السبت، 27 يوليو 2019

Alhurmar Aikin Haji


Hudubar Masallacin Annabi na shaikh Abdullahi dan Abdurrahman Albuaijan 23/11/1440AH
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya tattaro zuwa gare shi wanda ya nemi mafaka, Ya tanadi Aljannar ma'awa ga wanda ya nufe shi.
Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, ya daidaita bisa al'arshi, kuma ya yi hukunci,lalle kowani mutum da abin da ya nufa, na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne,bai bata ba kuma bai kauce hanya ba, kuma bai furuci bisa son rai face wahayi da ake yi masa, ya isar da sako ya bada amana ya yi wa Al'uma nasiha kuma ya yi umarni da takawa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa, da wanda ya bi su da kyautatawa ya hana rai ga soye soye rai,
 Bayan haka lalle mafi alherin zance shine maganar Allah,wanda aka saukar, kuma maga mafi gaskiya ita ce :
Ku saurara dukkan kome abin da ya ke ba Allah ba bata ne, kuma mafi alherin shiriya shi ne shiryarwar Annabi Muhammad dan Abdullah abin fifitawa, kuma mafi sharrin zance shi ne fararrun  mai kirkirare da ya zama bidiah, ko jahili mai wauta mai batarwa,ya ku bayin Allah, ina muku wasiyya da ni kai na da ku ji tsoron Allah don ita ce wasiyar Allah ga mutanen farko da na karshe, ( Hakika mun yi wasiya ga wadanda aka bawa littafi gabanninku da ku kan ku da ku ji tsoron Allah)
 Ya ku musulmai! Lalle Allah na halittan abin da ya so ya kuma yi zabi, hakika ya zaba cikin mala'iku manzanni da kuma cikin mutane.
Ya fifita ramadan bisa sauran watanni na lokaci, ya zabi Daki mai alfarma ya sanya shi dakin farko da aka sanya wa mutane,ya fifita shi ya sanya shi mazauni ya sanya shi gun samun lada da aminci ga mutane,da aminci ya albarkace shi ya sanya shi Alkibla,ya tattale shi ya ba shi alhurma,ya girmama shi ya sanya shi wurin ibada na tushe, (Allah ya sanya kaba daki tsararre ma'aunin Addini ga mutane)
Ya sanya Alhurma ga shingensa, ya sanya shi daki dadadde ya kira zuwa ga a nufe shi,Ibrahim ya ce : (ka  shelanta ga mutane a hajji za su zo ma a tafe da akan abin hawa zasu zo daga kowane sako)
             Ya ku musulmai! Ku amsa kiran Allah " mun amsa kiranka ya Allah kuma mun amsa kiranka ya Allah! Mun amsa kiranka ba ka da abokin tarayya ya Allah mun amsa kiranka! Lalle dukkan godiya da ni'ima naka ne kuma mulki ma naka ne baka da abokin tarayya.
Ya ku bayin Allah! Lalle musulunci Akida ne da Ibadoji da dabiu da halayya an gina shi akan abubuwa guda biyar, ; rukunnai wadanda sune tushe :Ta An karbo daga Ibnu Umar Allah ya kara yarda a gare shi da mahaifinsa ya ce :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : "An gina musulunci a kan abubuwa guda biyar; Akan su kadaita Allah da tsaida sallah da bada zakka da Azumin watan ramadan da hajji"Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
  
 Ya ku mutane!Lalle Allah ya wajabta hajji  a gare ku, to ku yi hajji,  Allah Madaukakin sarki yace (kuma akwai hajjin Dakin domin Allah, akan mutane ga wanda ya samu ikon zuwa gare shi)
Hajji ibada ce ta rayuwa, kuma karshen al'amari da cikan rukunan musulunci, a ciki ne Allah Mabuwayi da daukaka ya saukar da
(A yau na kammala muku Addininku,kuma na cika ni'ima ta a gare ku, kuma na yard da musulunci ya zama addini a gare ku)
An karbo daga Abu Said Alkudri cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :; Allah Madaukakin sarki ya ce;Lalle bawa na na bashi lafiyan jikin shi, kuma na yalwata mishi a rayuwa, shekaru biyar bai zo gare ni to lalle hasrarre ne) Ibnu Hibban ne ya fitar da shi a sahihinsa.
   Ku sauke farillun Allah, ku nufi dakin Allah (kuma ku cika hajji da umara domin Allah!)
Ya ku bayin Allah!
Hajji rukuni ne na wajibi kuma farilla ne na dole Alkur'ani mai girma ya yi nuni ga hakan da muhimmin labari mai girma, Hajji na cikin ibadoji mafi daraja, da ayyuka mafi girma  na neman kusancin Allah, da masa biyayya, yana daga darajoji yana goge kusakurai yana kankare munanan laifuka har da manyan su.An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: Duk wanda ya yi hajji don Allah bai yi jima'i ba kuma bai yi fasikanci ba zai koma kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi) Bukhari ne ya rawaito.
 Kuma Tirmizi ya rawaito a littafinsa Assunan ya ku inganta shi daga Abdullahi dan Mas'ud Allah ya kara yarda a gare shi ya ce ;Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: ku biyar da hajji da umara domin suna gusar da talauci da zunubai kamar yadda zuga zugi ke tafiyar da dottin karfe da zinari da azurfa.Hajji mabrur bai da sakayya sai Aljanna)
Ya zo cikin sahihu Muslim daga Abu Huraira an tambayi Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ko wani aiki ne ya fi falala? Sai ya ce :Imani da Allah:aka ce sa'anan sai me? Sai yace : jahadi a tafarkin Allah sai aka ce sai me? Sai ya ce : Hajji Mabruri)

Ya ku jama'ar musulmai!
Lalle Allah mai tsarki ne bai karba sai mai tsarki, to duk wanda ya nufi aikin hajji to ya kame daga Haram, to ya zabo daga dukiyarsa halal, An karbo daga Abu Huraira yace Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :( Lalle Allah Mai tsarki ne bai karba sai mai tsarki, lalle Allah ya umarci muminai da abin da ya umarci Manzannai sai ya ce (ya ku Manzannai ku ci daga tsarki kuma ku yi aiki na kwarai lalle ni masani ne ga abin da ku ke aikatawa) kuma ya ce: ( ya ku wadanda suka yi imani ku ci daga mai tsarkin abin da muka azurta ku) . sai ya ambaci wani mutum yana tsawaita tafiya mai gashi a tsatsaye da kura yana daga hannayen shi sama yna cewa : Ya Ubangiji na ya Ubangiji na a halin abincinsa na haramun ne, abin shansa na haramun ne, kuma tufafinsa na haramun ne kuma an ciyar da shi abin kalace na haramun.
Allah ya sanya ni da ku cikin wadanda suke jin magana su bi mafi kyansa, wadannan su  Allah ya shiryar wadannan su ne ma'abota hankula.
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah da ya bada kuma ya ni'imta, ya kuma shiryar zuwa ga shiriya kuma ya yi ilhama, ya bayyana daidai ya kuma fahimtar,ya sanya hajji mafi darajan aiki kuma mafi girma,
 Ya ku musulmai!
Lalle kuna wata mai alfarma da Allah ya shar'anta alfarmanta ya girmama shaninta ya yi gargadi game da zalunci a cikinta sai ya ce:( Lalle kidayan watanni a gurin Allah guda shabiyu ne a littafin Allah a ranar da ya halicci sammai da kasa, daga cikinsu akrajab da muwai guda hudu nasu alfarma) uku daga cikin su a jere suke Zulka'ada da zulhajji da Muharram da rajab,na mudar. Sannan ya ce wannan wani wata muke ciki sai muka ce Allah da ManzonSa ne suka fi sani sai ya yi
Shuru har sai da muka tsammaci zai ambace shi da wani sunan ne, sai yace ase ba zulhajji ba ne sai mka ce : E sai yace wani gari ne wannan sai muka ce Allah da ManzonSa ne suka fi sani sai ya yi shuru har muka zaci zai ambace shi da wani suna da ba shi ba sai yace Ase ba wannan bane gari mai alhurma? Sai suka ce e shine.sai yace to a wace rana muke?sai suka ce Allah da Manzonsa ne suka fi sani. sai ya yi
Shuru har sai da muka tsammaci zai ambace shi da wani sunan ne, sai yace ase ba a ranar suka muke ba? Sai suka ce: E   haka ne sai ya ce : To lallai jininku da dukiyanku da mutunci a gare ku haramun ne, kamar alhurma wannan ranar taku a wannan gari naku a wannan wata taku., za ku hadu da Ubangijinku zai tambaye ku game da Ayyukanku, ku saurara : kada ku koma a baya na kafurai sashinku na dukan wuyan sashi, to ku saurara wanda ya ke nan ya sanar da wanda bai nan, don ta iya yiwuwa wanda za a isar zuwa gare shi ya kiyaye fiye da wanda ya jiyo.ku saurara! Shin ko na isar da sako, shin ko na isar da sako) Bukhari da muslim ne suka rawaito.
Lalle watan zulkida shine watan farko cikin watanni masu alfarma da suke hade, a cikinsa ne Annabi ya kasance ya yayin da mushrikai suka hana shi shiga,da umaran da ya yi a shekaran da ta kewayo a zulkida ne ya yi ta a lokacin da ya yi sulhu da su, azulkada a yayin da ya yi sulhu da su, da umarar ji'irrana wanda ya raba ganimar hunain,da umara da ya yi da hajjinsa.  Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Ya ku bayin Allah !
lokaci na hajji lokaci ne na biyayya da da'a da kyauta, kuma karama ce  samun kyautar,
ya kasance a jahiliyya abin alfahari ne shayarwa ga Alhazai da suturce kaba da bata kulawa.suna munafasa a cikinta, da musulunci ya zo sai ya tabbatar da haka, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shiya yiwa Abbas izini da ya kwana a makka a dararrakin kwanan mina don shi,ya zo gurin da ake shayarwa  da ya nemi da a shayar da shi kuma ya sha ya tafi ta gun masu zamzam a halin suna shayarwa suna aiki sai yace (ku yi aiki lallai kuna kan aiki na kwarai,)  yace (Ba don kar a yi galaba a kanku ba da na sauka har na sa igiya a nan fa ya yi nuni ga kafadansa) Bukhari ne ya rawaito.
Allah ya yi gyadan dogo ga kasar Saudiya cikin hidima da ta ke yi na wurare masu tsarki, da amintar da shi ga masu dawafi da masu itikafi da masu rukui da sujada, ya mata baiwa na hidima da karbar bakuncin Alhazai da 'yan umara da masu ziyara ko shige da fice, tare da tausaya musu da gabatar da hidima da ta dace a gare su, da agaza musu wurin sake nauyin ibadojinsu,da shinfida musu dukan wata hanya ta aminci da zaman lafiya gare su, to Allah ya saka wa jagororinmu da shugabanninmu da sakayya mafi  alheri da cika da kamala da kyau da tsarki, bisa abin da suke tashi da shi na hidima ga masallatayya biyu masu alfarma da daukaka da masu tahowa gare su.
Ya ku bayin Allah! Ku kuna guri ne da ya fi soyuwa a gurin Allah, to ku bada hadin kai wurin ganin ku taimakawa ma'aikata masu tsare tsare da hidima, Allah ya karba mana ni da ku, ya mana gamon katar.
Alhazai ga daki mai alfarma,…
Hakika kun yi kokari kun yi dace na amsa kiran Allah na haji wajibi, to ku dage wurin yinta da cikata bisa yadda zaa karbe ta, ku nemi sanin hukunce – hukuncenta, na gargade ku da ku nesaci jima'I da fasikanci da jayayya (Haji watanni ne sanannu to duk wanda ya shiga aikin haji cikinsu babu batsa ko fasikanci ba musu a hajji)
   Ku sa nitsuwa da tsanaki, ku yi aikin jinkai idan an samu cunkoso, ku yi nesa da turereniya, ku tausayawa masu rauninku,domin a dalilinsu ne ake azurta ku a baku nasara.
 An karbo daga jabir yace Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya goyi Usama abayansa ya taso daga Arfa yana matse linzami dabbarsa Alkaswa kanta na taba tankin dabbar ya na nuni da hanunsa na dama da (ya ku mutane Natsuwa natsuwa) a duk lokacin da ya zo wani dutse daga cikin duwatsu sai ya dan saki linzami gareta har ta haura har ya iso muzdalifa) .Muslim ne ya rawaito


الأحد، 30 يونيو 2019

kuma abin da ya ke a gare ku na ni'ima to daga Allah ne


Hudubar Masllacin Annabi na shaikh Abdulbari Bin Awad Assubaiti 25/10/1440Ah 28/6/2019Ac
Ni'imomin Allah ga bayinSa suna da yawa ba za'a iya iyakance su ba,mai dunbin yawa ne da ba za a iya kwalkwale su ba, suna bibiyan juna basu karewa :Allah Madaukakin Sarki ya ce : (Allah ne wanda ya halicci sammai da kasa, kuma ya saukar da ruwa daga sama sa'anan ya fitar game da shi daga 'ya'yan itace, arziki  domin ku, kuma ya hore jirgin ruwa yayi gudu a cikin teku da umarninSa, kuma ya hore muku koguna.kuma ya hore muku rana da wata suna madawwama biyu, kuma ya hore muku dare da wuni. Kuma ya baku dukkan abin da ku ka roke shi, kuma idan kun kidaya ni'imar Allah ba za ku lissafe ta ba, lalle ne mutum hakika mai yawan zalunci ne mai yawan kafurci ).
Samuwan abubuwa masu amfani da tunkude  cutarwa da ma dukkan alheri da bawa yake samu ni'ima ce daga Allah zuwa gare shi ; na ilimi da imani da aiki da zuriya da masauki da abin hawa da walwala da nasara Allah Madaukakin sarki ya ce (kuma abin da ya ke a gare ku na ni'ima to daga Allah ne) kuma lura da abin da ya ke kewaye da mu yana kaimu ga jin niimar Allah , Allah madaukakin sarki ya ce (To mutum ya duba zuwa ga abincinsa) kuma ya ce (To mutum ya duba daga me aka halicce shi).
Muminai na dubi ga ni'imar Allah na ciki da na waje: hakan sai ya kara musu imani ya kusanto da su ga Ubangijinsu suna masu ikirari da baiwarsa da alherinSa da falalarSa a gare su, Allah madukakin sarki ya ce : (suna yin gori gare ka don sun musulunta, kace kada ku yi gorin kun musulunta a kai na, Aa Allah ne ke yi muku gori domin ya shiryar da ku ga imani, idan kun kasance masu gaskiya.)
Mumini da kaifin hankalinsa da nunan tunaninsa; na dubi ga ni'imomin Allah da ke kewaye da shi, Allah madaukakin sarki ya ce yana mai sifanta halin muminin da zai karbi aikinsa : (Har a lokacin da ya kai ga mafi karfinsa,kuma ya kai shekara arba'in yace ya Ubangiji na! ka kange ni, domin in godewa ni'imarka, wadda ka ni'imta a kaina, da kuma a kan mahaifa na biyu, kuma domin in aikata aikin kwarai, wanda ka ke yarda da shi)
 Idan zuciyar bawa ta cika da imani; ni'ima ta godiya ga ni'imar sai ta tabbatu a gare shi, sai kai komonsa  su gyaru halayensa su tsarkaka,sai ya yi dace, Allah madaukakin sarki ya ce yana mai gori ga bayinSa: (kuma Allah ya soyar da imani a gare ku, kuma ya kawata shi a cikin zukatanku, kuma ya kyamatar da kafirci da fasikanci da sabo zuwa gare ku, wadannan sune shiryayyu. Bisa ga Falala daga Allah da ni'ima, kuma Allah Masani ne Mai hikima).

Ikirari da ni'imar Allah na daga cikin abin da ke hukunta tuna ni'imomin Allah, da kuma jingina su ga wanda ya bada su - daukaka ya tabbata a gare shi,- wanda ke dakon ni'imomi to ba zai gushe ba yana tuna mai bada su, wanda shi ne Allah Madaukaki  Mai ni'imtarwa da dukkan ni'imomi wadanda muke jujjuyawa a cikinta,
Yin ikirari da ni'imar Allah shine mabudin dukkan Alheri, zai sanya harshen mumini yana furta (Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mai mulki ranar sakayya)  a tsawon wuninsa da darensa.
Idan musulmi ya tabbatar da ni'imar Allah a kan sa, ya yi ikirari da falolin UbangijinSa da ke kewaye da shi,; to lalle zai yi amfani da wadannan ni'imomin wurin neman yardar Allah Madaukaki, ga Annabi Sulaiman Amincin Allah ya tabbata a gare shi yana rokon UbangijinSa; (ya Ubangiji ka cusa mini in gode wa ni'imarka, wadda ka ni'imta ta a gare ni, da kuma ga mahaifana biyu, kuma in aikata aiki na kwarai, wanda kake yarda da shi, kuma ka shigar da ni sabo da rahamarka a cikin bayinka salihai,)
Ga Annabi musa abokin maganar Allah yana kulla alkawari ga Ubangijinsa     ; ( Yace Ya Ubangiji! Domin abin da ka ni'imta shi a kai na saboda haka ba zan kasance mai taimako ga masu laifi ba)
Idan musulmi ya tabbatar da ni'imar Allah a kan sa, to zai bayyana wadannan ni'imomin ne halin yana mai godiya da yabo, ba yana mai alfahari da girman kai ba, Allah madukakin sarki ya ce:    (kuma amma ni'imar Ubangijinka sai ka fada (domin godiya). Wato ka labarta wa mutane abin da Allah ya ma na ni'ima kana mai girmama wa ga Mai ni'imtarwan.
Ya zo a hadisi ( Idan Allah ya yi ni'ima ga bawa to yana so ya ga gurbin ni'iman a gare shi).Baihaki ya rawaito da isnadi hasan.
An karbo daga Abul Ahwas Aufu dan malik dan Nadlah daga Babansa yace :( Na zo ga Manzon Allah a halin ina wani yanayi na tufafi mara fasali, sai ya ce : kana da dukiya? Sai na ce :E, sai yace daga wani irin dukiya? Sai na ce : daga dukkan nau'i Allah ya bani; na daga rakuma da bayi da dabbobi, sai yace : To idan Allah ya baka dukiya ta aga hakan tare da kai).Ibnu Hibban ya rawaito a sahihinsa
  Idan ni'imomi sun tattaru ga rayuwar bawa ;to fa wani albishir ne na alheri ga ma'abocinsu muddin ya fahimci hakkinsu da ke kan shi kuma ya sauke wajibi, kuma ya sarrafa su ta hanyar da ke nuna godiya da bauta ga Allah.Amma wanda ya rudu da kansa ya yi jiji da kai da abin da Allah ya bashi na ni'ima har ma ya jinginta ta ga kansa kamar yadda Allah ya ambata a kur'ani bisa harshen Fir'auna yayin da ya ke cewa : (kuma Fir'auna ya yi kira a cikin mutanensa, yace : ya mutane na! ashe mulkin masar ba a gare ni yake ba? Kuma wadannan koguna suna gudana daga karkashi na? ashe ba ku gani ba)
 Haka ma Karuna yace( An bani shi akan wani ilimi wanda yake gare ni kawai)
To irin wannan ni'imar ce take juyawa azaba alherinta ya zama sharri samunta ya zama bala'i.
Mafi girman godiya ita ce gaggauta wa zuwa ga ibada Allah yace (A'a Allah kadai zaka bauta wa kuma kasance cikin masu godiya).
To kuma idan bawa ya yi kokari wurin bautawa Ubangijinsa yana mai godiya a gare shi bisa ni'imominsa, to lallai sakayyarsa a gurin Allah na daga cikin irin aikin da ya yi. Allah Madaukakin sarki ya ce : (Lalle wannan ya kasance sakayya a gare ku, lalle aikin ku ya kasance abin godewa).
Bawa ba zai iya sauke nauyin godiyan ni'immomi ba duk yadda ya yi kokari , ya isan mishi ya yi kokari ya samu yardan Allah Madaukaki! Ya samu ya yi godiya na gabadaya da godiya na musamman, a duk lokacin da ni'ima ta sake samuwa sai ya sake mata sabuwar godiya. Ya zo a hadisi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce (wanda ya ce idan ya wayi gari; Ya Allah abin da ya wayi gari da ni na ni'ima ko wani daga cikin halittunka to daga gareka ne yake kai kadanka baka da abokin tarayya kuma dukkan yabo da godiya naka ne to hakika ya sauke nauyin godiya na wannan rana, wanda ya ce idan ya yi yammaci Ya Allah duk abin da ya yi yammaci da ni na ni'ima ko daya daga cikin halittunka to daga gareka yake kai kadanka baka da abokin tarayya, to yabo da godiya ya tabbata agreka to hakika ya sauke nauyin godiya na wannan dare).
kuma  (An karbo daga Rifaa dan Rafi' Azzuraki ya ce mun kasance wata rana muna salla a bayan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yin da ya daga kansa daga ruku'u kuma ya ce :Allah ya amsa ga wadanda suka gode mishi sai wani mutum a bayan shi ya ce:Ubangijinmu godiya ta tabbata gareka ,godiya mai yawa tsarkakakkiya mai albarka a cikinta yayinda Manzon Allah ya idar da sallah sai ya ce: wanene yayi magana dazu? sai wanan mutumi ya ce nine ya manzon Allah! sai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce hakika naga mala'iku talatin da dori suna rige rige waye zai fara rubuta ta )Hakim ne ya rawaito da ibnu hibba da isnadi ingantacce
 Musulmi zai yi gaggawa zuwa kofan adu'a yana rokon Ubangijinsa da ya mishi ilhama na godiya, domin ya kankare tawaya da nakasa, ababin niimomi (kuma ka samu masu godiya bisa niimarka masu kuma kyawtata yabo da ita agare ka to ka karbe ta ka cikata agare mu )Ibnu Hibban ne ya rawaito.
Amma wanda idonsa ya makance daga ganin ni'imomin Allah to hakika wannan ya fada  rabon shaidan da waswasinsa da makircinsa, kura'ani ya hakaito hakan daga gare shi (saannan zan zo musu daga gaba garesu kuma daga baya garesu kuma daga damansu da kuma hagunsu ba za ka samu mafiya yawansu ba suna masu godiya)
Musulmi na gafala daga riskan ni'imomin Allah a gare shi yana mai   rainata ma a lokacin da ya ga abin da ke hanun wasu na ni'imomi. A cikin sahihu muslim daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(ku yi dubi zuwa ga na kasa da ku kar kuyi dubi zuwa ga wanda ya ke sama da ku domin haka ya fi dacewa don kar ku rena niimar Allah a gare ku.
Na daga cikin munanta ladabi ga  Allah dulmuya cikin ni'imomi da manta Mai yin ni'imar da kuma zurfafa wa cikin farin ciki da manta Mai yaye bakin ciki  da bacin rai, Allah Madaukakin sarki ya ce (kamar wancan ne Allah ya ke cika niimarsa a kanku tsammaninku kuna mika wuya )
(To idan sun juya to abin da ya wajaba a kanka shi ne isarwa bayyananniya) (suna sanin niimar Allah sa'annan kuma suna musantawa kuma mafi yawansu kafirai ne )kuma ya ce: (kuma wanda ya musanya niimar Allah bayan ta zo mishi to lalle ne Allah mai tsananin ukuba ne).
                 
                           Huduba ta biyu
 Mai hankali ya na kiyaye amfani da  ni'imomin Allah ba tare da ya yi sakaci da hakkin Allah a ciki ba  da bauta da godiya, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (Idan ka ga Allah yana baiwa bawa abin da ya ke so alhali shi kuma bawan yana saba mishi to lalle hakan a gareshi daurin talala ne sannan sai aka yayeta da wannan ayan(saannan kuma A lokacin da suka manta abin da aka tunatar da su da shi sai muka bude a kansu kofofin dukkan kome har a lokacin da suka yi farinciki da abin da aka basu, muka kama su kwasam, sai gasu sun yi tsuru- tsuru, sai aka katse karshen mutanen,wadan da suka yi zalunci, kuma godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai ) Ahmad da Baihaki ne suka rawaito Albani ya inganta shi.

Kuma musulmi na sanya bautarsa a hade da abin da ya ke riska na ni'ima, idan an bashi ni'ima sai ya yarda in an dauke sai ya yi fushi, to wannan sifa ce abin zargi,
 Allah Madaukakin sarki ya ce (kuma cikin mutane akwai mai bauta wa Allah bisa gefe, sa'annan idan wani alheri ya same shi sai ya natsu da shi, kuma idan wata fitina ta same shi sai ya juya baya akan fuskarsa ya yi hasarar duniya da lahira.
An karbo daga Abdullahi dan Abbas Allah kara yarda a gare su, yace: (kuma cikin mutane akwai mai bauta wa Allah bisa gefe,) Mutum ne zai zo Madina idan matarsa ta haifi da dokin sa ya haihu sai ya ce : wannan Addini ne mai kyau, idan matarsa bata haihu ba dokin sa bai haihu ba sai ya ce : wannan mummunan addini ne).

الجمعة، 21 يونيو 2019

kofofin tuba


Hudubar Masllacin Annabi na 11-10 -1440AH/14-6-2019 AD na Sheikh Abdullah bin Abdurrahman Albu'aijan.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna gode masa muna neman taimakonsa muna neman gafararsa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi duk wanda ya batar da shi ba zaka sama mishi majibinci mai shiryarwa ba.
Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, ya halitta kuma ya daidaita abin halitta ya kaddara (abin da ya so) ya shiryar, na shaida Annabi Muhammad bawansa ne kuma manzon sa ne, wanda ya turo shi da gaskiya da shiriya, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbansa da duk wanda ya bi sawun shi,ya bi tafarkinsa da kyautatawa har zuwa ranar sakayya,
Bayan haka: Lallai mafi alherin zance shi ne littafin Allah, kuma mafi alherin shiryarwa shine shiryarwa Muhammad dan Abdullah, Mafi sharrin al'amura sune fararrunta, dukkan fararrun abubuwa bidiah ne, dukkan bidiah bata ne dukkan bata na wuta.
Ya ku bayin Allah … ku ji tsoron Allah cikin abin da ya umarta, ku hanu daga abin da ya hana ya tsawatar, ku sani dukkan karami da babba ana rubuta shi, (ya ku wadanda suka yi mani ku bi Allah da takawa, kuma rai ya dubi abin da ya gabatar domin gobe, kuma ku bi Allah da takawa lalle Allah mai kididdigewa ne ga abin da ku ke aikatawa,)
Ya ku bayin bayin Allah!
Lokaci na albarka da falala da alheri da da'a ranakunsa ya kare an nade ayyukansa, lalle wata ne mai girman falala, tasirin sa a cikin Al'uma na da ban mamaki, masu nasara cikin shi sun ribata,masu kokari cikinsa sun samu ganima,ina ma da mun san wanda aka karbi ayyukansa mu mishi barka! Wane ne baa karba mishi ba mu jajanta mishi,
Madalla da farincikin wanda suka rabauta, Allah ya musu ilhamar tuba, ya datar da su ga biyayya, muna roka musu Allah da ya karba musu ya dora su kan daidai.
Ya  kaiton hasarar wadanda suka rasa wannan alheri aka katange  su daga Ubangijin su, damammaki a rayuwa suka kwace musu.ga lokutan alheri basu ribaci komai ba sai hasara da nadama,
Sai dai ya jama'ar musulmi ! kofofin tuba basu gushe ba suna bude ba a rufe su ba bayan watan ramadan,Ubangijinmu mabuwayi da daukaka yana karbar tuba daga bayin sa a kowane zamani da guri  (Shi ne yake karbar tuba daga bayin sa kuma yana yafe munana, kuma ya san abin da kuke aikatawa).
     Ya tabbata daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :Lalle Allah ya fi farinciki   da tuban bawansa mumini  akan mutumin da  yake cikin kasa ta sahara wacce  ke da ababan halakarwa   yana tare da dabbarsa  abin cin shi da abin shan sa na kanta   sai ya yi bacci , da ya farka sai ya ga ta tafi  ya yi ta nemanta  har sai da  kishi ya cimmasa  sai ya ce bari na koma wurina da na kasance a cikin shi  sai na je na yi bacci har ma na mutu  sai ya dora kanshi  a bisa damtsen shi don ya mutu yana halin haka  sai ga dabbarsa a kan sa  tare da ita ga guzurin shi da abin cin shi  da abin shan sa  sai  ya rike linzamin ta yayi kuskure don tsananin farin ciki yana mai cewa ya Allah kai ne bawana ni ne Ubangijin ka  .
An karbo daga Abu Huraira  Allah ya kara yarda a gare shi ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce:(Idan wani yanki na dare ya shude ko kuma wani sulusin  shi , Ubangijin mu mai tsarki da daukaka zai sauko  zuwa ga  sama na  duniya  sai ya ce:-
Ko shin akwai mai tambaya na ba shi , ko shin akwai mai roko na amsa mishi , shin akwai mai neman gafara a gafarta masa har gari ya waye  . Muslim ne ya rawaito)
Zuwa ga wanda daman ramadan ya kwace mishi  to ka yi gaggawa zuwa ga tuba  kafin lokaci ya tsere   da kuma shammatan ajali kada ka yanke tsammani don duk dan adam mai kuskure ne  abin zargi  na ga wanda ya doge  kuma alhali yana da Ubangiji mai gafarta zunubai kuma bai nemi gafarar sa ba , ba don kun kasance kuna kusakurai ba kuma kuna neman gafara da  Allah ya tafiyar da ku ya kawo wasu mutane wadan da suna kuskure kuma suna neman gafara sai Allah ya gafarta musu .
YA KU BAYIN ALLAH:
Ku ji tsoron Allah kuma ku nemi gafarar sa  kuma ku koma zuwa gare shi ku mar da'a  kada ku jinkirta tuba domin  mutuwa na zuwa bagtatan  .
Allah madaukakin sarki ya ce :-(Ku tuba suwa ga Allah gaba dayanku ya ku muminai  ko za ku  rabauta)
Kuma ya ce :-( Ka ce  ya ku bayi na wadanda suka   barnatawa kawunan su  kada ku yanke tsammani daga rahamar Allah lallai Allah yana gafarta zunubai baki daya  lallai shi mai gafara ne kuma mai jin kai .  Ku koma zuwa  ga Ubangijinku  ku mika wuya gare shi  kafin azaba ya zo muku  sa'annan ba za a taimaka muku ba , ku bi mafi kyaun  abin da aka saukar gare ku daga Ubangijin ku  tun kafin azaba ya zo muku  bagtatan a halin kuna baku sani ba  kada rayi ta ce  ya hasara ta  bisa  abin da na yi sakaci a janibin Allah  , ko da na kasance cikin  wadan da suke masu isgili  ko kuma ta ce ina ma da Allah ya shirye ni  da na  kasance cikin masu takawa  , ko kuma ta ce ya yin da ta ga azaba  ina ma da ina da kome da na kasance cikin masu kyautatawa 

YA KU MUSULMAI:
Lallai ibada na da tasiri  cikin halayen ma'abocinta Allah madaukakin sarkiya ce :-(Lallai sallah na hani ga alfasha  da munkari)
Na daga cikin alamomin karban ayyuka  akwai canzawan halayen zuwa mafi kyan hali  a daya bangaren kuma  yana daga cikin alamomi na  rasa alheri da rashin karban aiki  akwai komawa baya  daga da'a  bayan shudewan ramadana  yanayin halaye ya canza zuwa mafi muni  domin sabo sashi na janyo sashi , madalla da kakkyawa bayan mummuna  sai ta goge ta  mafi kyaunta kuma shi ne kyakkyawa bayan kyakkyawa  tana mai binta , ku roki Allah tabbatuwa akan da'a har zuwa mutuwa  kuma ku nemi tsarin Allah  daga juyawar zukata  haka nan kuma daga warwarewa bayan daurewa .

 Abin mamaki da munin  kaskanci  na sabo  bayan izza ta da'a  tir da  talauci na  kwadayi bayan wadatuwa da wadatan zuci  ku roki Allah tabbatuwa , ya tabbata daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :-( Lallai dayanku  zai yi aiki irin na 'yan aljanna  har sai ya kasance tsakanin shi da ita  face zira'I  sai littafin sa ya rigaya  , sai ya yi aiki irin na 'yan wuta sai ya shige ta ,  kuma lallai dayan ku zai yi aiki irin na 'yan wuta   har sai ya kasance tsakanin shi da ita face zira'I sai littafin shi ya rigaya sai ya shigeta  Buhari ne ya rawaito)
Ina fadin abin da kuke ji ……….

HADUBA TA BIYU

Dukkan yabo da godiya sun tabbata  ga Allah wanda  yake karban tuba daga bayin sa  kuma yake yafe kusakurai kuma ya san abin da kuke aikatawa ,  kuma yana amsa kiran wadan da suka yi imani kuma  suka yi aiki na kwarai   kuma yana kara musu daga falalar sa .
 YA KU MUSULMAI :
Watanni dukan su lokuta ne na ibada  ko da sun sha banban  sun saba a wurin fifiko  da ayyuka  rayuwa dukkanta   dama ce ta aiki  da biyayya   ko wanne yana wayan gari yana mai saida kan sa akwai mai 'yantata akwai kuma mai halakata ,  kuma kowa ana yassare mi shi abin da aka halicce shi  akanta   , .
To ku sabarwa kawunan da da'a ku nemi taimako game da ita da tuba  da neman gafara  da komawa zuwa gare shi da marairaicewa  da kuma murakaban Allah  guda mai rinjayi  a sirri kuma da bayyane a dare da wuni .
 (Ku bar  sabo na zahiri da na badinin  sa  lallai wadanda suke aikata laifi za a sakanya musu da abinda suka kasance suna aikatawa)
YA KU BAYIN ALLAH:
Ku rantawa Allah rance kyakkyawa , ku kaddamarwa kawunan ku abu mai amfani , (Duk wani abu da za ku kaddamar wa kawunan ku na alheri za ku same shi a wurin Allah).
(Wane ne zai rantawa Allah rance mai kyau sai ya ribanya mishi ribanyawa mai yawa).
Sannan ku sani cewa azumi garkuwa ne , dukkan aikin dan adam  na shi ne  sai azumi to shi na Allah ne zai sakanya game da shi , to duk wanda zai iya  a cikin ku ya azumci azumi shida a shauwal  to lallai hakan na daga cikin sunna  kuma aiki ne na musdafa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
An karbo dga Abu ayubal Ansari Allah ya kara yarda a gare shi ya ce  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbataa agare shi ya ce :-(Duk wanda ya yi azumin ramadana  sannan ya bi da guda shida  a shauwal  zai kasance kamar ya yi azumi na shekara ne )Muslim ne ya rawaito
Sabo da kyakkyawa guda na da lada goma kamarta,to ramadana na da ladan wata goma, guda shidan kuma ladan wata biyu, kuma adadin watanni a gurin Allah goma sha biyu ne,
Ba laifi mutum ya yi azumin a jere ko a rarrabe, muddin dai a cikin watan shauwal ne, tamkar tana matsayin sunnoni ne na ratibi game da sallolin farilla,tana cike gurbin tawaya ne da aka samu a farilla.

        YA KU MUSULMAI :
Ku ji tsoron Allah,iya iyawanku,ku yi riko da addininku,ku kankame sunnar Annabinku, ku kuma gyara tsakaninku,ku kiyaye hadin kanku, da garinku, ku zama hanu guda kan abokin gabanku, ku roki Allah da ya tabbatar da ku ya datar da ku,
Bayan haka YA KU MUSULMAI :
Lallai abin da masu ketare iyaka suka suka aikata na harbi kan 'yan kasa da mazauna, da tsorata amintattu, da zubar da jinin wanda bai ci ba bai sha ba.da yara da mata, da keta alfarman wurare masu tsarki manya da gari mai alfarma, na daga cikin manyan laifuka abin ki ga dukkan addinai, kuma yana cin karo da ginshikai na musulunci, Alla maida musu sharrinsu a kan su.ya sanya yakinsu a tsakaninsu, kuma ya yanke karshensu.
Ya Allah ka kare wannan kasa da kariyarka.

الجمعة، 17 مايو 2019

ka yi sujada ka kusanto


Hudubar Masllacin Annabi na sheikh Abdulbari Bin Awad Assubaiti 12 Ramadan 1440Ah
Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga  mafificin halittun Allah,
Bayan haka !
A kalmomi biyu na karshen farkon sura da aka saukar a Alkur'ani Allah yana cewa:(Kuma ka yi kujada ka kusanto ) an karbo daga  Abu Huraira  Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :-( lokacin da bawa ya fi kusanci da Ubangijin shi shi ne a halin yana sujjada , to ku yawaita adu'a ) Muslim ne ya rawaito
Sujada shi ne mafi daukakan hali na bawa , a cikin shi ne mutum zai ji dadin rusunawa mabuwayi mai girma  da kuma  kawa irin na kankan da kai ga mai rahama mai jin kai , wasu lokuta ne na karamci da albarka  wanda ba su da iyaka .
 Acikin sujada ne a ke jin dadin da baya misaltuwa   da yaye walwalan zuciya  wanda ba alkalamin da zai iya iyakance shi  yana  kaurar da musulmi daga kunci ,  zuwa ga yalwa mai fadi  na kasa  cikin sararin samaniya  sabo da haka ne  (Aisha Allah ya kara yarda a gare ta  ta sifanta tsayuwan daren Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da cewa; yana sujjada  guda da zai kai dayan ku ya karanta aya hamsin  kafin ya dago)  Buhari ne ya rawaito .
Sujada na kara wani haske na imani   daga ma'abocin shi ya jefa wani walwala a zuciya da natsuwa  ya bashi wani  gairmamawa , Allah madaukakin sarki ya ce :-(Muhammadu Manzon Allah ne , kuma  wadan da suke tare da shi  suna masu  tsanani ga kafurai  masu tausayi a junan su  za ka gansu suna masu yawan ruku'u da sujada  suna neman falala daga wurin Allah  da yarda  alamun su  na fiskan su na gurbin sujada )
Asujada ne Ubangiji ke kasancewa kusa da wanda ya roke shi  , Ubangiji mai tsarki    yana kusa da wanda ya roke shi  , mai amsawa ne ga wanda ya nemi ganawa da shi   mai badawa ne ga wanda yayi fata gare shi  duk wanda ya kusanci Allah to lallai zai riski kyauta mafi yalwa daga Ubangijin shi, kuma ya samu matsayi mafi
aminci da yakini da kariya mai karfi  ,  Allah madaukakin sarki ya ce (To amma (  idan mai mutuwan ya kasance daga makusanta   sai hutawa  da kyakkyawan abinci da aljanna mai ni'ima )
Makusantan suna da Rauhun shi ne;  hutu  da natsuwa da farin ciki  da kuma annashawa , Raihan   shi ne suna da ya tattaro dukkan  wani jin dadi na  jiki  na daga abinci ne ko abin sha  da makamantan su ,  da  (aljanna mai ni'ima) wanda a cikin ta akwai abinda ido bai gani ba kuma kunne bai ji ba kuma bai halarto a tunanin wani dan adam  ba yana yiwa makusantan shi albishir yayin  halartowan mutuwan su da wannan albishir din  wanda  rayuka ke kusa da su fire sabo da tsabar jin dadi da farin jiki , (ka yi sujada kuma ka kusanto )      
A ko wani sujada kana da daukaka na daraja   da kusanci na matsayi  da kuma kusanci na wuri  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :- (Ba wani bawa da zai yi sujada  don Allah face an rubuta mishi kyakkyawa da ita , an kankare mishi mummuna da ita  an kuma daga darajar ku da  ita  , to ku yawaita yin sujada ) Ibn Maja ne ya rawaito da isnadi ingantacce
To kyautan Allah bai  karewa duk wanda ya kusance shi sai ya saukar da shi bisa falalan sa daraja irin na Annabawa  da siddikai da shahidai  da salihai , Manzon Allah tsira  da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da Rabi'ata Dan Ka'ab Al-Aslami a lokacin da ya nemi kusanci da Manzon Allah a aljanna  sai  ya ce da shi:-(  ka taimaka mini akan kanka da yawan sujada)   Muslim ne ya rawaito

     (ka yi sujada kuma ka kusanto ) a cikin sujada ne alamomi na gaskatawa da imani ke bayyana alamomin yakini da mika wuya ke fitowa fili , an karbo daga Aliyu dan Abi Dalib  Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :-  ya kasancen  daga  cikin adu'o'in manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a sujadan sa  Allahumma laka sajadtu , Aya Allah don kai na yi sujada , wabika amantu , da kai ne kuma na yi imani  wa laka aslamtu, kuma da kai na mika wuya  ,  fiska ta ta yi sujada ga wanda ya halicce ta ya sauwara ta  ya tsagi jinta da ganin ta  tsarki ya tabbata ga Allah mafi kyaun masu halitta )Muslim ne ya rawaito
(ka yi sujada kuma ka kusanto ) lalle sujada na    cikin ibada  wanda dukkan halitu suka yi tarayya suka tattaru a kanta (Kuma ga Allah abinda yake cikin sammai da kasa na dabba da mala'iku suke yin sujada , kuma basu kangara .  Suna tsoron Ubangijin su daga bisan su  kuma  suna aikata abinda ake umarnin su )
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce ni ina ganin abinda bakwa gani kuma ina jin abinda bakwa ji , sama ta yi  kara kuma ta cancanci ta yi karan sabo da  babu wani bigirea na yatsu fa ce mala'ika yana daure da fiffigen shi yana mai sujada ga Allah , wallahi da kunsan  abinda na sani da kunyi dariya dan kadan kunyi kuka mai yawa . Da ba ku ji dadi da mata ba akan shimfidi  da kun fita kwararo –kwararo  kun yi kururuwa  kuna kara  zuwa ga Allah ) Nasa'I da Ibn Maja ne suka rawaito  da Ahmada.
1.   (ka yi sujada kuma ka kusanto ) ka yi sujada kana mai rokon Ubangijin ka kana mai kiran mahaliccin ka  , kana mai kankan da kai zuwa ga masoyin ka , kai din nan kana aljanna ne daga cikin aljannoni na duniya , ka yi sujada sujudan mai tsoron Allah   a duk lokacin da ka ji ayoyin alkur'ani , bayanansa suka ratsa ma zuciya.

 Allah madaukakin sarki yana cewa (Kuma yana abun karatu  mun rarraba shi domin ka karanta shi ga mutane akan jinkiri,  kuma mun sasaukar da shi sassaukarwa  ka ce ku yi imani da shi ko kuwa  kada  ku yi imani ,   lalle ne  wadan da  aka  baiwa  ilimi  gabaninsa  idan ana  karatun sa  akan  su   suna   faduwa   ga habobin  su  suna masu sujada )
(Kuma suna cewa tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu lallae ne wa'adin Ubangijin mu ya kasance hakika abin aikatawa , kuma suna faduwa ga habobin su  suna  kuka  kuma  yana  kara  musu  tsoro  )
(ka yi sujada kuma ka kusanto ) kuma duk lokacin da ka tuna jinkirin ayukan ka kuma ka ji zafin zunuban ka da gafalar ka  ka rinka kwankwasa kofar tuba da neman gafarar ka  to Allah  madaukaki yana cewa  yana mai siffanta Annabin sa Dauda  Amincin Allah ya tabbata a gare shi
(Dauda ya tabbatar da cewa mun fitine shi ne, sabo da haka,  ya nemi Ubangijin sa gafara  kuma ya fadi yana mai sujada  kuma ya mayar da al'amari ga Allah , sabo da haka muka gafarta masa wancan .  Kuma lallai yana da wata  kusantar daraja a wurin mu da kyawun makoma )
(ka yi sujada kuma ka kusanto ) Idan bakin ciki ya tananta a gare ka , matsaltsalu sun kyawaye ka   ga fitintinu sun dame ka , to lalle sujada  yayewa ne ga dukkan wani bakin ciki   duk wanda zuciyar sa  ya kuntata   mutane suka bata mishi rai to, ya yawaita salla da sujada da adu'a   Allah madaukakin sarki ya ce :- ( Hakika mun sani cewa  zuciyan ka na kuntata   sakamakon abinda suke  fadi to ka yi  tasbihi da godiy a ga Ubangijin ka  ka kasance cikin masu sujada  )
 Sujada na kashe fushin Uabangiji mai rahama kuma  yana  haifar da yardan sa  tsarki ya tabbata ga Allah  madaukaki :- Ya zo a sahihi ingantacce  na Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi (kan cewa idan mutane sun tsaya a farfajiyan ranar alkiyama  aka tafi neman  ceto   wurin Annabawa, har suka kai ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,sai suka ce ya Muhammad ba ka ga halin da muke ciki ba? Ba ka ga musibar da ta same mu ba? Sai yace "Da ma neman ceton tawa ce" sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tafi ya yi sujada a karkashin Al'arshi, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yace : sai na nemi izinin Ubangiji na sai ya ban izini,shi na gode mi shi,da wasu yabo da ba zan iya su yanzu ba, wanda Allah zai min ilhamar su, sai na fadi ina mai sujada sai a ce ya Muhammad daga kanka, ka fada za a saurare ka, ka roka zaa baka, ka nemi ceto za a baka.) Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Sai Allah ya sanya sujada a matsayin ceto kuma tsani don fita daga azabar matattarar kiyama.
A duk lokacin da ka samu wasu alheri da kyauta mai yawa daga Mai rahama to ka fadi ka yi sujada ga  Allah    don godiya  bisa ni'imarsa.
An karbo daga Abu bakrata yace a duk lokacin wani abu na farin ciki ya samu Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai ya fadi ya yi sujada ga Allah)Su biyar suka rawaito banda Nasa'i
An karbo daga Abdurrahman Bin Auf  Allah ya kara yarda a gare shi ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya yi sujada sai ya tsawaita sujadan sannan sai ya daga kansa sai ya ce " Lalle Jibrilu ne ya zo ya mini albishir sai na yi sujada don godiya ga Allah" Ahmad ne ya rawaito Hakim kuma ya inganta shi.

Huduba ta biyu
Bayan haka!
Mamakin da kyaun sauyawan mutumin da zai kwankwadi dadin sujada a dararrakin ramadana da falalarsa,Allah Madaukakin sarkin yace :(Daga wani sashe na dare ka yi masa sujada kuma ka masa tasbihi dare mai tsawo,)   
Allah Madaukakin sarkin yace :(Da wadanda suke kwana suna sujada da tsayuwan dare) Allah Madaukakin sarkin yace (Shin wanda yake mai tawaliu tsawon dare  yana mai sujada ku yana mai tsayuwa ga sallah yana tsoron lahira kuma yana fatan rahamar Ubangijinsa(yana daidai da waninsa?)
Ya kai mai tsere zuwa ga aikin alheri a ramadan, ka yi gaggawa  a tafiyarka zuwa ga ubangijinka.
Hasara dukkan hasara shine a haramtawa bawa ni'imar sujada gaba ga Ubangiji.
Idan dan'adam ya karanta sajada sai yayi sujada sai shaidan, sai shaidan  ya kebe yana kuka yana cewa : ya bonenSa- A riwayar Abu kuraib "ya bone na"
An umarci dan Adam da sujada sai yayi to yana da Aljanna.
An umarce ni da sujada sai na ki to gashi zan shiga wanda) Muslim ne ya rawaito
Duk wanda ya yi girman kai bai yiwa Ubangiji sujada  ba a duniya ba, to ba  zai   iya yin haka a lahira ba in an kiraye shi da haka.
An karbo daga Ada'u dan yasar daga Abu Said Allah ya kara yarda a gare shi yace  :Na ji  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:UbangijinMu zai yaye kwabrinsa sai dukkan wani Mumini da mumina, su yi sujada  sai yasaura kawai wanda ya kasance mai yin sujada don riya da neman a ji. Sai ya je don yayi sujada sai bayansa ya zamza  shinfida guda).Bukhari ne ya rawaito