Hudubar Juma'a
a Masllacin Annabi 6-12-1439AH
Sheikh Salah bin
Muhammad Al- Budair
Hudubar farko:
Dukkan yabo da godiya
sun tabbata ga Allah , godiyar da ta dace da ni'imarsa da kyautarsa, na shaida
ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya,
ba abi bauta bisa cancanci koma bayansa.Na shaida cewa Annabinmu kuma shugabanmu Muhammad bawansa ne kuma
Manzonsa ne , Annabinsa ne zababbensa
abin kaunarsa ,Majibincinsa yardajjensa, abin kulawarsa, tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi da
Iyalan shi da sahabban shi salati madawwami
muddin gari na waye wa haske na bayya
Bayan haka ya ku
musulmai! Ku ji tsoron Allah ta hanyar
aiki zuwa ga neman yardarsa da nesatan saba masa .
( ya ku wadan da
suka yi imani ku ji tsoron Allah
cancancin tsoronsa kar ku mutu face kuna musulmai)
Ya ku musulmai!
Hakika iska kakkamsa ta
kada tsarkakakka daddada wacce ke dauke da kamshin ayyukan Hajji da ruhinsa,
da labaransa da manyan alamominsa da farillansa, da Haramin Allah mai
aminci da ya cika shi da karama
da kawa da kaye da tsarkaka da
daukaka,
Ga tawagar Alhazai suna
nufan Dakin Ka'aba suna (talbiyya ) amsa kira daga kowane sako mai zurfi suna
cike da farin-ciki da dadin rai da washewar
zuciya.
Wannan tawagar Allah din wanda ta fiskanto
zuwa ga Ubangijinta cikin gaggawa ta shimfida tafukan kaskanci tana mai
rusunawa , sai ga idanuwanta na cika da
hawaye , adu'o'in ta na daguwa zuwa sama
Gare ka na zo ya Ubangiji ina mai amsa kira
*** Ka albarkaci hajjina da adu'o'I na
ya Ubangiji
Na zo babu guzuri fatana ne kyautar ka *** Baya hasara duk wanda ya nemi kyautan ka
Alhazan dakin Allah ku girmama harami kuma ku ga girmar alfarmar sa ku kiyaye matsayin sa ku bada kariya ga kwarjinin sa , ku kiyaye bin doka da oda , ku yi nesa da abin
da zai kawo matsala a aikin haji ko kuma
zai sabawa manufofin shi ko kuma zai ci
karo da hadafin shi haji ba wuri ne na husuma da cece ku ce
ba da musu ba kuma gune na taron gangami ko zanga-zanga ba ba kuma gu ne na daga tutoti na
ta'assubanci ba ko na
kungiyanci ba Hajji girman shi ya fi a ce wuri ne na bajekolin sabani da kungiyanci da mazhabanci ko guri ne na bangaranci na siyasa ba .
Ya ku Alhazai da masu Umra ku nemi fahimtar fikhun
Hajji da sharudan isan sa da siffan aiwatar da shi kafin ku sanya ihrami ku nufi dakin ka'aba mai alfarma sau dayawa Alhaji kan
aikata wani babban al'amari har
sai ya kai gari mai tsarki sannan ya kama aikin shi na hajj sannan gashi bai san hukunce-hukuncen shi
ba bai kyautata cika shi ba sai ya koma zuwa garin shi yana mai halin ya
bar wani rukuni ko ya
yada wani sharadi ko kuma ya yi sakaci
da wani abu na wajibi ko ya aikata wani abin da aka hana mai ihrami ya aikata , ko ya zo da wani abu da aka yi gargadi a
kai .
YA TAWAGAN
ALHAZAI DA MAZU UMRA DA MAZIYAR
TA :
Akidar musulunci ta hada ku , farillan hajji ya sa ku a tsari dankon zumuncin addini ya hada ku to,
ku tausayawa juna ku yi ludufi
, ku yi taimakekeniya kada ku
yi tunkudedeniya kar ku yi cunkoso kar
ku yi fada ku tausayawa masu rauni ku shiryar da wanda suka bace ku taimaki gajiyayye mabukaci .
Wajibi ne a gare ku ku tausaya ku yi dako
da saukin lamari da yafiya da
barin cunkoso da kuma janyo natsuwa da kuma jin tsoron Allah a cikin zuciya da lazimtar mutuntawa da tausasawa , .
Na hore ku da ku yi nesa daga jidali da
musu da dadin baki da kiyaye cece ku ce da jayayya
da kuma wasa irin na magana ku
nisaci fadin batsa da alfasha da
yasassar magana da kauracewa juna da zage-zage da suka
lakuba marasa kyau, ku kiyaye Hajjin ku
daga kazantar shirka , da najasar bidi'o'I da fararrun abubuwa .
Ku nisanci ketare iyaka ku jefi jamra da kananan duwatsu wanda girman su bai
fi na gujjiya ba ko kuma kwallan dabino , ko kuma
kan yasu ku kiyaye ketare iyaka
na shari'a ku yi koyi da masoyi abin kauna
zababbe tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi , a ibadodin ku da ayukan ku na hajji ku yawaita tuba da istigfari ku bayyana kankan da kai da marairaicewa da
nadama da nuna bukatuwa , da nuna
talauci da nuna bukata ga Allah domin
ku dinnan ku na wurin da rahama ke zuba
kuma kuna bigire da wurin karba
da wurin da ake sa ran karban adu'a
da gafara da 'yantawa daga wuta
ku tuna girman wurin da darajan zamanin Allah na karban adu'o'in ku da
amsawa da neman gafarar ku da yarda da karban Hajjin ku da sanya
aikin ku ya zama abin godiya
zunuban ya zama abi gafartawa Hajjin ku
ya zama wadda aka yi da'a ne a cikinta
, wanda ya yi hajji baiyi batsa ba bai yi fasikanci ba zai koma kamar yanda mahaifiyar shi ta haifiyar shi ta haife shi, shi hajjin
da aka yi da 'a a cikin shi bai da sakayya sai aljanna ina fadin abin da kuke
ji kuma ina neman gafaran Allah , ku
nemi gafaran Allah domin shi mai yawan
gafara ne ga masu komawa gare shi da
tuba.
HUDUBA TA BIYU
Dukkan yabo da godiya
sun tabbata ga Allah wanda bisa ludifin sa ya tattara wanda ya tattaro na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai
Allah wanda shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya ya warkar da ni'imar sa da mutumin da ciwon sa
ya sa ya yanke tsammani daga magani na
shaida cewa Annabin mu kuma shugaban mu Muhammad bawan sa ne kuma Manzon sa ne
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabban shi , tsira
mai wanzuwa da aminci mai bibiyan juna .
BAYAN HAKA:
YA KU MUSULMAI:- ku ji tsoron Allah ku yi murakabarsa
, ku mishi biyayya kada ku saba masa, (ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron
Allah ku kasance tare da masu gaskiya )
YA KU MUSULMAI :
Ranar arfa rana ne mai daraja
da daukaka kuma idi ne mai girma ga ma'abota maukif rana ne
da ake 'yanta wuyaye a cikin shi ana sauraron adu'o'i kuma a amsa rana ne wanda alherin Ubangijin mu ya yawaita
kuma ya dadada, ba wani rana da Allah ya
fi 'yanta bawa daga wuta kamar ranar
arfa lallai yana kusanta sannan ya yi
alfahari da su gaban mala'iku sannan ya ce mai wadannan suke so .
Adu'an da ya fi ko wanne albarka da yalwa
a wurin lada da saurin amsawa
shi ne Aduar Arfa, to ku yi kokari da kankan da kai da kyautata yabo , da Adu'a
, kuma mustahabbi ne yin azumin ranar Arfa ga wanda bai hajji, azumtar ta na
kankare zunuban shekarar da ta gabata,
da shekara da ta biyo ta.
Mustahabbi ne yin
kabbarori a karshen sallolin farillah, tun daga asuban ranar Arafa har zuwa
ranar karshe na ayyamu al-Tashrik, wanda aka tsere wa a wani sashe na sallah to zai kawo su kabbarorin
ne bayan ya rama sallarsa, Alhazai za su
fara kabbarorin ne daga azahar na ranar Babbar sallah.
Ya ku Musulmai!
Ku yi kabbarori a sassa
da nahiyoyi,ku yi kabbarori a gine gine da sarari, ku yi kabbarori a gidaje da
jeji, ku yi kabbarori a safiya da maraice, ku yi ta kabbarori har ya cika sama,
Allahu Akbar
Allahu Akbar la'ilaha illal lahu Allahu
Akbar walillahil Hamd
Ku yi salati da aminci
ga Ahmadu mai shiryarwa mai ceto ga
dukka halittu, wanda ya mishi salati guda Allah zai mishi guda goma.
Ya Allah ka yi dadin
tsira ga bawan ka kuma manzonka Muhammad,
ya Allah ka yarda da iyalanshi da sahabbai da mu ya mai karamci mai kyauta.
Ya Allah ka daukaka
Musulunci da Musulmai ka kaskantar da shirka da mushrikai, ka rusa makiya Addini,
ka sanya garuruwan musulmai cikin aminci da natsuwa da kwanciyan hankali da
zaman lafiya ya Ubangijin talikai
Sannu Kowa,
ردحذفSunana Mista, Rugare Sim. Ina zaune a Holland kuma ni mai farin ciki ne yau? kuma na gaya wa kaina cewa duk wani mai ba da bashi wanda zai tseratar da ni da iyalina daga mummunan halinmu, zan koma ga duk mutumin da ke neman bashi a kansa, ya ba ni farin ciki a gare ni da iyalina, na kasance ina buƙatar aro na € 300,000.00 don fara rayuwata gaba daya kamar ni uba daya ne da yara 2 Na hadu da wannan mai gaskiya kuma Allah yana tsoron mai bada rancen da zai taimake ni da rancen € 300,000.00, shi mutum ne mai tsoron Allah, idan kana bukatar aro Kuma za ku biya bashin don Allah ku kira shi ku gaya masa cewa (Mr, Rugare Sim) yana nuna muku shi. Tuntuɓi Mista, Mohamed Careen ta imel: (arabloanfirmserves@gmail.com)
MAGANAR BAYANIN AIKIN LATSA
Sunan rana......
Suna na tsakiya .....
2) Jinsi: .........
3) Bukatar Lamuni: .........
4) Tsawon Lamuni: .........
5) Kasa: .........
6) Adireshin Gida: .........
7) Lambar Waya: .........
8) Adireshin Imel ..........
9) Gashi na wata-wata: …………… ..
10) Aiki: ...........................
11) Wanne rukunin yanar gizo kuka kasance game da shi …………… ..
Godiya da kuma mafi kyawun gaisuwa.
Email arabloanfirmserves@gmail.com