الجمعة، 25 يناير 2019

ALBISHIR A MUSULUNCI


Hudubar Masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na shaikh Abdulmuhsin Alkasim 19-5-1440
Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna gode masa kuma muna neman taimakonsa
Muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu  da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, wanda ya batar kuma babu mai shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya,kuma na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa. Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa.
Bayan haka, ku ji tsoron Allah -ya ku bayin Allah- cancancin tsoronSa, don cikin tsoron Allah akwai karuwar  ni'ima da tunkude azaba.
Ya ku musulmai! Addinin musulunci addini ne na fidira yana kira zuwa ga kyakkyawan kuduri da kyawawan dabiu, da sifofi abin yabawa, yana lura da yanayin halin da mutum ke ciki, kuma ya faranta masa rai a yanzu, kuma ya kwadaitar da shi fatan alheri a nan gaba, da yi wa halittu albishir da abin da zai dadada musu rai, a matsayin bauta ga Allah da kusanci, Allah ya ce : (ka yi albishir ga muminai). Hakika Allah ya siffanta kanSa da hakan sai yace: (wancanninka shine abin da Allah ke albishir ga bayinSa)     sabo da girman matsayi irin na albishir a cikin zukata mala'iku ke zuwa da shi, Allah Mabuwayi da daukaka ya ce:(Hakika manzanninMu sun zo wa Ibrahim da bushara). Yin bushara ga bayin Allah muminai na daga cikin manufa na turo manzanni, Allah Madaukakin sarki ya ce :(Ba mu turo manzanni ba face masu albishir masu gargadi)
Isa amincin Allah su tabbata a gare shi ya zo da albishir sai Allah ya ce : (Kuma ina mai albishir da wani manzo da zai zo a bayana sunansa Ahmad)
Kuma yana cikin siffofi mafi kyau na mutanen farko, (A yayin da mai albishir ya zo sai ya jefa ta (rigar) akan fiskarsa sai ya koma mai gani)
Allah ya turo Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da bushara na falaloli da  gidajen aljanna masu ni'ima ga Al'umarsa,Allah madaukakin sarki ya ce : (Ba mu turo ka ba face mai albishir kuma mai gargadi)
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance mai yawan Albishir ne ga sahabbansa, dukiya ya zo mishi daga kasar Bahrain sai ya ce da su (Ku yi bushara da fatan alheri na abin da zai dadada muku rai) Bukhari da Muslim ne suka rawaito.  
Na daga cikin koyarwarsa ya kan tura masu da'awa ga sassa na duniya don su yi wa mutane bishara da ni'ima ta musulunci, sai yace da Mu'az dan Jabal da Abu Musa Allah kara yarda a gare su a yayi da ya tura su yaman :(ku saukaka kada ku tsananta, ku yi bushara kada ku kore mutane,) Bukhari da Muslim ne suka rawaito,
Hakika Allah ya bada labari cewa na daga cikin siffofin muminai albishir ga junansu, (kuma idan aka saukar da wata sura to daga cikinsu akwai wadanda suke cewa: wanene a cikin ku wannan sura ta kara masa imani? To amma wadanda suka yi imani, to ta kara musu imani, kuma su suna yin bushara (da ita).  Wato sashe na yi wa sashe albishir da baiwa da Allah ya yi musu.
A addinin musulunci akwai albishir masu yawa daya bayan daya  ga mabiyansa, bushara mafi girma ga wanda ya tabbatar da tauhidi (kuma wadan da suka nesanci shaidanu ga bauta musu kuma suka maida al'amari ga Allah,suna da bushara , To ka bayar da bushara ga bayi na)
To idan bawa ya tsayu a kan biyayya ga Allah da kadaita shi to yana da albishir da gidajen Aljanna na ni'ima, (Lalle wadannan da suka ce Ubangijinmu shine Allahm sa'annan suka daidaitu Mala'iku na sauka a gare su(lokacin zuwan ajalinsu) suna ce musu) kada ku ji tsoro kuma kada ku yi bakinciki, kuma ku yi bushara da aljanna.wanda kun kasance ana yi muku wa'adi da ita.
   Duk wanda ya hadu da Allah bai hada shi da wani to albishirinsa Aljanna ne, Mala'ika jibrilu amincin Allah ya tabbata a gare shi ya ce da Manzon Allah (ka yi albishir ga Al'umarka cewa Duk wanda ya mutu bai hada Allah da wani to zai shiga Aljanna.)Bukhari da muslim ne suka rawaito
To duk wanda ya bi Alkur'ani da sunna Allah na mishi albishir da gafara da lada mai girma, (kana yin gargadi kawai ga wanda ya bi Alkur'ani ne kuma ya ji tsoron Mai rahama a fake, to ka yi masa bishara da gafara da wani sakamako mai karamci ).
Tushen shiriya shine ilimin da ya hadu da aiki  Allah madaukakin sarki yace :(wadan da suke sauraron magana sa'annan su bi mafi kyaunta, wadancan sune Allah ya shiryar da su, kuma wadancan su ne masu hankali).
Kuma shi musulmi mai kankan da kai ga Ubangijinsa mai mika wuya ga umarninSa, mai tawaliu ga halittunSa zai samu bushara, Allah madaukakin sarki ya ce : (Kuma ka yi bushara ga masu kankantar da kai)   
Duk wanda wata musiba ta same shi sai ya maidawa Allah lamarin shi ya yi hakuri bisa ga abin da Allah ya hukunta ya kaddara, to yana da albishir daga Ubangijin talikai. Allah madaukakin sarki ya ce : (ka yi albishir ga masu hakuri wadan da idan musiba ta same su sai su ce :lalle ne mu daga Allah muke kuma gare shi za mu koma. Wadannan akwai kyakkyawan yabo daga ubangijinsu da wata rahama kuma wadannan su ne shiryayyu.)
Kyautayi ga Allah da halittunSa alheri ne a duniya da lahira Allah ya ce : (ka yi albishir ga masu kyautatawa).
Kuma muminai ana musu albishir da daddadan rayuwa da sakayya mai girma. Allah madaukakin sarki ya ce: (ka yi albishir ga muminai suna da wani falala mai girma daga Allah).
Na daga cikin falalarSa gare su yi musu bushara da abin da Allah ya alkawarta musu na gidajen Aljanna masu ni'ima da dukkan abin da suke fata a cikinta. Allah madaukakin sarki ya ce : (Wadanda suka yi imani kuma suka yi ayyukan kwarai  suna cikin fadamun aljanna suna abin da suke so, a wurin Ubangijinsu waccan fa ita ce falala mai girma. Wancan shi ne Allah ke bayar da bushara da shi ga bayinSa wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyuka na kwarai).
Bisharori masu yawa na bin juna cikin rayuwar duniya har bayan mutuwa. Allah madaukakin sarki ya ce : (To lalle masoyan Allah babu tsoro a gare su kuma ba bakinciki. Wadanda suka yi imani kuma suna jin tsoron Allah. Suna da bushara a cikin rayuwar duniya da ta lahira babu musanyawa ga kalmomin Allah, wancan shine babban rabo mai girma  ).
Idan mutuwa ta zowa mumini sai a mishi bushara da mafi daukakan masaukai Manzon Allah tsira amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Mumini Idan mutuwa ta zo mishi zaa mishi albishir da yardar Allah da karamarSa sabo da haka ba wani abu da ya fi soyuwa a gare shi fiye da abin da ke gaba gare shi, sai ya so haduwa da Allah to Allah ma ya so haduwa da shi,) Bukhari ne ya rawaito.
Malaiku na cewa ka fita ya kai rai mai tsarki, ana maka albishir da hutawa da kyakkyawan abinci, da Ubangiji wanda ba zai yi fushi ba, sannan a haura da shi zuwa sama, sai a bude mishi sai a ce :wanene wannan sai su ce wane ne, sai a ce maraba da rai mai tsarki wanda ya kasance cikin jiki mai tsarki, ka shiga kana godiya,ana ma bushara da hutu da abinci, da Ubangiji ba zai yi fushi ba, ba zaa gushe ba ana fada mishi haka har a kai ga saman da Allah Mabuwayi da daukaka ke cikinta,)Ahmad ne ya rawaito.
   Idan kiyama ta tsaya bishara zata bayyana a fiskar muminai, Allah madaukakin sarki ya ce : (wasu fiskoki a wannan ranar masu haske ne, masu dariya masu bishara)
Suna da bushara a yanayi mafi tsanani, lokacin da mutane zasu kasance a kan siradi bisa jahannama, Allah mai tsarki da dauka ya ce : ( Rãnar da zã ka ga mũminai maza da mũminai mãtã haskensu nã tafiya a gaba gare su, da kuma dãma gare su. (Anã ce musu) "Bushãrarku a yau, ita ce gidajen Aljanna." Ruwa na gudãna daga ƙarƙashinsu sunã mãsu dawwama a cikinsu. Wannan, shĩ ne babban rabo maigirma. )
Idan sun shiga aljanna suna da sakayya mai yawa a wurin Ubangijinsu.(  kuma ka yi bushãra ga waɗanda suka yi ĩmãni da cewa: Lalle ne sunã da abin gabãtarwar gaskiya a wurin Ubangijinsu.)
Musulmi na so wa 'yan'uwansa abin da ya ke so wa kan sa, kuma yana kokari don ya faranta musu, bishara da alheri na cikin kofofi mafi sauki na ribatar zukata, idan wata ni'ima ta sabunta ga dan'uwanka na  addini ko duniya, to ka mishi Albishir da ita,kamar yadda mala'iku suka yi wa Annabi Ibrahim albishir da Isma'il Amincin Allah su tabbata a gare shi, Allah madaukakin sarki ya ce : (  Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro mai haƙuri)
  Sun yi mishi bishara da Ishak Amincin Allah ya tabbata a gare shi Allah madaukakin sarki ya ce : ( Kuma Muka yi masa bushãraDa Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne.)
An yi albishir ga zakariyya da Da bayan ya yanke tsammani  (Allah Ya karɓa) "Yã zakariyya! Lalle ne Mũ, Munã yi maka bushãra da wani yãro, sunansa Yahaya. Ba Mu sanya masa wani takwara ba a gabãni).
 Wani Malaika ya sauka ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wanda bai taba sauka ba :(Bushara gare ka da haske biyu da aka baka ba wani Annabi da aka bawa su kafin kai, fatiha da karshen suratul bakara ba za ka karanta su ba sai an baka su.)Muslim ne ya rawaito.
Na daga cikin koyarwarsa Manzon Allah su tabbata a gare shi,Albishir ga wanda wani bakinciki ya yaye a gare shi, ya ce da Aisha Allah kara yarda a gare ta: (Albishirinki ya A'isha, amma Allah ya barrantar dake)
Mace tagari mai biyayya ga mijinta sakayyarta Aljanna ne,Jibrilu amincin Allah su tabbata a gare shi ya sauka ga Annabi sai yace :(Ya Manzon Allah ga khadija nan tana zuwa da kwano acikin shi akwai miya ko abinci ko abin sha, to idan ta zo ma to ka isar mata da gaisuwa daga Ubangijinta kuma daga gare ni, kuma ka mata bushara da gida a Aljanna na Zinari ba hayaniya a ciki ko gajiya,)Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Kaifin hankali na ga rarrashin wanda halinsa ya kyautata idan wani abu ya dame shi sai a mishi bushara da fatan alheri, a farkon saukan wahayi ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai ya shiga gun khadija Allah kara yarda a gare ta sai ya ce da ita :(Hakika na tsoracewa kai na, sai ta ce da shi:, A'a albishir na rantse da Allah, Allah ba zai taba kunyata ka ba har abada). Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Duk wanda ya lazimci gaskiya ba tare da ketare iyaka ba, ko jafa'i to yana da bushara ta lada mai yawa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (ku kirdadi daidai ku kusanto ku yi bishara) Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Allah na farinciki da tuban bawa sabo da falala da karamci irin nashi, kuma ranar da bawa zai tuba zuwa ga Allah shine mafi alherin ranaku a gare shi a duniya, sabo da abin da tuba ke janyowa ga bawa na maslaha a duniya da lahira, Ka'ab dan Malik bai halarci yakin tabuka  ba,Allah ya yarda a gare shi, shi da abokan nasa biyu ba tare da wani uzuri ba, sannan Allah ya karbi tubansu, sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana mai albishir ga ka'ab, sai yace : (Bushara a gare ka  da rana mafi alheri a gare ka tun daga randa mahaifiyarka ta haife ka),
Kuma duniya kan kuntata ga wanda ajalinsa ya kusato, amma kuma yana jin dadin kalamai masu dadi, da zai ji ta sabo da kusacin kaurarsu ga gidan lahira bai san ina ya nufa ba,  Mutuwa ta zo ga  Amru dan As, sai ya yi kuka mai tsawo, sai dansa na cewa : Ya baba na a se Annabi bai ma albishir da kaza ba)Muslim ne ya rawaito.
 Mafi girman abin da musulmi zai yi albishir da shi shi ne daukakan wannan addini da isan sa duk inda dare da rana ya isa,
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Yi wa wannan al'uma bishara  da daraja  da daukaka, da addini da nasara da samun mulki a doron kasa)Ahmad ne ya rawaito). Ahmad ne ya rawaito
Duk wanda aka mar albishir da alheri ya zama mustahabbi ne a gare shi da yayi wa Allah sujada na godiya, kuma ya saka wa wanda ya mishi albishir da abin da zai iya,Ka'ab dan Malik Allah ya kara yarda a gare shi ya ce  a hadisin kissarsa da sahibansa : (A yayi da ina zaune a halin da Allah ya ambata game da mu, hakika raina ya kuntata, kasa ta min kunci da duk fadinta, sai na ji mai yekuwa ya cika dutse da sautin sa yana cewa :ya ka'ab dan Malik Albishirinka, sai yace :sai na fadi ina mai sujada, sai na san cewa yayewan bakinciki ya zo, wasu masu albishir suka tafi ta gun sahibai na, wani mutun yayi gudu haye kan doki zuwa gare ni, wani mai   kokari daga kabilar Aslama ya hauro dutse to sautin nasa har ya fi  dokin sauri, yayin da wanda na ji sautin nasa ya iso sai ya min albishir,sai na tube tufafi na biyu na tufatantar da shi su sakayya ga albishir da ya yi min, Wallahi ban mallaki waninsu ba,sai na ari wasu tufafi biyu na sanya su, sai na tafi zuwa ga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ,sai ga mutane suna ta tara na tawaga tawaga suna mini barka da karbar tuba, suna cewa: Barkanka da tubar da Allah ya amsa ma).Bukhari da Muslim ne ya rawaito.
Bayan haka ya ku musulmai:
Ba wani addini da ya fi addinin musulunci kyau, don shi addini ne na farinciki da jindadi, yana  kwadaitarwa gurin cusa walwala ga al'uma, mafi dacewan mutane da alherin musulunci sune musulmai, Bushara tushe ne cikin kiran halittu zuwa ga addini, da kwadaitar da shi cikin zukatarsu.
Ina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan abin jefewa,
 (Yã kai Annabi! Lalle Mũ Mun aike ka kanã mai shaida, kuma mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. 
  Kuma mai kira zuwa ga Allah da izninSa, kuma fitila mai haskakãwa. 
  Kuma ka yi bushãra ga mũminai cħwa, sũnã da falala mai girma daga Allah.) 
 
Allah sa mini Albarka ni da ku cikin Alkur'ani mai girma.


Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa kyautatawarsa, godiya ta tabbata agare shi bisa taufikinsa da datarwarsa, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, sabo da girmama sha'aninSa, kuma na shaida Annabinmu Muhammad bawanSa ne kuma Manzonsa ne,tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa da karin  aminci tabbatace mai yawa.
Ya ku Musulmai:
Mafi girman mai albishir a musulunci shine Alkur'ani mai girma, dukkan shi shiryarwa ne da albishir Allah madaukakin sarki ya ce : ( kuma Mun saussaukar da Littãfi a gare ka dõmin yin bãyani ga dukkan kõme da shiriya da rahama da bushãra ga mãsu mĩƙa wuya (Musulmi). 
Kuma da Kyautata yabo ga wanda ya kyautata ba tare da ya nemi hakan ba, na daga cikin albishir na kusa ga mumini, an ce da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,(bani labarin mutumin da yana aikata aikin alheri kuma mutane na yabonsa bisa haka, sai manzon Allah yace : Ai bushara ce ta mai gaugawa ga mumini.)Muslim ne ya rawaito.
Mafarki na kwarai na farantawa ba ya korewa kuma yana cikin masu bishara, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Ba abin da ya rage na annabtaka sai masu bushara, sai suka ce: menene masu bishara? Sai yace : Mafarki nagari,) Bukhari ne ya rawaito.
Allah na turo iska ne da bushara ta ruwan sama don ya farantawa mutane rai  kafin saukarsa da bayan saukarsa.
Kuma akwai daga ãyõyinSa, ya aika iskõki mãsu bãyar da bushãra)  
Daddadan lafazi na bishara ne da alheri, kuma yana cikin kyakkyawan fata, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Ba rabuwar cuta ko camfi kuma kyakkyawan fata na burge ni sai suka ce : menen kyakkyawan fata ? sai yace daddadar kalma).Bukhari da muslim ne ya rawaito.
Sannan ku sani lallai Allah ya yi muku umarni da salati da aminci bisa ga Annabinsa

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق