in mun kasance masu yin hakan ne , sai dai muna hurga gaskiya akan bata domin ya rusa shi sai gashi ya gushe , kuna da bone na daga abinda kuke siffantawa), Allah Subhanahu wa Ta'ala ya ke cewa (hakika mun halicci a saman kutara'ika guda bakwai , bamu kasance bisa ga halittan mu gafalallu ba) Mai tsarki ya ce (ba mu halicci sama da kasa ba da abinda ke tsakanin su haka kawai da sunan bata a banza ba sai dai wannan zaton wadanda suke kafurai ne to bone ya tabbata ga wadanda suka kafurce na daga wuta) Allah subhanahu ya ke cewa (shin ko kun zaci mun halicce ku wasa na kuma ba za ku koma zuwa gare mu ba? To Allah ya daukaka daga wannan mai mulki na gaskiya, ba abun bautawa da gaskiya sai shi ubangijin al'arshi mai girma) Allah Madaukakin sarki ya ce (Allah shi ne wanda ya daga sammai ba tare da gofwanni ba , sannan ya daidaita bisa al'arshi kuma ya horar da rana da wata duk suna gudu zuwa ga wani ajali abun ambato, yana tafiyar da al'amura yana rarrabe a'ayoyi , ko zaku sakankance game da haduwa da uban gijin ku) .

Allah Subhanahu wa ta'ala ya ce:(ba wani abu a doron kasa na daga dabba face Allah ne mai azurtata kuma ya san matabbatan ta kuma da inda ta ke a'adanan ta dukkan haka yana cikin littafin bayyananne)

Allah madaukakin sarki ya ce:(masani ne na gaibu kuma baya kwace masa ko da na kwayan zarra abunda ke sama ne ko a kasa ko mafi kankanta akan haka ko mafi girma face yana littafi bayyananne) Allah Madaukaki ya ce (rayi bata kasance da ta mutu ba face da izinin Allah abu ne rubutacce mai lokaci ) Allah bai wakilta halitta ba zuwa ga wanin Sa sai dai ya halicci duniya ne wanda ake gani da gaskiya shi ne tauhidi da kuma da'a duka , dukkanin su da gyara da gyaruwa ga doron kasa , Allah Madaukakin sarki ya ce:(ya ku mutane, ku bautawa ubangijin ku wanda ya halicce ku da wadanda suke kafin ku ko zaku ji tsoron Allah wanda y sanya muku doron kasa mai shinfida sama kuma gini. Ya saukar da ruwa daga sama sai ya fitar da 'ya'yan itace da shi arziki a gare ku,to kada ku sanya wa Allah kishiya a halin kuna sane. )

Allah Madaukakin sarki ya ce : (Ban halicci aljanu da mutane ba face don su bauta min, ba na bukatar arziki daga gare su, kuma ba na bukatar da su ciyar da ni lalle Allah Shine Mai azurtawa Ma'aboci karfi)

Hakika Allah ya turo manzanni, na karshen su shine shugabanmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, don ya yi gyara a doron kasa na daga da'a  da tsarkake ta daga shirka da abubuwa masu halakarwa,(  Hakika mun turo ga kowace al'uma Manzo da a bautawa Allah kuma a nesaci dagutu ) kuma ya ce Allah Subhanahu wa ta''ala ya ce: (kada ku yi barna a doron kasa bayan manzanni sun gyarata da littatafan da aka saukar):(hakika mun turo cikin ko wace al'umma manzo da su bautawa Allah kuma su nisan ci dagutu) Allah Subhanahu wa Ta'ala ya ce:(kada ku yi barna a doron kasa bayan an gyarata) bayan manzanni sun gyarata da litttatafai wadanda aka saukar

Hakika  Allah ya umarni manzanni amincin Allah su tabbata a gare su  da su ji dadi da abinda ya halatta musu na rayuwan duniya daga tsarkaka  kuma su dimanci da'a wa Allah wanda kasa ata gyaruwa sai da ita .

Allah Madaukakin sarki ya ce: (ya ku manzanni ku ci na daga tsarkaka (dadada) kuma ku yi aiki na kwarai lallai ni din nan bisa ga abinda ku ke aikatawa ina sane), mabiya manzanni su ne muminai wadanda aka yiwa umarni suyi koyi da shi a fadin sa (ya ku wadanda suka yi imani ku ci daga tsarkaka din da muka azurta ku da shi kuma ku godewa Allah in kun kasance shi kadai ku ke bautawa) Allah Subhanahu wa ta'ala ya ce (ka ce wa ya haramta kawa na Allah? Wanda ya fitar ga bayin sa da kuma tsarkaka na daga arziki? Ka ce: su din nan ga wadanda suka yi imani ne a rayuwan duniya kuma ya kebanta ranar alkiyama gare su)   manzanni amincin Allah su tabbata a gare su da mabiyan su muminai sun sanya wannan duniyan gaba daya wuri ne da kuma lokaci ne na ayyukan da'a da kuma gyara sun sanya shi wato kamar wurin tsallakawa ne da ayyukan alheri da kuma neman aljanna da kuma ayyuka na kwarai amfanin su duka gaba daya yana komawa ne zuwa ga mutum, amfanar da halittu ta hanyan tashi da rukunnan musulunci da sauran ayyuka na da'a yana bin wannan rukunnan ne, ya kai musulmi kada ka raina ayyukan da'a komin kankantan su na daga wani abu, baka sani ba a ciki wani aikin ne zai shigar da kai  aljanna kuma ya tsiratar da kai daga wuta.

An karbo daga Jabir Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (kar ka rena wani abu na daga aikin alheri lallai daga cikin abubuwa na ma'arufi ka hadu da dan uwanka fiska a sake) Bukari bda Muslim ne suka rawaito.

An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce(wani mutumi yana tafiya a wani  hanya sai ya samu wani reshi na kaya akan hanya sai ya dauke shi ya ja shi baya sai Allah ya gode mishi kuma ya gafarta mishi)

Bukari da Muslim ne suka rawaito.

 An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cewa : (wata mace mazinaciya taga kare a wata rana yana shawagi a wurin rijiya yana lallage da harshen sa saboda tsananinkishi sai ta cire huffin ta ta cika shi da ruwa ta bashi ta bashi ya sha sai aka gafarta mata) Bukari da Muslim ne suka rawaito, Allah Madaukakin sarki ya ce:(lallai Allah baya zalunta ko na kwatankwacin kwayan zarra in har ta kasance kyakkyawa ce zai ribanya ta ne kuma ya bada daga gare shi lada mai yawa).

Muminai sun riki wannan duniya wani zamani ne kuma wuri ne domin ayyukan da'a, amma wadanda basu yi imani da Allah ba da ranar lahira suka kafirce to sun riki wannan duniya ne wani lokaci ne da kuma wani wuri ne na su na bin soye soyen rayuka na daga abubuwan da aka haramta da bin kyalakyalai masu gushewa da kuma aikata ayyukan sabo mafi girman laifi shi ne shirka da Allah, wato bawa ya riki wani abu da ya ke halittacce yana kira shi yana rokon shi yana fata daga gare shi kuma ya dogara gare shi kuma yana neman taimakonsa kuma yana neman a'agajinsa ya daga mishi bukatun shi da abubuwan da ya ke nema, kuma yana ragaba zuwa gare shi wurin arziki ko kuma nasara ko kuma ya rika daga murya da shi wurin neman yaye tsanani da bakin ciki wannan shi ne shirkan da Allah ba ya gafartawa, tsarki su tabbata a gare shi sai dai ta hanyar tuba, Allah Subhanahu wa Ta'ala ya ce:(lallai Allah baya gafarta da ahada shi da wani amma yana gafarta abinda ke kma bayan haka ga wanda ya so duk wanda ya hada Allah da wani to hakika ya bata batya wanda ya ke nesa), Allah Madaukakin sarki ya ce: (lallai sha'anin shi duk wanda ya ke shirka da Allah to Allah ya haramta a gare shi aljanna kuma makoman sa wuta ne kuma azzalumai basu da mataimaka), wanda zasu biyo bayan wannan su ne manyan zunubbai suna cikin girman laifuka ne masu girma bayan shirka gwargwadon barna zunubi da kuma gwargwadon sabawa, bawa ke zaluntan ransa tsakanin shi da kuma Allah ya tuba kuma daga gare su Allah sai ya gafarta mishi amma abubuwa da su ke na abinda aka zalunci  bayi to Allah baya gafartawa har sai utun ya maidawa wanda aka zalunta hakkin sa kafun ranarda babu dirhami ko dinari sai dai kawai kyawawa ne da za a bawa wanda aka zalunta na daga kyawawantun wanda ya yi zaluncin  idan har kyawawan sa sun kare sai a dauka daga laifukan wancan wanda aka zalunta a jefa mishi shi wanda ya yi zaluncin sannan a hurga shi a cikin wuta, an karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:(duk wanda ya kasance yanada wani abu da ya zalunci wanin shi na daga dan uwan shi na daga mutuncin shi ne ko wani abu nashi to ya warware tun kafun wannan ranan ya zo, ranan da zai kasance babu dinari ko dirhami, idan mutum ya kAsance yanada ayyuka na kwarai sai a dauka daga gare shi gwargwadon wanda ya zalunta, in kuma ya kasance yanada kyawawa sai a dauki daga kyawawan sa in ya kasance baida kyawawa sai a dauka daga munanan sahibin nasa sai a dora mishi) Muslim ne ya rawaito da Tirmizi.

An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (lallai ku bada hakkoki zuwa ga ma'abotan su tun kafun ranan alkiyama, ranan da za a yi kisasi daga akuya mara kaho daga akuya mai kaho wanda ta soketa da shi) Muslim ne ya rawaito.

Da mutum zai kubuta daga nauyin hakkoki a wurin abubuwa na zalunci to da muminai sun kubuta masu biyayya daga neman hakkoki na zalunci a tsakanin su , an karbo daga Abu Sa'id Alah ya kara yarda a gare shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (za a kubutar da muminai daga wuta bayan sun tsallake siradi sai a kange su a wani wuri da ake cewa kandara tsakanin wuta da aljanna sai a musu kisasi sashin su a yiwa sashi kisasi daga abunda wani ya zalunci wani wanda ya kasance tsakanin su a duniya har zuwa lokacin da aka tsarkake aka tsabtace su sai a musu izini da  su shiga aljanna na rantse da wanda raina ke wurin Sa zan same su sun fi shiryuwa zuwa ga matsayi a aljanna da matsayin da na kasance a gare shi a duniya) Bukari ne ya rawaito.

Ya kai musulmi: na horeka da zunubbai ko da a idonka kanana ne, domin lallai a wurin Allah abu ne mai girma, an karbo daga Abdullahi dan  Umar Allah ya kara yarda a gare su daga Annabi tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi ya ce: (wata mace ta shiga wuta a sakamakon kyanwa wanda ta daure ta bata sake ta ba ta ci daga ciyayin kasa) Bukari da Muslim n suka rawaito.

Manzon Allah tasira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (na horeku daga abubuwa na raina zunubbai domin su din nan su suke taruwa ga bawa Har su halaka shi), Allah Madaukakin sarki ya ce: (ya ku bayiNa wadanda suka yi barna wa kawunan su kada ku yanke tsammani daga kawunan ku daga rahamar Allah lallai Allah na gafarta zunubbai gaba daya lallai shi din nan mai gafara ne kuma mai jin kai)(kuma ku koma zuwa ga ubangijin ku ku mika mishi wuya tun kafun azaba ya zo sannan baza ku yi nasara ba) (ku bi daga abunda ya fi kyau cikin abunda aka saukar muku na daga ubangijin ku tun kafin azaba ya zo bagatatan a halin ba ku sani ba)

Allah ya sa min albarka ni da ku a cikin alkur'ani mai girma

 

Huduba ta biyu:

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin talikai majibincin masu takawa mawadaci daga halittunSa da'an masu da'a baya amfanar da shi haka nan kuma sabon masu sabo baya cutar da shi ina kyautata yabo ga ubangijina kuma ina gode mishi bisa ga ni'imomin Shi da waninshi ba ya iya kidinye su wanda muka sani da wanda ba mu sani ba, na shaida ba abun bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarauyya , mulki nashi ne wanda ya ke ma'aboci gaskiya kuma bayyananne na shaida Annabin mu kuma shugaban mu Muhammad bawanSa ne kuma Manzon Sa ne amuntacce ya Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka bisa ga bawanKa kuma manzonKa Muhammad da 'yalan shi da sahabban shi baki daya .

Bayan haka:

Ku ji tsoron Allah cancancin takawa ku yi riko da igiya mai arfi na musulunci .

Ya ku musulmai:

Lallai na daga cikin abinda ke kankare zunubai kuma ya ke kara kyawawa kuma ya ke tsarkake ayyuka shi ne ayyuka na kwarai kuma ya ke goge da ke cikin ayyuka na kusanci abinda ke koran shaidanu kuma shi ne ambaton Allah Mabuwayi da daukaka daga dukkan hali.

Allah Madaukakin sarki ya ce: (ya ku wadanda suka yi imani ku ambaci Allah ambato mai yawa kuma ku yi tasbihi a gare shi safiya da maraice), an karbo daga Abdullahi dan Umar Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: wani ya zo wurin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai ya ce: ya Manzon Allah: shari'o'i  na musulunci sun min yawa to da wanne zan yi riko dunkulalle? Sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke cewa: (kada harshen ka ya gushe yana danye daga ambaton Allah)Ahmad ne ya rawaito da Tirmizi.

Ya ku bayin Allah lallai Allah da mala'ikunSa suna salati ga Annabi, ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce.

  

 

 

 

ABUBUWAN LURA DAGA SURATUL DUHA

 

ترجمة خطبة الشيخ عبد الباري الثبيتي

  بالمسجد النبوي

اسم المترجم :أمين سعد

اللغة : الهوسا

التاريخ 6-3-1442هـ

Hudubar juma'a  na  masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na Shaikh AbdulBari Bin  Awad Assubaiti 6-3-1442Ah

Hudubar farko:

 

Sura ce da ta sauka a zuciyar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai ta debe masa kewa ta share masa radadin da yake ji ta wanke masa zafin da ya ke ji, ta kuma jefa masa natsuwa a cikin zuciyarsa.

Wahayi ya katse wa Manzon Allah na wani lokaci, sai masu dako na dako da masu shakku na jefa shakku sai Allah ya saukar (Allah na rantsuwa da walaha. Da dare idan duhu ya lullube shi. Ubangijinka bai barka ba kuma bai kaurace ma ba).

   Wannan Sura ta fito da matsayin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da kaunar Allah  da ya ke masa  da kusancin shi da falalar sa ,  sabo da ya kaunaci Allah da gaske  sai Allah  ya  kaunace shi   (Ubangijinka bai barka ba kuma bai kyale ka ba)

 ta yaya Ubangijin shi zai juya mishi baya  zai juyawa zuciyan da ya ke samun nitsuwa da shi  da ganawa da shi yakan ji dadi da ayoyinSa da maganganunsa wallahi ba zai yi nesa ba da bawanda da ya allaka zuciyan shi da shi  sai  ma ya kusanto shi ya manna shi a jiki ya daukaka sha'anin sa ,  ya bashi matsayi

Wannan ayan tana magana ne da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi  kuma tana magana ne da dukkan wani  mumini da mumina   wanda ya yi gaskiya tare  da Allah  ana jefa a cikin zuciya   wani shu'uri na kaunan Allah  da kuma kusancin shi  da kuma ma'iyyarSa  wato kasancewa tare da shi kuma tana kwararo wani abu na  sa'ada da yarda da kuma  jin dadi Allah madaukakin sarki yana cewa:- a cikin hadisin kudusi (BawaNa ba zai gushe ba yana kusanta na  da nafilfilu har sai na kaunace shi  idan na so shi sai in  kasance jin shi da yake ji da shi  da ganin sa da yake gani da shi  da hanunsa da  yake damka da shi da kafan sa  da yake  tafiya da ita  , idan ya roke ni zan bashi  idan ya tambaye ni zan bashi  in kuma ya tambaye ni zan biya mishi bukatanshi.)

(Kuma lallai lahira  ya fi ma alheri akan duniya ), lallai wato karshen al'amari a gare ka shi ya fi ma alheri  akan farkon shi  manzon Allah tsira da  amincin Allah su tabbata a gare shi bai gushe ba yana haurawa darajoji  na daukaka  Allah yana karfafan shi  da addinin sa kuma yana taimakon shi  yana datar da shi a kowani  halayen shi  har zuwa lokacin da ya rasu  a kowani rana da yake shudewa na rayuwarsa  Allah yana kara mishi daukaka  da buwaya  a cikin shi  kuma ya taimake shi da taimako akan taimako  da karfafa akan karfafa  har lokacin da ya ga mutane sun shiga addinin Allah tawaga-tawaga , to hakika ya gaskata  Allah  Allah ya yiawa AnnabinSa gaskiyan Alkawari da ya mi shi  ta inda ya bude masa garin makka  ya yada da'awarsa a gabashin duniya  da yammacin ta  lallai lahira ya fi  duniya , lallai karshe ita tafi  alheri akan farko  a dukkan abin da Allah ya  kaddara  lallai bawa yana mu'amala ne  tare da Ubangiji mai karamci  yana wa bayinSa jarabawa sannan kuma  ya yaye musu bakin ciki  al'amarin ya kare zuwa ga yalwa  dukkan wata hala da ta jinkirta daga cikin yanayin  ka to, lallai  tana da falala bisa ga halin da ya gabta (Kuma lallai lahira  ya fi ma alheri akan duniya )     

  Allah ya san cewa ManzonSa ya sancewa lahira ta fi  duniya a gare shi  Allah madaukakin sarki yana cewa  na tattalawa bayiNa salihai abin da idanuwa basu taba gani ba  kunne ba ta taba ji ba  zuciyan wani dan adam bai taba  hararo shi ba  shi ne kuma ya ke cewa wurin  da ake ajiye bulala a aljanna ya fi alheri akan duniya da abin da ke cikin ta  an bawa Annabi zabi  a rashin lafiyar shi  tsakanin  da  ya rayu a duniya iya yanda zai  rayu, da  kuma abin da ya ke wurin Allah  sai ya zabi abin da ya ke wurin Allah  duk wanda yake da hankali  na shiriya ya  san  cewa  lahira ya fi alheri akan duniya , lallai duniya  mai karewa ne  kuma  dukkan wanda  ya ke doronta kuma zai kare  sai ya rage  fiskan Ubangijin ka kadai  zai wanzu ma'aboci daukaka  da karamci  wannan  ma'ana  na asali  yana tunkuda musulmi  zuwa ga ya kyautata imanin shi ya  ya gyara  ayukan sa  ya tsarkake  rayuwarsa kuma  ya habaka ayukansa a lokutansa (Ubangijinka zai baka har sai ka yarda)  ana karanta wannan aya  a dukkan zamani  da suka shude  ana kuma kawata  kunnuwa da shi  zuciya na raurawa tana hakaito  matsayin da ke lullube  yana kuma hakaito matsayin wanda aka bawa  da kuma matsayin wanda ya ke  bayarwa  wanda akan kanshi yana da ma'ana  da madalulin sa  kyauta ne , madalla da irin wannan  kyauta  daga mai bada kyauta  wanda baya saba alkawari  ba kuma wani falala bayan kyautar sa  ba wani kari  akan ladanSa kuma ba  iyaka bisa ga ni'imarSa,

 Allah ya bashi wani matsayi madaukaki  da sammai madaukaka ya kusantar da shi ga Annabawa gaba daya  ya sanya shi cikamakin Annabawa  ya sanya al'umarsa mafificiyar al'umu ya sanya littafinshi da ya saukar zuwa gare shi shi ne mafi darajan   littatafai  ya sanya shari'arsa kuma shi ne mafi alherin shari'o'i  ya daukaka ma'abotansa ya daraja matayensa  kuma ya bashi na daga falala wanda ba za a iya iyakance shi ba  Allah madaukakin sarki ya ce tsarki ya tabbata  ga wanda in ya ga dama zai sanya maka wanda  ya fi haka alheri  daga gare shi gonakai wanda  koramai na gudana a karkashin sa  kuma ya sanya maka benaye  ya bashi ceto  ga mutanen da suke a maukif  har lokacin da Allah zai yi hukunci a tsakanin su   da ceto kuma ga ma'abota Aljanna  har su samu su shiga .

Yarda da kyautan Allah  ga wanda ya fiskanto  zuwa ga Allah  sai Ubangijinsa ya so shi , wanda Ubangijin shi ya so shi kuma zai kusanto da shi  ya kawo shi kusa  kuma ya yardar da shi ,  ya bashi nitsuwa ta zuci  da kwanciyar hankali,  har zuciya da cikakken natsuwa da  hutu  ya gusar mishi da bakin ciki da bacin rai  amma kuma abin da ya ke lahira  yana cikin rayuwa ne yardajjiya to ki koma zuwa ga Ubangijin ki kina yardajjiya  abin yarda , kina mai yarda kuma abin yarda (ashe Ubangijinka bai same ka maraya ba kuma  ya baka mafaka  ya same ka batacce kuma baka da shiriya kuma ya shiryar da kai , ya same ka kana talaka kuma ya wadata ka)  to kamar yanda ya bashi mafaka yana matsayin  maraya  kuma ya shiryar da shi da wahayi to da wannan kuma ya wadatar da shi da dukkan wani abin da ya sha-gabansa  a dukkan matakai na rayuwarsa   Allah ya wadata shi da tarbiyanSa, tarbiyan Abu –Dalib  ya yin da aka samu  rashin Abu-Dalib  sai Allah ya wadata shi da  dukiyan Khadija , yayin da aka rasa wannan sai Allah ya  wadata shi da dukiyan Abubakar , yayin da aka rasa hakan sai Allah ya  umarce shi da hijira  ya wadata shi da taimakon  mutanen madina .

A cikin wadannan ni'imomi  wanda Allah ya yi baiwada shi ga Annabin sa  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  idan mai bakin- ciki  yayi lura  da ita  sai ya gusar mishi da musiba , ko kuma ya samu wasu matsaltsalu a kan hanya da  wasu musibu  to lallai wannan za ta bude mishi kofofi ne  da suke na fatan alheri  da kuma wani gun shiga  abun sha mai  dadi na alhini  kuma ya cika shi da azama da aiki  kuma ya kiraye shi zuwa ga ya yarda duk wani yanke tsammani  ko yanke kauna  ya yada duk wani abin da ke ga zai kawo mishi rashin nasara  ya samu sakankancewa  a dukkan tafiyan sa da rayuwarsa  sabo da gamayyan rahamar Allah  da kuma kyautanSa da bayida iyaka amma shi maraya kada a fi karfin shi  amma kuma matambayi ba a tsawatar mishi  wadannan ayoyi suna isar da ma'ana ne na shiryayyen rayuwa wanda   aka assasa ta akwai daukan nauyi da tausayawa kuma kira ne ga dukkan wanda Allah ya yiwa ni'ima da matsayi bayan da ya kasance ba a sanshi ba , ya  bashi mafaka bayan maraya ne  ya wadata shi bayan talaka ne  ya daga sha'anin sa bayan  ya kaskanta da ya godewa ni'imar Allah .

Kada ka yi rinjaye kada ka fi karfin maraya kada ka walakanta shi ka tsawata  mishi sai dai ka  kyautata mishi ka tausasa mishi  kar ka kasance ga masu rauni kana  mai jabbaranci kada ka yi girman kai kada ka zama mai zafin rai  kana mai maida miskinai  ta hanyar rahama tausasawa da amma ga ni'imar Ubangijinka to ka bada labari .

 

Huduba ta biyu

 rayuwa domin ka ga ni'imomin Allah a gare ka a da can baka kasance komai ba  har  zuwa lokacin da ka wayi gari kana wani abu abin abin ambato ni'imar Allah a ko wani kai komo  da numfasawa ni'imar samarwa da ni'imar shiryarwa da ni'imar lafiya da zaman lafiya da ji da gani da dukiya da zuriya da ni'iman bacci da shiryarwa da fadaka ko farka da ni'imar Allah tun daga kanka har zuwa tafin kafan ka , (A kawunan ku ashe ba za ku yi lura ba) ka yi lura da ni'imomin Allah cikin abin da ya hore maka na daga rana da wata da koramai da koguna da itatuwa da dabbobi da dare da yini ka yi lura  ka yi lura bisa ga ni'imomin Allah ka labarta da su bisa ga hanyoyi na tabbatarwa da rusunawa da yarda  da kuma wafa'I domin wannan ni'ima su dauwama falalan su kuma  ya dauwama , domin ka rika jin wannan ni'ima din tare da kai domin ka rika jin falala na wannan ni'ima , kuma ka san hakkinSa sai halinka ya canza daga gafala zuwa ga mai da'a daga kuma mai gajartawa zuwa ga mai godiya ka godewa Allah a wurin fadi da aiki, a zuciya da gabbai sai Allah ya dada hore maka ni'imomin cikin abinda Allah ya shar'anta maka  .

(Ina rantsuwa da hantsi, da dare a lokacin da ya rufe(da duhunsa)Ubangijin ka bai yi maka bankwana ba kuma bai ki ka ba , kuma   lalle ta karshe ce  mafi alheri a gare ka daga ta farko , kuma lalle ne Ubangijinka zai yi ta baka kyauta har sai ka yarda , ashe bai same ka maraya ba sa'annan ya yi maka makoma , kuma ya same ka ba kada shari'a  sai ya shiryar da kai  kuma ya same ka matalauci sai ya wadata ka  sabo da haka , amma maraya to, kada ka rinjaye shi  , kuma amma mai tambaya kada ka yi masa tsawa , kuma amma ni'imar Ubangijinka sai ka fada (domin godiya )).