Hudubar Farko:
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah,
Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah da iyalansa da sahabbansa da
wanda ya bi su,Bayan haka.
A wani hali da aka samu kai a ciki na ababan
shagaltarwa da hanyoyi da zasu yi awon gaba da mutum na harkan abin duniya,sai
a samu musulmi ya gafala daga wasu hakkoki da gina alaka ta zamantakewa, wani
kan manta ko share tunanin dawowa kan tafarkin gyara tsarin rayuwar shi da
kyautata alakarsa, shekaru na tafiya ranakun rayuwa na shudewa, ana dada samun
rata da yin nesa da juna, sai rayuwa ta zama ba dankon zumunci, a rasa tausayin juna.
Musulunci ya bada kulawa ga alaka ta
zamantakewa, kuma ya sanya lada mai kwadaitarwa da janyowa da gaggawa zuwa gare
ta.don a samu hadewar zukata da karfafa zumunta,da amsa bukatun juna, kuma
al'uma zata dabiantu da kyawawan halaye da nagartattun ayyuka, sai mizani ya
nauyaya, a daga darajojin mutum, idan an bada hakkoki alaka ta yi kyau, sai
al'uma ta zama ta dunkule ta yi karfi.
Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Hakkin Musulmi akan Musulmi shida ne,sai
aka ce da shi menene su ya manzon Allah? Sai ya ce : Idan ka hadu da shi ka
mishi sallama, idan ya gayyace ka to ka amsa mishi idan ya nemi nasiha to ka yi
mishi, idan ya yi atishawa ya godewa Allah to kace da shi yarhamukallah (Allah ya maka rahama), idan ya
yi rashin lafiya ka ziyarce shi, idan ya rasu to ga bi jana'izarsa.
Hadisi ne mai girma da ke bude sarari na
kusantar juna da kauna, kuma hakan zai bada sabon rayuwa, Allah Madaukakin
sarki ya ce :( Kuma ya sanya soyayya a tsakanin
zukatansu, da ka ciyar da abin da ke cikin kasa gaba daya da baka sanya soyayya a
tsakanin zukatansu ba,kuma amma Allah ya sanya soyayya a tsakanin zukatansu
lalle shi ne Mabuwayi mai hikima).Anfal 63
Farkon hakkokin musulmi bisa musulmi kalma ce
ta kauna da hadinkai, gaisuwa ta 'yan Aljanna ita ce Assalam, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
ya ce : (Ba za ku shiga Aljanna ba har sai kun yi imani, ba za ku yi imani ba
sai kun kaunaci junanku, ashe ba zan nusar da ku ga abin da in kun aika shi
zaku kaunaci junanku? To ku yada sallama a tsakaninku)
Sallama mabudi ne na kauna zuwa ga zuciya, kuma
mabudi ne na neman izini ga kowace kofa, yana kawo albarka da habaka da kari a
rayuwa.
Allah
Madaukakin sarki ya ce : (To idan kun shiga wasu
gidaje, ku yi sallama a kan kawunanku,gaisuwa daga gurin Allah mai albarka mai
dadi).
Sallama sako ne na aminci,kuma alama ce
na ma'abota imani,wanda ya san ma'anarsa da matsayinsa, yayi rayuwarsa ta
hakika ya san falalarsa,to zuciyarsa zata tsarkaka dabiunsa zasu gyaru, Al'umarsa
zata daukaka a addinance kuma a duniyance.
Allah Madaukakin sarki ya ce : (Da shi Allah yana shiryar da wanda ya bi yardarSa, zuwa
ga hanyoyin aminci, kuma yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske da
izininSa,kuma yana shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya.)
Na daga cikin hakkokin musulmi bisa dan uwansa
musulmi akwai amsa gayyatarsa, ya halarci walimarsa ya dadada zuciyarsa. Da taya
shi farinciki, kuma gayyaceceniya ga juna na haifar da kauna da hadinkai. Kaiwa
juna ziyara da haduwa yana haifar da kauna, a cikin wannan yanayi akan samu
warwarewan rikici, masu hankali na kauda kai bisa suka da zargi sai dankon
zumunci ya kara karfi, rashin jituwa ya kau,
Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Idan an gayyaci dayanku zuwa ga abinci to
ya amsa,idan ya so ya ci idan bai so ba ya bari).
Kimar walima ba ana auna shi ba ne da girman
abin da aka ciyar ba ko yawan abin da aka kashe ba, sai dai kawai don akyautata
manufa ta 'yan uwantaka da sada zumunci tsakanin musulmai, amma yin
almubazzaranci a cikin walima ba abin a yaba ba ne, don sharia bata yadda da
haka ba, kuma yana cire albarka,
Allah Madaukakin sarki ya ce : (ku ci ku sha amma kada ku yi barna lalle shi bai son mabarnata)Aaraf 31
Hakki na uku cikin hakkokin musulmi shi ne ka
yi wa dan'uwanka nasiha, cikin lumana da
tausasawa, nasiha sako ne na kauna daga musulmi
zuwa ga dan'uwansa,sabo da yana son sa ya ke masa fata na dukkan alheri, kuma
yake tsorace masa dukkan sharri. Mai nasiha na da matsayi madaukaki a addini,
da daraja ta kololuwa ranar da mutane zasu tsaya gaba ga ubangijin talikai, a
lokacin da mai nasiha zai yi nasiha to shi mai gaskiya zai buda kirjinsa don
nasihar ya kuma saurare ta da zuciyarsa, kuma ta karbe ta da daukakawa ba zai
maida ta ba, sabo da wani mummunan zato da ya ke yi wa mai nasihan,ko wata
fassara da ba daidai ba,
Hakika sarkin muminai Umar Allah
kara yarda a gare shi ya ce;( Allah ya yi rahama ga duk wani mutumin da ya
nusar da mu ga laifukanmu).
Akwai banbanci nesa ba kusa ba tsakanin mutumin
da zai yi nasiha yana mai kauna mai nusarwa mai tausayi yana nasiha tare da
suturcewa, da wanda zai yi lullubi nasihar ya maida ta mayafi, sabo da wani abu
mara kyau a zuci, da zarar ya ci karo da wani abu, sai ya rika bin gajartawa na
'yan uwansa ya yi ta yabazawa, ya rika yada laifukan abokan zamansa, sai ya
rika aibata shi ya soki wannan ya tuhumi
wancan, ya taba mutuncin wadancan,
Hakki na hudu shi ne idan ya yi atishawa ya
godewa Allah to ace da shi
yarhamukallah, kowa na jin dadin a yi mishi adua, yana kuma fatan karin
rahama, Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce : (Aduar mutum ga dan'uwan shi musulmi a boye
karbabbiya ce An wakilta wani mala'ika ta kansa a duk lokacin da ya yi wa
dan'uwansa adua ta alheri sai Mala'ikan da aka wakilta ya ce :Amin, kai ma Allah ya baka kwatankwacinsa).
Atishawa ni'iama ce daga Ubangiji ga bawa wacce
ta cancanci a gode a yaba, a cikin cewa Yarhamukallahu da adua gare shi
da ambaton Allah akwai fusata shaidan da kuma tunkude shi, umarni da aka yi ga
mai atishawa da ya yi adua ga mai sauraronsa, da shi kuma da zai mishi adua da
gafara da shiryuwa da gyaruwan shani,
wanda ke nufin komi nashi ya yi kyau ya daidaita.
Na daga cikin hakkokin musulmi a kan musulmi
akwai ziyartar shi a halin bai da lafiya, sabo da maralafiya yana fama da jiki,
watakila ma rashin lafiyan kan iya kai wa makwanni ko watanni, bai iya runtsa
ido ko ya samu kwanciyar hankali, yana kururuwa yana jujjuyawa sabo da radadi
da zafin ciwo, yana neman aduar da Allah zai tabbatar mishi da sauki da ita,kuma
darajarsa ta dagu dalilinta, yana bukatar ziyara da za ta rage mishi zafi da
kalma wacce za ta debe mishi kewa na daga bakinciki da yake fama, da shafa na
tausayawa da zai ji yana kusa da 'yan uwansa, Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Duk wanda ya je
dubiya ga mara lafiyan da ajalinsa bai zo ba, sai ya fadi (As'alullaha
Rabbal Arshil Azim an yashfiyaka) ina rokon Allah ubangijin Al'arshi mai
girma da ya baka lafiya, har sau bakwai face sai Allah ya bashi lafiya.
Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Allah Mabuwayi da Daukaka zai ce a ranar
alkiyama : Ya wane na yi rashin lafiya baka ziyarce ni ba, sai yace :Ta yaya
zan ziyarce ka kana Ubangijin talikai, sai yace baka san bawa na wane ya yi
rashin lafiya ba ba ka ziyarce shi ba? Da ka ziyarce shi da ka same ni a gun
shi)
Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Duk wanda ya ziyarci mara lafiya to yana
cikin dausayin AlJanna sai aka ce mene ne dausayin Aljanna sai ya ce :abin anfani na aljanna)
Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Duk wanda ya ziyarci maralafiya, ko ya
ziyarci wani dan'uwansa don Allah, sai mai kira ya kira shi: ka tsarkaka
takunka ma ta tsarkaka,kuma ka riki masauki a aljanna)
Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Duk wanda ya ziyarci maralafiya bai zai
gushe ba cikin rahama har sai ya zauna, idan ya zauna sai ya tsunduma ciki.)
Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Ba wani mutum musulmi da zai ziyarci musulmi
face Allah ya turo malaiku dubu saba'in suna nema masa gafara a kowace sa'a ce
ta wuni har sai ya yi yammaci,kuma a kowane lokaci ne na dare har gari ya waye,)
Huduba ta biyu:
Yayin da muka yi lura da hakkoki da nau'ukansu
da manufofinsu : za mu sani bisa yakini cewa hakkin musulmi akan dan'uwan shi
abu ne mai ci gaba har zuwa mutuwarsa,ku zai zarce har bayan mutuwarsa: da bin
jana'izarsa, da yi mishi adua, a cikin haka akwai girmama shi da daukaka
shaninsa,da kimanta matsayinsa,kamar yadda waki'in alkawari tsakanin
muminai ke fassarawa, wannan shine abin
da kullin 'yan uwantaka ke hukuntawa.
Abin mamaki da girman wannan addini na
musulunci, abin mamaki da gamewar manhajarsa, abin mamaki da kyan ni'imarsa da
garabasarsa, Addini ne da ya daukaka zaukin bawa da kawarsa, kuma ya tsarkake
ayyukan bawa da zancensa, ya tsarawa musulmi abubuwa na sirrinsa da na bayyane.
Idan mutum musulmi ya mutu zaa wanke shi a sa
mishi likkafani a mishi salla a mishi adua a raka shi zuwa kabarinsa,a binne
shi da kasarsa, kuma ana kula da kaburbura kada wani abu na walakanci ya same
su,
Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Duk wanda ya bi jana'izan musulmi yana mai
imani da neman lada ya kasance tare da shi har aka masa salla aka gama binne wa
to zai koma da lada kiradi biyu,ko wani kiradi ya kai kwatankwacin Dutsen
Uhudu.)
Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Duk wanda ya wanke musulmi ya kuma rufa
mishi asiri to shi ma Allah zai suturce shi daga zunubai, wanda ya yi mishi
likkafani Allah zai tufatar da shi tufafin sundusi(Alhariri).
Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Idan kun zo yi wa mamaci salla to ku
kebance adua gare shi).
An karbo daga zaidu dan Sabit
Allah kara yarda a gare shi yace :( Mun fita tare da Annabi tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi, yayin da ya iso Baki'a sai ga wani sabon kabari
sai ya tambaya game da shi, sai suka ce wance ce, yace: sai ya gane ta, sai
yace :Me ya sa baku sanar da ni ba? Sai suka ce : ka kasance kana baccin kailula
kuma kana azumi sai mu ka ji nauyin kada mu cutar da kai, sai ya ce : kada ku
yi haka, kada wani daga cikin ku ya rasu face kun sanar da ni muddin ina
tsakaninku, domin salla ta a gare shi rahama ce,sai ya zo kabarin sai muka yi
sahu a bayansa sai ya yi mar kabbarori guda hudu).
Dukkan al'umar da take bada hakkoki don da'a
ga Allah da koyi da sunnan Manzon Allah, to zata dunkule ta yi karfi mazajenta kuma zasu
samu daukaka, haka kuma duk makiyi mai musu dakon sharri ba zai samu kofa ba da
zai jefa musu sharri ba ko dama da zai wargaza tsakaninsu ba, ko ya datse kauna
da ke tsakanin 'ya'yan al'umar ba.
Allah Madaukakin sarki ya ce : (Wadanda suka zo bayansu suna cewa ya Ubangijinmu ka
gafarta mana da 'yanuwanmu wadanda suka
gabace mu da imani, kar ka sanya wani kulli a cikin zukatanmu game da wadanda
suka yi imani, ya Ubangijinmu lalle kai Mai tausayi ne mai jinkai).
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق