Hudubar Juma'a na Masllacin Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi, sheikh Abdullah bin Abdurrahman Al-Buaijan 13-12-1439
HUDUBAR FARKO
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda da ni'imarsa ne ayyuka
nagari ke cika, ina gode mishi tsarki ya tabbata a gare shi,ina neman
taimakonsa bisa abin da ya shude da abin da zai zo, na shaida, ba abin bautawa
da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, ya yi wa Alhazai
baiwan kammala hajjinsu, bayan sun tsaya
a farfajiyan arfa.
Na shaida Annabi Muhammadu bawan
sa ne kuma manzon sa ne Ubangijin shi ya turo shi da shiriya da hujjoji bayyanannu tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi da iyalan shi da sahabban shi da
gaisuwa mafi tsarki.
BAYAN HAKA:
Ina muku wasiyya ya ku bayin Allah da kuji tsoron Allah , domin tsoron
shi shi ne mafi alherin tufafi kuma shi
ne mafi alherin guzuri kuma shi ne
mafificin hanya zuwa ga yardan Ubangijin bayi
( Ya ku wadanda suka yi imani in
kun ji tsoron Allah zai sanya
muku haske da zai banbance tsakanin
karya da gaskiya zai kankare muku
miyagun ayyukan ku zai gafarta muku zunuban ku
Ubangiji ma'aboci falala ne mai
girma ).
Maziyarta dakin Allah mai
alfarma
Albishir ga wanda ya amsa kira kuma * ya nufi ta bigiren wurare masu tsarki ,yana mai hailala yana
neman rahama.
Barkanku Alhazai maziyarta dakin Allah mai alfarma tun da Allah ya
shiryar da ku ya karrama ku,ya muku baiwa na saukake muku hajji wanda da yawa
daga cikin mutane basu samu iko ba.
Barkan ku da kuka samu
datarwa don sauke ayukan haji
daya daga cikin rukunnai guda biyar na musulunci
kuka amsa kira kuka kyautata sauke nauyi .
Barkan ku an daga darajojinku an gafarta muku zunuban ku an kankare muku kusakuran ku an sitirce muku laifukan ku da izinin Allah Masanin
gaibi .
Barkan ku kun ciyar da dukiya kun bada lokaci kun bada karfi da kokari kun kutsa cikin
wahala da gajiya kun bada kyautan
abubuwa mafi tsada na ku .
Kun bar iyalai da
kasashe kun amsa kiran mai girma
da daukaka kun zo kun hallara a gu mafi
daraja da daukaka kun tsiraita
daga adon ku da tufafin ku kun
fiskanci Allah da kura kuna masu
talbiya kuna kai bici-bici kuma kuna masu talbiya kuna masu kankan da
kai kuna marairaicewa kuka nemi mafaka a gare shi shi kadan
shi kuna masu ikilasi to albishirin ku –albishirin ku to, Allah shi ne mafakan masu jinkan masu yin
jinkai shi ne mafi karamcin masu karamci, ba ranar
da Allah ya fi 'yanta bayi daga wuta kamar ranar Arfa kuma lallai yana
kusantowa sannan ya yi alfahari da ku ga
mala'iku, sai ya ce wadannan bayi na ne sun zo min suna bici - bici da kura, daga kowani sako mai zurfi, suna neman rahama
ta suna tsoron azaba ta, ina kuma ace da sun ganni? Da zunubanku sun kai adadin turbaya ko tudun kumfan kogi da na
gafarta muku, ku tafi ya ku bayi na na gafarta muku,
Albishirinku ya ku mutanen Arfa wanda
*** da shi Allah ke gafarta zunubai ya yi rahama.
'yantattu nawa ne aka kammala 'yanta su a ciki*** Wasu kuma suna can suna ta kokarin aikin, kuma
Ubangijin shi ne mafi rahama
YA KU MUSULMAI:
Masu ziyartan dakin Allah mai alfarma
a wadan nan ranaku a aikace kamar
cewa suke yi , ga mu mun dawo mun kuma komo masu tuba muna masu godiya
ga Ubangijin mu .
Farin ciki na lullube da
su suna masu komawa kasashen su da
garuruwan su a halin sun kammala ayukan
su na hajji sun sauke nauyin su , (
Ka ce da falalan Allah da rahamar sa
sabo da haka su yi farin ciki shi ya fi
alheri daga abin da suke tarawa
.)
To ta iya yiwuwa su koma kasashen su kamar yanda mahaifiyar su ta
haife su , za su koma da ganima da ke
sanya yabo da godiya an gafarta zunubai zan suturce aibi an
kankare kusakurai .
To dukkan godiya da yabo sun
tabbata ga Allah bisa kamalar sa da
daukakar sa , kuma dukkan godiya da yabo sun tabbata ga
Allah da
ya shiryar da mu zuwa ga wannan
kuma ba mu kasance da mu shiryu ba , ba don Allah ya shiryar da mu ba.
YA TAWAGAN ALHAZAI :
Lallai ko wani fiskantowa na da juyawa haka nan ko wani haduwa na da rabuwa da kuma abin labartawa, bayan mun ga alhazai suna tahowa daga ko wani
sako mai zurfi da gari na nesa don su halarci abubuwa masu amfani a gare
su runduna-runduna masu yawa da gangami
daban-daban a wurare masu tsarki na
ibada , wanda hakika harsunan su ya saba da juna da launukan su da garuruwan su da kuma jinsin su da kuma shekarun su sai dai musulunci ya
hade su ya maida alkiblan su
daya da ayukan hajjin
su suna masu ihrami da tufafi iri guda
suna masu talbiya da kira iri guda sun taru a farfajiya guda hakika Allah ya hada zukatan su da ka ciyar da abin da yake doron kasa gaba
daya da ba ka hada zukatan su ba amma Allah ya hada zukatan su .
Bayan kammala ayukan haji sai ga tarun jama'a masu yawa da adadi masu
dumbin yawa suna bankwanawa wuraren
ibadan da suke tsananin shauki a zuciyar
su da gabban su, yana nuni da cewa:-
Gidajen mu kuna da matsayi a
cikin zukatan mu
Taron nan na al'uma suna ta rabuwa
cikin yanayi da za ka gani a
ido na ban tsoro kuma mai tasiri, wani
abu ne na daukan darasi mai girma da jama'a suka shaida .
Lallai wanna rabuwa din bayan
haduwa na wani lokaci kankani yana tunatar da mu rabuwa irin na duniya da kuma
sauyin al'uma bayan al'uma karni
bayan karni a haifi wannan al'uma a yi
barka da su a fiskance su a yi bankwana da wancan al'uma a jajanta musu
a kaurar da su , ( Dukkan wanda ke
kanta zai kare fiskan Ubangijin ka ne
zai wanzu ma'aboci daukaka da girmamawa
).
YA TAWAGAN ALHAZAI :
Lallai a hajji akwai abin wa'azi ga me
wa'azantuwa kuma lallai da'a tana
da wani amfani da tasiri a cikin zuciya ,
salla tana hani da alfasha da abin ki
amma ambaton Allah ya fi girma ,
hajji kuma wani mashaya ne na kwankwadan tsorn Allah (Ku yi guzuri
mafi alherin guzuri shi ne tsoron Allah
).
To ita ibada idan bata kusantar da mutum zuwa ga Allah ba tana nisatar da shi ga abin da Allah ya
haramta ba , to fa lallai wannan ibada
mai algus ce ko kuma wacce ta sabawa addini,
Allah madaukakin sarki ya ce :-(Lallai Allah na karba ne kawai daga
masu takawa).
YA KAI ALHAJI:
Abin da ke kan ka na farilla ka rama shi
abin da kuma ke doron kasa na wani abokin jayayya to ka yardar da shi abin
da ke kanka na hakki kuma ka bayar da shi
ka tsaida farillun Allah kuma ka yi kokari a sha'anin su ka lizimci sunnan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
a dimance shi ka nemi tsira da kubuta ka sabunta
alkawari tsakaninka da Allah da azama da cika alkawari da ikhlasi, .
YA KU ALHAZAI:
Lallai Allah mai shaida ne
akan dukkan komai ( ba ya fada daga wata magana face mai zaman dirshan yana
nan gare shi ) Makogoron ku ya shake kuna ta fadin kalmar tauhidi duwatsun
makka na amsa kuwwan talbiyar ku har
zuwa ranar idi Allah mun amsa kiran
ka kuma Allah mun amsa kiran ka , mun
amsa kiran ka ba ka da abokin tarayya ,
dukkan yabo da godiya sun tabbata
gare shi da mulki duka na ka ne ba ka da abokin tarayya ,
To a yi bara'a daga shirka to a yi bara'a daga shirka domin Allah bai karbar aikin da akwai
kwatankwacin kwayar zarra na shirka a
ciki, hakika kuma ya ce ( Ni na wadatu daga abokan tarayya duk
wanda ya yi wani aiki ya hada ni da wani
a ciki na barshi da shirkar sa) muslim
ne ya rawaito.
(To ku bautawa Allah kar ku hada shi da wani ), to ku lizimci shari'ar ku ku kiyaye addinin ku
.
BAYAN HAKA:
YA KU MUTANE:- Lallai Ubangijin ku daya ne mahaifinku guda
ne ku saurara ba fifiko tsakanin
balarabe akan ba'ajame , ko ba'ajame akan balarabe ko ja akan baki ko baki akan ja sai da tsoron
Allah , to lallai Allah ya haramta a
gare ku jinannakin ku da dukiyoyin ku ,
da mutuncin ku , kamar alfarmar
ranar suka a watan zulhijja a garin
makka, ku saurara kar ku koma a baya na
kafurai sashi na dukan wuyan sashi .
YA KU ALHAZAI :
Wannan shari'ar Ubangijin ku ne
kuma wasiyyar Annabinku ne to ku lizimce ta hakan shi ya fi alheri a gare ku a wurin
Mahaliccin ku ,.
HUDUBA TA BIYU
Dukkan yabo da godiya sun tabbata
ga Allah bisa kamalan addini da cikan ni'ima
da bayyanar hanya da bullowar
hujja da kammalan aikin hajji godiya wanda zai cika ni'imomin sa
mabanbanta tsira da amincin Allah
su tabbata ga Manzannin sa da Annabawan
sa .
Maziyarta dakin Allah mai
alfarma lallai na daga cikin alamomin
karban da'a akwai daidaituwa akan tafarki da kuma tabbatuwa da dukufa akan
shi , da kuma yiwa rai hisabi
bisa ga gajartawa da sakaci da
take yi wadannan su ne sifofin masu tsoron Allah masu kushu'i da ikhlasi (Allah na tabbatar da wadanda
suka yi imani da tabbataccen zance a
rayuwar duniya da ma lahira kuma Allah
na batar da azzalumai ).
Ku saurara lallai daidaituwa akan tafarki shi ne hakikanin mika wuya
da tabbatuwa akan addini da gaskiya da wafa'i .
An karbo daga Sufyan dan
Abdullah Assakafi Allah ya kara yarda a
gare shi ya ce : na ce ya Manzon Allah ka fada min wata ,magana a cikin musulunci wanda bazan tambayi wani ba koma
bayanka sai ya ce: ( ka ce na yi imani da Allah sannan ka daidaitu )
Muslim ne ya rawaito .
Daidaituwa akan tafarki shi
ne kubuta daga tsoro da
aminta daga kwadayi da bacin
rai , kuma albishir ne mai girma( Lallai
wadanda suka ce Ubangijin mu Allah ne sannan suka daidaita mala'iku na sauka a gare
su:- kada ku ji tsoro, kada ku yi bakin
ciki kuma ana muku albishir da aljanna
wadda aka kasance ana muku alkawari da ita 0)
Tsayuwa a kan tafarki yana daga
cikin darajoji na kamala ba wanda zai samu haka sai ma'abota himma da dabi'u hakika mai izza da daukaka ya ce:-( ku cika
alkawarin Allah idan kun yi alkawari
kada ku warware rantse-rantse bayan karfafata alhali kun sanya Ubangiji wakili
akan ku hakika Ubangiji ya san abin da
kuke aikatawa , Kada ku kasance kamar matar nan da ta
warware kadin ta bayan inganta shi , a
warware) .
Maziyarta dakin Allah mai
alfarma : lallai na daga cikin wajibi akan ko wani
musulmi ya godewa Allah mabuwayi da
daukaka bisa ga abin da yayi na ni'ima na aminci , da zaman lafiya ,ga
wannan kasa mai albarka, wacce take
karban wadannan adadi mai yawa na daga musulmai daga sassa daban-daban na duniya
take tashi da karban bakuncin su
da kimtsa musu wuraren ibada
cikin mafi kyaun mutsayi kuma ta
gabatar musu da hidimomi mafi daukaka
gwargwadon iyawa wanda ke fitowa
kai tsaye karkashin kulawan mai hidima ga Masallatayya biyu masu Alfarma, da mataimakin sa amintacce Allah ya kiyaye su, to godiya da
kimantawa da jagororin mu masu tsayuwa
akan hidimawa musulunci da musulmai godiyar Allah ga kokarin su, kuma Allah ya
karbi ayukan su ya rubuta hakan cikin ma'aunin
kyawawan su.
YA KU ALHAZAI:
Ku lizimci bin doka da oda da tsari wanda ke taimakawa wurin sauke hidima kuma
ya saukaka a gare ku hanyoyi na
gudanarwa sa'annan kuma yana bada kaso
mai yawa wurin kawo aminci da zaman lafya a rayuwa ku tausayawa kawunan ku, ku nisanci sabawa doka
da oda .
Allah ya sanya hajjinku abin da'a
ne kokarin ku kuma abin godewa ne zunuban ku kuma abin gafartawa ne ya mai da
ku zuwa ga iyalanku da gidajen ku cikin aminci kuma cikin ganima kuna masu samun lada da
farin ciki da annashuwa.
Muna mikawa Allah ajiyar addinin
ku da amanar ku da karshen ayukan ku Allah ya muku guzuri da tsoro Allah , ya
gafarta muku zunuban ku ya tabbatar muku gurace-guracen ku , ya riskar da ku
zuwa ga cimma muradan ku da fatan ku ,
lallai shi mai ji ne kuma mai amsawa.
Wannan kenan to, ku yi salati da
aminci ,- Allah ya muku rahama- bisa ga mafificin halittu.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق