Hudubar idi na masallacin Annabi
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi 1-10-1441Ah /24/5/2020Ad
Na Shaikh Abdullahi dan
Abdurrahman Al-Buaijan
Huduba ta farko
Allah Mai girma Allah Mai girma, Ba abin
bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah Mai girma kuma Allah Mai girma kuma
dukkan yabo da godiya na Allah ne, Allah
ne Mafi girma Mai girma, dukkan yabo da
godiya masu yawa sun tabbata ga Allah, Tsarki ya tabbata ga Allah safiya da
maraice godiya sun tabbata ga Allah bisa datarwanShi da kyautatawanShi , godiya
bisa ga yalwan kyautanSa da baiwarSa dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah
wanda ya shiryar da mu zuwa ga musulunci ya kuma datar da mu zuwa ga azumi kuma
da tsayuwan dare dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya
kwararamana daga cikin taskokin kyautanSa , abinda ba ya iyakantuwa shi ne
wanda ya fi dacewa a bauta wa kuma shi ne yafi dacewa da a ambata kuma shi ne
wanda ya fi cancanta da a godewa kuma Allah mai girma ya shar'anta mana
shari'o'I da hukunce hukunce kuma ya sa sauki a ciki dukkan yabo da godiya sun
tabbata ga wanda ya fara kuma ya ke maidawa , Ma'aboci al'arshi Madaukaki , mai
yafiya kuma mai yawan gafara mawadaci abun godiya mai aykata duk abinda ya so ,
wanda ya shiryar da shi ne zai samu walwala kuma shi ne wanda ke kan daidai wanda
kuma ya baar to shi ne tsinanne daga rahama abun korewa wanda ya shiryar da shi
zuwa ga hanyan tsira to shi ne shiryayye .
Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai
Allahshi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya ga dukkan komai mai sheda ne shi
yayi ni'ma a gare mu da shedawa na tauhidi da kuma shaidawa cewa Muhammadu
bawanSa ne kuma ManzonSa ne zababbe cikin bayinSa Ma'boci manhaji shiryayye da
kuma abin bi wanda ya ke na daidai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
da iyalanSa da sahabbanSa salati na din din din har zuwa ranan alkawari
Bayan
haka :
Muna muku barka da ranan idi, Allah ya sa muku
albarka a cikin dukkan wani abu sabo ya sa ku walwala da bushara ya sa muku
kari, Allah mafi girma Allah mafi girma ba abin bautawa da gaskiya sai Allah
Allah shi ne mafi girma dukkan yabo da godiya naShi ne.
Ya ku musulmai , ban kwana irin na ramadana kafin 'yan
kwanaki ne mu ke fiskantan watan ramadana gashi a yau kuma muna mishi ban kwana
yana kokarin shudewa ya zama cikin zamani abin tarihi haka nan ne kuma lokacin ya
ke tafiya rayuwa shekaru na mutum su kare wata mai daraja ya tafi dararrakinsa
da abun rayawa da wuninsa abun dulmuya a cikin bauta gajiyansa ya tafi
wahalansa ya kare ladansa kuma ya tabbata in Allah ya so wata ne mai albarka da
falala da kuma alheri da kuma da'a wanda ranakunsa sun kare an kuma nade
ayyukansa masu rabauta sun ci riba sun masu kokari kuma sun
samu ganima, ina ma da mu san wadanda aka karma musu mu taya su murna,
mu kuma san wadanda aka maida musu jajanta musu!
Ya farin cikin wadanda suka rabauta! Hakika
Allah ya musu ilhama na tuba, ya datar da su ga da'a, muna rokon Allah ya karba
musu kuma ya basu daidaituwa a kan tafarki.
Ya kaiton wanda ya yi hasara, hakika sun rasa
alheri, an musu shamaki daga Ubangijinsu, damammaki na rayuwa sun kwace musu,
da lokuta na alheri basu ribace shi ba sai hasara da nadama, sai dai kofofin
tuba basu gushe ba suna bude ba a rufe su bayan ramadana,kuma Ubangijinmu Mai
daukaka da buwaya yana karbar tuba daga bayinSa a dukkan lokaci da wuri,
(Kace ya ku bayi na wadanda suka
barnata ma kawunansu!kada ku yanke tsammani daga rahamar Allah, lalle Allah na
gafarta zunubai gaba daya kuma shi Mai gafara ne Mai jinkai).
Ya ku musulmai!
Lallai na daga cikin alamu na karbar ayyuka
akwai sauyawa daga wani hali zuwa hali mafi kyau, to ku roki Allah tabbatuwa
akan daa har zuwa mutuwa, ku nemi tsarin Allah daga juyawar zuciya, da kuma
lalacewa bayan gyaruwa, abin mamaki da dabbancin kaskancin sabo bayan daukaka
na da'a, ya tabbata daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,(Lalle dayanku zai yi aiki irin na 'yan aljanna har sai ya
kasance tsakaninsa da ita zira'i sai littafinsa ya rigaya sai ya yi aiki irin
na 'yan wuta sai ya shigeta, kuma lalle dayanku zai yi aiki irin na 'yan wuta
har sai ya kasance tsakaninta da shi saura zira'i sai ya yi aiki irin na 'yan
aljanna si ya shige ta.)
Allah Mai girma Allah Mai girma, Ba abin
bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah Mai girma kuma Allah Mai girma kuma
dukkan yabo da godiya na Allah ne.
Ya jama'ar musulmai… [ fiskantar karamar idi da
farinciki da taya murna]
Muna muku murna da idin karamar sallah, hakika
Allah ya rubuta muku lada kuma ya yafe muku laifukan ku, ya gafarta muku
zunubai ya daga darajojinku kuma ya kankare muku kurakurai, ku godewa Allah ku
roke shi karbar ayyuka da tabbatuwa. Muna taya ku murna da kuka fifita yardar
Allah bisa ga jin dadi na duniya da sha'awe sha'awe, kuka kyautata kuma kuka
cika kuka yi abin da ya dace na ibada, kuka samu mafi girman sakayya in sha
Allahu, barkanku da samun yin azumi kuma barkanku da samun tsayuwa, barkanku da
yawaita ayyuka na da'a, barkanku da farin ciki na idi da kawa na idi da
walwala, ku ji dadi da duk wani abu da ya ke sabo.
Allah Mai girma Allah Mai girma, Ba abin
bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah Mai girma kuma Allah Mai girma kuma
dukkan yabo da godiya na Allah ne.
Ya ku bayin Allah! Yafiya da rangwami.
Lalle Allah ya cikamake azumi da idi karama mai
albarka kuma ya sanya ta cikin manyan alamomi na addini, na daga cikin sunnar
mafificin Annabawa da Manzanni a bayyana farinciki a tsakanin musulmai da
bayyana jin dadi da walwala da annashawa da kawa, to ku yada abubuwa na kauna kyawawa, da kalamai masu dadi, ku jefa duk
kayan kamshi da dadadawa.
ku yada
walwala a doron kasa da ku yi
dariya da sifa ta murmushi mai ban kaye, ku yi gaishe gaishe na idi domin yana
kara kauna ta kuma karfafi soyayya da 'yan uwantaka,
ku shigar da farinciki a zukata, ku binne
kyashi da bakinciki, ku shigar da farinciki ga iyalai da makusanta da makwabta,
ku yi wasici ga juna da gaskiya da rahama, ku tausayawa wanda ke doron kasa sai
wanda ke sama ya tausaya muku.
Yau rana ne na afuwa da kauda kai da rangwami,
wanda ke son afuwa da gafara daga Allah to ya yafe ya ya kuma yi afuwa ga
mutane, domin sakayya na kasancrwa ne da irin nau'in aikin da mutum yayi, Allah
Madaukakin sarki ya ce (su yi rangwame su yi afuwa,
shin ba ku son Allah ya gafarta muku)
(kuma lalle ne wanda ya yi hakuri ya
gafarta to shi wancan aiki haki yana daga manyan al'amura).
Ku yi
afuwa ga wanda ya yi zalunci ku dauke kai daga wanda ya muzguna.
(kuma ku yi gaggawa zuwa ga neman
gafara daga Ubangijinku da wata Aljanna fadinta sammai da kasa ne)
Yau rana ne na biyayya da kyautatawa,to ku
kyautata kamar yadda Allah ya kyautata zuwa gare ku Allah yana son masu
kyautatawa , a yau rana ne na sada zumunci , da kauna , ku sada zumuncin wanda
ya yanke muku ku bawa wanda ya hana ku , ku yafe wa wanda ya zalunce ku ba wai
mai sadarwa shi ne wanda mai rama abinda aka mishi ba na alheri , a yau rana ne
na sanin yakamata to ku yi wasici wa junan ku da masu rauninku ku yi musu
wasici da alheri ku tausayawa kananan ku , kuma ku girmama manyan ku , ku
kyautata zuwa ga talakawan ku , ku shigar da farin ciki a cikin zukatansu da
annashawa ku yaye musu bakin ciki da bacin rai kuma ku magance musu ciwonda
suka ji ku ji tsoron Allah ku kyautata ku sulhunta tsakanin ku kada shaidan ya
fitineku ku yi sulhu tsakanin 'yan uwanku .
An karbo daga Abu huraira Allah ya kara yarda a
gare shi ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya
ce:(ana bude kofofin Aljanna ranan litini da
alhamis sai a gafartawa dukkan wani bawa wanda ba ya hada Allah da wani sai
mutumin da kawai ya kasance tsakaninshi da dan uwan shi akwai gaba sai a ce da
shi a sararawa wadannan har lokacin da suka yi sulhu ku jira wadannan mutane
biyu sai sun yi sulhu ku jira wadannan mutane biyu har sai sun gyara tsakanin
su) Muslim ne ya rawaito .
To ku gyara kawunanku ya ku bayin Allah bisa ga
tsarkake zukatan ku da kuma aminci zukata ku jaddada alaka na kauna da soyayya
tsakaninku da tausayi imanin dayan ku ba zai cika ba har sai ya so ma dan uwan
shi abinda ya so ma kanshi kuma ku yi kyauta za ku so juna .
Allah mai girma , Allah mai girma , Allah mai
girma ba abin bautawa da gaskiya sai Allah , Allah mai girma Allah mai girma
dukkan godiya nashi ne .
Bayin Allah :
Lallai ku din nan 'yan uwa ne daga uba da uwa (A'adam
da Hawwa'u) sai dai shaidan yana iya rarraba tsakaninku ya jirkita zaman
lafiyan tsakanin ku da 'yan uwantakan ku hakika ya fidda mahaifan ku biyu daga
Aljanna ta hanyan rudi, ya byyana tsakaninku kuma adawa da kiyayya to ku yi
riko da igiyan Allah ku yi sulhu tsakanin 'yan uwanku ku jo tsoron Allah kada
ku rarraba kada ku cece ku ce sai ku dare karfinku ya tafi.
An karbo daga Abu huraira ya ce Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (kada
ku yanke zumunci kada ku juya wa juna baya kada ku yi gaba kada ku yi hasada
kada ku yi tajassusi (leken asiri) kuma kada ku yi bincike,kada ku yi munajasha
ku kasance bayin Allah 'yan uwan juna, ku kasance 'yan uwa kamar yadda Allah ya
umarce ku)Muslim ne ya rawaito.
Allah
Mai girma Allah Mai girma, Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah Mai
girma kuma Allah Mai girma kuma dukkan yabo da godiya na Allah ne.
Ya jama'ar musulmai… [Tasirin akida a tarbiya]
Lalle Allah ya zaba muku musulunci, to kada ku
mutu face kuna musulmi, to ku kiyaye tushen shi da rukunan shi, ''An gina musulunci akan abubuwa guda biyar , shaidawa ba
abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, da
tsaida sallah, da bada zakkah, da azumin ramadana da yin Hajjin dakin Allah''.
Ku kiyaye imani domin shine tushe kuma a kan
shi a ke gini, shine tsagoron addini da dalakin shi, shine (Imani da Allah da mala'ikunSa da littatafanSa da
MazanninSa da ranar lahira da imani da kaddara na alheri da sharri).
Ku yi kokari wurin murakabar Allah a kowani
zamani da kowani wuri, don shine hakikanin ihsani wato (ka bautawa Allah kamar kana ganinSa to in ba ka ganinSa
shi yana ganinka)
Ya ku bayin Allah Tauhidi shine tushen addini
kuma abin rikon shi mai karfi, kuma shine asali da ake gini a kan shi, da kuma
hukunce hukunce, bisa shi ne ake karbar ibada kuma ya inganta ko akasin haka, da ayyukan da'a da shi ne ake samun tsira na duniya da lahira
kuma shine hakkin Allah a kan bayi, An karbo daga Mu'azu dan Jabal ya ce na
kasance goye akan jaki da ake kira Ufairu a bayan Annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi, yace : sai yace ya Mu'azu ko ka san hakkin
Allah akan bayi da hakkin bayi a kan Allah? Sai na ce : a'a Allah da ManzonSa suka fi sani, sai yace
: (Hakkin Allah akan bayi shine su bauta masa
kada su hada shi da wani, hakkin bayi kuma a kan Allah shine kada ya azabtar da
wanda ba ya hada shi da wani.yace sai nace ya manzon Allah ba zan yi wa mutane
albishir ba? Sai yace a'a kada ka musu albishir su saki jiki) Buhari
ne ya rawaito.
Lalle tauhidi shine mabubbuga na hadin kai da
fahimtan juna da 'yan uwantaka. Da shi ne ake samun haduwar kalma kuma al'uma
ke zama tsintsiya madaurinki daya. Da shi ne ake zartar da alakoki ko a kulla
wani abu. Da shi ne al'uma ke iya tsayawa a kan kafanta a samu zaman lafiya.
Ku godewa Allah bisa ga shiryarwa kuma ku roke
shi tabbatuwa a kanta.
Allah Mai girma Allah Mai girma, Ba abin
bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah Mai girma kuma Allah Mai girma kuma
dukkan yabo da godiya na Allah ne.
Ya ku
musulmai! [Tasirin ibada da muamaloli]
Ku maida hakkoki zuwa ga ma'abotanta, ku sauke
abin da ke kan ku nauyi, ku bada amana ga ma'abotanta, ku bawa dan kodago
hakkinsa kafin zufansa ya bushe,
An karbo daga Abu Huraira Allah kara yarda a
gare shi ya ce : (Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( wanda ya kasance yana da wani abu na
zalunci da ya ci wa dan'uwansa na mutunci ne ko waninsa to ya warware daga gare
shi tun a yau kafin ya kasance dinari ko
dirhami in ya kasance yana da aiki na
kwarai sai a dauka daga gare shi gwargwadon abin da ya zalunta, in kuma bai da
kyawawa sai a dauka daga laifukan sahibin nasa sai a dora masa.) Buhari
ne ya rawaito.
Ya ku bayin Allah! Ku cika alkawura da kuma yarjejeniya a hakkoki
da muamala da suran abubuwa na cinikayya cikin hukunce hukunce da aka dora muku
na hakkoki (Duk wanda ya cika abin da ya yi wa Allah
alkawari to zai bashi lada mai girma).
Domin
hakan na cikin abin da ke karfafa zumunci da alaka, kuma ya kara kauna da
soyayya, ya kuma kara aminci da tausayawa juna,
An karbo daga nu'uman dan Bashir Allah ya kara
yarda a gare shi ya ce : na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi yace : (Lalle halal a bayyane ya ke
kuma haram a bayyane ya ke a tsakanin su akwai wasu al'amura masu rikitarwa, da
yawa daga cikin mutane basu san su ba, duk wanda ya tsoraci shubhohi to ya
kubutar da addininsa da mutuncinsa, to duk wanda ya fada cikin shubhohi to ya
auka cikin haram, kaman mai kiwo ne yana kiwo ne a bakin iyaka yana kusa da ya
fada a ciki, ku saurara ! lalle kowane sarki na da iyakansa,ku saurara iyakan
Allah shine abin da ya haramta, ku saurara lalle a cikin jiki akwai wata tsoka
idan ta gyaru to dukkan jiki ya gyaru, idan ta baci to dukkan jiki ya baci, ku
saurara ita ce zuciya).
Ku bi umarnin Allah, ku kame daga abin da ya
haramta,ku nesaci shubhohi ku gyara niyoyi, ku sabonta zumunci da kauna da soyayya
da alakoki.
Allah Mai girma Allah Mai girma, Ba abin
bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah Mai girma kuma Allah Mai girma kuma
dukkan yabo da godiya na Allah ne.
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah da
ya yalwata ni'imomi, ya kiyaye mu daga azaba, ya tula mana mamako na karamci.
Allah Mai girma Allah Mai girma, Ba abin
bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah Mai girma kuma Allah Mai girma kuma
dukkan yabo da godiya na Allah ne.
Ya ku bayin Allah ! ku ji tsoron Allah a
sirrace da bayyane, ku lazimci Alkur'ani da sunnoni, ku nesaci alfahasha wanda
ya bayyana da abin da ya boyu, ku nesaci shubuhohi, Da shubuhohi da sabuba na
fitintinu ko Allah zai dauke muku bala'i da jarrabawa.
Allah Mai girma Allah Mai girma, Allah Mai
girma, Ba abin bautawa da gaskiya sai
Allah kuma Allah Mai girma kuma Allah Mai girma kuma dukkan yabo da godiya na Allah ne.
Ya jama'ar
musulmai! [ Ayyukan idi karama]
Allah ya shar'antawa bayinSa da su cike azumin
ramadan da zakkan fidda kai, da sallar idi da kabarbari da ambato, girmamawa da
godiya ga Allah bisa ni'imar cikan azumi da tsayuwa, hakika sharia ta wajabta zakkan
fidda kai ga musulmai wanda tsarkaka ne ga mai azumi daga wass, da batsa kuma
abinci ne ga miskinai, lokacinta shine kafin fita zuwa sallar idi, duk wanda ya
jinkirtata to ya wajaba a gare shi ya gaggauta fitar da ita, duk wanda ya fitar
kafin sallah to zakka ce a gare shi ,karbabba, wanda kuma ya fitar bayan idi to
ita sadaka ce daga cikin sadakoki, An karbo daga dan Umar Allah ya kara yarda a
gare shi shi da mahaifin shi ya ce :(Manzon Allah
ya wajabta zakkan fidda kai sa'i guda na dabino ko kuma sa'i guda na sha'iri
bisa ga bawa da da na miji da mace da kuma yaro da babba na daga musulmai).
Buhari ne ya rawaito.
Na daga cikin manyan alamomi na addini ga
musulmai a ranar idi kabbarori, kuma sunna ne ga maza da mata, tun daga faduwan
ranan karshe na ramadana Allah Madaukakin sarki ya ce ; (Kuma don ku kammala adadi kuma ku girmama Allah bisa shiryar
da ku da yayi ko za ku gode)
Allah Mai girma Allah Mai girma, Ba abin
bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah Mai girma kuma Allah Mai girma kuma
dukkan yabo da godiya na Allah ne.
Allah Mai girma Allah Mai girma, Allahu mai girma, Ba abin bautawa da gaskiya
sai Allah kuma Allah Mai girma kuma Allah Mai girma kuma dukkan yabo da godiya na Allah ne.
Ya ku
musulmai!
Hakika uzuri ya killace ku a wannan yanayida
aka samu kai a ciki da naku sa rashin halartar idi, to ku yi kwadayin yin ta a
gidajenku, kuma lokacinta na farawa ne tum daga dagowar rana har zuwa zawali, zai yi kabbarori bakwai
araka'ar farko, a raka'a ta biyu kabbarori biyar, sai ya karanta suratul q wal
kurani majid ko sabihisma rabbika a
raka'ar farko, a raka'a iktarabatissaatu wan shakkal kamar ko hal'ataka hadisul
gashiya,ko da abin da ya sauwaka na daga kur'ani.
Allah Mai girma Allah Mai girma, Allahu mai girma, Ba abin bautawa da gaskiya
sai Allah kuma Allah Mai girma kuma Allah Mai girma kuma dukkan yabo da godiya na Allah ne.
Ya taron mata!
Lalle
Allah Mai hikima ne a cikin gudanarwarsa, Masani ne cikinhalittunsa da
mulkinsa, adalci ne al'amarinSa da hukuncinSa. Ya tura sako da bayani ya saukar
littafi don mutane su tsaida gaskiya da mizani ta ti umarni da adalci yin adalci
ya yi hani ga zalunci da tawaye hakki sai ya ce : (lalle na umartanku da ku maida amana zuwa ga ma'abotanta,
idan kuka yi hukunci tsakanin mutane to ku yi hukunci da adalci.)
Hakika Allah ya yi adalci tskanin maza ga mata
a shariarSa da hukunce hukuncenSa ya kuma kebance kowannensu da abinda ya dace
da halittarsa da kudurarSa da karfinsa ya daidaita tsakaninsu a komabayan haka
na daga magana da karramawa da alkawarin lada da azaba da kuma dora nauyi na
sharia.
Hakika musulunci ya bada kariya ga mace ya
shar'anta hakkokinta ya daukaka matsayinta ya yi umarni da a bata kulawa a kuma
ciyar da ita a mutunta tam a gyara a katange ta, hakika Annabi ya yi wasiya ga
mace a Hajji bankwana, na daga cikin abin da ya ambata (Ku saurara ku yi wasiyya ta alheri game da mata, lalle
su mataimaka ne a gre ku,, ku saurara lalle kuna da hakki a kan matayenku, su
ma suna da hakki a kan ku,
Hakkinsu mata a kan ku ku kyautata zuwa gare su cikin tufatar da su
, Tirmiz ne ya rawaito.
Ya ku taron mataAllah!
Gudumawar da mace za ta bada ranar idi kamar
gudumawar da na miji zai bada ne, zata yi tarayya wurin yada farinciki da
karfafan dankon zumunci da afuwa da rangwami da gyara, da tsarkake zukata da
karfafan alakoki da hamaka kauna da sada zumunci da yin ziyzrce ziyarce, da
taimakawa talakawa da miskinai da marasa galihu da yin ma'arufi. (ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicce ku daga rai guda ya halitta
masa matarsa daga gare shi ya kuma yada daga gare su maza masu yawa da mata, ku
ji tsoron Allah da ku ke magiya da shi ku ji tsoron mahaifa, lalle Allah ya
kasance a gare ku mai tsaro).