الجمعة، 28 ديسمبر 2018

Laduban safara /Tafiya


Hudubar Masallacin Annabi na sheikh Abdullahi bin Abdurrahman Albuaijan 28-12-2018/21-4-1440AH
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah,Mai bada dauki ga masu neman agajin gaggawa, mai amsa aduar wadanda suka shiga halin kaka-nikayi, Mai yaye bakinciki daga masu bakinciki, Mai yalwan ni'ima ga bayi baki daya, to kuma babu wata dabba a doron kasa face ga Allah arzikinta ya ke, kuma yana sanin matabbatarta da ma'azarta, duka suna cikin littafi bayyananne, yana aikata abin da ya so kuma ya hukunta abin da ya yi nufi.(kuma shine mai sassaukar da girgije (ruwa) a bayan sun yanke kauna,kuma yana watsa rahamarSa, kuma yana Majibinci Mai godiya).
Muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu  da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, wanda ya batar kuma babu mai shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, shaidawar da na ke fatar tsira a dalilinta ranar Alkiyama,kuma na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne ya isar da sako ya sauke amana,ya yi nasiha ga Al'uma kuma yayi jahadi don Allah cancancin jahadi har mutuwa ta zo mishi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa baki daya,
Bayan haka:
To ina muku wasiya – ya ku bayin Allah- da ni kai na da mu ji tsoron Allah,
Ita ce waiyar mutanen farko da karshe, (Hakika mun yi wasiya ga wadanda aka bawa littafi gabanin ku da ku kan ku da ku ji tsoron Allah).
       Ya ku bayin Allah:
(ku sani cewa rayuwar duniya wasa ce da shagala da kawa da alfahari a tsakaninku da gasar wadata ta dukiya da 'ya'ya kamar misalin shuka wadda yabanyarta na bayar da sha'awa ga manoma, sa'anan ta kekashe har ka gan ta ta zama rawaya, sa'annan ta koma rauno, kuma a lahira akwai azaba mai tsanani da gafara daga Allah da yarda.kuma rayuwar duniya ba ta zama ba face dan jin dadin rudu kawai.)
Duniya ni'ima ce mai gushewa kuma inuwa ce mai wucewa, (Abin sani kawai misalin rayuwar duniya kamar ruwa nemuka saukar da shi daga sama, sa'annan tsiron kasa ya garwaya da shi: daga abin da mutane da dabbobi su ke ci, har idan kasa ta riki zinariyarta ta yi kawa,kuma mutanenta suka zaci cewa sune masu ikon yi a kanta sai umarninMu ya je mata da dare ko da rana sai mu maishe ta girbabba kamar ba ta wadata ba a jiya, kamar wannan ne mu ke rarrabe ayoyi, daki –daki ga mutane wadanda suke tunani,)
Ya jama'ar musulmai!
Duniya littafi ne budadde wanda Allah ya yi kira da a karanta shi a yi lura da ma'anoninsa, kuma ya sanya mana lura da ma'anonin da tunani game da su a matsayin ibada.(Lallai ne a cikin halittan sammai da kasa, da sabawar dare da yini, da jirage wadanda suke gudana a cikin teku (dauke) da abin da ya ke amfanin mutane, da abin da Allah ya saukar daga sama, daga ruwa sai ya rayar da kasa, da shi a bayan mutuwarta, kuma ya watsa a cikinta daga dukkan dabba,kuma da juyawar iska da girgije horarre a tsakanin sama, da kasa : hakika akwai ayoyi ga mutane masu hankalta.)
Ya ku bayin Allah   :sau da yawa kunci kan zowa mutane ba mai yaye shi sai Allah, sau da yawa tsanani kan sauka wa mutane ba mai dauke shi sai Allah! Sau da yawa bala'I kan sauka ga mutane ba mai kauda shi sai Allah.(ko wane ne yake karbawa mai bukata idan ya kira shi, kuma ya sanya ku mamayan kasa? Shin akwai wani abin bauta tare da Allah)
Yayin da ake cikin yanayi na bazara mai matsanancin zafi da kekasa irin nata to sai ga kasa na cikin fari, ga awaki sun tsamure,ga rijiyoyi sun kafe,ga itatuwa sun bushe fure sun yankone,kayan marmari sun karanta,shuki ya mutu,nono ya motse ba ruwa.
Sai ga Allah tunda shi ke sanja yanayi ya turo iska da albishir gabanin rahamarSa kuma ya saukar da ruwa  a bayan sun yanke kauna,kuma yana watsa rahamarSa, kuma yana Majibinci Mai godiya. Sai kasa ta rayu da izinin Allah ta riki zinariyarta ta yi kawa, sai rayuwa ta samu annashawa, yanayi ya sauya ya yi launi, tsarki ya tabbata ga wanda yayi turo giragizai, ya tsirar da iri, tsarki ya tabbata ga wanda ya raya kasa bayan mutuwarta, (ko wane ne ya halitta sammai da kasa kuma ya saukar muku daga sama wani ruwa, Muka tsirar da gonakai da shi masu sha'awa, ba ya kasancewa gare ku ku tsirar da itacensu?shin akwai abin bautawa tare da Allah? Allah ya daukaka! Allah ya daukaka! Allah ya daukaka!.
Rayuwa na sanjawa bayan saukan rahamomi  sai buri ya kada a samu fatan alheri,sai farinciki ya cika zuciya da jindadi da yalwa, (Sai ka dubi alamomin rahamar Allah,yadda ya ke rayar da kasa a bayan mutuwarta lalle wannan(Mai wannan aiki) tabbas mai rayar da halitta ne, shi mai iko ne ga dukkan komai).
Ya ku bayin Allah ! Ni'imomin Allah ba su lissaftuwa, kuma kyautarsa ba a iya kwalkwale ta,abin da ya ke gurin Allah ba a samunsa sai ta hanyar masa da'a da yardarsa da da gode masa bisa ni'imominsa, ( kuma da lalle mutanen alkaryu sun yi imani kuma suka yi takawa da hakika mun bude musu albarkoki daga sama da kasa,)
Sunnar Allah a halittunSa (kuma a lokacin da Ubangijinku ya sanar lalle ne idan kun gode hakika ina kara muku,kuma lalle ne idan kun kafirta, hakika azaba ta tabbas mai tsanani ce,)
Yaku jama'ar Musulmai!
Kafurcewa ni'ima sababi ne daga cikin sabuba na bala'i da tsanani, kuma Allah ya gargade mu kuma ya buga mana misali :(Kuma Allah ya buga misali wata alkarya ta kasance amintacciya,natsattsiya, arzikinta yana zuwa mata a wadace daga kowane wuri,sai kafirta da ni'imomin Allah, sabo da haka Allah ya dandana mata tufafin 'yunwa da tsoro sabo da abin da suka kasance suna sana'antawa).
A kissar garin Saba'I akwai wa'azi (Lalle hakika akwai aya ga Saba'awa a cikin mazauninsu: gonakin lambu biyu, dama da hagu, "Ku ci daga arzikin Ubangijinku, kuma ku yi godiya gare shi. Gari mai dadin zama, da Ubangiji Mai gafara" sai suka bijire, sabo da haka muka saki malalin Arimi (Dam) a kan su, kuma muka musanya musu gonakinsu biyu da wadansu gonaki biyu masu 'ya'yan ita ce kadan: talakiya da goruba da wani abu na magarya kadan, wancan, da shi muka yi musu sakamako sabo da kafurcinsu.kuma lallai ba mu yi wa kowa irin wannan sakamako face kafurai)
Sa'anan ya ce : (kuma suka zalunci kansu, sabo da haka muka sanya su labran hira kuma muka kekkece su ko wace irin kekkecewa. Lalle a cikin wancan akwai ayoyi ga dukan mai yawan nhakuri mai yawan godiya).
Ku godewa Allah bisa nh'imominsa zai kara muku, ku gode mishi bisa falalarsa, da kyautarsa da Allah ya muku rahama
(ku nemi gafarar Ubangijinku, sa'annan kuma ku tuba zuwa gare shi zai saki sama akan ku tana mai yawan zubar da ruwa kuma ya kara muku wani karfi ga karfinku.)
(Ku nemi gafara daga Ubangijinku lale ne shi ya kasance mai gafara ne. ya sako(girgijen) sama a kan ku da ruwa mai bubbuga, kuma ya yalwata mu game da dukiya da 'ya'ya, ya sanya muku (albarka) ga gonaki,ku ya sanya muku koguna).
Muna neman gafaranka ya Allah donkai mai yawan gafara ne, ka turo mana Ruwan sama maibubbuga.
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya yi halitta ya daidaita ya kaddara ya kuma shiryar,ya fitar da abin cin dabboi, sai ya sanya shi kekasassa baka,ya sanya hutu shakatawa a addininmu akwai tausayi da rahama cikin shariarmu.
Ya ku bayin Allah:
Hutu  ranaku ne na watayawa da shan iska da yinguzuri, da yawa daga cikin mutane na karkata zuwa ga tafiyar da ita cikin tafiye tafiye a doron kasa,ba laifi ga hakan ba tare da barna ba wurin sarayar da lokaci,babu ketare iyaka cikin wasa da abubuwan da aka halarta.
Ya ku Musulmai!
Addini ya game dukkan  yanayi da dan adam ke ciki, hukunce- hukuncensa ya game zaman gida da na tafiya, ya dace ga musulmi ya san hukunce –hukunce da laduba na tafiya kamar yadda yake sanin na zama a gida da halin rashin tafiya,
Na daga cikin hukunce –hukunce da laduba na tafiya akwai bankwana da iyalai da aduar hawa mota, da fita,An karbo daga ibnu Umar cewa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan ya daidaita a kan rakuminsa sai ya yi kabbarori sau uku,sannan sai ya ce (subhanallazi sakkhara lana hazihi wama kunna lahu mukrinin wa inna ila rabbina la munkalibun,Allahumma inna nas'aluka fi safari na haza Albirra wattakwa wa minal amali ma tarda Allahumma hauwin alaina safara na haza wadwi anna bu'udahu, Allahumma Antassahibu fissafari walkhalifatu fil Ahl, Allahumma inni A'uzu bika min wa'asa'issafar wa ka'abatil manzar wa suil munkalabi fil mali wal Ahl,)idan ya dawo kuma sai ya fadi hakan ya kara da : (Ayibuna ta'ibuna abiduna lirabbi na hamiduna)
Ma'ana : Tsarki ya tabbata ga wanda ya hore mana wannan, alhali kuwa  ba mu kasance masu iya rinjaya gare shi ba) kuma lalle mu hakika masu juyawa muke ga Ubangijinmu.)  ya Allah muna rokonka biyayya da takawa a wannan tafiyar tamu, muna rokonka na daga aiki irin wanda ka yarda da shi,ya Allah ka bamu sauki a tafiyan nan tamu,ka nade mana nisanta,Ya Allah kai ne ka ke tare da mu lokacin tafiya kuma kai ka ke maye mana a iyalanmu, ya Allah ina neman tsarinka daga tsanani irin na tafiya da mummunan gani, mummunar juyowa cikin dukiya da iyalai,) in ya dawo sai ya fadi haka ya kara da (mun komo muna tuba kuma masu bauta ga Ubangijinmu suna godiya.)
Na daga cikin laduban tafiya ya zabi rana da ya dace,yana da kyau a ce ya zabi alhamis,da kuma lokaci da ya fi, to idan sammako ya fi hakan ya yi kyau, An karbo daga ka'ab dan Malik Allah kara yarda agare shi ya ce (sau da yawa idan Annabi ya zo zai yi tafiya ya kan fita  ne ranar Alhamis, kuma ya kasance yana cewa ya Allah ka sa albarka ga Al'uma ta cikin sammakonta, idan zai tura mahara ko runduna zuwa yaki ya kan tura su ne farkon wuni),
Sakhr ya kasance dan kasuwa ne kuma ya kan tura kayan hajar sa a farkon wuni, sai ya kudance dukiyarsa ya yawaita)Tirmizi da Abu Dauda suka rawaito, Albani ya ce yana da kyau.       
Na daga cikin laduba na tafiya ka zabi abokan kwarai salhai,kada mutum ya tafi shi kadai,(Daga Ibnu Umar Allah kara yarda agare shi yace Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : Da mutane sun san abin da ke cikin kadaici da mai tafiya bai yi tafiya ba cikin dare shi kadan shi)  
Na daga cikin laduba na tafiya kula da sauke nauyin wajibabbu, da tsaida sallah,hakika Allah ya mana gargadi game da sakaci da ita ko  jinkirtata,(Bone ya tabbata ga masu sallah, wadanda suke shagalta daga sallarsu)
Na daga cikin sunna a halin tafiya a gajarta sallah mai raka'a hudu, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Kuma idan kunyi tafiya babu laifi a kan ku ku rage  daga sallah)
Kuma shari'a ta bada dama ga mazaunin gida da ya yi shafa akan kuffi tsawon dare da wuni, ga matafiyi kuma kwanaki uku da dararrakinsu,
Na daga cikin laduban tafiya akwai kulawa da bangaren  aminci, da tsarin tafiya, da rashin yin wasa, da jefa kai ga halaka da yin kasada da rayuka.
Na daga cikin laduban akwai nesatan gurbata muhalli da yada shara dadotti da  kazanta a guraren da ba a kebance don su ba, da rashin cutar da abokan shakatawa da damunsu, da runtsa ido daga Abubuwan huruminsu da kamewa daga abin da ya kebance su, da kiyaye tsayuwa a kan hanyarsu da gurin wucewarsu, da kiyaye bata kayan al'uma abubuwansu, da abin da ya ke na hidimarsu.
Ya ku musulmi:
Duk wanda ya so fita cikin tafiya ta tudu,kuma nisan tafiyar ta kai a yi mata kasaru to ya samu ya yi karbi saukin da aka yi ga matafiyi, Musulunci Addini ne na sauki da tausasawa, bai sanya muku wani abu na kunci a addini ba.
Ya Allah ka daukaka musulunci da musulmai.          

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق