الأحد، 22 مارس 2020

KIYAYE HARSHE A MUSULUNCI


Hudubar Masllacin Annabi na SheikhAbdulmuhsin Bin Muhammad Alkasim 4-7-1441AH / 28-2-2020 AH
Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna gode maSa kuma muna neman taimakonSa
Muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu  da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, wanda ya batar kuma babu mai shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya,kuma na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa. Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa.
Bayan haka, ku ji tsoron Allah -ya ku bayin Allah- cancancin tsoronSa, duk wanda ya ji tsoron Ubangijinsa zai tsira wanda ya bijire daga ambatonSa zai fadi.
Ya ku musulmai :
Ni'imomin Allah ga bayi basu kididdiguwa, (kuma duk wani abu da ke gare ku na ni'ima to daga Allah ne).
Harshe na daga cikin ni'imomi masu girma da wasu ludufa na daga aikin Allah masu ban mamaki, Allah ya baiwa da shi ne ga bayinSa sai yace :(Ase bamu sanya idanuwa biyu gare shi ba da harshe da lebba biyu)?
da shi ne ilimi da bayani da karrama Dan-Adam ke samuwa Allah Madaukakin sarki ya ce :(Mai-rahama, ya koyar da Alkur'ani, ya halicci mutum, ya sanar da shi bayani.)
Duk abin da ya ke fada ana kiyaye shi a sahifarsa wacce da ita zai hadu da Ubangijin Shi ranar Alkiyama, Allah Madaukakin Sarki ya ce :(Ba ya furuci da wata magana face like da shi akwai mai tsaro halartacce) sabo da haka ne Allah ya umarci bayinSa da su fadi magana madaidaiciya, sai yace : (ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah ku fadi magana madaidaiciya) kamar kuma yadda ya umarce su da fadi magana mafi  dadi mafi kyau, (kuma ka ce wa bayiNa su fadi kalma wacce take mafi kyau)
Na daga cikin wajibabbun imani kiyaye harshe face daga alheri, Manzon Allah tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Duk wanda ya kasance yana imani  da Allah da ranar lahira to ya fadi alheri ko ya yi shuru.) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
   Allah ya yabi bayinSa muminai da suke bijirewa wasa na fadi ko aiki sai yace : (Da wadanda suke juya baya ga lagawu(wasa).  
Musulmi shine wanda ya kiyaye harshensa, Manzon Allah tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Musulmi shine wanda musulmai suka kubuta daga sharrin harshensa da hannunsa).  Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Ta hanyar kiyaye shi ne ake samun fifikon matsayi tsakanin bayi, an tambayi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wa ya fi alheri cikin musulmai sai yace shine wanda musulmai suka aminta daga harshensa da hannunsa).Muslim ne ya rawaito.
Kuma Aljanna sakayya ne ga wanda ya kiyaye harshensa. Manzon Allah tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Wa zai kiyaye min bakinsa da farjinsa  na lamunce mishi aljanna). Buhari ne ya rawaito.
Harshe karamin abu ne amma yana da amfani mai yawa.kuma ya kan iya kasancewa mai tsananin cutarwa sabo da haka Annabi ya nemi tsari daga sharrinsa sai yace : ,  (Ya Allah ina neman tsarinka daga sharrin harshe na) Abu Dauda ne ya rawaito.
Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tsoracewa sahabbansa da al'umarsa shi, Sufyan dan Abdullahi Assakafi Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :Nace ya Manzon Allah me ka fi tsorace min? sai ya rike harshensa ya ce :wannan).Tirmizi ne ya rawaito.
Bisa tsoronsa ne  sahabbai suka tafi, Abubakar Allah ya kara yarda a gare shi ya fitar da harshensa sai ya ce : (wannan shi ya kai ni ya baro ni).
Ibnu Abbas ya kasance yana rike harshensa sai ya ce :(kaitonka ka fadi alheri za ka rabauta ko ka yi shuru daga mummuna zaka kubuta, in ba haka ba to ka sani zaka yi nadama).

Harshe hadarinsa na da girma a duniya da lahira, sau da yawa kalma guda kan bata rayuwar mutane, Ibnu Mas'ud Allah ya kara yarda a gare shi yace : (Ba wani abu da ya fi bukatar kulle shi a kurkuku na tsawon lokaci kamar harshe na).   
Magana kan halaka ma'abocinsa har ya hadu da Allah yana Muflisi Manzon Allah tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi ya ce : (ko kun sansa muflis sai suka ce Muflis shine wanda bai da dirhami ko wani abu na kayan jin dadi, manzon Allah yace : Lalle muflis a cikin al'uma ta shine wanda zai zo da sallah da azumi da zakka, ya zo a halin ya zagi wannan yayi kazafi ga wannan, ya ci dukiyar wannan ya zubar da jinin wannan ya daki wannan, sai a bawa wannan daga kyawawansa, wancan ma a bashi daga kyawawansa, idan kyawawansa sun kare kafin a kare biyan bashin da ke kansasai a dauko daga laifukansu a dora kansa sannan a jefa shi wuta.) Muslim ne ya rawaito.
An tambayi Annabi game da abin da ya fi shigar da mutane wuta sai yace baki da farji) Tirmizi ne ya rawaito.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :(lallai bawa zai yi magana da kalma ba zai bayyana mishi (hadarinta) ba, zai zame cikin wuta a dalilinta fiye da nisan mahudan rana da mafadanta) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Mafi girman laifi na harshe shine kiran wanin Allah da sanya mishi kishiya Allah Madaukakin Sarki ya ce :(wa nene ya fi bata sama da wanda ya ke kiran wani komabayan Allah wanda ba zai amsa mishi ba har zuwa eanar alkiyama a halin su sun gafala daga adu'arsu)
(Duk wanda ya mutu a halin yana kiran wanin Allah to zai shiga wuta.) Buhari ne ya rawaito.
Na daga cikin rokon wanin Allah akwai neman ruwan sama ta hanyar amfani da taurari, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : Allah Madaukakin sarki ya ce a hadisul kudsi ( An wayi gari cikin bayi na akwai mai imani da ni da kuma mai kafurci, to duk wanda yace : Mun samu ruwa ne da falalanAllah da rahamarSa to wannan shine wanda ya yi imani da ni kuma ya kafurcewa taurari)  Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Neman tsari daga wanin Allah ba abin da ya ke karawa mai yinsa sai tsoro da rauni, Allah Madaukakin Sarki ya ce : (Kuma lalle ne shi, wasu maza daga cikin mutane sun kasance suna neman tsari da wasu maza daga cikin aljanu, saboda haka suka kara musu girman kai).
Na daga cikin shirka da Allah a magana akwai rantsuwa da wanin Allah, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :( wanda ya rantse da wanin Allah to  hakika ya kafirta ko kuma ya yi shirka).Muslim ne ya rawaito
(wanda ya rantse da wani addini ba musulunci ba bisa karya da gangan to shi ya zama kamar yadda ya ce ) bukari ne ya rawaito
(wanda ya rantse da amana to baya tre da mu) abu dauda ne ya rawaito
Allah tsarki ya tabbata a gare Shi ya na da cikakken kamala na mulki na saki waiwai wanda ya sa suna irin wanda Allah ya kebanta da shi  to Allah zai kaskantar da shi manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ya ce : (mafi kaskancin suna a wurin Allah shi ne mutumin da zai sa suna sarkin sarakuna ba wani mai mulki sa Allah) bukari da muslim ne suka rawaito al'mari na Allah ne shi shi kadan shi ba a' hada shi da wani a mashi'arSa tsarki ya tabbata a gare Shi a ta bangaren daidaitawa a lafazi ne ko a ma'na Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ya ke cewa (kada ku ce Allah ya so wane ma ya so sai dai ku ce Allah ya so sa'an nan wane ma ya so) Abu Dauda ne ya rawaito.
Kaddara kudura ce daga gurin Allah da imani da shi kuma rukuni ne cikin rukunan imani, baa cewa ina ma da na aikata kaza da kaza zai faru da kaza," ba don ba" na bude aikin shaidan.
Fushi bisa abin da Allah ya kaddara na daga magana na cikin al'amarin jahiliyya.
(mai kukar mutuwa in bata tuba ba daga aikinta zata tashi a ranar alkiyama tana tare da rigar karfe na harshen wuta). Muslim ne ya rawaito.
       Allah ke tafiyar da dare da wuni, kuma zagin zamani na warware imani ko kuma yana raunana shi,
 Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ya ke cewa (kada ku zagi zamani domin Allah shine zamani). Muslim ne ya rawaito.
Wanda ya munana zato ga Allah ya kuma yankewa halittun Allah tsammani daga rahamarSa, to hakika ya kai kansa ga ukuba ta Allah, wani mai ibada a cikin banu isra'ila yace da wani mai sabo a cikinsu : (wallahi Allah ba zai gafarta wa wane ba, sai Allah yace da shi wane ne ya ke min shishigi da rantsuwar bazan yafewa wane ba, to lalle hakika na gafarta masa kai kuma na rusa aikinka) Muslim ne ya rawaito.
Abu Huraira –Allah ya kara yarda a gare shi yace : "Na rantse da wanda rai na ke hanunSa ya fadi kalmar da ta halaka masa duniyarsa da lahirarsa"
(Wanda yace mutane sun halaka to shine mafi halakarsu)
Sanin ilimin gaibi ya kebanta ne ga Allah subhanahu wa taala, Allah Madaukakin Sarki ya ce : (Kace babu wanda ya san abin da ya faku a cikin sammai da kasa face Allah),
  (wanda ya je gun mai duba ya tambaye shi daga wani abu  to ba zaa karba mishi wata sallah har dare arba'in). Muslim ne ya rawaito.
(wanda ya je gun boka ko mai duba kuma ya gaskata shi cikin abin da ya ke fadi, to hakika ya kafirta da abin da aka saukarwa Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)Ahmad ne ya rawaito.
Na daga cikin mafi girman muharamai fadin magana game da Allah ba tare da ilimi ba,
Allah Madaukakin Sarki ya ce : (Kace abin sani Ubangiji na ya haramta alfahasha abin da ya bayyana daga gare su da abin da ya boyu da zunubi da rarraba jama'a ba , da wani hakki ba kuma da ku yi shirki da Allah ga abin da bai saukar da wani dalili ba gare shi , kuma da ku fadi abin da ba ku sani ba , ga Allah ) izgianci da addini ya na  fitar da ma'bocin shi daga cikin addinin Allah madaukakin sarki ya ce : (Ka ce shin da Allah da kuma a'yoyinSa da ManzonSa kuka kasance kuna izgilanci ?) (kada ku kawo wani uzuri hakika kun kafirta a bayan imanin ku)
Kuma karya na daga cikin munanan zunubbai da alfasha masu aibi kuma shi ne asalin dukkan sharri shi ne kuma ya ke cikin alamomi na munafunci yana shiryarwa zuwa ga fajirci , lallai fajirci yana shiryarwa zuwa ga wuta mutum ba zai gushe ba ya na kirdadan karya har a rubuta shi a wurin Allah makaryaci .
Mafi munin karya shi ne wanda ya kasance a kan Allah da Manzon Sa Allah subhanahu wa ta'ala yana cewa (kuma a Ranar Kiyama kana ganin wadanda su ka yi karya ga Allah fuskokinsu suna masu yin baki . Ashe, babu mazauni a cikin jahannama ga masu girman kai ) Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( duk wanda ya min karya da gangan to ya shirya makomansa a cikin wuta) Muslim ne ya rawaito ,( duk wanda yarantse bisa karya yan mai tune ga al'marin da ya shudai to rantsuwanSa rantsuwa ce ta gamus (nitsatstsiyan rantsauwa cikin zunubai )
(duk wanda ya rantse bisa ga dukiyan mutum musulmi ba tare da hakki ba zai hadu da Allah ahalin Allah ya na fushi da shi ) Bukari da Muslim ne suka rawaito , na daga cikin karya shi ne iddia'a'I wurin dangantaka Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(ba wani  mutumin da zai jingina kanshi ga wani mahaifinshi a halin yana sane face ya kafurta ,ko ya yi da'wan wani dangin da ba nashi ba to ya shirya makomansa a wuta ) Bukari da Muslim ne suka rawaito .
Na daga cikin manyan zunubbai shaidan zur Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Ashe ba zan baku lbarin mafi girman zunubbai ba? sau uku sai suka ce iye ya Manzon allah sai ya ce : hada Allah da wani da kuma cin zarafin iyaye sai ya zauna da yana kishingide ne sai ya ce ku saurara da fadin zur bai gushe ba yana ta maimaitata har muka ce ina ma da ya yi shuru ,) Bukari da Muslim ne suka rawaito . dukkan  musulmi a kan musulmi haramun ne jininSa sa dukiyanSa da mutuncinSa , na daga cikin manyan zunubbai mutun ya zagi iyayensa suka ce : ya Manzon Allah yaya mutun zai zagi iyayenSa ?( sai ya ce iye , (ya zagi baban wani wanin kuma ya zagi babanshi ya zagi uwar wani wanin kuma ya zagi mamanshi ) Bukari da muslim ne suka rawaito .
Na daga cikin abubuwa masu halakarwa akwai kazafin mata katangaggu gafalallu mumunai Allah madaukakin sarki ya ce (lallai ne wadanda suke jifar mata masu kamun kai gafilai, muminai an la'ne su a cikin duniya da lahira kuma suna da azaba mai girma) kage jifan wanda ya barranta ne daga abinda bai tare da shi Allah madaukakin sarki ya ce (kuma wanda ya yi tsiwir-wirin  kuskure ko kuwa zunubi sa/annan kuma ya jefi wani barrantacce da shi to lalle ne ya tattali kirkiran karya da zunubi bayyananne)
 Cin naman wani shine ambaton dan'uwanka da abin da bai so, kuma yana cikin manyan zunubai Allah madaukakin sarki ya ce (kada sashenku su yi giban sashe) Ibnu Abbas Allah ya kara yarda a gare shi shi da mahaifin shi- yace : (Allah ya haramta giba kamar yadda ya haramta mushe)
 Na daga cikin laifuka na harshe kai komo da annamimanci tsakanin halittu Allah Subhanahu yake cewa : (kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, walakantacce. Mai zunde mai yawo da gulma mai hana alheri mai zalunci mai zunubi).
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Mai annamimanci ba zai shiga a ljanna ba) Bukari da Muslim ne suka rawaito.
Yahya bin kasir Allah ya mishi rahama yace :(Mai annamimanci kan bata cikin saa guda abin da mai sihiri ke batawa a shekara guda.)
Zagin Musulmi fasikanci ne (ba wani da zai jefi wani da fasikanci ko ya jefeshi da kafurci face ta dawo zuwa gre shi muddin bai kasance wan nan ma'bocin shin hakan ya ke ba) Bkari ne ya rawaito tsine wa mumini kaman kashe shi ne duk wanda ya tsine wa wani wanda ba ahlinta ba to tsinuwan za ta dawo kanshi mumini bai kasance mai yawan suka ba ko yawan tsinuwa ba Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (lallai masu yawan tsinuwa basa kasancewa masu ceto kuma basa zama masu shaida a ranar alkiyama ) Muslim ne ya rawaito .
Izgilanci ga halittu yana cikin nau'in girman kai ya isa sharri mutum ya rena dan uwanshi musulmi Allah madaukaki ya ce (ya ku wadanda suka yi imani kada wadansu mutane su yi izgili game da wadansu mutane mai yiwuwa ne (abin yi wa izgilin) su kasance mafifita daga gare su (masu izgilin), kuma wadansu mata kada su yi izgili game da wadansu mata mai yiwuwa ne su kasance mafifita daga gare su , kuma kada ku aibanta kanku , kuma kada ku jefi juna da miyagun sunaye na lakabobi tir da suna na fasicci a bayan imani kuma wanda bai tuba ba to wadannan su ne azzalumai) abubuwa guda hudu ya cikin abubuwan jahiliyya alfahari da dangi da suka da nasaba da kuma neman saukan ruwa ta hanyan amfani da taurari da kuma kukan mutuwa .
Kamar yadda musulunci ya harrama zagin rayayyu haka ma kuma ya harrama zagin matattu Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (kada ku zagi matattu, domin sun riga sun shude zuwa ga abinda suka kaddamar) Bukari ne ya rawaito . kai musulunci ya hana zagin iska ma da ma zazzabi da kuma dabbobi da ma wasun hakan duk wanda ya bayyana mummuna to hakika ya kai kanshi ga tonon silili daga wurin Allah Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (dukkan aiumma na suna samun waraka amma banda masu bayyana sabo) Bukari da muslim ne suka rawaito .  

KARI'A DAGA CUTAR KORONA


Hudubar Masallacin Annabi na shaikh Salah Bin Muhammad Albudair 11-07-1441

Hudubar farko
Ya ku musulmai
Hakika an yi suka ga duniya a huhunshi da wani irin cuta na korona wanda ya cire fatan ido saboda tsana ya ragewa jiki karfinta ya yaki garurruwa kuma ya shigeta ya yi kaca kaca da yanayi ya keta farfajiya kuma ya lalata iska tsarki ya tabbata ga wanda ya ke saukar da cuta kuma ya bada izini da yaduwa idan ya so ba don komi ba sai don jarabawa da godawa da kuma tunatar wa da tsoratarwa to ku tsorata zuwa ga ambaton Allah tare da neman gafaranShi ku koma zuwa ga Allah ku nemi kariya daga gareShi ku kiyaye ambaton Allah ku roki Allah da addu'ui wanda suka tabbata daga sunna ba abunda ya fi amfani wajen magamce annoba   kamar adduwa da kuma gaskiyar komawa ga Allah
 ya ku musulmai:
 wadan nan annoban suna kasancewa ne san nan kuma suna zama ba komai ba so dayawa annoba ta kan sauka kuma ta zo ta fi ta bayyana kuma ta zo ta boyu ta bibiyo kuma sannan ta zo ta juya baya , an karbo daga Anas dan Malik Allah ya kara yarda a gare shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(fatan alheri na burgeni sai suka ce menene fatan alheri sai ya ce : kalma mai dadi) Bukari da muslim ne suka rawaito larabawa suna ambaton abu na dafi da mai lafiya suna ambato abu karyayye da wanda aka mikar da shi aka gyara shi ba don komi suke yin hakan ba sai don neman fatan alheri suna ambaton mutane masu tasowa ga tafiya kafila saboda fatan alheri Allah ya dawo da su lafiya ma'na ana fatan dawowansu , to ku yada abinda ya ke na fatan alheri da kuma natsuwa kada dayanku ya zama na kamar raidiu ma'na mai yada abinda ya ji ko kuma mutumin zai falga ya firgita mutane a duk lokacin da ya ji wani labari sai ya yada shi ya baza shi
ya ku musulmai :
Ku ji tsoron cututtuka da za su iya cutarwa da wurarenda annoba su ke, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (duk wanda ya ji tsoron sharri to za a bashi kariya daga gare ta) Ibnu abiddunya ya fito da shi ga hadisin abu huraira yanada kuma shahid da za su karfafeshi .
Ku rufe fusakanku yayin atishawa ko tari ku rufe da hankacif da makamantansu domin kada dayan ku ya cutar da abokin zaman shi ta hanyan tartsatsin da ke fita daga bakinsa ko hancinsa da wadannan kwayoyin cuta wanda ke yaduwa ta hanyan atishawa ko kuma tari ana iya samun yaduwar da umarnin Allah ta hanyan shakan numfashin burbushin kwayoyin  cututtuka ta iska da kuma ba haya da suka barbazu na mutumin da ke tare da wannan cutan An karbo daga abu huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (idan dayanku ya yi atishawa to ya saka tafin hanunshi akan fiskanshi kuma yayi kasa da sautinshi) Hakim ne ya fito da shi  , ku wanke hannaye kafin cin abinci da bayan shi da bayan biyan bukata (bayan zagawa ban daki) da bayan shafan wanda ake tsoron yaduwan cutan ta hanyan tabashi da duk wani abinda ya taba hannaye biyu na cuta na daga zufa ne ko kuma na kazanta ko kuma ko wani abu makamancin haka , An karbo daga A'isha Allah ya kara yarda a gare ta ta ce:( Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata  a gare shi ya kasance idan ya nufi ci ko sha a halin yana halin mai janaba  sai ya wanke hannayenshi san nan sai ya ci ko ya sha)Imamunnasa'I ya fito da shi , an karbo daga Abu huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (duk wanda ya kwana a hanunshi akwai gamru bai wanke ba wani abu ya same shi to kar ya zargi kowa sai kanshi) Ahamad  ne ya fitar da shi.
Kuma gamru shi ne warin abinci ko danshin abinci da maikonsa ko dankonsa domin kananan kwari su kan iya nufoshi da wasu abubuwa masu dafi a halin mutum yana bacci sai su cutar da mutum ko su harbeshi ko su ma mishi illa su sa mishi rashin lafiya
Ya ku musulmai :
Yin shamaki daga wanda cuta mai raba ke tare da shi bisa ala'da ba laifi  an karbo daga Abu huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (ka gujewa kuturu kamar yanda za ka gujewa zaki) Bukari ne ya fito da shi .daga sharid dan suwaid alssakafi ya ce : ya kasance cikin wasu tawaga daga sakif wani mutumi kuturu sai Annabi ya tura zuwa gare shi yana mai cewa (lallai mu mun karbi  mubaya'anka amma ka kom)Muslim ne ya fito da shi , Annabi bai mishi mubaya'a ta hanyar runguma ba ko kuma hada jiki ba ko kuma fiskanta ba saboda cakudayya da mai kuturta na daga cikin sabuban yaduwa a ala'dance , masu tantancewa cikin malaman ilimi su tafi akan cewa kutare idan sun yawaita ana iya hana su zuwa masallatayya da wuraren sallan juma'a har sai lokacin da aka tabbatar ba zai  raba ba , ba zai yadu ba wasu daga cikin malaman ilimi suka ce game da kuturtako kutare to idan sun yawaita za a iya akama musu guri na daban kamar yanda aka yi da marasa lafiyan makka , kuma an karbo daga Abu huraira Allah ya kara yarda a gare shi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(kada a shigar da marasa lafiya cikin masu lafiy) Bukari da Muslim ne suka rawaito , shi mara lafiya shi ne ana nufi a nan wato  rakumin da ya ke mai cuta shi kuma mai lafiya a nan ana nufin rakumin dfa ya ke ingantacce bai da cuta Annabi ya hana a hada su rakuma marasa lafiya tare da masu lafiya domin  tsoron yaduwan cutan da kuma kiyayewa daga juyawa na cututtukan da kuma annoba kuma annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi umarni da cewa idan annoba ta auku a gari mutum ba ya ciki to kada ya shiga garin idan kuma ya kasance yana ciki kada ya fita daga garin domin guje mata , an karbo daga usama dan zaid Allah ya kara yarda a gare shi shi da mahaifinshi ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (annoba wani tsawatarwa nr ko azaba ne Alla ke turota zuwa ga banu isra'ila koma wadanda su ke kafun su idan kun ji ta a kasa to kar ku je garin idan kuma ta faru a kasa kuna cikinta to kar ku fita daga garin domin tsoronta) Bukari da Muslim ne suka rawaito .
Ya ku musulmai :
Mustahabbi ne kada mutum ya sha sauran mara lafiya wanda cutansa na raba a ala'dance saboda  daukan kariya abu ne da shari'a yayi umarni da shi.
(Annabi ya hana game da sha daga bakin tulu) Bukari ne ya rawaito shi , a wurin Hakim kuma ya ce (saboda hakan yana doyayashi) a wurin Tirmizi kuma (Annabi ya hana a numfasa a cikin kwano ko kuma a hura a cikinshi ) Ibnu hajar ya ke cewa : (saboda ta iya yuwuwa numfasawan ya fito tare da wani nyawu ko majina ko wani tartsatsi mara kyau sai ya bashi wani wari da bayi da dadi sa ya kazantar da shi ko ko waninsa shi abin shas din)'' ya kare .
Amma hadisin da ya zo na cewa nyawun mumini ga mumini waraka ne ko kuma sauran mumini waraka ne ma'na (sauran ruwan da mumini ya sha ya rage) to wannan hadisi ne na karya kirkirarre ba yi da asali .
Ya ku musulmai :.
Ku rufe kwanuka ku daure bakin jaka saboda tsoron annoba da cuta da kiyayewa daga kananan dabbobi masu cutarwa da kuma dafi , an karbo daga Jabir dan Abdullahi ya ce na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce yana cewa (ku rufe kwanuka ku daure bakin jaka domin a shekara akwai wani dare da annoba ke sauka baya wucewa a kwano da ke bude ba marfi face sai ya sauka ko kuma jaka da ba a daure ba sai annoban ya sauka a cikin shi) Muslim ne ya rawaito.
Allah ya kiyaye mu da ku daga masu bijirowa munana da kuma abubuwa masu sauka na bala'I ina fadin abunda ku ke ji kuma ina neman gafaran Allah ku ma ku nemi gafaranShi lallai shi mai karban tuba ne ga masu komawa gare shi       


Huduba ta biyu
Ya ku musulmai :
Runguma da sumbatan juna abu ne da ya halatta sai dai likitoci sun  yi hani game da shi a wannan zamani da fairos korona ya bayyana saboda kiyayewa daga yaduwan shi ,shi wannan annoba da kuma kula da hakan yana cikin hikima da kuma hankali da kuma fikhu malaman fikhu sun yi amfani da maganan likitici amuntattu a cikin dayawa daga cikin hukunce hukunce kaman fadin imamu shaf'I game da ruwa da aka sa shi a rana ya ce : bana karhanta ruwanda aka dumama shi da rana sai dai idan ta bangaren likitoci  ne suka karhanta .
ya ku musulmai :.
Na daga cikin kariya da musulunci ya yi nuni zuwa gare shi shi ne kiyaye jikuna da haramcin cin abunda ke da fika na daga zakanyu da kuraye ko kerkece da kare da  kuma kenwa da makamantansu da dukkan wani abu mai faracuna na daga tsuntsaye kamar shaho da jalbe haka nan kuma da cin abinda ya ke cin mushe da kazanta da najasa kamar alhanzir da cin dukkan wani abun kazanta kamar duji da hudahuda da da kuma jamagu da birrai da kwari da zanbur da makamantansu na daga dabbobi wadanda ba sa cikin abincin musulmai an karbo daga ibnu Abbas Allah ya kara yarda a gare shi , shi da mahainsu ya ce : Manzon Allah ya yi hani game da cin sdukkan wani abu mai fika na daga zakayyu da kuma masu faracuna na daga tsutsaye)  Imamu muslim da ibnu hibban suka fito da shi kuma lafazin nasa ne wadannan namukan sun kumshi wasu kwayoyin cuta ne da tsutsotsi da wasu dufailiyyat da suke sanya rashin lafiya wanda ke sabbaba hadari ga hankali da kuma fahimta da jiki abun mamaki da irin girma na musulunci, abun mamaki da irin falalolinshi da abubuwa kyawawa a cikinshi da hukunce hukuncenshi da shari'ansa wanda ya assasa kiwon lafiya na kariya da kuma yaki da yaduwan cuta da kiyayewa daga gare shi gudanarwa na bada kariya wadanda wannan hukuma ta wannan kasa ta dauka mamlala al arabiyya assu'udiyya don hana yaduwan wannan cuta na fairos korona daga ciki akwai dakatar da shiga kasar saudiyya da manufan umra ko ziyaran masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na sifa na wucin gadi na nuni ga hikima irin na wannan doka din da aka sauke da kuma daukakan manufansa bayyanan manufofinsa da girman fa'idansa da kuma abunda zai kai ya komo da abinda zai zama ya amfanar bisa ga lafiyan jiki da kuma garurruwa
Ku roki Allah samun lafiya domin ba abawa bawa wani abu ba bayan yakini da yafi sama da samun waraka da  
** idan ka ga wanda Allah ya jarabeshi to ka nemi tsari **ga Allah daga sharrin bala'i mai sauka
Ku yi salati da amunci bisa ga Ahmadu mai shiryarwa mai ceton talikai gaba daya .

HAKURI BISA BALA'I


Hudubar Masallacin Annabi na shaikh Abdullahi Bin Abdurrahman Albuaijan  18-7-1441AH /12-3-2020AC
Hudubar Farko:
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Mai amsa adu'a Mai yaye bakin ciki da bala'i ina gode mishi bisa ni'imomi daban daban, muna neman tsarin Allah daga sharrin abin da ya halitta na daga  bala'i da annoba yana sanya shi ga wanda ya so kuma ya tunkude shi daga wanda ya so.
Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke bai da abokin tarayya, kasaita da yabo nashi ne da buwaya da girmame girmame da dawwama da wanzuwa duka nashi ne,  na shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne cikamakin Annabawa ma'abocin isra'i da mi'iraji da tabki da kuma lema, tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi da iyalansa da sahabbansa da wanda ya bisu da kyautatawa a halin sauki da kuma halin cuta.
 Bayan haka:
lallai mafi  kyan  zance shi ne littafin Allah mafi  alherin shiriya  shi ne  shiriyan  Manzon  Allah tsira da amincin Allah su tabbatauma a gare shi mafi sharrin al'amura sune fararrunta, dukkan bidi'a bata ce kuma dukkan bata na wuta.
ya ku bayin Allah : ina muku wasiyya da ni kaina da tsoron Allah, domin ita ce  mafaka, kuma  da bin sunnar  Annabi ne  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ake samun kubuta (Ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah rai ya dubi abin da ya kaddamar sabo da gobe, ku ji tsoron Allah, lallai Allah Masani ne ga abin da ku ke aikatawa).

Ya tawagar musulmai
Duniya gida ce ta musibu da kuma bala'u da kuma jarabawowi da kuma fitintinu  gida ce ta jin zafi da kuma haduwa da ba- zata, gida ce ta radadi da kuma azaba da kuma lafiya da kuma cuta da rashin lafiya da kuma waraka da sauki da kuma bala'i gida ce ta farin ciki da bakin ciki, gida ce ta jin rashin dadi da kuma bacin rai da tsanani da wahalar duniya, kurkuku ce ga mumini kuma aljanna ce ga kafiri, akwai yawan musibu da kuma jarabawowi wanda  Allah ke jarraba mai da'a da fajiri da su, na mumini da kafiri, ba a jira bayan lafiya sai rashin lafiya bayan samarta sai tsufa, bayan wadatuwa sai talauci da rashi, hanyan rayuwa da ba ta canjawa kuma bata sauyawa daga su ne a duk yanda ilimi ya ci gaba aka samu habaka a'aha ko da dan adam ya kaura ne zuwa sarari na sama da kuma wata ko da ya kutsa cikin nitson karkashin kasa da koguna ya zauna a can dole ne zai hadu da tawaya da kuma gazawa kuma ilimi da hankali yana i'itirafi da gazawa irin na duniya.
(ya ku jama'r  aljanu da mutane in kuka samu damar ku fita daga sassan  sammai da kassai to ku fita, baza  ku fita ba sai da karfi ).
Lallai ita ce kudura  ta Allah wacce take tana da girma mashi'arSa da iradarSa  al'marinSa da hikimarSa dukkan wani abu a hanunsa ya ke al'mari nashi ne kafin da bayan, abin da ya so ya ke kasancewa, abin da bai so ba bai kasancewa, ba wani abu da ku ke so face abin da Allah ya so ba'a tambayan shi game da abin da ya ke aikatawa, sai dai al'marin shi idan ya so wani abu zai ce da shi ne kasance sai ya kasance tsarki ya tabbata ga Allah wanda mulkin komai ke hanun shi kuma zuwa gare shi za ku koma .

Ya ku bayin Allah :
Ya dace ga mumini a lokacin tsanani da yalwa da kunci da yalwa da wadata ya tuba zuwa ga Allah ya fawwala al'amarinshi zuwa gare shi ya nemi mafaka a wurin Allah  ya dogara gare shi duk wanda ya dogara ga Allah to Allah ya isam mashi kuma ya sani cewa duk wani abu da ya same shi bai kasance da ya kuskure shi ba duk kuma abin da ya kuskure shi bai kasance da ya sameshi ba abin mamaki da al'amarin mumini dukkan al'amuransa alheri ne a gare shi idan abu mai dadi ya same shi sai ya gode sai ya kasance alheri a gare shi idan kuma cuta ko wani abu mara kyau ya same shi sai ya yi hakuri hakan sai ya zama alheri gare shi (Ba wani abu da zai samu na musiba a doron kasa ko kuma a kan kawunan ku face yana rubuce a littafi kafun a halicce ta lallai hakan  ya ke gudana a wurin Allah, domin kada ku yi bakin ciki bisa ga abin da ya tsere muku ko kuma ku yi farin ciki bisa ga abin da ya zo muku Allah ba ya son mai takama mai  alfahari )
 To ya wajaba a gareku ku yarda ku nemi lada a wurin Allah ku nemi lada daga wurin Allah da sakayya ku mika wuya ga abin da Allah ya kaddarta ya hukunta ku sakankance ladan Allah bisa ga musiba da kuma cuta. Allah ya ce (ka yi albishir ga masu hakuri wadanda idan musiba ta same su sai su ce daga Allah muke kuma gare shi za mu koma wadan nan suna da kyakkyawan yabo daga wurin Ubangijinsu da kuma rahama wadannan su ne shiryayyu).

Huduba ta biyu

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya shar'anta halal da haram, Mahaliccin rayuka da jikkuna ya tunkude musibu da kuma rashin lafiya Mai yin ni'ma ga bayinSa da lafiya daga abubuwa masu bijirowa na dare da wuni daga  cikin bala'i ya sanya mishi rahama da daukaka da  kankaran zunubai daga cikin cuta ya sanya lada da kuma  adana da tsarkaka bisa ga lafiya da waraka ku kasance masu godiya bisa ga bala'i da azaba ku kasance masu hakuri, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu Muhammad amintacce da kuma bisa alayensa da sahabbansa da tabi'ai.

 
Ya ku bayin Allah :

Lallai annoba shi ne abin taimako  ga bakin ciki da kuma tashin hankali sa'an nan da ci baya da kuma tashin tasina gashi ya rikita sashi da yawa na duniya a cikin yan tsirarun kwanaki to ku yi kokari wurin tumbuke shi da kuma iyakance shi, An karbo daga Sa'd dan abi wakkas cewa ya tambayi  Usama dan zaid ya ce menene ka ji daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa game da annoba, Usama sai ya ce na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa (Annoba wata tsoratarwa ce ko kuma azaba ce da Allah ke turo ta ga banu isra'ila ko kuma ga wadanda suke kafin ku, to idan kun ji wani abu makamancinta a kasa to kada ku je kasan idan kuma ta faru a wata kasa kuna cikinta to kada ku fita domin guje mata) Muslim ne ya rawaito

Ya tawagan musulmai
Ku ji tsoron yada jita- jita, kage da kuma kambama abu da kuma tsoratarwa da isgilanci ku gode wa Allah bisa ga lafiya kada ku kai kanku ga bala'i ku ji tsoron sabuban yaduwar cuta da kuma wuraren annoba ku roki Allah lafiya da waraka da sauki  ku katangu da zikirori da adu'oyi duk wanda ya yi fata a wurin Allah ba zai yi hasara ba, ku gujewa kaddaran Allah zuwa wata kadarar Allah ku kankan da kai zuwa ga Allah kada kuma ku yanke tsammani daga rahamar Allah.

** ya ma'boci bakin  ciki lallai  bakin ciki yana  yayewa ****
** albishirinka  da  alheri domin mai yaye bakin ciki shi ne Allah ****
**shi yanke tsammani wani sa'i ya kan katse ga ma'bocin shi****
**kar ka yanke tsammani domin Allah shi ne mai isarwa ****

** Allah yana kawo sauki bayan bakin ciki****
**kar ka gaza ka gajiya lallai mai yayewa shi ne Allah****

**idan an jarrabeka to ka zama kana da aminci da Allah ka yarda  da shi****
**lallai wanda ya ke yaye bala'i shi ne Allah****

**idan Allah ya hukunta kawai ka mika wuya bisa ga kudurarSa ****

**mutum baida wani hila ko dabara cikin abin da Allah ya hukunta ****

**na rantse da Allah ba ka da wani koma bayan Allah ****

**Allah ya isan maka a ko wani abu kana da Allah ****

** ya ma'aboci bakin ciki lallai bakin ciki abin yayewa ne ****

** albishirinka da alheri lallai mai yaye bakin ciki shi ne Allah ****

Ya Allah Mai yaye bakin ciki ya mai amsa adu'a ka yaye mana bala'i ka dauke mana cuta ka gaggauto mana da waraka ka hore mana magani ba abin bautawa da gaskiya sai kai, tsarki ya tabbata a gare ka, mu mun kasance cikin wanda suka yi zalunci
Ya Allah ka tunkude mana tsada da annoba da riba da zina da girgizan kasa da bala'u da mummunan fitina abin da ya bayyana daga gare ta da abin da ya boyu daga gare mu musamman haka ma da sauran garuruwan musulmai baki daya.
Ya Allah ya Mai bada mulki makwarkwadan mu na hanunka hukuncin mu a hanunka ya ke abin da ka hukunta game da mu shi ne a'dalci muna neman tsari gareka daga mummunan kaddara da kuma fadawa kololuwa na tsiya da dariya na makiya da kuma saukan bala'i da yaduwar annoba , ya Allah ma'aboci  kasaita da girmame girmame ya Mai saukar da kyauta kai ne ka isar mana madalla kuma da abin dogaro ka gyara mana sha'ninmu gaba daya kar ka kyale mu zuwa ga kawunan mu ko da kebtawan ido ne muna rokonka amincin da bayansa babu jirkita  , da yarda wanda bayansa ba fushi da kuma yaye bakin ciki wanda bayansa ba bakin ciki , ya Alla gareka muka dogara kuma zuwa gareka muka mika wuya kuma zuwa gareka ne za mu koma muna neman tsarinka daga sharrace- sharracen kawunanmu da kuma sharrin ko wace dabba da kai ke rike da makwarkwadanta .                  
  

ALLAH MAI TAUSAYI NE GA BAYINSA


Hudubar Masallacin Annabi Na shaikh Ahmad Dalib 25/7/1441AH/ 20/3/2020AC
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah muna gode masa kuma muna neman taimakonsa da gafararsa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi, kuma duk wanda ya batar babu mai shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah,shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, na kuma shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma manzonSa ne.tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da aminci tabbatacce.
(Ya ku wadanda suka bada gaskiya ku ji tsoron Allah cancancin tsoronSa kada ku mutu face kuna musulmai)
(ya ku mutane ku ji tsoron Allah wanda ya halitta ku daga rai guda kuma ya halitta matarsa daga gare shi ya yada daga gare su mazaje masu yawa da mata, ku ji tsoron Allah da ku ke roko da (sunan) shi. Da zumunci, lalle Allah ya kasance mai tsaro ne a kan ku.)
(ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah ku fadi zance na daidai. zai gyara muku ayyukan ku kuma ya gafarta muku zunubanku, duk wanda ya ke yi wa Allah biyayya da ManzonSa to ya rabauta rabauta mai girma.)

Lalle zance mafi gaskiya shine littafin Allah,  kuma  mafi kyaun shiryarwa  shi ne shiryarwan Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, mafi sharrin al'amura shi ne  fararrun su , kuma dukkan fararrun abubuwa bidi'a  ne  , kuma dukkan bidi'a bata ce  , kuma dukkan bata na wuta 
Bayan haka:
Ya ku mutane
Ku sani lalle Ubangijinku Allah ne wanda ba abin bautawa da gaskiya sai shi,ya yalwaci dukkan komai a rahama da ilimi, ya halicci dukkan komai ya kaddara shi kaddarawa, ya iyakance dukkan komai a adadi, ya gudanar da shi gudanarwa,
Ya yi ludufi da abin da ya so cikin abin da ya ke so zuwa ga wanda ya so. Ya kasance da boyayyiyar kaddararSa da iliminSa mai zurfi goni ne Mai tausayi  ga abin da ya boyu na daga halittunSa , da kuma zartarwa ga hukuncin sa .
 Ya yi ludufi da basirarSa bisa ga abin da ya ke na gani na hakika sai ya riske shi, yayi ludufi   da jinSa ga boyeyyen sautuka  sai ya tantance su , ya yi ludufi da ilimin sa   ga abubuwan da suke kananu  masu halartowa a zuciya  sai ya  banbance su ,
    (Wanda ya fari halittan sammai da kasa,  ta yaya zai kasance yana da Da a halin  bai da mata , kuma  ya halicci  dukkan komai  a hali kuwa shi masani ne ga dukkan komai. Wancanninku shi ne Ubangijin ku ba abin bautawa da gaskiya sai shi  mahaliccin dukkan komai , to ku bauta mishi lallai shi  wakili ne ga dukkan komai,  gani ba ya riskan shi  a hali  kuwa shi  mai tausayi ne goni ).

(Kuma ku boye fadin ku ko ku bayyana shi , lalle shi masani ne  ga abin da ke cikin kiraza . Ku saurara ashe , bai sani ba ; wanda ya yi halitta alhali kuwa shi Mai tausayi ne  goni).
Ya yi ludufi ga abubuwan da suka boyu na wahayin sa  tun daga mulakutin sammai da ayoyinSa da ake karantawa wanda aka sauke su a rarrabe ga matayen Annabi ma'abota dakuna tun daga Baitul Izza har zuwa gidan Annabtaka
(Ku tuna abin da ake karantawa a gidajenku na daga ayoyin Allah da hikima kuma lalle Allah Mai ludufi ne mai bada labari).
Ya zartar da ludufin al'amarin shi, ruwa daga sararin sama zuwa doron kasa inda ba tsirrai ko shuka, ya shayar   da shi zuwa ga tsirrai   da jijiyoyin itace masu koshi da ruwa ya isar da ruwa mai dadin sha ga lambuna.

(Ashe ba ka ga Allah ya saukar da ruwa daga sama  sai kasa  ta zama koriya  lallai Allah mai ludufi ne kuma goni).
Ya zartar da ludufin shi cikin halittun shi  da irin ludufi na halittan sa  zuwa ga  mai raya bitane ya fitar da su, da tsanani irin na jiki  sai ya halaka ta,  da kuma  gungu mai yawa sai ya rarraba su, kuma da dunbin  dukiyaya halaka ya wargaza shi,  Ya yi shawagi  ga wuyan jabberawa  sai ya kaskantar da su,  da lafiya na yanayin su sai ya illantar da ita, da tabbatattun kafafuwan su sai ya zamar da su, ya daga benaye abin daukakawa sun  tsawaita da runduna  abin karfafawa, da masu yawan ibada da masu bauta  da masu keta iyaka da masharrata.
Ya haura zuwa ga  biranen rayuka masu cunkoso da jikuna da suke hade babu sauti na motsin kafa ko  shafa, kamar ba a rayu ba a jiya.
Ya yi gaba da masoya ya muamalance su da halin  makiya, sai suka zama sun yanke masa zumunci sun yi nesa da shi, sai shamaki ya katange tsakanin masoya juna.suna yiwa rogo kallon kitse tamkar yadda mai jin kishi ya ke kallon kawalwainiya.
Ba don komai ba sai don wani abu da ya faru daga gare mu, da wani abu da ya dauke daga gare mu, kada ku zaci cewa makiyi ya yi galaba ne, sai dai Mai kiyayewan ne (Allah) ya juya baya. Ko zasu kankan da kai, ko zasu komo, ko zasu wa'azantu.
Tsatsan zukata ta yawaita, to sai Masanin gaibi  ya tausasa, duk abin da ya yi tsauri zai yi rauni, kuma duk abin da ya yi taushi zai yi tsauri, domin Allah ya dauraye wadanda suka yi imani ya koke kafirai. Kuma ya san wadanda suka yi nifaka.kuma ya dauki fansa daga wadanda suka yi laifi ya warkar da zukatar muminai,kuma ya riki masu shahada a cikin su, lalle Ubangiji na Mai ludufi ne ga wanda ya so. lalle shi Masani ne Mai hikima.    

Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya isa, tsira da aminci ga AnnabinSa zababbe, da iyalansa da sahabbai ma'abota biyayya da wafa'i, da wanda ya bi da kyautatawa ya bi sawunsu.
Bayan haka ku ji tsoron Allah cancancin tsoronSa, duk wanda ya ji tsoron Allah zai sanya masa mafita kuma ya azurta shi ta inda bai zata ba. (Duk wanda ya dogara ga Allah to shi ya isan masa, Lalle Allah Mai iyar da umarninSa ne,) Lalle Allah ya sanya ma'auni ga dukkan komai.(Wanda ya ji tsoron Allah zai sanya masa sauki cikin al'amarinsa) (Wanda ya ji tsoron Allah zai kankare masa laifukansa kuma ya girmama ladansa.)
     Ya ku musulmai!
Allah Mai tausayi ne ga bayinSa yana tausaya wa mai karamin karfi dalilin mai rauni cikin halittu, ko da masu karfi sun ki, yana zartar da ludufinSa mai zurfi ga kaskantacce a cikin bayinSa ko da masu izza sun ki, yana azurta wanda ya so Shi Mai karfi ne Mabuwayi tsarki ya tabbata a gare shi,.. yana karanta ni'imomi masu yawa ga bayinSa kuma ya habaka kadan na daga da'a ga bawanSa,
Iya gwargwadon zurfin ludufi iya gwargwadon riskarsa, shine wanda in ka kira shi zai amsa ma, in ka nufe shi zai baka mafaka, kuma in ka kaunace shi zai kusanto ka, kuma idan ka masa da'a sai ya saka maka, idan ka saba masa sai yana iya baka waraka , idan ka juya masa baya sai ya kira ka, idan ka kusanto shi sai ya shirye ka.
Yana sakanya a gare ka in ka kyautata yana yafiya a gare ka in ka gajarta duk wanda ya rusuna a gare shi zai daukaka shi wanda ya nuna bukatuwa zuwa gare shi zai wadata shi ba ya bukata daga masoya wasu hanyoyi ko kuma sabuba umarninSa kusantarwa ne haninSa kuma ladabtarwa ne kyautanSa zabi ne haninSa adana ne matattaran ludufanSa tausasawa ne da kusantarwa shi makusanci ne mai amsawa duk wanda ya shaida Allah  ga  zuciyansa to zai dauke masa duk wasu abubuwa masu yawa mafi ludufi da kuma mafi girman shi mafi darajan shi da daukakan shi shi ne ya yi  ludufi cikin bayinSa ta hanyan taimakawa a cikin kaddara kuma da yarda da kuma tawali'u da  tuba da kankan da kai da komawa da rusunawa da imani.
Bayan  haka ya ku bayin Allah
Ku sanya gidajenku alkibila ku tsaida sallah ku yi da'a  ga wanda Allah ya jagorantar da al'amuranku a gare su cikin da'a wa Allah ku yi sallah ku yi salati da aminci bisa ga alkibila mafi tsarki da kuma mashaya na farin ciki da kuma  Annabi mafi daukaka da kuma waliyyi mafi kusa shugabanmu Muhammadu Annabi Ummiyi hakika Allah ya zabe shi, lallai Allah da mala'ikunSa suna salati ga Annabi .