الجمعة، 25 سبتمبر 2020

FALALAN SALLAR JAM'I

 

 

ترجمة الخطبة بالمسجد النبوي

اسم المترجم :أمين سعد

اللغة : الهوسا

التاريخ 8-2-1442هـ

Hudubar juma'a  na  masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na Shaikh  Abdullah Abuaijan 8-2-1442.AH /25-9-2020AD

 

Hudubar farko:

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah muna gode masa kuma muna neman taimakonSa kuma muna neman gafararSa muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu,duk wanda Allah ya shiryar da shi to babu mai batar da shi duk wanda ya batar da shi babu mai shiryar da shi,

.

Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah  shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya wanzuwa na shi ne  da yabo  kuma gudananar  da al'amura  a hanun shi ya ke da  hukunci  , yana tafiyar da al'amura zuwa doron kasa daga sama  yana aikata abin da ya so ,  ba abin da za ku so sai idan Allah ya so .

Na shida Annabi Muhammadu bawqnSa ne kuma ManzonSa ne ,  ya  isar da sako kuma ya sauke  amana  ya yi nasiha wa al'uma ya yi jahadi a tafarkin Allah cancancin jahadi , har mutuwa ta zo mi shi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi  da sahabbaan shi baki daya  .

Bayan haka:

Lallai littafin Allah shi ne zance mafi mikewa , shi ne kuma dalili  mafi  shiryarwa  kuma sunnan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  shi ne mafi alherin manhaji , kuma mafi adalcin tafarki  kuma abin koyi kyakkyawa  a wurin bi  kuma bata da kauce hanya na cikin kirkiran bidi'a  .

Ya ku bayin Allah   :

Ku ji tsoron Allah a cikin abin da ya yi umarni  , ku hanu daga abin da ya hana kuma ya tsawatar  (Ya ku wadan da kuka yi imani ku ji tsoron allah ku fadi  maganan da yake na daidai zai   gyara mu ku ayukan ku  kuma ya gafarta  mu ku zunuban ku ,  duk wanda  ya yiwa Allah da Mnzon sa da'a to hakika ya rabauta , rabauta mai girma)

Ya ku jama'ar Musulmi:

 Masallatayya dakuna ne na Allah  kuma mafi soyuwan bigire a gare shi an tanada su ne don bauta da sallah da ambaton Allah zuwa gare su wanda ya yi imani  da shi  kuma ya jibince shi  ya ke komawa (Lalle mai raya masallatan Sa shi ne  wanda y a yi imani da Allah da ranar lahira ,  ya tsaida sallah ya bada zakka bai ji tsoron wani ba face Allah ,  ya wuci wadancan   su kasance  cikin shiryayyu .)

Ba bu mai raya su sai muminai na gaskiya , Allah Madaukakin sarki ya ce :(Mushrikai ba su kasance da su raya masallatan Allah ba)

:(cikin wasu gidaje da Allah ya yi umarni da daukaka kuma a ambaci sunanSa cikin su, wasu mazaje suna tasbihi a gare shi safiya da maraice, kasuwanci bai shagaltar da su ko ciniki daga ambaton Allah da tsaida sallah da bada zakka suna tsoron wata ranar da zukata da ganai ke juyawa)

Allah ya yi alkawarin narkon azaba ga  wanda ya yi saddu ga tafarkin su  ya bata wuraren kiran sallan su da mihraban su  sai ya ce:- (Wa ya fi zalunci  sama da wanda ya hana masallatayyan Allah  da  a ambaci sunanSa a cikin su  kuma yayi aiki wurin rusa su  wadannan bai kasance ba a gare su da su shige su face suna halin tsoro ,  suna da wulakanci anan duniya a lahira kuma suna da azaba mai girma ) 

Ya ku bayin Allah :

Masallatai dakunan Allah ne , su ne mafifitan gurare da bigire, su ne makwancin wanda ke bautawa Ubangijinsa ya yi biyayya.

Daga wuraren kiran sallan su  ne ake maimaita shahadan tauhidi ko wace rana  bisa kunnuwa; na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah  na shaida Annabi Muhammadu Manzon Allah ne.

Daga wuraren kiran sallanta ne ake maimaita yekuwa zuwa ga sallah  kinshiki na musulunci , na  biyu daga   cikin rukunan sa masu girma , ku gaggauto zuwa ga sallah, ku gaggauto zuwa ga sallah , ku gaggauto zuwa ga babban rabo .

Daga mihirabansu  ne da mimbarorin su  sako na imani ya taso , ya bude zukata da kunnuwa , kuma ya goge duhun shirka da gumaka .

Su ne farkon makarantu na tarbiya da ilmantarwa a musulunci, tawaga irin na sahabbai masu  daraja daga nan su ka fito , sai suka kasance mafi cancantan mutane a ilimi da aiki.

Su ne farkon  tawagan da aka kafa  mimbari na da'awa , sai suka  yada musulunci dukkan duniya  da da'awa da jahadi da halaye .

Ya jama'ar musulmi:

Lallai mafifici kuma mafi daukakan ayuka a wurin Allah da girman matsayi awurin Allah  shi ne raya masallatayya  dakunan Allah (Abin sani kawai wadanda suka yi imani da Allah su ne ke raya masallatayyan Allah ).

Kuma raya masallatayya na  kasancewa ne ta hanyar gina su da bauta a cikin su   da fiskantar su don tsaida sallah da amsa kiran mai kira idan ya kira a gaggauto zuwa ga sallah .

An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi   ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gre shi ya ce :- (Da ace mutane sun san abin da ke cikin kiran sallah da sahun farko  sa'annan ba za su same su ba sai da kuri'a  to da sun yi kuri'a  kuma da ace sun san abin da ke cikin  diban garji  da sun yi tsere zuwa gare shi  da sun san abin da ke cikin isha'i da asubahi da sun zo mu su ko da da rarrafe ne ) Buhari da Muslim ne suka rawaito 

Ya ku bayin Allah:

Na daga cikin abin da ke daga darajoji ya kankare laifuka akwai yawan taku zuwa masallatayya,  An karbo da ga Abu Huraira yace :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : Shin bazan fada maku ba abin da zai kankare maku zunubanku ba,ya daukaka darajarku ba.sai yace:

"Yawan taku zuwa masallaci,kyautata alwala alokacin da ake kin taba ruwa, da zama jiran sallah bayan sallah, wannan shine ribadi wannan shine Ribadi) Muslim ne ya rawaito

An karbo da ga Abu Huraira yace :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Duk wanda yayi Sammako ko yayi yammaci zuwa Masallaci, Allah yayi masa tanadin mazauni a aljanna,duk lokacin da yayi Sammmako ko yammacin zuwa Masallaci).

Ya ku bayin Allah:

Ya ku mazowa dakunan Allah masu raya masallatan Allah, barkanku da samun mafi yalwan inuwa. Albishirinku da mafi kyau da cikan haske,  

An karbo da ga Abu Huraira yace :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Mutum bakwai suna cikin inuwar Allah ranar da ba wata inuwa sai inuwarSa sai ya ambaci  da mutumin da zuciyarsa ke ta'allake da masallaci) Buhari da Muslim ne suka rawaito.

An karbo daga Buraida al aslami Allah ya kara yarda a gare shi yace : -Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  yana cewa:

(Ka yiwa masu yawaita tafiya zuwa Masallaci cikin duhu da wani haske cikakke a ranar  alkiyama).

Abu Dauda da Tirmizi.

Ku sanya wa gidajen Allah wani kaso na daga lokacin ku , haka nan kuma da ibadojin ku ku sanya  wani kaso  na farilla , ku gabatar wa ibadun ku abin da zai amfane ku kuma Allah ya daukaka ku da shi ranan alkiyama , (kuma abunda ku ka gabatar wa kawunan kuy na daga alheri za ku same shi wurin Allah mafi girma a lada ku nemi gafarar Allah , Allah mai gafara ne mai jin kai)

 

Huduba ta biyu

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa datarwarSa godiya a gare \Shi bisa datarwan Shi da kuma baiwansa na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya ina mai girmama Sha'anin Shi na shaida cewa Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma Manzon Sa ne mai kira zuwa ga yardar Sa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da sahabban sa da aminci tabbatacce mai yawa.

Ya ku bayin Allah:

Sauke garilla cikin jama'a yana cikin manya manyan alamomi na musulunci kuma alamomi na imani (ku yi ruku'u tare da masu yin ruku'u), sallan jama'a ya ku bayin Allah yana daga cikin mafificin ayyuka kuma mafi daukakan da'a kuma mafi tsarkakan ayyukan kusanci kuma darajoji an karbo daga Abdullahi dan Mas'ud Allah ya kara yarda a gare shi ya ce (Duk wanda zai burge shi da ya hadu da Allah gobe yana musulmi to ya kiyaye wadannan salloli din a yayin da ake kira zuwa gare su domin lallai Allah ya shar'anta wa Annabin ku tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wasu sunnoni na shiriya, lallai su din nan duk suna cikin sunnoni na shiriya, da ace za ku yi sallah a cikin gidajen ku kamar yanda wannan wanda bai samu jam'I ba aka barshi ya yi sallah a gida to da hakika kun bar sunnan Annabin ku da kuma kun bar sunnan Annabin ku da kuwa kun bata , ba wani mutumi da zai yi tsarki ya kyautata alola sa'annan ya nufi zuwa masallaci cikin wadannan masallatan face Allah ya rubuta mishi a ko wani takawa da zai yi za a rubuta mishi lada a daga shi daraja da ita a kankare mishi laifi dalilin ta , hakika ba wanda ya ke barin sallah a cikin mu face munafiki wanda aka san shi da munafinci , hakika mutum ya kasance ana zuwa da shi ana tagire gire da shi tsakanin mutane biyu har a zo a tarar da shi cikin sahu) Muslim ne ya rawaito

An karbo daga Ibnu Umar Allah ya kara yarda a gare shi shi da mahaifin shi cewa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (sallan jama'a yafi sallan mutum daya da daraja ashirin da bakwai ) Muslim ne ya rawaito.

An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:(sallan mutum a cikin jam'I tana ribanya sallan sa a cikin gidan shi haka nan a kasuwan shi da da ribi ashirin da biyarsaboda haka nema idan mutum ya yi  alola ya kyautata alola sannan ya fita zuwa  ga masallaci ba abin da ke fitar da shi sai sallah to ba zai yi wani taku ba face dawannan takun an daga darajan shi da ita kuma an kankaare mishi kuskuren shi da ita idan ya yi sallah mala'iku ba za su gushe ba suna mishi salati muddin yana wurin sallan sa suna cewa : Allah ka yi dadin tsira a gare shi ya Allah ka mishi rahama, dayan ku ba zai gushe ba yana cikin sallah muddin ya tsaya jiran sallah) Bukari ne ya rawaito.

Ya ku bayin Allah:

Hakika hudubar musiba ta korona ya girmama ga musulmai ya lalata sallan jam'i bakin ciki da bacin rai sakamakon ta'allukin  zuciya ke yi da masallaci  sai radadin da shaukin da kwadayin ya yawaita ga mutane .

Hakika Allah ya zo da yaye bakin ciki sai ya sanya mafita ga ko wani kunci  da dukkan wani damuwa ya sanya mishi farin ciki , to ga shi masallatai an bude kofofin su an kimtsa su farfajiyan su an shirya  su, ga dakunan Allah suna jiran masu raya su da masu ziyartan su an daga sautukan kiran sallan su suna kira ku gaggauto zuwa ga sallah ku gaggauto zuwa ga sallah ku gaggauto zuwa ga babban rabo ku gaggauto zuwa ga babban rabo .

Muna godewa Allah kuma muna kyautata yabo a gare shi muna rokon shi da ya dauke abin da ya saura na daga wannan annoba kuma ya tunkude shi daga gare mu dukkan wani bala'i  kuma  ya cika mana cikakken lafiya da waraka ku gaggauto ya ku bayin Allah zuwa ga dakunan Allah ku amsa kiran mai kiran Allah idan ya kiraye ku zuwa ga Allah da Manzon Sa idan ya kiraye ku zuwa ga abin da zai rayaku kuma ya sa ku cikin walwala ya shiryar da ku, ku tsaida fuskokin ku a dukkan wuraren masallataiyya, ku kiyaye farilloli ta inda duk lokacin da aka yi kira zuwa gare su , (abun sani wanda ya ke raya masallatayyan Allah shi ne wanda imani da Allah da ranan lahira kuma ya tsaida sallah ya bada zakka kuma bai ji tsoron kowa ba sai Allah ya wuci wadannan su kasan ce cikin wadanda su ke shiryayyu) .

   

Yak u bayin Allah Lalle ambaton ni'imar Allah na daga abin da ya yin a ni'ima da shi ga wannan kasa mai albarka na ni'imar tauhidi da hadin kai da zaman lafiya da kwanciyar hankali da hidima ga masallatayya biyu masu alfarma da masu zuwa gare su, da bada kulawa ga batutuwa da suka shafi musulmai, da irin ayyuka na jinkai a lokuta daban daban, da tabbatar da zaman lafiya na duniya tun lokacin da aka kafa wannan kasa har zuwa wannan lokaci da muke ciki. Wanda zai sa mu godewa Allah ga wadannan ni'imomi, da kiyaye amincinta da dukiyanta da tabbatar da hadin kai irin na addini da dunkulewa irin na kasa daya mubaya'a irin ta sharia da lizimtar jama'a da jagoranci da ji da bi da adua ga shuwagabannin kasanta ya datar da su, Allah ya kiyaye kasar mu da sauran kasashen musulmai daga duk wani abu mummuna da abin ki, lalle Shi mai ji ne mai amsawa.

 

  

 

السبت، 19 سبتمبر 2020

FALALAN LIKITA DA LIKITOCI

 

 

ترجمة الخطبة بالمسجد النبوي

اسم المترجم :أمين سعد

اللغة : الهوسا

التاريخ 1-2-1442هـ

Hudubar juma'a  na  masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na Shaikh Salah Albudair 1-2-1442.AH /18-9-2020AD

 

Hudubar farko:

Ya ku musulmai:

Ilimin likitanci na daga cikin ilmuka mafi daukaka da amfani, kuma yafi girma da tasiri, kokari a cikin shi yana cikin dabi'u na masu daukaka, yin kasa da haka kuma wata ukuba ce kamar sauke nauyin abu mai wahala a wurin wahalan haurawa zuwa gare shi, ba gushewa mai neman ilimin likitanci yana mai haurawa zuwa gare shi yana hauhawa daraja bayan daraja har ya isa zuwa ga matsayi madaukaki da martaba mai daraja wanda ba kowa ya ke samunsa ba sai masu kokari  tsayayyu, ba kuma mai riskansa sai wanda ya dace kuma ya lizimci juriya.

 Imamushshafi'i ya ce:'' ilimi iri biyu ne: ilimin fikihu na addinai da kuma ilimin likitanci na jiki ''

Rabi'i ya ce: na ji Shafi'i yana cewa: ban san wani ilimi ba bayan halal da haram da yafi kyau kaman ilimin likitanci .

An ce: kar ka zauna a garin da babu shugaba da zai baka kariya, babu ruwa da zai shayar da kai, babu malami da zai baka fatawa babu likita da zai baka magani.

Musulunci ya kula da harkan likitanci kwarai da gaske dukkan kulawa, ka duba littafi na dibbu (likitanci) a cikin sahihulbukari da kuma babi na magani da rashin lafiya da rukiya a cikin sahihu Muslim da kuma kitabuddibbi a cikin sunanu Abi dauda, da littafi na dibbi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a cikin sunanuttirmizi da kuma littafi na dibb a cikin sunanu kubra na Nasa'i, da kuma littafin Addibb a cikin sunan Ibnu maja.

An rawaito daga Ibnu Masawaihi likita lokacin da ya karanta hadisin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da ya ke cewa (Ba wata jaka da dan Adam zai cika ta zama sharri a gare shi fiye da cikin shi, ya ishi dan Adam 'yan wasu lomomi da za su tsaida mishi kwankwason shi in ya kasance ba makawa to ku kasa shi kashi uku, kashi daya na abincinsa, kashi daya na abin shan sa, kashi daya na numfasawarsa).

Ya ce: da mutane za su yi aiki da wannan kalmomi da sun kubuta daga rashin lafiya da cututtuka, da ma an rasa asibitoci da  shaguna na magani, kemes sun zama ba amfani.

Larabawa suka ce: mafi alherin abin kalace shi ne na sassafe mafi alherin abin cin dare shi ne ………

Likita haziki kwararrae wanda ya ke ya kware suna amfani ne da magunguna wanda suke na boye da suka rufe suka sa yanar ido , allah ya sanya damtsenSa ya zama rahama, mishradansa ya zamana shafaka ciyakanSa ya zamana tsira sadarwanSa ya zamana karba, ribadinSa ya zamana magani, magungunanSa kuma ya zamana waraka.

Larabawa sun ambace shi da mai hikima mai tausayi saboda yana tausayawa ga mara lafiya yana mar muladafa, yana mannashi a jiki, Allah Shi ne wanda ya ke warkarwa kuma ya ke bada lafiya.

Likitoci bas]u da iko koda sun hadu da su koro waraka ga mara lafiya face da izinin Allah saboda Shi kadai ne mai bada waraka, wanda ya ke jarrabawa da cututtuka kuma ya ke bada taimako da magun guna ya kuma rahama da waraka, likita na mun fatan waraka ga idona*** shin akwai wani bayan Allah da ya ke likita?

Yayinda waraka ya zama daga cikin tushe na ni'imomi wanda mara lafiya baya samu sai daga wurin Allah ba wai daga wurin mai magani ba, Ibrahim alaihissalam ya ke cewa: (idan nayi rashi lafiya Shi ya ke bani waraka)

 An karbo daga suhaibu dan sinan arrumi Allah ya kara yarda a gare shi( a kissan wannan yaron wanda ya kasance yana warkarda makaho da kuma mai kuturta kuma yana bada magani da sauran cututtuka da izinin Allah,  sai bafaden sarki ya ji shi bayan kuma da ya makance sai ya zo wurin wannan yaron da wasu kyaututtuka masu yawa sai ya ce: menene wannan? Sai ya ce duka na tattaro naka ne idan ka warkar da ni, sai yaro ya ce: ni bana warkarda wani sai dai Allah ne ya ke warkarwa idan ka yi imani da Allah sai na ma addu'a sai ya baka waraka, sai ya yi imani da Allah shi ke nan sai Allah ya bashi waraka ya maida mishi ganinshi) Muslim ne ya rawaito.

** sai na wayi gari bana rokon likita don ya bani waraka don likitancin shi***

** sai dai ina kiranKa ne ya Mai saukar da ruwa***

Likitoci da nasis sunada falala da zance ba zai iya tattaro su duka  game su ba

** ka sani wadatanka kyautanka ba'a iya sakanyawa ***

Shin ana iya sakanyawa bisa ga abubuwa masu tsada na cikin kogi? ***

To ku kiyaye wa likitoci matsayin su da malaman jinya ku kiyaye musu matsayin su ku gode musu bisa kokarin su da irin bada lokacin su da suke yi, hakika sun tsaya gaba dayan su  wurin bada katanga mai kariya madaukakiya, domin kiyaye mutane daga fadawa ga mutuwa .da dulmuyar korona zuciyar da ba ta kokawa da farfajiya da ba a takawa.

Wasu kamshi na busawa don dadin yabo

                                       Irin nasu a ko ina ana shakansa.

Mun yabe su ba mu riska ba da yabon su

                                      Ba mu bar wata magana ba.

Yabo da rera waka ga irinku akwai dadi

                                     To me zan ce ne bayan ku din ku ne

Kun fifita marasa lafiya a kan yaranku

         Kauna da fifita wani akai ana sanin shi daga gare ku

 

Ya ku Musulmi!

Mustahabbi ne neman magani, idan barinsa zai kai ga halaka to ya zama wajibi.

An karbo daga Usama dan Sharik Allah ya kara yarda a gare shi yace : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :(ku nemi magani –ya ku bayin Allah- lalle Allah subhanahu bai sanya wata cuta ba face ya sanya mata magani banda tsufa )  

A wani lafazi (face mutuwa ) ya na nufin mutuwa. Ahmad da Ashabus sunan,

Idan al'amari mukaddari tabbatacce ya sauka lokaci da a ka yanka mishi ya kare magunguna sai su ki aiki dabaru su kare.

Hakika mutane kafin mu sun rabu da masoya

            Maganin mutuwa ya gagari duk wani likita.  

Sau dayawa halaka kan tsallake mara lafiya

          Ya tsira likitan shi ya mutu da itacen magani.

Likita na cewa da kai maganinka na guri na.

                                Idan gwada tafin hanu da zira'i

Da ace likita ya san maganin cuta

                Da zai maida mutuwa bai dandani  cece kuce ba

Mu kan sanya sababi ga magani idan mun yi rashin lafiya

    Shin magani na warkarwa daga mutuwa ne?

Muna zaban likita,ko likita na iya

    Jinkirta abin da aka hukunta

Numfasawarmu ba wani abu bane face a kididdige

  Kai komonmu ba wani abu ba ne face karewa

Ya ku musulmai!

Ya wajaba ga likita ya kwadaitar da mara lafiya ya sa musu tsammanin samun sauki, ya tausasa musu a wajen zance, ya jefa musu farinciki, ya yelwa, da yaye mishi bakinciki da sa mishi annashwa, da lausasa masa da gusar masa da tsoro, da damuwa a kwantar masa da hankali da firgici, da tunatar da shi da sanya mishi natsuwa.

Hakika an ce : Ludufi irin na likita shine rabin magani, dariya a fiskar mara lafiya kan saukake mishi radadin ciwo,yana jefa farinciki a gare shi yana tasiri da bai boyuwa, faruwan shi na ratsa jiki yana da fa'ida mai yawa.

Kuma likita mai tsauri da kaushin hali ya kan gitta wa mara lafiya ne tamkar iska mai kai hari ta tunbuke abin da ke gabanta tana rusa kyakkyawan fata irin ta zuciya, wanda ya tsorata mara lafiya da cuta ta ba zata ba tare da ya  yi wata shimfida ba ko mukaddima ko kankantar wa ba to hakika ya kara bata lamari ne, ya dada illa ne ga cutar.

Ya wajaba ga likita ya zama ya siffantu da hakuri da lura da hakkokin mara lafiya ya karya abin da ya samu mara lafiya ya karfafe shi ya girmama kokawansa.

 Ya ku likitoci ku riki hannayen marasa lafiyanku daga kunci na zafi da radadi zuwa ga yalwa na fatan alheri da taku irin na kunci zuwa ga farfajiya na yaye bakinciki.

Ya wajaba ga likita ya riki mara lafiya tamkar  kan shi sai ya bashi kariya ya mutunta shi ya kiyaye sirrinsa ya boye laifin  shi ya kame daga yada cutar da ya ke tare da ita wanda a cikin yaye ta akwai cutuwa gare shi, Ya wajaba kada ya yaye al'auransa sai idan ya kama na larura na bada magani.

Ya wajaba ga likita ya kirdada sannan kuma ya kiyaye ya kuma jinkiri da kuma yi jinkiri kar ya yi gaggawa wurin binciko cutan da kuma bada maganinta ya tabbatar daga illa na wannan  rashin lafiyan da kuma ya nemi shawara cikin al'amura da suka rikice mishi kada ya yi gaggawa ya bar abkawa ga abu muddin bai kware ba.

Ya haramta mutum ya bada magani wanda baida iliminshi, wanda bayi da kwarewa ko gwanancewa, a duk lokacinda mutum ya kekeren likitanci bisa jahilci ya bawa marasa lafiya magani hakika ya ruudar da mutane kuma ya hujumi da gjahilcinsa bisa ga abin da ya ke na lalata rayuka kuma ya bijiro zuwa ga abin da ya ke wato tahawwuri tare da kuma munanta bada magani zowa ga cutarwa da gan gan to ya wajaba a ladabtar da shi kuma abin da ya ellanta ya biya saboda hadisin Utbatu Umru dan Shu'aibu daga babansa daga kakansa ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce : (duk mutumin da yayi liktanci bisa karya a hali bai san likitanci ba to shi din nan zai biya abin da ya lalata) Abu dauda ne ya fitar da shi da Nisa'I a wurin darakutni kuma akim ya inganta shi (duk wanda ya yi likitanci a kuma shi ba likita ba bai iya likitanci ba sai ya kashe rayi ko kasa da haka to lallai shi zai biya).

Baya halatta ga mai yin likitanci bisa jahilci ko kuma shi likita wanda bai kware ba ya je ya rika yin aikin tiyata ko kuma ya fiskance ta domin iya gudanar da ita hakika ya dauka wa kanshi laifi kuma ya yi zalunci ya yi barna , kuma dole ya biya abin da ya yi kuskure a ciki da abin da aka samu na matsala.

Shi likita wanda ya ke ma'aboci sana'ansa likitanci idan hanunshi ya yi wani laifi ko ya kuskure irin kuskurenda makamantanshi ba sa yin irinshi ko kuma ya yi sakaci ko kuma ya gajarta ko kuma ya ketare gona da iyaka, to shi zai iya biyan asaran da ya biyo.

Kaddabi ya ce: '' ban san wani sabani ba cewa wanda ke bada magani idan ya ketare iyaka ya laata mai rashin lafiya shi ne zai biya abin da ya lalata, haka nan wanda ya ke bada magani a ilmance ko kuma a aikace bai sansu ba to mai ketare iyaka ne , idan ya haifar da wani abu sakamakon wannan abin da ya yi to dole ne ya wajaba ya biya diyya ''

Shi kuma likita jahili wanda zai iya haifar da mutuwa ya shuka abubuwa na tsoro, ya kai ga halaka idan har ciwo ya kara ruruta to zai bayyana a nan irin sakaci irin na likita.

***………………………………***……………………

 

 ya haramta ga likita ya bada magunguna wanda mara lafiya bai bukatanshi , ya haramta ya yiwa mara lafiya kari cikin abin da ba zai sha ba ko ba za a markada ba ko ba za a yi allura ba kafun ya tantance shi na daga wani illa kawai bisa ga zargi ko kuma bisa zato ko kuma kawai ya raya irin maganin da za a bashi , cututtuka ba'a iya magance su da wahami ba abun nufi shi ne gusarda rashin lafiyan ba sai don a gusar da shi ta fiskan amuntacce wanda hakan ba zai haifar da wani cutan ba ko kuma wani illa yafi tsanani ba.

Ya haramta ribatan mara lafiya amishi wasu gwaje -gwaje da aune aune da diban jini wanda ba bukatansu ko kuma ba wata fa'ida cikin tafiyar da su sai kawai kasuwanci ko kuma kwace dukiyan marasa lafiya , tir da irin wannan dukiya din , dukiya ne da bazai amfanu ba ba zai habaka ba sai bisa kasuwanci da radadin mara lafiya da kuma wanda suke cikin halin zazzabi.

Na daga cikin likitoci da kuma masu kemest wanda suke bada magani ga mara lafiya bisa ga wani farashi tare da akwai wani madadin shi wanda yafi dacewa kuma mai sauki a wurin farashi yana yin haka ne domin manufan ya habaka wa kamfani magungunanta ko kuma domin ya samu wasu sashi na garabasan da kamfanin ke gabatarwa saboda maslahansa a fifitata akan maslahan mara lafiya ba zai yi haka ba sai wanda zuciyarsa ba rahama ko yana kusa da ya rasa rahama da kuma rashin tsoron Allah da rashin alkawari da kiyaye amana.

An karbo daga Anas ya cewa: ba sa'annin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke  mana huduba face ya ce: (babu imani ga wanda ba yida amana babu addini ga wanda bayi da alkawari) Baihaki ne ya fito da shi.

Ku kiyaye dajjalai na daga 'yan tsubbu masu bada magani wadanda suke masu da'awan likitanci wadanda suke bude wuraren asibitoci da akwai shubuha a cikin su suna karban marasa lafiya ba tare da wani izini na hukuma ba kuma sunada ikon bada waraka bisa ga wasu cututtuka suna saida kayakin aiki  da suke akwai zamba a ciki ko algus.

Muna gargadan musulmai kar su gaskata wadanda suke ba ma'abota fanni ba a likitanci wadanda suna yada bayanai da siffantawa irin na likita ta hanyan kafafan sada  zumunta suna saida rudu suna wasa da rayuwa na marasa lafiya suna sadar da cutuwa bayyananne wanda ake da yakini a madadin lafiyan mutane da kuma jikinsu.

 

Suna yada abubuwa na mafi hadari kuma suna afkawa gidaje ku kiyaye su kar ku rudu da wadannan azzalumai masu barna a doron kasa mujrimai a hakkin rayi na dan Adam wanda musulunci ya zo domin kiyaye shi ya bashi kariya kuma ya haramta keta alfarman shi.

Ya ku musulmai:

Hakika Allah ya dauke rayin Abatil abubuwa na bata irin na bokaye da hujjoji da Alkur'ani, to ku kiyaye bokaye da kuma dajjalai da kuma masu buga kkasa ko taurari da masu sha'awaza konkulomboto wadanda suna da'awan ilimin gaibi da gano abubuwanda suke na zuciya da sanin abubuwanda suka boyo, to ku kiyaye wadannan dajjalan masu bada magani wadanda sun fita daga magani na shari'a sun kare akai suka shigarda wasu abubuwa na bidi'o'I wanda su ke masu laifi masu fusatawa, ku kiyaye masu yaudara masu rufa ido makaryata wadanda suke da'awan bada magani ga wanda aka ma sihiri da kuma wadanda suke aljani ya shafe su da kuma wadanda suke masu farfadiya ta hanyan shakewa ko ratayewa ko daurewa ko duka ko bada wasu dalasimai , da de wasu kulumboto suna saida wasu layu da kuma wasu abubuwa dunkulallu da kuma tamima ,hatimai da kuma wasu kariya da suke yi domin neman waraka da kuma abubuwa da ake daurewa da wasu rukiya na shirka wanda suna habaka da barna da kurafa suna saida abubuwa da suke na wahami wanda bata zayyanuwa a ganta sai ga ma'abota raunin hankali da akida  An karbo daga Imran da Husan Allah ya kara yarda a gare ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (Baya cikin mu duk wanda ya yi shu'umanci haka nan kuma ko wanda aka yima, kuma baya cikin mu wanda ya yi bokanci ko wanda aka mai bokanci ko kuma ya yi sihiri ko yasa aka mishi sihiri, duk wanda ya yi kulle kulle da wanda ya zoma boka ya gaskata shi cikin abin da ya ke fada to ya kafurce abin da aka saukar wa Muhammad) Bazzar ne ya fito da shi.

Duk wanda ya je wurin wadanan dajjalan to shi ma yana tarayya da su wurin alhaki saboda bakinsu da muninsu ya yi yawa kuma suna habaka abin da suke na barnan su to ya wajaba a isar da bangarori na tsaro don duba mataki da za su dauka ga wadannan kazantattu , ya haramta a boye sha'anin su ko a musu shiru .

*** ya fi mana sauki ba kusa ba da jikin mu ya cutu ***

*** mutuncin mu da hankalin mu ya tsira ***

Ina fadin abin da kuka ji kuma ina neman gafaran Allah ni da ku da kuma sauran musulmai daga dukkan zunubbai da kusakurai ku nemi gafaran Shi domin Shi mai gafara ne ga masu komawa gare Shi.

 

Huduba ta biyu:

Ya ku musulmai:

Halittu ana nufansu da jarabawoyi, hakika an ce: muddin kana wannan gida, kar ka yi mamakin faruwan abin da ya ke mai aukuwa  jirkitacce, kar ya kasance cikin wadanda idan wani abu na cuta ya same su sai su firgita su gaza hakuri sai zuciyan su ya dare su yi nesa, yanke kauna daga rahamar Ubangijinsa ya tuna fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi (lallai bawa idan yana da wani matsayi a wurin Allah ba zai riske shi ba ta hanyar ayyukan shi sai Allah ya jarrabe shi a jikin shi ko dukiyarsa  ko kuma a dan shi sa'annan sai ya sa shi ya yi hakuri bisa hakan don ya hadu da shi har ya kai shi wani matsayi wanda Allah Ta'ala ya riga ya rubuta shi  a gare shi) Abu dauda ya fitar da shi.

Wani daga cikin magabata ya ke cewa: '' ba don musimun duniya ba da mun zo kiyama muna talakawa''

Kais binu Ubad ya ke cewa:'' awowinda aka yi na wahala suna tafiyar da awowin da aka yi na kusakurai ''

Kada mumini ya yi fatan aukuwan ukuba sai dai ya roki Allah waraka , an karbo daga Anas da Malik Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: (Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ziyarci wani daga cikin musumai ya rame ya zama kaman wani dan tsako, sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da shi shin ka kasance kana addu'a da wani abu ne? ko kana rokon Allah da shi? Sai ya ce e, na kasance ina cewa '' ya Allah : muddin zaKa mini ukuba a lahira abin da zaKa min ukuba da shi a lahira to ka sanya min shi a nan duniya sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Subhanallah! Ai Ba zaka iya shi ba inama ka ce: Ya Allah ka bamu kyakkyawa a nan duniya ka bamu kyakkyawa a lahira ma ka kare mu daga azaban wuta? Sai ya roki Allah da ya bashi waraka). Muslim ne ya rawaito.

***Idan ya yi rashin lafiya to hakurin shi ba zai yi rashi lafiya ba ***

*** idan yayi zazzabi to azaman sa ba zai yi zazzabi ba***

***  idan ya mika wuya to ba wai ya rage ba ne sai dai ***

*** na kubuta ni daga alhumam zuwa humam ***

    

Ku yi salati da aminci ga Ahmad alhadi mai ceton dukkan halittu wanda ya yi salati a gare shi guda daya Allah zai mishi salati guda goma.       

 

 

 

 

 

   

                               

 

 

 

 

 

الجمعة، 11 سبتمبر 2020

TARIHIN ANNABI TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI

 

ترجمة خطبة المسجد النبوي

اللغة : الهوسا

المترجم : أمين سعد

التاريخ :23-1-1442هـ

Hudubar Masallacin Annabi Tare da shaikh Abdullah bin Abdurrahman Albuaijan 23-1-1442AH 11-9-2020Ad

Hudubar farko:

Dukkan yabo  da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya cikamake manzancin sama da shari'armu ya kuma cikamake annabawa da manzanni da Annabimmu ya sanya al'umar mu tsaka-tsakiya, mafi alherin al'umar da aka fitarwa mutane

 

Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai bashi da abokin tarayya, yana halittan abin da yaso kuma yayi zabi, na shaidah cewa Annabi Muhammad bawansa ne kuma Manzosa ne, mustafa kuma zababbe cikin zababbun zababbu.

 

Ya isar da sako kuma ya sauke amana kuma yayi nasiha wa al'umah kuma yayi jihadi a tafarkin Allah cancancin jihadi har yakini yazo mishi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabban shi da wanda ya bisu da kyautatawa har zuwa ranan sakayyah.

 

 bayan haka:

 

lallai mafi gaskiayan zance shine littafin Allah, mafi kyan shiryarwa shine shiriyar Muhammad dan abdullahi, sharrin al'amura kuma sune fararrunta, dukkan wata fararriyar abu bidi'a ce, dukkan bidi'a bata ce, kuma dukkan bata na wuta.

 

Yaku wadanda sukai imani kuji tsoron Allah cancancin tsoronshi kuma kada ku mutu face kuna musulmai

 

Ya jama'ar musulmi, mutum yana tare da wanda yake kauna, kaunar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sharadi ne a imani, kuma mafificin hanya don kaunar Annabi sallallahu alaihi wa sallam, shine sanin rayuwarsa da halayensa da dabi'unsa, to ku san Annabinku domin ku san kimansa da matsayinsa, sai a samu kaunarsa ta samu da kuma da'a gare shi ba dayanku da zai yi imani har sai ya kasance Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance mafi soyuwa a gare shi akan kansa da dansa da mahaifinsa da ma dukiyarsa da mutane baki daya.

Ya ku bayin Allah:

Allah yana zaban manzanni cikin malaiuku da kuma a cikin mutane ma hakika Allah ya zabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, daga mafi tsadar ma'adinai da mafi tsada da kyau, Allah ya karrama shi kuma ya fifitashi akan sauran mutane, Allah Madaukakin sarki yace: (Hakika Manzo yazo muku daga cikinku yana mishi nauyi abin da ya wahalar da ku, mai fata ne ga muminai kuma mai jin kai mai tausayi).

 

Ya sanya shiryarwarsa ma'auni ne domin wurin falala da kamala, (Hakika ya kasance a gareku ga Manzon Allah abin koyi ga wanda ya kasance yana fatan Allah da kuma ranar lahira.)

Allah ya tsarkake shiryarwarSa da halittanSa da kuma iliminSa da hankalinSa da fadinSa da aikinSa ,Allah ya tsarkake shi tsarkakewa cikakkiya a zahiri da badini ya tsarkake shi a hankalinsa sai ya ce (sahibinku bai bata ba kuma bai kauce hanya ba) ya tsarkake shi a ganinshi sai ya ce:(gani bai kauce ba kuma bai wuce gona da iri ba) ya kuma tsarkake shi a kirjinsa(zuciyarsa) sai ya ce (ase ba Mu fadada maka zuciyanka ba?) ya tsarkake shi a ambatonsa sai ya ce:(sai Mu ka daga ambatonka gareka) ya tsarkake shi a tsarkinsa sai ya ce:(Muka dauke maka laifinka) ya tsarkake shi a gaskiyansa sai ya ce: (baya furuci bisa son rai) ya tsarkak shi a iliminsa sai ya ce :(ma'abociai tsananin karfi ne ya koyar da shi) , ya tsarkake shi a hakurinsa sai ya ke cewa: (mai tausayi ne da jin kai ga muminai) ya tsarkake shi a halitansa na gaba daya sai ya ce:(lallai kana kan dabi'u masu daraja).

Ya ku bayin Allah:

Lallai Allah Ta'ala ya halicci bayinSa suna masu karkata zuwa ga addinin Annabi Ibrahim gaba dayan su hakika sai shaidanu suka zo musu sai suka yi awon gaba da su daga addinin su suka haramta musu abunda Allah ya halatta musu suka umarce su da su yi shirka da Allah kuma cikin abin da Allah bai saukar da wani hujja ba lallai Allah ya yi dubi zuwa ga doron kasa sai ya fusata da su ,larabawansu da ajamawansu  sai saura daga cikin mutanen ahlil kitabi sai ya zabi a tsakaninsu mafi tsadan ma'adinai ma'abota izza da daukaka mabubbuga na alheri da falala , ya karramasu ya tsarkake su mafi karramansu da tsarkakansu shi ne Muhammad dan Abdullahi dan Abdulmuttalib balarabe bakuraishe kuma bahashime uwarsa Aminatu 'yar wahab bakuraishiya .

Ya zaba mishi mafificin wuri sai aka haife shi kuma ya taso aka turo shi a Makka uwar alkaryu , kuma masaukan wahayi ya kasance haifuwarsa a Rabi'ul'auwal ne shekaran giwaye, bayan haka da kwatankwacin shekaru dari shida da talatin da biyu daga haihuwar almasihu Isa alaihissalam dan Maryam aka haifi Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi , ya turo shi zuwa ga Makka a shekarunshi ya dumfari arba'in ya mutu kuma yana sittin da uku na daga shekaru .

Ya jama'ar musulmai:

Manzon Allah ya rayu ya dandani daci irin na maraici mahaifin shi ya rasu a halin shi yana cikin mahaifiyarsa, mahaifiyar shi ta rasu yana kwatankwacin shekara shida na daga rayuwansa, sai kakansa Abdulmuttalib ya dauke shi shekaru biyu har zuwa ya rasu sai baffan shi Abu dalib ya jingina shi sai ya zama yana kewaye da shi yana kiyaye shi yana bashi kariya har zuwa lokacinda ya rasu yana dan shekara goma daga turowa manzanci .

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance shi kadai ne a wurin mahaifansa , bashi da wani dan uwa ko dan uwa hakika Allah ya tattaro mishi siffofi na alheri da falaloli da ta'adodi da dabi'u kyawawa yayi harkan kasuwanci ya fita zuwa sham ba so daya ba ya fita tare da baffanshi a kasuwanci haka nan kuma ya fita kasuwancin Khadija matarsa 'yar Kuwailid kamar yanda ya yi kiwon dabbobi bisa ga wasu silalla ga mutanen garin Makka .

Ya auri Khadija 'yar kuwailid shekarunshi na ashirin da biyar , ita kuma ta kasance mafificiyar me taimakawa da kuma bada gudumawa , ta haifa mishi dukkan 'yayanda ya ke da su maza banda Ibrahim shi uwarsa Mariya ce alkibdiyya .

Yayin da ya kai shekaru arba'in Allah ya zabe shi kuma ya turo shi kuma ya cikamake Annabawa da Manzanni da shi sai ya fara da'awan shi zuwa ga tauhidi da kuma yin nesa da shirka ya kuma kwadaita zuwa ga kyawawan dabi'u na alheri da umarni da kyakkyawa da hani da mummuna da zalunci da barna, yana Makka na tsawon shekaru goma sha uku yana kira a boye da kuma a bayyane dare da wuni sai suka rinka sanya hannayen su a kunnuwansu suna makirci makirci mai girma suka rufa tufafinsu kuma suka doge suka yi girman kai girman kai suka ketare iyaka suka yi musu suka karyata suka cutar kuma suka yi izgili suka tuhume shi da sihiri da kuma kahana (bokanci) da kuma hauka , Allah ya girmama bala'I ga mabiyansa da kuma masu taimakonsa sai mutanen Makka suka yita azabtar da su suka kokkore su basu musu ukuba ba face sai don sun yi imani da Allah Mabuwayi abun godiya .

Ya ku bayin Allah:

Allah ya yi izini ga AnnabinSa da yayi hijira zuwa ga Daibatuddaiba (Madina) inda zama ke yin dadi kuma gida na imani ta inda ya ke shi ne masulala na imani ta inda rundunan Allah Ansarawa suke, wadanda suka mallaki gida kuma da imani kafun su suna son wandanda suka yi hijira zuwa gare su kuma ba'a samun wani abu a cikin zukatan su na bukata cikin abunda suka bada kuma suna fifitawa a kan kansu koda sun kasance sunada haja duk wanda aka kare shi daga rowan kanshi to hakika yana cikin wadanda suka rabauta.

Daulan musulunci ta fara tana habaka tana tasowa a garin Madina aka assasata a dan lokaci kankani , hukunce hukunce suka sauka sa'an nan sai ta rika tattaro mutane ana jihadi a tafarkin Allah ana yakan duk wanda ya yaki Allah da ManzanSa , aka kulla kulleleniya da alkawura da yarjejeniya da mawasik.

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya cigaba da zama a ciki shekara goma har zuwa lokacin da wasu abubuwa suka faru masu yawa da kuma shari'o'i da kuma yake yake a doron kasa tunda Allah ya shinfidata kuma ya kafa ta tarihi bai san wani farawanta ba har zuwa yau wasu alumma da suka fi gaskiya da a'adalci akan tsayuwa akan tafarki mikakke kuma fi soyuwa zuwa ga Allah game da wancan fatra da wancan jama'a .

Ina neman tsarin Allah daga sharrin shedan abin jefewa, Shi ne wanda ya turo cikin ummiyai Manzo cikinsu yana karanta a'ayoyinSa kuma yana tsarkake shi kuma yana karantar da shi littafi da hikima ko da da sun kasance kafin haka suna cikin bata mabayyane .

 

Huduba ta biyu:

     Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mai bayyana gaskiya mai daukakata mai kaskantar da karya kuma mai tunkude ta ya tura ManzonSa da shiriya kuma da addini na gaskiya domin ya bayyana shi akan addinai gaba daya ko da mushrikai sun ki.

 ya ku bayin Allah :

a tsakanin shekaru goma na lokacin zaman Madina Allah ya cika addininShi , mutane suka shiga addinin Allah tawaga tawaga musulunci ya shiga ko wani bangare na yankin kasashen larabawa, mutanenta suka rusunawa musulunci suka mika wuya a gare shi, wadannan watanni akwai abubuwa da suka faru a wannan lokaci

A shekaran farko: na hijira Annabi tsira da am incin Allah su tabbata a gare shi ya gina masallacinSa da kuma gidansa , ya hada 'yan uwantaka tsakanin muhajirun da ansar ya shar'anta kiran salla.

A shekara ta biyu: ya maida alkibla zuwa Ka'aba kuma aka farlanta azumin ramadana a ciki ne kuma aka farlanta sadakatulfidr zakkan fidda kai .

A ciki ne kuma aka yi yakin badar kuma a ciki ne Rukayyatu 'yar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ta rasu a ciki ne kuma Annabi Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya shiga da A'aisha , a ciki ne kuma aliyyu Allah ya kara yarda a gare shi ya auri fadima 'yar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi .

A shekara ta uku : an yi yake yake daga ciki akwai yakin uhud akwai kuma yakin banunnadir an haramta giya bayanta sannan kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya auri Hafsa 'yar Umar dan kaddabi , Usman kuma ya auri Ummu kulsum 'yar Manzon  Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi , kuma aka haifi Hasan dan aliyyu ga Fadima

A shekara ta hudu: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya auri ummu salama , aka kuma shar'anta taimama , aka ce kuma a wannan shekaran ne aka yi yakin kandak da kuma zatu rika'a a ciki , haka nan kuma sallan tsoro .

A shekara ta biyar: aka yi yakin daumatuljandal da kuma kuraiza , aka shar'anta kuma hijabi.

A shekara ta shida :aka yi sulhul hudaibiya da kuma bai'atul ridwan da kuma yakin banil mustalak, Rana kuma ta kisfe aka saukar da hukuncin zihari.

A shekara na bakwai : ne aka yi yakin kaibar kuma umra na kada'a Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi aure da Habiba da Maimuna da Safiyya da Mariyal kibdiyya , kuma Abu huraira ya musulunta.

A shekara na takwas: ne aka yi yakin mu'ta da zatussalasil , aka bude Makka a Ramadana, aka haifi Ibrahim kuma Zainab 'yar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ta rasu , a ciki ne kuma aka yi yakin Hunain.

A shekara ta tara: a ciki ne aka yi yakin tabuka Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi hajji da mutane , kuma Ummu kulsum 'yar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ta rasu , Najashi ma ya rasu kuma runduna runduna na zuwa suka yawaita.

A shekara ta goma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi hajjin ban kwana, kuma Ibrahin dansa ya rasu,Allah ya saukar da (idan nasara ya zo daga Allah da kuma budi)(ka ga mutane na shiga addinin Allah kungiya kungiya)(to ka yi tasbihi da godiya ga Ubangijinka kana mai neman gafararSa, lallai Shi ya kasance mai yawan karban tuba ne).

Ya ku bayin Allah:

(Dukkan rai zai dandani mutuwa,) (dukkan wanda ke doron kasa kuwa zai kare) .

Ya ce

shi  mutuwa kan da ke sara baya kaucewa ya yi ha'inci ***

Tabki ne mai dafi duk wanda  ya rayu zai sha shi**

A cikin Rabi'ul auwal ne a shekara na sha daya bayan hijira kuma hajjin ban kwana Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ji wani irin ciwo, na bada fansa da mahaifina da kuma mahaifiyata a gare shi , Allah ya bashi zabi sai ya zabi haduwa da Ubangijinsa ,

Ya Allah Arrafikul A'ala, ya Allah Arrafikul A'ala , lokacin rabuwa ya yi sai aka yi wasiyya kuma ya yi  ban kwana, duniya ta yi duhu sakamakon rabuwa da shi sai ga shi an shiga matsananci bakin ciki.

Wayyo Allah , abin mamaki da irin girman wannan bala'in da tsananin wannan musiban kai ba abin da ya kai wannan wahala ba wani lokaci da aka wuce shi mai nauyi irin wannan , hakika  wahayi ya yanke daga kasa sakamakon rasuwan Annabi Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi , duniya ta yi duhu .

(Muhammadu ba wani ba ne face Manzo hakika Manzanni kafin shi sun shude).