الجمعة، 11 يناير 2019

ka yi kwadayin abin da zai amfane ka


Hudubar Masallacin Annabi na sheikh AbdulBari Assubaiti 5/5/1440 AH /11/1/2019
Hudubar Farko
Nasara a rayuwa abin nema ne ga kowane mutum,manufarsa da muradinsa samun walwala da sa'ida,rayuka da zukata na karkata zuwa gare su,hakika Annabi ya zayyana mana abubuwa uku na samun nasara da walwala a rayuwar duniya da lahira, a hadisi mai yawan fa'idoji da girman amfani,a fadinsa (ka yi kwadayin abin da zai amfane ka ka nemi taimakon Allah kar ka gajiya).
(ka yi kwadayin abin da zai amfane ka); ka yi kokarin samun manyan manufofi masu ma'ana da kyawawan dabi'u madaukaka,da ibadoji mafi daraja,ka sanya wa rayuwarka manufa,kar ka tafiyar da shekarunka kara zube ba tare da tabbatar da  wata babbar gaya da kake so ka cinma ba, (shin wanda ke tafiya a kife a kan fiskarsa ya fi zama a kan shiryuwa ko kuwa wanda ya ke tafiya mike a kan hanya madaidaiciya) ?
(ka yi kwadayin abin da zai amfane ka) :sabo da rayuwar gajeruwa ce, bayan samarta sai tsufa, ga lafiya na samun barazana daga cututtuka, Ibnu Mas'ud Allah kara yarda a gare shi ya ce : (Ba abin da nayi nadama a kansa kamar ace rana ta fadi ajali na ya ragu, aiki na bai karu ba a cikin shi,)
(A ranar nan mutum zai yi tunani, to ina fa tunanin yake a gare shi! Yana dinga cewa kaito na ina ma da na gabatar (da aikin kwarai) domin rayuwa ta).
Wanda ya yi kwadayin abin da zai amfane shi zai shagalta ne da abin da zai kawo riba a gare shi, da ganima mai tsada   da ayyuka da suka fi yawan lada kuma suka fi soyuwa ga Allah,  don haka ne ma sahabbai suke tambayan Annabi  mafi darajan ayyuka da daukaka  wani mutum ya ce :'' ya Manzon Allah menene musulunci ? sai Manzon Allah ya ce :- '' (Zuciyan ka ya mika wuya ga Allah  mabuwayi da daukaka  kuma Musulmai su kubuta daga harshen ka da hanunka) sai ya ce :-    a musulunci wani abu ne ya fi ? sai ya ce ''imani  sai ya ce : ; to meye imani ?   sai ya ce ka yi imani da Allah da mala'ikunsa da littatafansa da manzanninsa , da  tadawa  bayan mutuwa'' sai ya ce wani imani ne ya fi ?  sai ya ce '' hijira'' sai ya ce to menene hijira ?  sai ya ce ka kauracewa mummuna )
Na daga ciki fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : (sallar jam'i ta fi sallar daidaiku da daraja (27) ashirin da bakwai)
Da fadinsa :(Dirhami guda ya riga dirhami dubu dari ).
wanda ya  yi kwadayin abin da zai amfane shi to zai kirdadi abin da gurbinsa zai wanzu,falalarsa ya dauwama a duniya, ya zarce zuwa rabauta a lahira, Allah Madaukakin sarki ya ce :(kuma a cikin su akwai mai cewa: ya Ubangijinmu ka bamu mai kyau a cikin duniya da mai kyau a lahira,kuma ka tsare mu daga azabar wuta. Wadannan suna da rabo daga abin da suka sana'anta, kuma Allah mai gaggawan sakamako da yawa ne.)
  Abin da ake nufi da kyakkyawa biyu shi ne ; ni'imar duniya da na lahira  musulmi mai lura  wanda ke kwadayin abin da zai amfane shi  zai fara ne da kan shi ya gyarata  , hakanan kuma zai wadatu  ga dukkan abin da bai shafe shi ba   Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :-  (yana daga cikin kyautatuwan musuluncin mutum  yabar abin da bai shafe shi ba ,.)
Duk wanda   ya bar abin da bai shafe shi ba ya shagalta da abin da ya shafe shi  to musuluncin shi zai kyautata  ,  ya kebanta don abubuwan da suka fi muhimmanci , ya kuma daukaka da ayukan shi   ya tsarkake ran shi da  da dabi'un shi da harshen shi  ya zama mai kula da rayin shi   , kuma  ya zama mai gadin halayen shi yana mu'amala da kan shi da gaskiya da adalci .
Shu'aibu Amincin Allah ya tabbata a gare shi ya ce  da mutanen shi :-( kuma ba ni nufin in saba muku zuwa ga abin da nake  hana ku daga gare shi  , ba ni nufin kome face gyara gwargwadon   da na sami dama  . kuma  muwafakata ba ta zama ba face ga Allah a gare shi na dogara kuma zuwa gare shi nake komawa da rusunawa).
Kwadayin abin da zai amafanar yana sa a fiskantar da karfi zuwa ga gini da habaka kasa  yana haifar da albarka a rayuwa  ya sanya aiki ya zauna da gindin shi ya kafu  Allah madaukakin sarki  ya ce :- ( Amma abin da ke amfanan mutane zai zauna a cikin kasa ).
 Kwadayin abin da zai amfanar yana bukatar a samu karfi  na  mu'amala  tare da  ababan jin dadi tare da bukatun rayi, don ba kowane abu da ake sha'awa ne mai amfani ba, kuma ba kowane abin ki ba ne mai cutarwa ba, sai da shi mutum mai hankali zai fifita amfani mai girma mai yawa akan amfani na yanzu dan kankani,Allah Madaukakin sarki yace :
(Aa ha ba haka ba kuna son mai gaggawar nan (Duniya) ne.kuna barin ta karshen(Lahira).
Kuma ya ce: (Akwai fatar cewa ku ki wani abu alhali shine mafi alheri a gare ku, kuma akwai fatar cewa kuna son wani abu alhali kuwa shine mafi sharri a gare ku, kuma Allah ne yake sani kuma ku ba ku sani ba.)
Abokantaka da wanda zai amfanar na daga cikin abubuwa na tilas a kwadayin abin da zai amfanar, domin dukkan aboki na koyi ne da aboki.akwai bambanci nesa ba kusa ba abota da kasalalle da mai basira da hangen nesa. Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Mutum na kan addinin abokinsa ne, to dayanku ya dubi wanda zai yi abota da shi,)
Annabi Muhammadu () yana cewa: - “Misalin aboki nagari da abokin banza, kamar misalin mai daukar turare ne da mai hura zuga-zugi, mai daukar turare ko dai ya shafa maka ko ka sayi turare a wurinsa ko kuma ka ji kamshi mai dadi a wurinsa, mai hura zuga- zugi kuma ko ya kona maka kaya ko ka ji wari a wurinsa” Bukhari ne ya rawaito
Idan abubuwan amfani suka taru ga musulmi to sai ya gaggauta zuwa ga aiki, don kowa an saukake mishi aikin da aka halicce shi dominsa,to abin da aka shar'anta ga ko wane mutum ya aikata abin da ya ke da ikon yi na daga alheri,kamar yadda Allah Madaukakin sarki yace :(ku ji tsoron Allah gwargwadon abin da ku ka sami iko)
Hakika ta kan iya kasancewa abin da bai fi falalan ba ka ke da iko akai fiye da abin da ya fi falala, kuma ka samu lada ta gun shi fiye da wanda ya fi falala, to abin da ya fi ga musulmi ya nemi abin da yafi amfani a gare shi, to a shaninsa wannan shi ya fi, ba wai zai nemi abin da ya fi fifikon falala na gabadaya ba,Idan mutum na da uzuri ko zai wuyata a gare shi yin abin da ya fi falala, to lalle Allah ya raba ayyuka kamar yadda ya raba arziki,
Duk yadda mutum ya kai da kwadayin ya samu abin da zai amfane shi to ba zai iya cinma manufarsa ba da burinsa ba face idan Allah ya taimake shi ya datar da shi ya yi mishi muwafaka (ka yi kwadayin abin da zai amfane ka ka nemi taimakon Allah) shine wanda tsarki ya tabbata a gare shi kuma ake neman taimako daga gare shi, wanda dukkan halittu ke neman mafaka a gare shi,bisa zabi ko larura,kowa na neman taimakonsa a halin tsanani ko sauki,da halin yelwa ko cuta, a ko yaushe mutum na cikin bukatan taimakon Allah, a dukkan halin da ya ke ciki,a dukkan al'amuran addininsa da na duniyarsa,to neman taimakon Allah da rokon shi agaji bisa yardarsa na daga cikin adua mafi amfani, kuma shine abin da harshen muminai ya fi nanatawa da karfafawa, raka'a bata cika a sallah muddin ba a ambace ta ba.(kai kadai muke bautawa kuma kai kade muke neman taimako)  
Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Ina ma wasiyya ya kai Mu'az kar ka bar fadin wannan adu'a karshen kowace sallah,: (Allahumma a'inni ala zikrika wa shukrika wa husni ibadatika)ya Allah ka taimake ni bisa ambatonka da gode maka da kyautata bauta maka).
Al'istianatu Billah: shine bawa ya tabbatar kuma ya gamsu da raunin karfinsa da dabararsa, kuma karfi da dabara na Allah ne shi kadai Albarka da daukaka su tabbata a gare shi,sabo da bawa na da gazawa na cin gashin kan shi wurin janyo wa kan shi amfani ko tunkude wa kansa cutarwa. Ba mai taimaka mishi a maslaharsa ta duniya da lahira face Allah shi kadai, duk wanda Allah ya taimakawa to shine ya samu taimako,duk wanda Allah ya tabar da shi shine tababbe.to wannan shine tabbatar da Lahaula wala kuwwata illa billah  
(Kada ka gaza) sako ne na himmatuwa da tasowa a shiga fagen aiki, da bigire na kokari da kyauta da jajarcewa wajen tinkaran wahalhalu da fiskantar kalu bale, don raya kasa, Allah Madaukakin sarki yace : (shine ya kaga halittar ku daga kasa kuma ya sanya ku masu raya ta da zama a cikinta).

Huduba ta biyu
(Kada ka gaza) don mai gaza wa ya kayyade kansa da wani abu na kashe jiki,da dabaibaye tafiyarsa da wahami na  kasala, ya mika tunaninsa ga saka burace –burace, gazawa na bude aikin shaidan, kuma mabudi ne na dukkan sharri da fadinsa ina ma da kaza da kaza da na yi kaza, yana bijiro mishi da bakinciki da bacin rai,da tsoro da rowa, da taruwan bashi da finkarfin mazaje sabo da haka ne yana daga cikin aduar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi:(Allahumma inni auzu bika minal hammi wal huzun, wa'ajzi walkasal walbukhli waljubn wadala'iddain wa galabatir rijal)      
Ya Allah ina neman tsarin ka daga bakinciki da bacin rai da gazawa da kasala da rowa da tsoro da yawan bashi, da galaba namazaje.
Wanda ya zauna tare da masu gazawa, to bashi da wata kima a cikin al'uma, kuma bai da tasiri a kasa, bai da matsayi a cikinAl'uma,wanda ya yi zaman kashe wando da rashin aikin yi, to ya fita daga insaniya (DanAdamtaka), Duk wanda ya saba da kasala ya karkata  zuwa hutu to kuwa zai rasa hutu, wannan hadisi ne maigirma ya tatttaro a dunkule dukkan hanyoyi na yin nasara, duk wanda yayi kwadayin abubuwa masu amfani to ya yi kokari acikinta ya bi sabubanta, ya nemi taimakon Ubangijinsa wurin samunta da cikan ta to hakan shi ne kamalarsa da dacen sa, to a duk lokacin daya daga cikin wadannan abubuwa uku suka tsere masa to alheri zai tsere masa dai dai gwargwadonta,
(ka yi kwadayin abin da zai amfane ka ka nemi taimakon Allah kar ka gajiya).












   
   

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق