الاثنين، 30 يوليو 2018

'YAN UWANTAKA A MUSULUNCI


HUDUBAR  JUMA'A NA MASALLACIN ANNABI NA  SHAIK ALIYU AL-HUZAIFI  14\11\1439
HUDUBAR FARKO
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mabuwayi mai hikima , mai rahama mai jin kai ina kyautata yabo ga  Ubangijina  ina kuma gode masa bisa  ni'imomin sa wadanda muka sani da wadan da ba mu sani ba  to shi din nan ahli ne na  a ambace shi ba za a manta shi ba a kuma gode mishi ba za a saba mishi ba ,  shi ne mawadaci mai karamci , na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaadai yake bashi da abokin tarayya , madaukaki mai girma  na shaida Annabin mu kuma shugaban mu Muhammad  bawan sa ne kuma Manzon sa ne  wanda Allah ya fifita shi akan bayin sa ga dukkan dabi'u na karamci , ya Allah ka yi dadin tsira da  aminci bisa ga bawan ka kuma Manzonka   Muhammad da iyalan sa da sahabban sa  masu shiryarwa zuwa ga tafarki mikakke  bayan haka ku ji tsoron Allah  ta hanyar neman kusanci zuwa gare shi da neman yardan shi da barin abubuwan da ya haramta su  ba masu rabauta sai masu tsoron Allah    ba masu hasara sai masu sabon  Allah mabarnata  .
             Ya ku musulmai  :
Mumini  shi  mai karfi ne da imanin sa  sa'annan kuma mai karfi ne da 'yan uwan sa,   Mumini yana karkata ne zuwa ga imanin sa da  Ubangijin sa a lokacin tsanani  da bakin ciki  kuma yana riko da  imanin sa  da Ubangijin sa a lokacin da wasu shubuhohi suka bulla    da kuma sha'awe –sha'awe   kuma yana ganin haske ne da imanin sa a lokacin duhun fitintinu da musibu Allah sai ya kare shi da imanin sa lokacin sauki da lafiya da faraga  domin kar ya fada ya halaka  cikin jin dadin abubuwan da aka haramta .
      Allah yakan raya shi da imanin sa a duniya irin rayuwa mai albarka  mai walwala  abin yarda  mai amfani   kyakkyawa mai kyakkyawan karshe  da imanin sa da Ubangijin sa ne zai riski daraja madaukakiya  bayan mutuwa  Allah madaukakin sarki yake cewa: (  lallai wadan da suka yi imani suka yi aiki na kwarai Ubangijin su zai shirye su   dalilin imanin su  kwaraimai na gudana a karkashin su  a cikin lambuna masu ni'ima  adu'a an su a cikinta shi ne  tsarki ya tabbata a gare ka ya Allah  gaisuwan su kuma a cikinta aminci   , karshen da'awar su shi ne dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai  , ).
                      An karbo daga salman Allah ya kara yarda a gare shi  daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Abin mamaki da al'amarin mumini lallai dukkan al'amarin sa alheri ne  ba wanda yake da wannan face mumini  idan abin jin dadi ya same shi sai ya gode to sai hakan ya zama alheri a gare shi idan kuma cuta ya same shi sai ya yi hakuri sai hakan ya zama alheri a gare shi  ) Muslim ne ya rawaito
              To shi mumini  madaukaki ne  mai walwala ne kuma wanda ya yi dace ne da imanin sa  kamar yanda mumini  yana da karfi ta hanyar 'yan uwan sa   domin 'yan uwantaka na musulunci ya fi karfi akan 'yan uwantaka na jini sabo da haka ne ma    gado ke datsewa tsakanin musulmi da kafiri, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Musulmi baya gadan kafiri haka kafiri baya gadan musulmi) Buhari da Muslim ne suka rawaito   daga hadisin Usama dan Zaid Allah ya kara yarda a gare su , to, 'yan uwantaka na Musulunci ya fi girma  akan alaka  da zumunci  da dunkulewa  Allah madaukakin sarki ya ce : ( muminai maza da muminai mata sashin su waliyyai ne ga sashi    suna umarni  da kyakkyawa kuma suna hani ga mummuna  suna kuma tsaida sallah suna kuma bada zakka kuma suna yiwa Allah da'a da Manzon sa wadan nan Allah zai jikan su , lallai Allah mabuwayi ne mai hikima) . Allah madaukakin sarki ya ce : ( Lallai muminai 'yan uwan juna ne)     Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Musulmi dan uwan musulmi ne ba zai zalunce shi ba ba zai tabar da shi ba) .  muslim ne ya rawaito shi
                To 'yan uwantaka na musulunci yana kasancewa ta hanyar taimakekeniya  a addini da karfin hadin kai  Allah madaukakin sarki ya ce  ga Annabin shi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : (  Shi ne wanda ya karfafe ka da taimakon shi  da kuma muminai ya kuma hada zukatan su  da ka ciyar da duk abin da ke doron kasa gaba daya da ba ka iya hada zukatan su ba sai dai Allah shi ya hada zukatan su, lallai shi din nan mabuwayi ne  mai hikima ) kuma Allah madaukakin sarki ya ce : ( Ya ku wadanda kuka yi imani  ku ji tsoron Allah cancancin tsoron shi  kada ku mutu face kuna musulmai , ku yi riko da igiyan Allah  baki daya  kar ku rarraba  ku ambaci ni'imar Ubangiji a gare ku zamanin da kuka kasance makiya juna   sai kuka zama 'yan uwa sabo da ni'imar Allah  ,   a da kun kasance a gabar rami  na wuta   ya tsamo ku daga gare ta  )
          'Yan uwantakan addini yana kasancewa ne   ta hanyar taimakekeniya  wurin tabbatar da maslahohi  da tunkude barna  da bada kariya  ga al'umma  daga masu ketare iyaka  Allah madaukaakin sarki ya ce: ( ku yi taimakekeniya akan da'a da kuma tsoron Allah , kada ku yi taimakekeniya akan laifi da kiyayya ) Allah madaukakin sarki ya ce : ( Ya kasance a cikin ku akwai wata al'uma da tana kira zuwa  ga alheri, kuma suna  umarni da kyakkyawa  , kuma  suna hani da  mummuna  wadannan sune masu rabauta ).
     'Yan uwantaka na musulunci  yana kasancewa ta hanyar jin kai da tausayawa juna  da kuma  taimakekeniya  , da kuma  hadin guiwa  wurin samar da abin da al'uma ke bukata  da kyakkyawan tsarin rayuwa  Annabi  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce : ( Misalin muminai cikin kaunar su da son junan su da tausayawa junan su kamar  gangan jiki ne guda     idan wani gaba ya tabu da rashin lafiya  sai sauran jikin ya amsa  da zugi da rashin bacci ) Buhari ne ya rawaito da muslim daga Hadisin Abu Musa Al-ash'ari  
       Na daga cikin abin da ke kawo dadin rayuwa akwai wanzuwar kauna a tsakanin  musulmai   Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (   Na rantse da wanda raina yake hanun shi  ba za ku taba shiga aljanna ba har sai kun yi imani  , ba za ku yi imani ba kuma har sai kun so junan ku  , ase ba zan nusar da ku  bisa ga aabin da idan kun aikata shi za ku kaunaci junan ku ba  to ku yada  sallama a tsakanin ku .,
    YA JAMA'AR MUSULMI:
     Rayuwa fa ba za ta daidaita ba har sai kun tashi da hakkoki na 'yan uwantaka na musulunci   ,  to abubuwan da suke na wajibi akwai wanda suke  na Ubangiji madaukakin sarki , wannan shi ne wajibi mafi girma  da kadaita Allah da bauta mishi ,  daga ciki kuma akwai abin da yake hakki ne na  halittu  ,   kuma hakkokin musulmai iri uku ne :-
            Mafi girman su shi ne fifita wani akan kai (isar) wato gabatar da bukatar musulmi   da hakkin shi akan hakkin kai  wannan ita ce daraja da muhajirun suka rabauta da ita da kuma ansar Allah ya kara yarda a gare su  Allah madaukakin sarki ya ce: (Wadanda suke zaune a madina suka kudure imani tun gabanin su  suna son wanda yayi hijira gare su ya yi kaura  basa hasada da abinda ya basu   suna fifitawa 'yan uwan su a kan kansu  koda akwai wani bukata a gare su izuwa  abinda suka fifita   wani da shi , wanda aka kiyashe shi kwadayin kansa   wadancannin ka   su ne hakikanin marabauta ).
        Wannan na maimaituwa a ko wani zamani   da ko wani wuri  idan imani ya cika  tarihi ya kiyaye mana   wasu sifofi na fifita wani akan kai masu yawa a lokuta daban-daban  
 Daraja  na tsakatsakiya kuma daga cikin darajoji na 'yan uwantaka  shi ne mutum musulmi ya    so wa dan uwansa abin da ya so wa kan sa an karbo daga Anas Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (     Imanin dayan ku ba zai cika  ba har sai ya so wa dan uwan shi abin da yake so wa kanshi) Buhari da Muslim ne suka rawaito
         Mafi daraja na kasa kuma  wanda musulmi zai tashi da shi game da hakkin dan uwan shi musulmi shi ne ka kame sharrin ka daga gare shi ,  ba za ka zalunce shi ba a jini ne ko dukiya ko mutunci  , ba za ka zare harshen ka ba akan shi   ko hanun ka  ko kuma ka tawaye mishi wani hakkin  da yake na shi ne  ,  ko ka hana shi hakkin sa  tare da yin kokari  yin abin da Allah zai datar da kai zuwa gare shi na alheri, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da Abu zarri (kuma ka kame sharrinka daga mutane, domin hakan sadaka ne gare ka a kan ka,)
Ya ku musulmai!
Lallai abin da ya fi cutar da 'yan uwantaka na musulunci shine bidi'a mai batarwa, don dan bidi'a yana kiyayya ga duk wanda  bai aminta da bidi'arsa, ba abin da zai hada zukatar musulmai sai akidar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa , su ne masu son juna don Allah, na karshen su na son na farkonsu, Allah Madaukakin sarki ya ce: ( Wadan da suka zo bayansu suna cewa  :Ya Ubangijinmu ka gafarta mana  da 'yan uwan mu da suka gabace mu da imani kar ka sanya kulli cikin zuciyarmu game da wadan da suka yi imani ya Ubangijinmu kai mai tausayi ne mai jinkai)
Na daga cikin abin da ke cutar da 'yan uwantaka ta musulunci akwai fifita duniya akan lahira, da mutuwa don ita. Har ya zama  mafi yawan mutane kan haka suke 'yan uwantakarsu, da gina kiyayya kan kawar duniya da jin dadinta.
Na daga cikin abin da ke cutar da 'yan uwantaka  zalunci da yaduwar wannan zalunci ta hanyar hana mutane hakkokinsu, ko kwace hakki, don rayin dan adam na tsanan duk wanda ya zalunce ta, kuma tana neman daukar fansa, daga gare shi,
Na daga cikin abin da ke cutar da 'yan uwantaka  na musulunci akwai hasada, domin yana janyo gaba da kiyayya.
Na daga cikin abin da ke haifar da illa ga 'yan uwantaka na musulunci mutum ya rika ganin kansa  a matsayin kamili  ya ke  ganin waninsa  da reni da tawaya. To ga ku jama'ar musulmi jikunanku sun hadu a farillu  na musulunci, a hajji da juma'a da  sallar jam'i da sallolin idi, to ku hada zukatanku a kan akidar magabata na kwarai, da kur'ani da sunna , ku tuna cew za ku koma ga Allah Madaukaki, ku bar duk wani abu da ke kange ku daga gaskiya, ku tsaya gaba ga Ubangijinku huntaye tsirara, ba kaciya, ba wani abu tare da ku sai kyawawan ayyukanku da munana, to ku zo wa kyawawan ayyuka ku kiyayi munanan ayyuka,Allah Madaukakin sarki ya ce : (ku yi gaggawa zuwa ga gafara daga Ubangijinku  da Aljanna fadinta ya kai sammai da kasa an tanade ta don masu tsoron Allah. Wadan da suke ciyarwa a lokacin sauki da tsanani, da masu hadiye fushi da masu yafiya ga mutane, Allah na son masu kyautatawa,)
Allah sanya mini albarka ni da ku cikin Alkur'ani mai girma,
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah a kowane hali, muna neman tsarin shi daga hali irin na 'yan wuta, wadan da ayyukansu ya jefa su cikin wulakanci da azaba, ina gode wa Ubangiji na bisa ga kyauta mai girma,Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya Mai girma Maabocin daukaka, Na shaida Annabin mu kuma shugabanmu Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa ne.
Allah ka yi dadin tsira a gare shi da sahabbansa da iyalai, bayan haka ku ji tsoron Allah ku mishi biyayya, ku kiyayi fushinsa  da bushewar ido cikin saba masa, ya ku bayin Allah hakika hujja fa ta tsayu a kanku, hanya ta bayyana a gare ku, kuma duk wasu uzurori sun yanke, to ku fiskanci aiki kada buri ya rude ku, Allah Madaukakin sarki na cewa : (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijin ku ku kiyayi wata rana da Mahaifi ba zai fanshi dansa ba ko shi  da ya fanshi mahaifinsa  da wani abu ba, Alkawarin Allah gaskiya ne kada rayuwar duniya ta rude ku, kada kuma wani abin rudi ya rude ku daga Allah)
To ku tuna mutuwa da abin da ke bi mata na daga azaba  da ba mai kubutar da mutum daga shi sai ayyuka na kwarai, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce ku yawaita ambato mai datse jin dadi, wato mutuwa ,
Ya ku bayin Allah lale Allah da Mala'ikunsa su na  salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce,
Har karshen Adua.    
  

الجمعة، 20 يوليو 2018

DOGARO GA ALLAH A MUSULUNCI


HUDUBAR MASALLACIN ANNABI NA SHAIKH  HUSAINI ALI SHAIK  7\11\1439
HUDUBAR FARKO
A irin wannan zamani wanda kalubalen sa sun yi yawa , wanda hadarin sa ya girmama ga dan adam , hadari irin na rayuka  da tsoracewa zuriyawa ,  da  wahalhalu irin na neman abin masarufi,  zuwa ga abubuwan da ba su da iyaka na ban tsoro, wanda ke wucewa ga dan adam a wannan zamani  cikin abinda ba zai kidanyu ba  ko ya boyu ba  anan ne  bukata zata girmama lalura za ta tsananta  zuwa ga sanin abinda zai kai bayi zuwa  ga himma madaukakiya  da kuma  karfin azima  domin su riski maslahohi da ake fata  da  abubuwan masu amfani da ake bukata  .
              Lallai dan adam a duk lokacin da yake da karfin basira da cikan yakini, da alkawarin Allah mai tsarki  to, a wannan lokacin  ba zai juya kai zuwa ga abin da zai ba shi tsoro ba muddim ya  riki sababi ya kuma dogara da mai kawo sababi  sai dai ma ya rabauta da manufofin sa  kuma ya samu nasara wurin cimma bukatun sa .
           Lallai dan adam a duk lokacin da ya maida al'amarin shi ga Allah  ya yanke  zuciyar sa daga ta'allakuwa ga halittu ya tashi da abin da Allah ya shar'anta  a gare shi ,  na daga sabuba na zahiri  da kuma na shari'a  zai zame ma'abocin himma madaukakiya  wanda  hakika ya sabarwa kansa  bi ta kan wahalhalu har ma abubuwan da suke na tsanani sun saukaka a gare shi  muddin zuciyar sa  ba komai a cikinta sai dogaro ga Allah  da kuma  jingina zuwa gare shi, sabo da yana da yakini da tabbaci na alkawarin Allah Allah Madaukakin sarki ya ce : ( Duk wanda ya ji tsoron Allah  to, Allah zai sanya masa yayewa ya azurta shi ta inda bai zato, Duk wanda ya dogara ga Allah to Allah ne mai isar mishi )
Wani daga cikin magabata yace : ( Da ace mutum zai dogara ga Allah da gaskiyar niyya  da sarakuna sun bukace shi da na kasa da su, to ina ga wanda majibincinsa Mawadaci ne abin godiya ne ta yaya zai bukaci wani?
Lalle duk wanda ya dogara ga Allah ya maida mishi lamuransa gabadaya gare shi Mai tsarki  yana kallon duniya da lahira duka mulki ne na Allah, halittu dukkaninsu bayi ne na Allah, da arziki da dalilanta duk a hanun Allah su ke,  kuma yana ganin hukuncin Allah abu ne mai zartuwa a doron kasa baki daya, sabo da haka ne ma Allah ya umarci bayinsa  da  su  dogara gare shi sai ya ce : (ka dogara ga Rayayye da bai mutuwa) kuma ya ce : (Ga Allah kadai zaku dogara in kun kasance muminai)
To duk wanda bai kula da umarnin Ubangijinshi ba zai fada cikin musibu da tsanani  kuma ba zai cin ma burinsa ba ba zai kubuta daga abin da ya ke tsoro ba.
Tawakkali :Lafazi ne mai girman ma'ana mai  da madaukakiyar manufa, Duk wanda ya dogara ga Allah shi ne ya rike shi a matsayin wakil  wanda ke tashi da al'amuransa ya lamunce mishi gyaruwansa. Wanda ya isan masa a komai bai tare da wani jin nauyi ko wahala ba.
Mai dogaro ga Allah shi ne wanda yake da aminci da yakini game da ubangijinsa ta yadda ba wani rabon shi  da zai kwace mi shi.  Lallai hukuncin shi baya canzawa kuma baya sauyawa   Allah madaukakin sarki ya ce : (  Arzikin ku yana cikin sama   da abin da aka alkawarta muku , Na rantse da Ubangijin sama  da kasa lallai shi dinnan gaskiya ne   tamkar yanda kuke furuci ).  Yana daga cikin ma'anonin wannan aya  Allah madaukakin sarki  bai tsaya ga lamunce azurta halittu ba kawai sai da ya kara da rantsuwa akan haka , Hassan Allah ya mishi rahama ya ce :
(Allah ya tsinewa wasu mutane  , Ubangijin su ya rantse musu amma ba su gaskata shi ba)   an rawaito cewa mala'iku sun ce    banu adama sun halaka sun fusata Ubangiji har sai da ya yi rantsuwa  bisa ga  azurta su  Manzo Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (  Da kun dogara da Allah canancin dogaro da ya azurta ku kamar yanda ya ke azurta tsuntsu suna wayan gari a yunwace  su yi yammaci a kwashe ) Ahmad ne da tirmizi da Ibn Maja suka rawaito shi  kuma isnadin shi ingancecce ne a wurin malamai masu tantancewa.
          Mai dogaro ga Allah Mabuwayi da daukaka mai gaskiya ne a wurin dogaron sa ga Allah cikin saukake al'amuransa  da kuma  janyo misjhi amfani  ,  da tunkude cutarwa  mai aminta ne da alkawarin Allah  kuma mai sakankancewa ne  kan cewa  tare da mika al'amuran shi ga Allah zai cimma manufofin sa ,  kuma ya  kubuta daga abin da yake tsoro .
     Mai dogaro ga Allah   yana mika al'amarin shi ne ga Allah sabo da  yarda da yake da shi ga Allah da kyautata zato a gare shi , shi dinnan zai yanke alakar sa da wanin Allah zai yanke dubi zuwa ga sabuba bayan ya kimtsa  musu ya tashi da  su ,  yana kuma barranta daga  dabarar sa ko kokarin sa  face ga Allah madaukaki mai girma  sabo da kebanta da ya yi da halittawa da gudanarwa  da cuta da amfanarwa da kyauta da hanawa , ya san kuma lallai abinda Allah ya so shi zai wakana abin da bai so ba bazai faru ba .
    Mai dogaro ga Allah yana dogaro ne a dukkan al'amura   da kuma sabuba  shi kuma sabuba  kamar wasu  tsani ne  wanda ba'a dogaro akan su, shi bawa   zai kula da sabuba na zahiri sai dai ba zai dogara  akan su ba da zuciyar sa  sai dai ma  ya dogara da mahalicci mai gudanarwa  kuma ya  mika wuya  a cikin hukuncin Ubangiji  da kudurarsa da  abin da ya so.
      BAYIN ALLAH:-
  Duk wanda ya tabbatar da tsoron Allah  kuma  gaskata dogaron sa  ga majibinci   to hakika   ya samu babban abin bukata   .
    Duk wanda ya mika al'amuran sa ga Ubangijin sa ya dogara ga mahaliccin sa   yana mai kadaita shi  ya koma gare shi  mai yawan       kai kukan shi gare shi  yana mai tuba  yana kuma  bin dokokin shi   yana mishi da'a  to, Allah zai sanya mishi yayewa daga ko wani  bakin ciki , kuma ya sanya mishi mafita daga ko wani kunci  kuma ya azurta shi ta inda bai zata ba  kuma ya riski alheri mai yawa  kuma ya kare shi daga dukkan wani cuta da sharri  karshen shi kuma ya zama rabauta da nasara  da taimako  mai karfi Allah madaukakin sarki ya ce game da bawa na kwarai : (Kuma ina mika al'amari na zuwa ga Allah lalle Allah masani ne ga bayinsa, sai Allah ya kare shi daga miyagun abin da suka yi nufi sai mummunar azaba ta sauko ga Fir'auna da mutanensa)     
            Allah madaukakin sarki ya ce : (  wadan da mutane suka ce da su wato  hakika mutane sun tara  (runduna) don ku ku ji tsoron su sai ta kara musu ban gaskiya sai suka ce Allah  ne mai isar mana madalla da abin dogaro  sai suka koma da sakamako daga Allah da kari suka koma sumul tare da riba  , wani abu mummuna bai same su ba suka bi yardar Allah  Allah mai falala ne mai girma ).
 An karbo daga dan Abbas Allah ya kara yarda a gare shi   HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL   Annabi Ibrahim ya fade ta  a lokacin da aka jefa shi a wuta  kuma Annabi Muhammad ya fade ta  lokacin da   suka ce (  Hakika mutane sun tara runduna don ku )  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa  (Duk mutumin da idan yazo fita gidan shi yana cewa BISMILLAHI TAWAKKALTU ALALLAH  WALA HAULA WALA KUWWATA ILLAH BILLAH  ) sai a ce da shi  an shiryar da kai  , kuma an isar maka an baka kariya  sai shedan kuma yayi nesa da shi  Abu Dauda ne ya rawaito shi da  Tirmizi da Nasa'i da isnadi ingantacce.
   
HUDUBA TA BIYU
YA KAI MUSULMI : -
Ka maida al'amarin ka zuwa ga Allah  ka yi dogaro na gaskiya gare shi  ka yi aiki da abin da ya shar'anta na sabuba ka aminta da cewa  lallai wanda yake gudanar da al'amura daga sama  zuwa kasa  masani ne  da abin da ya boyu  da abin da ke zuciya  wanda ya iyakance dukkan al'amura  ta kowace fuska  mai iko ne da cikakkiyar kudura  ma'abocin  cikan abin da ya so  yana kewaye da kai da ludufi irin na ilimin sa  da kyautata gudanarwa , wanda ba wanda zai iya sani cikin halittu ko kuma wani haziki ya fahimce shi , ka shagaltu da sha'anin ka ka kebe don bautawa Ubangijinka   ka samu yakini kan cewa duk wanda ya dogara gare shi to fa ya isar masa, kuma zai kasance amintacce daga hadura  kuma ya samu cikakken natsuwa da kwanciyar hankali .
    Lallai duk wanda bai sani ba *** shin abin da  ake kauna ne  alheri ko kuma  abin da aka ki
   To lallai ya dace  ya maida abin da ya gagara a gare shi *** zuwa ga wanda ya isar mishi
  Ku saurara dukkan biyayya na shi ne wanda game da tausayi  *** ya fi mamma da baba jin kai .
  


الخميس، 19 يوليو 2018

kyautata sakayya a musulunci


Hudubar Juma'a na Masallacin Annabi  29-10-1439 AH /12-7-2018 M
Shaikh Abdulbari Bin Awad Assubaiti

Na daga cikin abin da ya ke jigo ne ga musulmi da dabiunsa : mutunta ma'abota mutunci, da sakanya  kyautatawa da mafi kyau, wannan wata dabi'a ce mai girma a musulunci  gun mu'amala, wato sakanya ta kyautatawa a musulunci  ita ce kyautatawa kwatankwacinta. Allah Madaukakin sarki ya ce :( Babu wani sakamako na kyautatawa sai kyautatawa) Arrahman 59
 Shi musulmi bai manta  ma'abotar  falala a kansa, duk wanda ya mishi wani ihsani zai tuna kyautatawarsa, zai kuma gode masa ya kimanta alherin da suka masa, ba zai manta ba a duk rintsi na rayuwa, da matsaltsalun  fitintinunta, da duk wanda wani dankon zumunci da kauna ya hada su, da wata muamala da ta wakana a baya, ko da an samu wani sabani  na wata  rana ko rashin fahimtar juna, Allah Madaukakin sarki ya ce : (kar ku manta falala da ke tsakanin ku) Bakara
Manzon Allah shi ne shugaban masu wafai ( mafi kyautata sakayya). Ya koyar da mu mafi kyan kyautata sakayya, ya kuma bayyana  falalar matarsa Khadija a halin tana raye da bayan mutuwarta , ya kasance yana yawaita ambatonta da gode mata da nema mata gafara yana cewa : Ai lalle ita ta kasance kaza da kaza,   wasu lokutan ma ya kan yanka akuya ya yayyanka ya turawa kawayen khadija) Bukhari da muslim ne suka rawaito.
Lokacin da musulmai suka yi nasara a yakin Badar suka kama mutum saba'in cikin kuraishawa Manzon Allah sai ya fadi kalmarsa  shahararriya :( Da Mud'am dan Adiyyi na raye sannan ya min magana kan wadannan doyaya da na mika mishi su) Bukhari ne ya rawaito. Tare da cewa Mud'im dan Adiyyi ya mutu kafuri, amma kafurcin sa bai hana a ambata alherinsa  da ya yi ba, da karrama shi da abin da ya dace.
Kissoshin Annabawa na cike da ambaton falalar masu falala,  na daga ciki akwai abin da ya zo a kissan Musa Amincin Allah ya tabbata a gare shi da mahaifin mata biyu da ya shayar da su.
Allah Madaukakin sarki yace : (Sai dayarsu ta zo masa tana tafe  cikin kunya sai ta ce: baba na hakika yana kiranka don ya saka maka ladan shayarwa da ka mana) sai musa ya hadu da sakayyar kyautatawarsa  wanda mahaifin mata biyun ya saka masa sabo da mutuncinsa.
Musulunci  ya daga darajan wanda ya kyautata ma ya ma ihsani, har ma ya karfafi da ka saka mishi,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Bai gode wa Allah duk wanda bai gode wa mutane) Ahmad ne ya rawaito da isnadi ingantacce da Ibnu Hibban a sahih nasa Ma'anarsa shi ne Allah bai karbar godiyan bawa bisa kyautatawarsa zuwa gare shi muddin bawan bai gode wa mutane bisa kyautatawarsu gare shi. Kuma yana butulce wa kyautatawar su. Sabo da gamewar abubuwa  biyun. Kuma na daga cikin ma'anar hadisin : Duk wanda al'adarsa butulce wa ni'imar  mutane  da rashin gode musu ,to haka nan zai rika butulce wa Allah ya bar gode masa   madaukakin sarki.  yana daga cikin ma'anarsa : - cewa duk wanda baya godiya ga mutane to fa; tamkar wanda baya godiya ga Allah ne  .
       Yana daga cikin sifofi na maida martani mai kyau  wanda ma'abota cika alkawri mai kyau suke sakayya da shi  , ya kunshi fadi da aiki  da ma zuciya  Allah madaukakin sarki ya ce :- (Idan an gaishe ku da gaisuwa  to ku gaida mai gaishe ku da  mafi kyau daga gare ta ko ku maida irinta .) ( To ku mayar da mafi kyau daga ita )
      Idan Musulmi ya mayar da gaisuwa da kwatankwacinta  ko da mafi kyau daga ita , kuma kyakkyawa  kwatankwacinta ko wadda ya fi ta! , daddadan kalma da kwatankawacinta ko wacce ta fita kyau , kyauta da kwatankwacinta ko wadda ya fi kyau daga ita,    to zuciyar mu sai su  tsarkaka  , zumincin mu sai ya karfafa  dankon zumuncin mu sai ya yi kwari,  sai sabani tsakanin mu ya yaye  .
       Matakin farko na maidawa ma'abota falala falalar su  shi ne;  yarda da falalar tasu ,  da kuma tabbatar da cancancin  godiya gare su , to wannan kuma  wata dabi'a ce da yake kan musulmai da ya dace su lizimce ta ; wanda Annabin rahama ya fiskantar zuwa gare ta  , kuma ya yi kira zuwa gare ta .
          Cika alkawari na daga cikin  kyautatuwan  Imani   Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce ( Duk wanda ya  aikata muku wani abu mai kyau to ku saka mishi ) Abu Dauda ne ya rawaito da Nasa'i  da Ahmad da isnadi ingantacce
     A cikin hadisin Hakim da Baihaki    Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fiskanci tsohuwa  da fara'a  da annashuwa    yayin da ta fita Aisha Allah ya kara yarda a gare ta   sai ta tambaye shi  sai ya ce : (Ya Aisha ai ita dinnan ta kasance  tana zuwa mana a zamanin kadija , kuma lallai kyautata alkawari na daga cikin imani ) Albani ya fitar da shi a   cikin silsila ingantacce .
Musulunci ya saukaka hanyoyin sakanyawa ma'abota falala  da abin da mutum Musulmi zai iya ; da kalma mai dadi, da adu'a gare shi na alheri  da kuma  haduwar musulmi da dan'uwan shi Musulmi  cikin sakun fiska da fara'a  , wannan na daga cikin cikan wannan addinin da laduban sa  da kyawunsa  don a samu wanzuwar  zumunci da kauna da soyayya
.An karbo daga Abu zarri Allah ya kara yarda a gare shi ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (   Kar ka raina wani abu na daga aiki mai kyau ko da a ce ka hadu da dan'uwan ka ne cikin sakin fiska ) muslim ne ya rawaito.
    Kyautata yabo da gaskiya  :- Yana daga cikin nau'ukan mayar da abu mai kyau ga ma'abota falala, An karbo daga Jabir Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (  Duk wanda aka yiwa kyauta to, ya yi sakayya game da shi wanda bai samu ba kuma ya kyautata yabo , domin lallai wanda ya kyautata yabo to ya yi godiya  wanda kuma ya boye to ya butulce  wanda kuma ya siffantu da abin da ba a bashi ba to kamar wanda ya  saka tufafi biyu ne na karya) Abu dauda ne ya rawaito shi da Tirmizi da isnadi mai kyau   .
    Na daga cikin  nau'i na maida martani mai kyau  ga ma'abota falala saka musu  da yin adu'a mai kyau  gare su,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:  ( Idan ba ku samu abin da za ku saka musu da shi ba  , to ku yi musu adu'a  har  sai kun san hakika kun  saka musu ) Abu Dauda ne ya rawaito shi da Nasa'i da Ahmad da isnadi mai kyau.
        Daga Usama Dan Zaid Allah ya kara yarda a gare su shi da Baban shi ya ce :- Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :-(Wanda aka  kyautata a gare shi, sai ya ce : ga wanda ya mishi wannan aikin: Allah ya saka maka da alheri hakika ya kai kololuwa cikin   yabo) Tirmizi ne ya fito da shi da Nasa'i  da isnadi mai kyau.
    Wanda ya ara maka dukiya yana da kyau ka kyautata  wajen  biyan  bashin da maidawa da godiya.
   A cikin rayuwar Musulmi akwai bangarori na mutane  ma'abota falala,wadanda  kyautatawansu tsayayye ne kuma falalar su dauwamamma ce, kyautatawan su kuma yalwatacciya ce,  kuma wanda ya fi su girman falala shi ne Manzon Al'umma  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wanda Allah ya fitar da mu a dalilin shi daga duhu zuwa haske.
      Yana daga  cikin  mafi  yawan falala ga mutum a cikin mutane    kuma wanda yafi hakki a gare shi  na cika alkawari da kyautatawa  akwai iyaye biyu  wadanda suka kyautata zuwa gare shi suka bashi tarbiya tun yana karami  Allah madaukakin sarki ya ce :- (  Ubangiji ya yi umarni da kyautatawa iyaye kyautatawa idan dayan su ya isa girma  nan gare ka ko dukkan su su biyu to kada ka ce da su affafairan  kada kuma ka yi musu tsawa ka gaya musu magana mai girma mai taushi )   kuma Allah madaukakin sarki ya ce : (   Ka tausasa musu janubinka  mai taushi  horarre  don jin kai gare su ,  ka ce : ''Ubangiji  ! ka jikan su  kamar yadda suka jikaina  lokacin da suka rene  ni  ina dan karami ) .
    Daliban ilimi suna da wani nau'i  na wajibin cika alkawari  da kyautatawa ga malaman su  ta hanyar yi musu adu'a; sakamakon falala da suke da shi akan su,  Abu Hanifa ya yi adu'a wa malamin shi Hammad    Abu Yusuf shi ma  ya yi adu'a wa malamin shi Abu Hanifa , Imamu Ahmad Bin Hambal Allah ya mi shi rahama ya ce : (  Ban taba kwana ba tun shekara talatin da suka wuce har sai na yi adu'a  ga Shafi'i  na kuma nema mishi gafara .
       Mata da miji a tsakanin su akwai   kyautatawa da ke bin juna  da kuma kyakkyawa a tsakanin su ,  wanda ko wannen su ya kyautatawa dan'uwan sa kamar wani ado ne a  rayuwar sa  wanda ko wannen su dadin rai ne da amfani a zuciyan dan uwan sa ,  to kiyaye wannan alkawarin da kyautata mu'amala  da dauke kai daga kusakuran juna  na cikin sakayya mai kyau  domin lallai kyawawa suna tafiyar da munana, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( kada wani  mumini ya tsani  wata  mumina  idan har ya ki wasu dabi'u daga gare ta to akwai wasu dabi'un nata da zai gamsu da su ) muslim ne ya rawaito .
            HUDUBA TA BIYU
 Lallai abin da ya faru mai radadi na kwanannan wanda ya kasance  kafin wasu 'yan kwanaki a garin BURAIDA  wanda har ya kai ga an kashe wani jami'in tsaro  lallai  abun takaici ne da ke nuni ga jahilci da rashin hankali da dimuwa  lallai wannan tunani ne irin na da'ish masu kafurtawa  ,  suna furta numfarfashin su a jikon karshe na rayuwar su , alhali mu kuma muna da yakini cewa tunanin su  zai zo ya faku batan su kuma zai zo ya fado , wanda yake so   ya karya zaman lafiyan mu  ya kuma girgiza amincin mu ,to ba zai cinma manufarsa ba  kuma ba zai kai ga cimma muradinsa ba  kuma zai koma da hasara bayyananne  da falalan Allah  sa'annan tare da bibiyan jagororin al'amuran mu , da fadakan jami'an tsaron mu  da kuma malaman mu  Allah madaukakin sarki ya ce : (  Kuraishawa sun bautawa Ubangijin   wannan dakin  sabo da sabawan su da tafiya  ta dari da ta damuna  su bautawa Ubangijin wannan dakin  wanda ya ciyar da su sabo da yunwa ya amintar da su don tsoro ).
      Hakika duniyar Musulmi suna samun albishir na gaba daya  haka nan ma jama'ar Afganistan musamman  da taron karawa juna sani kan zaman lafiya da mai hidima a masallatayya guda biyu madaukaka  ya yi kira zuwa gare shi  wanda kungiyan hadin kan musulmai na duniya ya shirya a garin makka mai daraja  ,   wanda ya kwadaitar bisa watsi da harkan kashe-kashe da rarrabuwa , da kuma kira zuwa ga gyara da hadin kai   da komawa zuwa ga hukunce-hukunce na shari'a a yayin husuma da sabani .
           Wannan sako na zaman lafiya  daga masaukan wahayi na hukunta  gaggautawan mutanen Afganistan  zuwa ga  rungumar zaman lafiya ,  musamman malamai daga cikin su tare da aiki wurin tabbatar da aminci da kwanciyar hankali a garin su  bayan karon battan su da ya tafiyar da danye da busasshe( be bar komai ba ) Allah madaukakin sarki ya ce : (  Ubangiji ya alkawarta ga wadanda da suka bada gaskiya daga cikin ku suka yi aiki na gargaru lallai zai mayar da su kalifofi a cikin kasa   tamkar  yadda ya sanya wadan da suke gaban su  lallai zai tabbatar musu da addinin su wanda ya yarda da shi gare su  lallai zai musanya musu aminci bayan tsoron su da za su dinga bauta min ba za su shirkanta komai

الاثنين، 9 يوليو 2018

Nesatan majalisan mabarnata


Hudubar Masllacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  na shaikh Salahu Bin Muhammad Albudair 22/10/1439h
YA KU MUSULMAI:
Nisantar zama da masu sabo  da guje musu, da barin farfajiyan su  da kauracewa wuraren su  da yanke abokantaka da su da gujewa tafiya tare da su  abu ne da ke nuna hangen nesan mutum  da kuma basirar sa .
                   Kubuta daga Laila  da makwabciyarta *** shi ne kar ka bi  ta  kwari daga cikin kauyukanta
 Zukata na da rauni shubuhohi na yawan fizga, fitintinu na tasowa , masu  basira   suna nisantar majalisan wadanda suke da cutar zuci, masu bata imani  kuma suna kiyayan  abokantaka da   fitinannu fandararru daga sunna  masu kaucewa duk wasu harka na musulunci da kama kai da dabi'u irin na musulmai .
 Idan ka kasance  kai lafiyan ka kalau   amma ka yi abokantaka da maara lafiya  ka kasance aboki gare shi , to kai ma fa ka zama mara lafiya .
Duk wanda ya zauna a majalisan wasu mutane wadda a cikin shi akwai sabo ko bidi'a , to ya wajaba a gare shi ya musu inkari da hikima tare da daddadan kalma  da wa'azi mai kyau da kuma dalili wanda ke bayyana gaskiya , mai gusar da shubuha,   idan har yana da ikon ya yi inkarin kuma bai yi inkarin ba  to ya kasance  zai yi tarayya da su a alhaki,  idan ya gagara kuma yin inkari a gare su  to fa ya wajaba a gare shi da ya bar majalisar tasu , sabo da zaman tare da cakudaidainiya na haifar da sabo da  kuma  koyi da abun , da kuma kyaliya  ga munkari  da kuma kauna a zuciya , kuma ta iya yiwuwa ma  fitinar ta fado a kan shi , Amru dan Kais ya ce (  Kar ka zauna da ma'abota bata sai zuciyarka ta bata ) Allah madaukakin sarki ya ce : (Alhali hakika ya saukar a gare ku cikin alkur'ani cewa idan kun ji ayoyin Allah ana kafirta da ita ana isgili da ita wato kur'ani , to, kada ku zauna tare da kafiran nan sai sun kutsa cikin wani zancen ba wannan ba , hakika ku yayinnan in kuka zauna tare da su kamar su kuke a cikin zunubi ) Imamu Addabari ya ce  : (A cikin wannan aya akwai nuni na bayyane bisa ga hanin zama da ma'abota  bata , na ko wani iri a cikin su  'yan badi'a ne ko fasikai  yayin kutsawan su cikin batar su shaikhul Islam Ibn Taimiyya Allah ya yarda da shi ya ce :  (Baya halarta ga wani da  ya halacci majalisan da ake barna bisa son zabin shi ba tare da wani lalura ba  kamar yanda ya zo a hadisi  Manzon Allah tsira da  amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (duk wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira to kada ya zauna a teburin da ake shan giya a kanta )  An daukaka kara zuwa ga Umar dan Abdul'aziz game da wasu mutane da suke shan giya  sai ya bada umarni da a musu bulala sai a kace da shi lallai a cikin su akwai mai azumi, sai ya ce  ku fara da shi , ase ba ku ji fadin Allah madaukakin sarki (Alhali hakika ya saukar a gare ku cikin alkur'ani cewa idan kun ji ayoyin Allah ana kafirta da ita ana isgili da ita wato kur'ani , to, kada ku zauna tare da kafiran nan sai sun kutsa cikin wani zancen ba wannan ba , hakika ku yayinnan in kuka zauna tare da su kamar su kuke a cikin zunubi)   Umar dan Abdul-aziz Allah ya yarda da shi  ya bayyana  cewa  ( masu halartan wurin sabo kamar masu aikata shi ne)
           Sabo da haka ne malamai suke cewa  idan aka gayyace shi zuwa ga walima wanda cikin shi akwai barna kamar shan giya da goge baya halatta da ya je sabo da Allah madaukakin sarki ya umurce mu da mu hana barna gwargwadon iyawa, duk wanda ya je bisa zabin shi to hakika ya    sabawa Allah da Manzon sa sabo da barin abin da aka umarce shi da shi  na daga kin inkarin sa da hani game da shi .  to idan ya kasance  hakan  , to  ina ga wanda zai halarci majalisan shan giya bisa  zabin sa ba tare da wata lalura ba  kuma bai hana barnan ba kamar yanda Allah ya umarce shi , to fa ya zama abokin tarayyan fasikai a fasikancin su ,  to kenan ya zama kamar su .
     YA KU MUSULMAI :
Kar ku kara  yawan  'yan bidi'a da barna da sabo  daidai da rana guda  kar ku kasance cikin tarun ma'abota fitina da barna .
       An karbo daga Abdullahi Dan Abbas Allah ya kara yarda a gare su  cewa wasu mutane cikin musulmai  sun kasance tare da mushrikai  suna  kara aukin mushrikai  a zamanin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi , idan anyi harbi sai kifiya ya samu daya daga cikin su ya kashe shi  ko kuma ya soke shi  sai Allah ya saukar da fadin sa  ( Lallai wadan da mala'iku ke kashe su  mutane ne da suka zalunci kawunan su ) buhari ne ya fitar da shi .
      Duk wanda ya halarci majalisai na barna  domin debe kewa da su da farin ciki da aikin su  ko kuma ya yarda da aikin  ko ya yi kira zuwa gare su  ko ya karfafe su  ,  ko kuma ya karfafi  shafi  mai shubuha a yanar gizo  da kuma shafuka  wadda suke na barna  da fasadi  da shafuka masu adawa da  addinin mu   da akidar mu  da  dabi'unmu  da  garinmu  ya kuma sanya musu alamar yarda  da karfafa to hakika ya kara aukin su ne  ya zama kuma cikin su  .
  HUDUBA TA BIYU
YA KU MUSULMAI:
Kar ku bayyana sabo kar ku halatta abin da Allah     ya haramta kar ku rudu da fatawar masu sakaci da sassautawa   da kuma  tsaka-tsakiyan masu da'awan fikihu , masu bada fatawa ba tare da yakini ba ko kyautatawa ba  suna karkata zuwa ga daya bangare na bata da sunan sauki  da tsaka-tsaki da daidaito .
      Duk wanda ya bayyana sabo   ya aikata shi a fili to hakika ya fusata Ubangijin shi   kuma ya keta alfarmar shi  kuma ya raina ukubar sa  ya cutar da bayin Allah Muminai to ku ji tsoron Allah ya ma'abota musulunci kar ku rudu da ni'imomi da yalwa    kada ku yi amfani da kyauta da aka baku gurin aikata barna,  kada ku bayyana sabo alhali Allah ya muku ni'ima da rayuwa mai yalwa da abin sha mai kosarwa,  ga mutane a kewayen ku suna halin bakar yunwa na kashe su  da kuma mutuwa mai muni .