الجمعة، 21 يونيو 2019

kofofin tuba


Hudubar Masllacin Annabi na 11-10 -1440AH/14-6-2019 AD na Sheikh Abdullah bin Abdurrahman Albu'aijan.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna gode masa muna neman taimakonsa muna neman gafararsa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi duk wanda ya batar da shi ba zaka sama mishi majibinci mai shiryarwa ba.
Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, ya halitta kuma ya daidaita abin halitta ya kaddara (abin da ya so) ya shiryar, na shaida Annabi Muhammad bawansa ne kuma manzon sa ne, wanda ya turo shi da gaskiya da shiriya, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbansa da duk wanda ya bi sawun shi,ya bi tafarkinsa da kyautatawa har zuwa ranar sakayya,
Bayan haka: Lallai mafi alherin zance shi ne littafin Allah, kuma mafi alherin shiryarwa shine shiryarwa Muhammad dan Abdullah, Mafi sharrin al'amura sune fararrunta, dukkan fararrun abubuwa bidiah ne, dukkan bidiah bata ne dukkan bata na wuta.
Ya ku bayin Allah … ku ji tsoron Allah cikin abin da ya umarta, ku hanu daga abin da ya hana ya tsawatar, ku sani dukkan karami da babba ana rubuta shi, (ya ku wadanda suka yi mani ku bi Allah da takawa, kuma rai ya dubi abin da ya gabatar domin gobe, kuma ku bi Allah da takawa lalle Allah mai kididdigewa ne ga abin da ku ke aikatawa,)
Ya ku bayin bayin Allah!
Lokaci na albarka da falala da alheri da da'a ranakunsa ya kare an nade ayyukansa, lalle wata ne mai girman falala, tasirin sa a cikin Al'uma na da ban mamaki, masu nasara cikin shi sun ribata,masu kokari cikinsa sun samu ganima,ina ma da mun san wanda aka karbi ayyukansa mu mishi barka! Wane ne baa karba mishi ba mu jajanta mishi,
Madalla da farincikin wanda suka rabauta, Allah ya musu ilhamar tuba, ya datar da su ga biyayya, muna roka musu Allah da ya karba musu ya dora su kan daidai.
Ya  kaiton hasarar wadanda suka rasa wannan alheri aka katange  su daga Ubangijin su, damammaki a rayuwa suka kwace musu.ga lokutan alheri basu ribaci komai ba sai hasara da nadama,
Sai dai ya jama'ar musulmi ! kofofin tuba basu gushe ba suna bude ba a rufe su ba bayan watan ramadan,Ubangijinmu mabuwayi da daukaka yana karbar tuba daga bayin sa a kowane zamani da guri  (Shi ne yake karbar tuba daga bayin sa kuma yana yafe munana, kuma ya san abin da kuke aikatawa).
     Ya tabbata daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :Lalle Allah ya fi farinciki   da tuban bawansa mumini  akan mutumin da  yake cikin kasa ta sahara wacce  ke da ababan halakarwa   yana tare da dabbarsa  abin cin shi da abin shan sa na kanta   sai ya yi bacci , da ya farka sai ya ga ta tafi  ya yi ta nemanta  har sai da  kishi ya cimmasa  sai ya ce bari na koma wurina da na kasance a cikin shi  sai na je na yi bacci har ma na mutu  sai ya dora kanshi  a bisa damtsen shi don ya mutu yana halin haka  sai ga dabbarsa a kan sa  tare da ita ga guzurin shi da abin cin shi  da abin shan sa  sai  ya rike linzamin ta yayi kuskure don tsananin farin ciki yana mai cewa ya Allah kai ne bawana ni ne Ubangijin ka  .
An karbo daga Abu Huraira  Allah ya kara yarda a gare shi ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce:(Idan wani yanki na dare ya shude ko kuma wani sulusin  shi , Ubangijin mu mai tsarki da daukaka zai sauko  zuwa ga  sama na  duniya  sai ya ce:-
Ko shin akwai mai tambaya na ba shi , ko shin akwai mai roko na amsa mishi , shin akwai mai neman gafara a gafarta masa har gari ya waye  . Muslim ne ya rawaito)
Zuwa ga wanda daman ramadan ya kwace mishi  to ka yi gaggawa zuwa ga tuba  kafin lokaci ya tsere   da kuma shammatan ajali kada ka yanke tsammani don duk dan adam mai kuskure ne  abin zargi  na ga wanda ya doge  kuma alhali yana da Ubangiji mai gafarta zunubai kuma bai nemi gafarar sa ba , ba don kun kasance kuna kusakurai ba kuma kuna neman gafara da  Allah ya tafiyar da ku ya kawo wasu mutane wadan da suna kuskure kuma suna neman gafara sai Allah ya gafarta musu .
YA KU BAYIN ALLAH:
Ku ji tsoron Allah kuma ku nemi gafarar sa  kuma ku koma zuwa gare shi ku mar da'a  kada ku jinkirta tuba domin  mutuwa na zuwa bagtatan  .
Allah madaukakin sarki ya ce :-(Ku tuba suwa ga Allah gaba dayanku ya ku muminai  ko za ku  rabauta)
Kuma ya ce :-( Ka ce  ya ku bayi na wadanda suka   barnatawa kawunan su  kada ku yanke tsammani daga rahamar Allah lallai Allah yana gafarta zunubai baki daya  lallai shi mai gafara ne kuma mai jin kai .  Ku koma zuwa  ga Ubangijinku  ku mika wuya gare shi  kafin azaba ya zo muku  sa'annan ba za a taimaka muku ba , ku bi mafi kyaun  abin da aka saukar gare ku daga Ubangijin ku  tun kafin azaba ya zo muku  bagtatan a halin kuna baku sani ba  kada rayi ta ce  ya hasara ta  bisa  abin da na yi sakaci a janibin Allah  , ko da na kasance cikin  wadan da suke masu isgili  ko kuma ta ce ina ma da Allah ya shirye ni  da na  kasance cikin masu takawa  , ko kuma ta ce ya yin da ta ga azaba  ina ma da ina da kome da na kasance cikin masu kyautatawa 

YA KU MUSULMAI:
Lallai ibada na da tasiri  cikin halayen ma'abocinta Allah madaukakin sarkiya ce :-(Lallai sallah na hani ga alfasha  da munkari)
Na daga cikin alamomin karban ayyuka  akwai canzawan halayen zuwa mafi kyan hali  a daya bangaren kuma  yana daga cikin alamomi na  rasa alheri da rashin karban aiki  akwai komawa baya  daga da'a  bayan shudewan ramadana  yanayin halaye ya canza zuwa mafi muni  domin sabo sashi na janyo sashi , madalla da kakkyawa bayan mummuna  sai ta goge ta  mafi kyaunta kuma shi ne kyakkyawa bayan kyakkyawa  tana mai binta , ku roki Allah tabbatuwa akan da'a har zuwa mutuwa  kuma ku nemi tsarin Allah  daga juyawar zukata  haka nan kuma daga warwarewa bayan daurewa .

 Abin mamaki da munin  kaskanci  na sabo  bayan izza ta da'a  tir da  talauci na  kwadayi bayan wadatuwa da wadatan zuci  ku roki Allah tabbatuwa , ya tabbata daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :-( Lallai dayanku  zai yi aiki irin na 'yan aljanna  har sai ya kasance tsakanin shi da ita  face zira'I  sai littafin sa ya rigaya  , sai ya yi aiki irin na 'yan wuta sai ya shige ta ,  kuma lallai dayan ku zai yi aiki irin na 'yan wuta   har sai ya kasance tsakanin shi da ita face zira'I sai littafin shi ya rigaya sai ya shigeta  Buhari ne ya rawaito)
Ina fadin abin da kuke ji ……….

HADUBA TA BIYU

Dukkan yabo da godiya sun tabbata  ga Allah wanda  yake karban tuba daga bayin sa  kuma yake yafe kusakurai kuma ya san abin da kuke aikatawa ,  kuma yana amsa kiran wadan da suka yi imani kuma  suka yi aiki na kwarai   kuma yana kara musu daga falalar sa .
 YA KU MUSULMAI :
Watanni dukan su lokuta ne na ibada  ko da sun sha banban  sun saba a wurin fifiko  da ayyuka  rayuwa dukkanta   dama ce ta aiki  da biyayya   ko wanne yana wayan gari yana mai saida kan sa akwai mai 'yantata akwai kuma mai halakata ,  kuma kowa ana yassare mi shi abin da aka halicce shi  akanta   , .
To ku sabarwa kawunan da da'a ku nemi taimako game da ita da tuba  da neman gafara  da komawa zuwa gare shi da marairaicewa  da kuma murakaban Allah  guda mai rinjayi  a sirri kuma da bayyane a dare da wuni .
 (Ku bar  sabo na zahiri da na badinin  sa  lallai wadanda suke aikata laifi za a sakanya musu da abinda suka kasance suna aikatawa)
YA KU BAYIN ALLAH:
Ku rantawa Allah rance kyakkyawa , ku kaddamarwa kawunan ku abu mai amfani , (Duk wani abu da za ku kaddamar wa kawunan ku na alheri za ku same shi a wurin Allah).
(Wane ne zai rantawa Allah rance mai kyau sai ya ribanya mishi ribanyawa mai yawa).
Sannan ku sani cewa azumi garkuwa ne , dukkan aikin dan adam  na shi ne  sai azumi to shi na Allah ne zai sakanya game da shi , to duk wanda zai iya  a cikin ku ya azumci azumi shida a shauwal  to lallai hakan na daga cikin sunna  kuma aiki ne na musdafa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
An karbo dga Abu ayubal Ansari Allah ya kara yarda a gare shi ya ce  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbataa agare shi ya ce :-(Duk wanda ya yi azumin ramadana  sannan ya bi da guda shida  a shauwal  zai kasance kamar ya yi azumi na shekara ne )Muslim ne ya rawaito
Sabo da kyakkyawa guda na da lada goma kamarta,to ramadana na da ladan wata goma, guda shidan kuma ladan wata biyu, kuma adadin watanni a gurin Allah goma sha biyu ne,
Ba laifi mutum ya yi azumin a jere ko a rarrabe, muddin dai a cikin watan shauwal ne, tamkar tana matsayin sunnoni ne na ratibi game da sallolin farilla,tana cike gurbin tawaya ne da aka samu a farilla.

        YA KU MUSULMAI :
Ku ji tsoron Allah,iya iyawanku,ku yi riko da addininku,ku kankame sunnar Annabinku, ku kuma gyara tsakaninku,ku kiyaye hadin kanku, da garinku, ku zama hanu guda kan abokin gabanku, ku roki Allah da ya tabbatar da ku ya datar da ku,
Bayan haka YA KU MUSULMAI :
Lallai abin da masu ketare iyaka suka suka aikata na harbi kan 'yan kasa da mazauna, da tsorata amintattu, da zubar da jinin wanda bai ci ba bai sha ba.da yara da mata, da keta alfarman wurare masu tsarki manya da gari mai alfarma, na daga cikin manyan laifuka abin ki ga dukkan addinai, kuma yana cin karo da ginshikai na musulunci, Alla maida musu sharrinsu a kan su.ya sanya yakinsu a tsakaninsu, kuma ya yanke karshensu.
Ya Allah ka kare wannan kasa da kariyarka.

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق