الجمعة، 14 ديسمبر 2018

TSIRA DAGA TAFARKIN SHAIDAN


Hudubar Masallacin Manzon Allah na 6-4-1440/13-12-2018 na shaikh Aliyu Bin Abdurrahman Alhuzaifi
Hudubar farko
Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Alheri a hanunsa ya ke kuma mai iko ne akan komai, mai tsayawa ga kowane rayi kan abin da ya aikata, zai cika wa kowa abin da ya aikata ba ya zalunci ko da na kwayar zarra ne, in ma kyakkyawa ce sai ya ribanyata, kuma yana bada lada mai girma daga gare shi, Ina kyautata yabo ga Ubangiji na kuma ina gode masa bisa falalarsa mai girma, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, Masani Gwani, kuma na shaida Annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa ne, mai albishir mai gargadi, kuma fitila mai haske, ya Allah ka yi aminci da tsira da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammadu wanda aka turo da littafi mai haske, da iyalansa da sahabbansa wanda Allah ya daukaka addini da su ya kuma kaskantar da shirka abin kaskantarwa,
Bayan haka :
Ku ji tsoron Allah Madaukaki ta hanyar gaggautawa zuwa ga ayyukan alheri, da nesatan abin da aka haramta, zaku rabauta da darajoji mafi daukaka, kuma ku tsira da abubuwa masu halakarwa.
Ya ku musulmai: Lallai Allah ya muku alkawari na gaskiya, kuma ba sabawa ga alkawarin shi, kuma ba mai bin kadu bisa hukuncinsa, ya yi wa bayinsa masu biyayya alkawarin daddadan rayuwa a duniyarsu, kuma ya musu alkawari da kyakkyawan karshe a lahirarsu, zai saukar da yardarsa  a gare su, kuma ya jiyar da su dadi da niima mai dorewa a cikin Aljanna Madawwamiya tare da Annabawa da mutanen kwarai wadanda suka bi tafarki madaidaici, Allah Madaukakin sarki ya ce : ( Da a ce mutanen Alkaryu sun yi imani kuma suka yi takawa da mun bude musu albarkatu daga sammai da kasa)   
Kuma Allah Madaukakin sarki ya ce :(Da  ma'abota  littafi za su bada gaskiya su ji tsoron Allah da mun kankare musu miyagun ayyukansu daga gare su kuma da mun shigar da su Aljannatai masu ni'ima. Da sun tsaida Attaura da linjila da abin da aka saukar musu daga Ubangijinsu da sun ci daga bisansu da kasan kafafuwansu)
Wato da sun yi imani da Alkur'ani suka yi aiki da shi tare da imaninsu da littafinsu ba tare da sun jirkita shi ba, da Allah ya raya su rayuwa daddada a duniya, kuma Allah ya shigar da su Aljanna mai ni'ima a lahira, Allah ya ce cikin kwadaitar da Annabi Nuhu amincin Allah ya tabbata a gare shi: (sai nace ku nemi gafarar Ubangijinku, lalle ne shi ya kasance  maigafara ne, zai sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai bubbuga. Kuma ya yelwata ku da dukiya da 'ya'ya. Ya sanya muku albarka ga gonaki. Kuma ya sanya muku koguna.)
 An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi, yace Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : Lalle Allah Madaukakin sarki ya ce : (Duk wanda ya yi min gaba da masoyi na to hakika na shelanta masa yaki, ba wani abu da bawa na zai kusance ni da shi da ya fi soyuwa a gare ni fiye da abin da na wajabta a gare shi, bawa na ba zai gushe ba yana kusanta na da nafilfili har sai na kaunace shi, to idan na kaunace shi sai na kasance jinsa da ya ke ji da shi, da ganinsa da ya ke gani da shi, da kuma hanunsa da ya ke damka da shi,da kuma kafarsa da ya ke tafiya da ita,kuma muddin ya roke ni zan ba shi, haka kuma muddin ya nemi tsari na zan bashi kariya,ba wani abu da nake tantama game da shi wanda zan aiwatar da shi kamar taraddudi na bisa daukan rayin mumini, ya tsani mutuwa ni kuma na tsani na musguna mishi ). Buhari ne ya rawaito.
Hadisin na nuni ne cewa Allah bisa ludufinsa da karamcinsa da rahamarsa da ikonsa yana jibintan al'amuran bayinsa masu biyayya kuma ya gudanar da su ta hanya mafi kyau ta gudanarwarsa a rayuwarsu da bayan mutuwarsu, kuma alkawarin ubangijinmu gaskiya ne ba sabawa ko tashi,
 Allah madaukakin sarki ya ce : (Ya Ubangijinmu lalle kai ne mai tara mutane domin wani wuni wanda babu shakka a gare shi, lalle ne Allah ba ya sabawar lokacin alkawari).
 Allah madaukakin sarki ya ce (ya Ubangijinmu ka ba mu abin da ka yi mana alkawari akan manzanninka kuma kada ka tozartar mu a ranar kiyama, lalle ne kai ba ka saba alkawari.)
Kuma ya musu alkawari na gaskiya a lahirarsu, da fadinsa madaukaki (  Allah ya yi alkawari ga muminai maza da muminai mata da gidajen Aljanna koramu suna gudana daga karkashin su,suna madawwama a cikinsu da wuraren zama masu dadi a cikin gidajen Aljannar. Kuma yarda  daga Allah ce mafi girma. Wancan shi ne babban rabo mai girma.)
Mumunai na shaida abin da Ubangijinsu ya musu alkawari a rayuwarsu ta duniya, ladar Allah na bibiyar juna a gare su, kuma ni'imomin Allah na gamewa da su daya bayan daya, Allah madaukakin sarki ya ce : (Allah ya saka musu da sakamakon duniya da kuma kyakkyawan sakamakon lahira, kuma Allah yana son masu kyautatawa.)

Kuma a lahira, za su samu ladan da aka alkawarta musu, da wata ni'ima wacce bata yankewa, Allah (سبحانه) ya ce: "Shin fa, wanda muka yi ma wa'adi mai kyau, sa'annan shi mai haduwa da shi ne, yana zama kamar wanda muka jiyar da shi dan dadi irin na rayuwar duniya, sa'annan shi a Ranar kiyama yana daga masu shiga wuta?", [Kasas: 61].
      
Kuma, kamar yadda Allah ya yi kyakkyawan alkawari ga muminai masu biyayya, haka Allah ya tanadi narkon azaba ga kafiran da suke musun Allah, da masu sabo masu tsaurin kai, Kuma duk abin da ya gargade su na azaba abu ne mai aukuwa a gare su;
 Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: "Kuma wadanda suka kafirta suna jin dan dadi a Duniya, kuma suna ci kamar yadda dabbobi ke ci, kuma wuta itace mazauni a gare su", [Muhammad: 12].
Kuma Allah (سبحانه) ya ce: "Kuma duk wanda ya saba wa Allah da ManzonSa, to lallai yana da wutar Jahannama, suna masu dawwama a cikinta, har abada", [Jinn: 23].
Kuma rayuwar kafirai da masu taurin kai, a Duniya itace mafi munin rayuwa, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma wanda ya bijire daga Anbatona (wato, Kur'ani), to lallai yana da rayuwa mai kunci, kuma za mu tayar da shi a ranar Kiyama yana makaho", [Daha: 124]. Koda kuwa an basu abin Duniya!
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kada dukiyoyinsu da 'ya'yansu su burge ka ko baka sha'awa, lallai Allah yana nufin ya musu azaba da su a rayuwar Duniya, kuma rayukansu su fita alhalin suna kafirai" {Taubah: 85}.
        Kuma hakika an jarrabi Mutum da ababen da suke kawar da shi daga abin da zai amfanar da shi, su kuma aukar da shi cikin wadanda za su cutar da shi, a matsayin ibtila'i da jarrabawa, masu sanyaya guiwa kan ayyukan da'o'i, masu kawata aikin sabo; domin Allah ya san wanda zai yi gwagwarmaya da ransa, ya saba wa son zuciyarsa, daga wadan da za su biye wa rayukansu kan son zukatansu, sai su biye wa Shedanunsu, Sai kuma Allah ya fifita shiryayyu da basu darajoji, ya kuma yi ukuba ga masu bin soye-soyen zuciya masu halakarwa da ramuka a cikin wuta, Allah (تعالى) ya ce: "kuma lallai ne, za mu jarrabe ku, har mu san masu jihadi daga cikinku, da masu hakuri, kuma za mu jarraba labarunku" [Muhammadu: 31].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma wadanda suka yi kokari wajen neman yardarmu, lallai ne za mu shiryar da su hanyoyinmu, kuma lallai ne Allah, tabbas yana tare da masu kyautatawa ga addininsu", [Ankabut: 69].
        Kuma lallai Rai, na daga cikin manyan makiyan Mutum, kuma Shaidan baya iya shigar wa Mutum sai ta hanyar shi Rai, Allah (تعالى) ya ce: "Lallai ne rai, hakika mai yawan umarni ne da mummunan aiki, sai ga abin da Ubangiji ya yi rahama", [Yusuf: 53].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Ba komai suke bi ba face zato, da abin da rayukansu ke so" [Najm: 23].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma wanda ya sabawa rowar ransa, to wadannan sune masu babban rabo" [Tagabun: 16].
        Kuma Rai da abin da yake sifantuwa da shi; na jahilci da zalunci, yana nisanta ma'abucinsa daga gaskata wa'adin Allah, kuma yana kashe guiwar mutum daga ayyukan tsayuwa ga addini, sai su karkatar da mutum daga daidaituwa akan tafarkin Ubangiji, Ibnul-Kayyim –رحمه الله تعالى- ya ce: "Duk wanda ya san hakikanin Ransa, da dabi'unsa, to ya san shine mabubbugar dukkan sharri, kuma matattarar duk wani aiki mummuna. Kuma zai gane cewa lallai kowane alherin da aka gani tattare da shi, to tsagoron falalar Allah ne wanda ya yi baiwa da shi a gare shi, ba daga wannan ran ba ne, kamar yadda Allah (تعالى) yake cewa: (Ba domin falalar Allah a kanku da rahamarsa ba, da wani daga cikinku har abada bai tsarkaka ba), maganarsa ta kare.

        Kuma Rai bai kubuta daga jahilci da wauta ba, face ta hanyar ilimi mai amfani, wanda shari'a ta zo da shi.
        Haka, Rai bai kubuta daga zalunci, sai ta hanyar aiki na kwarai.
        Kuma babu makawa, Musulmi koyaushe ya rika nuna kwadayinsa zuwa ga Allah; yana rokonsa domin gyaruwan Ransa; An ruwaito daga Zaid bn Arkam (رضي الله عنه) ya ce: "Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana cewa: Ya Allah! Ka baiwa Raina takawarsa, ka tsarkake shi; domi kai ne mafi alherin mai tsarkake shi, kai ne masoyinsa kuma Majibincinsa. Ya Allah! Lallai ina neman tsarinka daga ilimi maras amfani, da zuciyar da bata da khushu'i, da Rai wanda bai koshi, da addu'ar da ba a amsa ta", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma Tirmiziy ya ruwaito daga hadisin Imrana bn Husain: Lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ilmantar da Husaini kalmomi biyu, wadanda zai rika addu'a da su: Ya Allah! Ka nusar da ni shiriyata, kuma ka tsare ni daga sharrin Raina".
      Kuma idan Rai bai tsarkaka ta hanyar ilimin shari'a da aiki na-kwarai ba, Sai jahilci da zalunci su dabaibaye shi, sai ta hade; da son zuciya, daga nan sai ma'abucinsa ya karyata alkawarin Allah, ya biye wa sha'awowinsa, sai kuma ya halaka ya dulmuya cikin ramukan hasara da azaba da wulakanci, sai ya yi hasarar duniyarsa da Lahira, Allah (تعالى) yana cewa: "Babu wanda yafi bacewa fiye da wanda ya biye wa son zuciyarsa, ba tare da wata shiriya daga Allah ba, Lallai ne Allah baya shiryar da mutane azzalumai" [Kasas: 50].
        Idan kuma Rai ya samu tsarkaka ta hanyar ilimi mai amfani da aiki na-kwarai, to sai ya rikide zuwa ga Rai wanda yake gaskata alkawarin Allah, natsattse, wanda ke mayar da lamuransa zuwa ga Allah, wanda ake masa alkawarin samun karamomi a lokacin mutuwa; Allah (تعالى) ya ce: "Ya kai wannan Rai natsattse * Ka koma zuwa ga Ubangijinka kana mai yarda, abin yarda * sai ka shiga cikin bayina, kuma ka shiga Aljannata" [Fajr: 28-30].
        Kuma mai yanke dukkan hanyoyin alkhairi, mai kira zuwa ga dukkan sabo da sharri, shine makiyin mutum; wato Shedan abin korewa daga dukkan rahama, mai dauda, mai najasa, Allah ya tsare mu daga gare shi; kuma Allah ya sanya shi ya zama ibtila'i ko jarabawa ga mutane da aljanu; Kuma wanda ya masa da'a zai kasance a wani matsayi mafi dauda, Wanda kuma ya saba wa Shedan, zai kasance a mafificin wurin zama (a Lahira(
        Jin dadin Iblisu da farin cikinsa da ni'imarsa na cikin batar da halittu da kawo barna; yana kiran mutum zuwa ga karyata alkawarin wa'ad da wa'id (na rahama, da narkon azaba), kuma yana kawata masa ababen haramun, kuma yana katange shi daga aikata farillai da mustahabbai, kuma yana sanya masa gurace-gurace na barna, kuma yana rudarsa da munanan waswasi, Allah (تعالى) ya ce: "Lallai Shedan makiyi ne a gare ku, sai ku rike shi makiyi, kuma lallai yana kiran kungiyoyinsa ne domin su kasance ma'abutan wutar Sa'ira" [Fadir: 6].
Kuma Allah (سبحانه) yake magana akan Iblisu; da cewa zai yi huduba ga mabiyansa a cikin wuta: "Kuma Shedan zai ce, a yayin da aka kare lamari, Lallai ne Allah ya yi muku alkawalin gaskiya, Ni kuma sai na muku wa'adi, sai na karya muku, kuma babu wani karfi a gare ni akanku, face na kira ku, sai kuka amsa mini; saboda haka; kada ku zarge ni, sai ku zargi kayukanku. Kuma ni ba zan zama mai amfani a gare ku ba, kuma ba za ku zama masu amfani a gare ni ba. Lallai na barranta da abinda kuke hada ni da shin a shirka, gabanin wanga lokacin. Lallai ne azzalumai suna da azaba mai radadi"Ibrahim: 22
        Kuma lallai Shaidan na da  wasu salo da matakai guda bakwai na batar da 'Dan-Adam :
1.   Domin Shedan yana kiransa zuwa ga kafirci,- Allah ya tsare,- kuma idan mutum ya amsa masa ga wannan, to lallai Shedan ya kai makura wajen batar da shi, sai kuma ya sanya shi, cikin rundunoninsa.
2.   Idan kuma bai amsa masa kan kafirta ba, To sai ya kira shi zuwa ga aikata bidi'a;
3.   Idan kuma ya tsira daga yin bidi'a ta hanyar riko da sunnah, da yin aiki da littafin Allah da hadisan Annabi SAW, to sai ya kira shi ga aikata manyan laifukan kaba'irai, har su rinjaye shi, su halakar da shi.
4.   Idan kuma bai amsa masa wajen yin manyan zunubai ba, sai ya kira shi zuwa ga aikata kananan laifuka na zunubai; yana mai sanya shi jin sauki ko raina su, domin ya doge akan aikata su, ya kuma yawaita, har su zama manyan laifuka sakamakon tabbatuwansa akansu, kuma sai ya halaka saboda nisantar tuba.
5.   Idan kuma bai amsa masa wajen yin kananan laifuka ba, sai ya shagaltar da shi da shagaltuwa da ababen halal, a madadin yawaita ayyukan da'a, sai ya shagaltar da shi da hakan kan yin guzuri da kokarin neman lahiransa.
6.   Idan kuma ya tsira daga wannan, to sai ya shagaltar da shi da ayyukan da ba sune suka fi falala ba, domin ya bar wadanda suka fi girman falala, saboda ladansa ya ragu; wannan kuma saboda ayyukan kwarai suna da fifiko cikin ladaddakinsu.
7.   Idan Shaidan ya gagara samun iko, akan wadancan gaba dayansu, to sai ya tirsasa rundunarsa da mabiyansa akan mumini, ta hanyar nau'ukan cutarwa da dangogin sharri.
        Kuma babu tsira daga sharrin Shedan, sai ta dawwama kan neman tsarin Allah, daga Shedan, da dawwama kan ambaton Allah Ta'alah, da kiyaye salloli a cikin jam'i saboda yin hakan (jam'i) garkuwa ne, mafaka, kuma tsira, da kuma ta hanyar tawakkali ga Allah Ta'alah, da dawwama kan yakar Shedan, da nisantar zaluntar bayi, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma imma wata fizga daga Shedan ta fizge ka, sai ka nemi tsarin Allah, lallai ne shi Mai ji ne Masani" [A'araf: 200].
        Kuma yana daga abinda ke katange mutane daga gaskiya ko tabbatuwa da tsayuwa akan addini, da son alkhairi (ya katange shi daga hakan gaba daya): SON DUNIYA DA YARDA DA ITA, AKAN LAHIRA, DA TARA DUNIYA DAGA HALAL DA HARAM, DA KARKATA ZUWA GARE TA DA MANCE GIDAN LAHIRA, Allah (تعالى) ya ce: "Lallai ne wadanda basu kaunar gamuwa da mu, kuma suka yarda da rayuwar duniya, kuma suka natsu da ita, da wadanda kuma suke gafalallu ne daga ayoyinmu * wadannan matattararsu Jahannama ce, saboda abin da suka kasance suke aikatawa" [Yunus: 7-8].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Shin kuna yarda da rayuwar Duniya ne daga Lahira? To, jin dadin rayuwar Duniya a cikin lahira, bai zama ba face dan kadan" [Taubah: 38].
        Kuma son Duniya abin adawa ce ga mutum, idan har ta mamaye zuciyar mutum, sai ya shagaltu da ita, ya kuma bijire daga yin aikin lahira, kuma mafi yawan mutanen da ke bayan kasa suna fifita rayuwar Duniya, Allah (تعالى) ya ce: "Kawai, kuna zabin rayuwar Duniya ne * Alhali, lahira ita ce mafi alheri, kuma mafi wanzuwa" [A'alah: 16-17].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma bone ya tabbata ga kafirai daga azaba mai radadi * wadanda suka fi son rayuwar Duniya fiye da ta Lahira, kuma suna kangewa daga hanyar Allah, kuma suna neman ta karkace, Wadannan suna cikin bata mai nisa" [Ibrahim: 2-3].
        Kuma babu hanyar tsira daga sharrin Duniya da cutarwarta, kuma babu kariya daga munanan halayenta, sai ta hanyar neman dukiya ta hanyoyin halal, wadanda aka shar'anta, da kuma jin dadi a cikinta da abinda Allah ya halatta, ba tare da an ketare iyaka ko an yi facaka da almubazzaranci ba, kuma ba tare da an nuna kasaita ko girman kai ga halittu ba, kuma ba tare da an nuna farin ciki da alfahari da ita ba, kuma ba tare da yin azarbabiya da abin duniya kan hakkokikn bayi ba.
        Kuma mutum dole ya san hakikanin duniya, da kasancewarta takaitaccen jin dadi ne na rudi, mai saurin gushewa, wanda halinta ka iya canzawa. Kuma ya rika tuna wannan lamari a koda-yaushe, saboda cikin haka, gyaruwar zuciyarsa ta ke; An ruwaito daga Almustaurad Alfihriy, daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), lallai shi ya ce: "Duniya kwatancinta da Lahira, ba komai ba ne, sai kamar dayanku ya sanya yatsarsa a cikin teku, sai ya ga da mai zai koma", Ahmad da Tirmiziy da Ibnu-Majah da Ibnu-Hibbana su ka ruwaito shi.
        Kuma sai mutum ya kasance cikin tsoron sharrin Duniya, da mummunar akibarta.
        Kuma ya ji tsoron kada Shaidan ya ce masa, Ai Allah ya baka wannan Duniyar ne, saboda falalarka, da ilimin da kake da shi na hanyoyin samunta, kamar yadda Shedan ya rudar da Karuna da irin wannan maganar, sai karshensa ya zama kamar yadda kuka sani.
        Kuma wani lamari mai muhimmanci, wanda ke wajaba akan mutum a cikin wannan Duniyar; shine: Ya fitar da hakkin Allah, daga cikin abinda yake da shi na Duniya, haka ya bayar da hakkokin halittu na wajibi, wanda sune: Bayar da zakkah da ciyar da iyalai da 'ya'ya, da bako, da taimakon mabukata, da ciyarwa ta dukkan kofofin alkhairi, da ikhlasi; ba tare da riya ko yin aiki domin a ji a fada, ko neman yabon mutane ba; saboda Riya tana lalata ayyuka.
        Kuma lallai manyan sahabbai ya kasance suna da tarin dukiya, sai dai kuma sune suka fi dukkan mutane gujewa Duniyar, Abu Sulaiman ya ce: Usman da Abdurrahman bin Auf sun kasance taskoki ne daga cikin taskokin Allah a duniyarsa, suna ciyar da dukiyarsu cikin biyayya a gare shi, kuma mu'amalarsu ga Allah ta kasance a cikin zukatansu; su biyu.
Kuma ya zo cikin hadisi cewa: (Ka guje wa Duniya (zuhudu) sai Allah ya so ka, kuma ka guje wa abin hannun mutane, sai mutane su soka). Ibnu-Majah ya ruwaito shi daga sahl bin sa'ad.
Ma'anar gujewa abin hannun mutane shine, kada mutum ya musu ta'addanci, ko ya zalunce su cikin hakkokinsu, ko ya yi fatan ganin gushewar ni'imomi daga gare su, kuma ya debe tsammani daga abin hannunsu.
Kuma yana daga cikin ZUHUDU ABIN YABO: Kada Mutum ya so daukaka cikin abin Duniya; Allah (تعالى) ya ce: "Wancan shine gidan lahira wanda muke sanya ta ga wadanda basu nufin daukaka a cikin rayuwar Duniya, kuma basu son barna, kuma akiba mai kyau tana ga masu takawa" [Kasas: 83].
Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na fadi abin da ku ka ji, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.



HUDUBA TA BIYU
       Dukkan Yabo da godiya sun tabbata ga Allah,
Ina Yabo Ubangijina ne cikin rayuwar Duniya da Lahira, Yana da sunaye mafiya kyau
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, Muna siffanta shi, kuma muna yabonsa da sifofinsa madaukaka,
Kuma ina shaidawa lallai Annabinmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, zababbe.
Ya Allah ka kara salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa, da sahabbansa, masu takawa.
Bayan haka … !!
Ku yi takawar Allah, iyakar takawa, kuma ku yi riko da addininsa wanda yafi karfi.
Ya ku Bayin Allah … !!
Lallai Ubangijinmu ya ce: "Ya ku mutane, lallai alkawalin Allah gaskiya ne; don haka kada Rayuwar duniya ta rudar da ku, kuma kada Shedan mai rudi ya rude ku game da Allah" [Fadir: 5].
Ya zo cikin wani hadisi cewa: "Mai hankali shine wanda ya yi hisabi ga Ransa, kuma yake aiki don abin da ke bayan mutuwa. Gajiyayye kuma, shine wanda ya bi son zuciyarsa, sai ya ke kwallafa gurace-gurace ga Allah", Hadisi ne hasan, daga Shaddad.
Kuma An ruwaito hadisi daga Ibnu-Abbas, daga Annabi, cewa: "Lallai Mala'ika yana da wata shafa ga zuciya; shafar mala'ika ita ce, gaskata alkawari, da gaskata labarin gaskiya. Kuma shima Shaidan yana da shafa cikin zuciya, shafar Shedan kuma ita ce karyata alkawari, da karyata labarin gaskiya".
Kuma musulmi wajibi ne ya rika hisabi ga Ransa, yana kokarin tsayar da ita akan tafarki madaidaici, kuma ya kiyaye makircin Shaidan, da bin son zuciyarsa, da ruduwa da rayuwar Duniya; domin jin dadin cikinta kadan ne.
        Ya ku Bayin Allah… !!!
        "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].

          

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق