السبت، 27 يوليو 2019

Alhurmar Aikin Haji


Hudubar Masallacin Annabi na shaikh Abdullahi dan Abdurrahman Albuaijan 23/11/1440AH
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya tattaro zuwa gare shi wanda ya nemi mafaka, Ya tanadi Aljannar ma'awa ga wanda ya nufe shi.
Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, ya daidaita bisa al'arshi, kuma ya yi hukunci,lalle kowani mutum da abin da ya nufa, na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne,bai bata ba kuma bai kauce hanya ba, kuma bai furuci bisa son rai face wahayi da ake yi masa, ya isar da sako ya bada amana ya yi wa Al'uma nasiha kuma ya yi umarni da takawa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa, da wanda ya bi su da kyautatawa ya hana rai ga soye soye rai,
 Bayan haka lalle mafi alherin zance shine maganar Allah,wanda aka saukar, kuma maga mafi gaskiya ita ce :
Ku saurara dukkan kome abin da ya ke ba Allah ba bata ne, kuma mafi alherin shiriya shi ne shiryarwar Annabi Muhammad dan Abdullah abin fifitawa, kuma mafi sharrin zance shi ne fararrun  mai kirkirare da ya zama bidiah, ko jahili mai wauta mai batarwa,ya ku bayin Allah, ina muku wasiyya da ni kai na da ku ji tsoron Allah don ita ce wasiyar Allah ga mutanen farko da na karshe, ( Hakika mun yi wasiya ga wadanda aka bawa littafi gabanninku da ku kan ku da ku ji tsoron Allah)
 Ya ku musulmai! Lalle Allah na halittan abin da ya so ya kuma yi zabi, hakika ya zaba cikin mala'iku manzanni da kuma cikin mutane.
Ya fifita ramadan bisa sauran watanni na lokaci, ya zabi Daki mai alfarma ya sanya shi dakin farko da aka sanya wa mutane,ya fifita shi ya sanya shi mazauni ya sanya shi gun samun lada da aminci ga mutane,da aminci ya albarkace shi ya sanya shi Alkibla,ya tattale shi ya ba shi alhurma,ya girmama shi ya sanya shi wurin ibada na tushe, (Allah ya sanya kaba daki tsararre ma'aunin Addini ga mutane)
Ya sanya Alhurma ga shingensa, ya sanya shi daki dadadde ya kira zuwa ga a nufe shi,Ibrahim ya ce : (ka  shelanta ga mutane a hajji za su zo ma a tafe da akan abin hawa zasu zo daga kowane sako)
             Ya ku musulmai! Ku amsa kiran Allah " mun amsa kiranka ya Allah kuma mun amsa kiranka ya Allah! Mun amsa kiranka ba ka da abokin tarayya ya Allah mun amsa kiranka! Lalle dukkan godiya da ni'ima naka ne kuma mulki ma naka ne baka da abokin tarayya.
Ya ku bayin Allah! Lalle musulunci Akida ne da Ibadoji da dabiu da halayya an gina shi akan abubuwa guda biyar, ; rukunnai wadanda sune tushe :Ta An karbo daga Ibnu Umar Allah ya kara yarda a gare shi da mahaifinsa ya ce :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : "An gina musulunci a kan abubuwa guda biyar; Akan su kadaita Allah da tsaida sallah da bada zakka da Azumin watan ramadan da hajji"Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
  
 Ya ku mutane!Lalle Allah ya wajabta hajji  a gare ku, to ku yi hajji,  Allah Madaukakin sarki yace (kuma akwai hajjin Dakin domin Allah, akan mutane ga wanda ya samu ikon zuwa gare shi)
Hajji ibada ce ta rayuwa, kuma karshen al'amari da cikan rukunan musulunci, a ciki ne Allah Mabuwayi da daukaka ya saukar da
(A yau na kammala muku Addininku,kuma na cika ni'ima ta a gare ku, kuma na yard da musulunci ya zama addini a gare ku)
An karbo daga Abu Said Alkudri cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :; Allah Madaukakin sarki ya ce;Lalle bawa na na bashi lafiyan jikin shi, kuma na yalwata mishi a rayuwa, shekaru biyar bai zo gare ni to lalle hasrarre ne) Ibnu Hibban ne ya fitar da shi a sahihinsa.
   Ku sauke farillun Allah, ku nufi dakin Allah (kuma ku cika hajji da umara domin Allah!)
Ya ku bayin Allah!
Hajji rukuni ne na wajibi kuma farilla ne na dole Alkur'ani mai girma ya yi nuni ga hakan da muhimmin labari mai girma, Hajji na cikin ibadoji mafi daraja, da ayyuka mafi girma  na neman kusancin Allah, da masa biyayya, yana daga darajoji yana goge kusakurai yana kankare munanan laifuka har da manyan su.An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: Duk wanda ya yi hajji don Allah bai yi jima'i ba kuma bai yi fasikanci ba zai koma kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi) Bukhari ne ya rawaito.
 Kuma Tirmizi ya rawaito a littafinsa Assunan ya ku inganta shi daga Abdullahi dan Mas'ud Allah ya kara yarda a gare shi ya ce ;Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: ku biyar da hajji da umara domin suna gusar da talauci da zunubai kamar yadda zuga zugi ke tafiyar da dottin karfe da zinari da azurfa.Hajji mabrur bai da sakayya sai Aljanna)
Ya zo cikin sahihu Muslim daga Abu Huraira an tambayi Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ko wani aiki ne ya fi falala? Sai ya ce :Imani da Allah:aka ce sa'anan sai me? Sai yace : jahadi a tafarkin Allah sai aka ce sai me? Sai ya ce : Hajji Mabruri)

Ya ku jama'ar musulmai!
Lalle Allah mai tsarki ne bai karba sai mai tsarki, to duk wanda ya nufi aikin hajji to ya kame daga Haram, to ya zabo daga dukiyarsa halal, An karbo daga Abu Huraira yace Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :( Lalle Allah Mai tsarki ne bai karba sai mai tsarki, lalle Allah ya umarci muminai da abin da ya umarci Manzannai sai ya ce (ya ku Manzannai ku ci daga tsarki kuma ku yi aiki na kwarai lalle ni masani ne ga abin da ku ke aikatawa) kuma ya ce: ( ya ku wadanda suka yi imani ku ci daga mai tsarkin abin da muka azurta ku) . sai ya ambaci wani mutum yana tsawaita tafiya mai gashi a tsatsaye da kura yana daga hannayen shi sama yna cewa : Ya Ubangiji na ya Ubangiji na a halin abincinsa na haramun ne, abin shansa na haramun ne, kuma tufafinsa na haramun ne kuma an ciyar da shi abin kalace na haramun.
Allah ya sanya ni da ku cikin wadanda suke jin magana su bi mafi kyansa, wadannan su  Allah ya shiryar wadannan su ne ma'abota hankula.
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah da ya bada kuma ya ni'imta, ya kuma shiryar zuwa ga shiriya kuma ya yi ilhama, ya bayyana daidai ya kuma fahimtar,ya sanya hajji mafi darajan aiki kuma mafi girma,
 Ya ku musulmai!
Lalle kuna wata mai alfarma da Allah ya shar'anta alfarmanta ya girmama shaninta ya yi gargadi game da zalunci a cikinta sai ya ce:( Lalle kidayan watanni a gurin Allah guda shabiyu ne a littafin Allah a ranar da ya halicci sammai da kasa, daga cikinsu akrajab da muwai guda hudu nasu alfarma) uku daga cikin su a jere suke Zulka'ada da zulhajji da Muharram da rajab,na mudar. Sannan ya ce wannan wani wata muke ciki sai muka ce Allah da ManzonSa ne suka fi sani sai ya yi
Shuru har sai da muka tsammaci zai ambace shi da wani sunan ne, sai yace ase ba zulhajji ba ne sai mka ce : E sai yace wani gari ne wannan sai muka ce Allah da ManzonSa ne suka fi sani sai ya yi shuru har muka zaci zai ambace shi da wani suna da ba shi ba sai yace Ase ba wannan bane gari mai alhurma? Sai suka ce e shine.sai yace to a wace rana muke?sai suka ce Allah da Manzonsa ne suka fi sani. sai ya yi
Shuru har sai da muka tsammaci zai ambace shi da wani sunan ne, sai yace ase ba a ranar suka muke ba? Sai suka ce: E   haka ne sai ya ce : To lallai jininku da dukiyanku da mutunci a gare ku haramun ne, kamar alhurma wannan ranar taku a wannan gari naku a wannan wata taku., za ku hadu da Ubangijinku zai tambaye ku game da Ayyukanku, ku saurara : kada ku koma a baya na kafurai sashinku na dukan wuyan sashi, to ku saurara wanda ya ke nan ya sanar da wanda bai nan, don ta iya yiwuwa wanda za a isar zuwa gare shi ya kiyaye fiye da wanda ya jiyo.ku saurara! Shin ko na isar da sako, shin ko na isar da sako) Bukhari da muslim ne suka rawaito.
Lalle watan zulkida shine watan farko cikin watanni masu alfarma da suke hade, a cikinsa ne Annabi ya kasance ya yayin da mushrikai suka hana shi shiga,da umaran da ya yi a shekaran da ta kewayo a zulkida ne ya yi ta a lokacin da ya yi sulhu da su, azulkada a yayin da ya yi sulhu da su, da umarar ji'irrana wanda ya raba ganimar hunain,da umara da ya yi da hajjinsa.  Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Ya ku bayin Allah !
lokaci na hajji lokaci ne na biyayya da da'a da kyauta, kuma karama ce  samun kyautar,
ya kasance a jahiliyya abin alfahari ne shayarwa ga Alhazai da suturce kaba da bata kulawa.suna munafasa a cikinta, da musulunci ya zo sai ya tabbatar da haka, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shiya yiwa Abbas izini da ya kwana a makka a dararrakin kwanan mina don shi,ya zo gurin da ake shayarwa  da ya nemi da a shayar da shi kuma ya sha ya tafi ta gun masu zamzam a halin suna shayarwa suna aiki sai yace (ku yi aiki lallai kuna kan aiki na kwarai,)  yace (Ba don kar a yi galaba a kanku ba da na sauka har na sa igiya a nan fa ya yi nuni ga kafadansa) Bukhari ne ya rawaito.
Allah ya yi gyadan dogo ga kasar Saudiya cikin hidima da ta ke yi na wurare masu tsarki, da amintar da shi ga masu dawafi da masu itikafi da masu rukui da sujada, ya mata baiwa na hidima da karbar bakuncin Alhazai da 'yan umara da masu ziyara ko shige da fice, tare da tausaya musu da gabatar da hidima da ta dace a gare su, da agaza musu wurin sake nauyin ibadojinsu,da shinfida musu dukan wata hanya ta aminci da zaman lafiya gare su, to Allah ya saka wa jagororinmu da shugabanninmu da sakayya mafi  alheri da cika da kamala da kyau da tsarki, bisa abin da suke tashi da shi na hidima ga masallatayya biyu masu alfarma da daukaka da masu tahowa gare su.
Ya ku bayin Allah! Ku kuna guri ne da ya fi soyuwa a gurin Allah, to ku bada hadin kai wurin ganin ku taimakawa ma'aikata masu tsare tsare da hidima, Allah ya karba mana ni da ku, ya mana gamon katar.
Alhazai ga daki mai alfarma,…
Hakika kun yi kokari kun yi dace na amsa kiran Allah na haji wajibi, to ku dage wurin yinta da cikata bisa yadda zaa karbe ta, ku nemi sanin hukunce – hukuncenta, na gargade ku da ku nesaci jima'I da fasikanci da jayayya (Haji watanni ne sanannu to duk wanda ya shiga aikin haji cikinsu babu batsa ko fasikanci ba musu a hajji)
   Ku sa nitsuwa da tsanaki, ku yi aikin jinkai idan an samu cunkoso, ku yi nesa da turereniya, ku tausayawa masu rauninku,domin a dalilinsu ne ake azurta ku a baku nasara.
 An karbo daga jabir yace Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya goyi Usama abayansa ya taso daga Arfa yana matse linzami dabbarsa Alkaswa kanta na taba tankin dabbar ya na nuni da hanunsa na dama da (ya ku mutane Natsuwa natsuwa) a duk lokacin da ya zo wani dutse daga cikin duwatsu sai ya dan saki linzami gareta har ta haura har ya iso muzdalifa) .Muslim ne ya rawaito


ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق