الجمعة، 17 مايو 2019

ka yi sujada ka kusanto


Hudubar Masllacin Annabi na sheikh Abdulbari Bin Awad Assubaiti 12 Ramadan 1440Ah
Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga  mafificin halittun Allah,
Bayan haka !
A kalmomi biyu na karshen farkon sura da aka saukar a Alkur'ani Allah yana cewa:(Kuma ka yi kujada ka kusanto ) an karbo daga  Abu Huraira  Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :-( lokacin da bawa ya fi kusanci da Ubangijin shi shi ne a halin yana sujjada , to ku yawaita adu'a ) Muslim ne ya rawaito
Sujada shi ne mafi daukakan hali na bawa , a cikin shi ne mutum zai ji dadin rusunawa mabuwayi mai girma  da kuma  kawa irin na kankan da kai ga mai rahama mai jin kai , wasu lokuta ne na karamci da albarka  wanda ba su da iyaka .
 Acikin sujada ne a ke jin dadin da baya misaltuwa   da yaye walwalan zuciya  wanda ba alkalamin da zai iya iyakance shi  yana  kaurar da musulmi daga kunci ,  zuwa ga yalwa mai fadi  na kasa  cikin sararin samaniya  sabo da haka ne  (Aisha Allah ya kara yarda a gare ta  ta sifanta tsayuwan daren Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da cewa; yana sujjada  guda da zai kai dayan ku ya karanta aya hamsin  kafin ya dago)  Buhari ne ya rawaito .
Sujada na kara wani haske na imani   daga ma'abocin shi ya jefa wani walwala a zuciya da natsuwa  ya bashi wani  gairmamawa , Allah madaukakin sarki ya ce :-(Muhammadu Manzon Allah ne , kuma  wadan da suke tare da shi  suna masu  tsanani ga kafurai  masu tausayi a junan su  za ka gansu suna masu yawan ruku'u da sujada  suna neman falala daga wurin Allah  da yarda  alamun su  na fiskan su na gurbin sujada )
Asujada ne Ubangiji ke kasancewa kusa da wanda ya roke shi  , Ubangiji mai tsarki    yana kusa da wanda ya roke shi  , mai amsawa ne ga wanda ya nemi ganawa da shi   mai badawa ne ga wanda yayi fata gare shi  duk wanda ya kusanci Allah to lallai zai riski kyauta mafi yalwa daga Ubangijin shi, kuma ya samu matsayi mafi
aminci da yakini da kariya mai karfi  ,  Allah madaukakin sarki ya ce (To amma (  idan mai mutuwan ya kasance daga makusanta   sai hutawa  da kyakkyawan abinci da aljanna mai ni'ima )
Makusantan suna da Rauhun shi ne;  hutu  da natsuwa da farin ciki  da kuma annashawa , Raihan   shi ne suna da ya tattaro dukkan  wani jin dadi na  jiki  na daga abinci ne ko abin sha  da makamantan su ,  da  (aljanna mai ni'ima) wanda a cikin ta akwai abinda ido bai gani ba kuma kunne bai ji ba kuma bai halarto a tunanin wani dan adam  ba yana yiwa makusantan shi albishir yayin  halartowan mutuwan su da wannan albishir din  wanda  rayuka ke kusa da su fire sabo da tsabar jin dadi da farin jiki , (ka yi sujada kuma ka kusanto )      
A ko wani sujada kana da daukaka na daraja   da kusanci na matsayi  da kuma kusanci na wuri  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :- (Ba wani bawa da zai yi sujada  don Allah face an rubuta mishi kyakkyawa da ita , an kankare mishi mummuna da ita  an kuma daga darajar ku da  ita  , to ku yawaita yin sujada ) Ibn Maja ne ya rawaito da isnadi ingantacce
To kyautan Allah bai  karewa duk wanda ya kusance shi sai ya saukar da shi bisa falalan sa daraja irin na Annabawa  da siddikai da shahidai  da salihai , Manzon Allah tsira  da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da Rabi'ata Dan Ka'ab Al-Aslami a lokacin da ya nemi kusanci da Manzon Allah a aljanna  sai  ya ce da shi:-(  ka taimaka mini akan kanka da yawan sujada)   Muslim ne ya rawaito

     (ka yi sujada kuma ka kusanto ) a cikin sujada ne alamomi na gaskatawa da imani ke bayyana alamomin yakini da mika wuya ke fitowa fili , an karbo daga Aliyu dan Abi Dalib  Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :-  ya kasancen  daga  cikin adu'o'in manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a sujadan sa  Allahumma laka sajadtu , Aya Allah don kai na yi sujada , wabika amantu , da kai ne kuma na yi imani  wa laka aslamtu, kuma da kai na mika wuya  ,  fiska ta ta yi sujada ga wanda ya halicce ta ya sauwara ta  ya tsagi jinta da ganin ta  tsarki ya tabbata ga Allah mafi kyaun masu halitta )Muslim ne ya rawaito
(ka yi sujada kuma ka kusanto ) lalle sujada na    cikin ibada  wanda dukkan halitu suka yi tarayya suka tattaru a kanta (Kuma ga Allah abinda yake cikin sammai da kasa na dabba da mala'iku suke yin sujada , kuma basu kangara .  Suna tsoron Ubangijin su daga bisan su  kuma  suna aikata abinda ake umarnin su )
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce ni ina ganin abinda bakwa gani kuma ina jin abinda bakwa ji , sama ta yi  kara kuma ta cancanci ta yi karan sabo da  babu wani bigirea na yatsu fa ce mala'ika yana daure da fiffigen shi yana mai sujada ga Allah , wallahi da kunsan  abinda na sani da kunyi dariya dan kadan kunyi kuka mai yawa . Da ba ku ji dadi da mata ba akan shimfidi  da kun fita kwararo –kwararo  kun yi kururuwa  kuna kara  zuwa ga Allah ) Nasa'I da Ibn Maja ne suka rawaito  da Ahmada.
1.   (ka yi sujada kuma ka kusanto ) ka yi sujada kana mai rokon Ubangijin ka kana mai kiran mahaliccin ka  , kana mai kankan da kai zuwa ga masoyin ka , kai din nan kana aljanna ne daga cikin aljannoni na duniya , ka yi sujada sujudan mai tsoron Allah   a duk lokacin da ka ji ayoyin alkur'ani , bayanansa suka ratsa ma zuciya.

 Allah madaukakin sarki yana cewa (Kuma yana abun karatu  mun rarraba shi domin ka karanta shi ga mutane akan jinkiri,  kuma mun sasaukar da shi sassaukarwa  ka ce ku yi imani da shi ko kuwa  kada  ku yi imani ,   lalle ne  wadan da  aka  baiwa  ilimi  gabaninsa  idan ana  karatun sa  akan  su   suna   faduwa   ga habobin  su  suna masu sujada )
(Kuma suna cewa tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu lallae ne wa'adin Ubangijin mu ya kasance hakika abin aikatawa , kuma suna faduwa ga habobin su  suna  kuka  kuma  yana  kara  musu  tsoro  )
(ka yi sujada kuma ka kusanto ) kuma duk lokacin da ka tuna jinkirin ayukan ka kuma ka ji zafin zunuban ka da gafalar ka  ka rinka kwankwasa kofar tuba da neman gafarar ka  to Allah  madaukaki yana cewa  yana mai siffanta Annabin sa Dauda  Amincin Allah ya tabbata a gare shi
(Dauda ya tabbatar da cewa mun fitine shi ne, sabo da haka,  ya nemi Ubangijin sa gafara  kuma ya fadi yana mai sujada  kuma ya mayar da al'amari ga Allah , sabo da haka muka gafarta masa wancan .  Kuma lallai yana da wata  kusantar daraja a wurin mu da kyawun makoma )
(ka yi sujada kuma ka kusanto ) Idan bakin ciki ya tananta a gare ka , matsaltsalu sun kyawaye ka   ga fitintinu sun dame ka , to lalle sujada  yayewa ne ga dukkan wani bakin ciki   duk wanda zuciyar sa  ya kuntata   mutane suka bata mishi rai to, ya yawaita salla da sujada da adu'a   Allah madaukakin sarki ya ce :- ( Hakika mun sani cewa  zuciyan ka na kuntata   sakamakon abinda suke  fadi to ka yi  tasbihi da godiy a ga Ubangijin ka  ka kasance cikin masu sujada  )
 Sujada na kashe fushin Uabangiji mai rahama kuma  yana  haifar da yardan sa  tsarki ya tabbata ga Allah  madaukaki :- Ya zo a sahihi ingantacce  na Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi (kan cewa idan mutane sun tsaya a farfajiyan ranar alkiyama  aka tafi neman  ceto   wurin Annabawa, har suka kai ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,sai suka ce ya Muhammad ba ka ga halin da muke ciki ba? Ba ka ga musibar da ta same mu ba? Sai yace "Da ma neman ceton tawa ce" sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tafi ya yi sujada a karkashin Al'arshi, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yace : sai na nemi izinin Ubangiji na sai ya ban izini,shi na gode mi shi,da wasu yabo da ba zan iya su yanzu ba, wanda Allah zai min ilhamar su, sai na fadi ina mai sujada sai a ce ya Muhammad daga kanka, ka fada za a saurare ka, ka roka zaa baka, ka nemi ceto za a baka.) Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Sai Allah ya sanya sujada a matsayin ceto kuma tsani don fita daga azabar matattarar kiyama.
A duk lokacin da ka samu wasu alheri da kyauta mai yawa daga Mai rahama to ka fadi ka yi sujada ga  Allah    don godiya  bisa ni'imarsa.
An karbo daga Abu bakrata yace a duk lokacin wani abu na farin ciki ya samu Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai ya fadi ya yi sujada ga Allah)Su biyar suka rawaito banda Nasa'i
An karbo daga Abdurrahman Bin Auf  Allah ya kara yarda a gare shi ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya yi sujada sai ya tsawaita sujadan sannan sai ya daga kansa sai ya ce " Lalle Jibrilu ne ya zo ya mini albishir sai na yi sujada don godiya ga Allah" Ahmad ne ya rawaito Hakim kuma ya inganta shi.

Huduba ta biyu
Bayan haka!
Mamakin da kyaun sauyawan mutumin da zai kwankwadi dadin sujada a dararrakin ramadana da falalarsa,Allah Madaukakin sarkin yace :(Daga wani sashe na dare ka yi masa sujada kuma ka masa tasbihi dare mai tsawo,)   
Allah Madaukakin sarkin yace :(Da wadanda suke kwana suna sujada da tsayuwan dare) Allah Madaukakin sarkin yace (Shin wanda yake mai tawaliu tsawon dare  yana mai sujada ku yana mai tsayuwa ga sallah yana tsoron lahira kuma yana fatan rahamar Ubangijinsa(yana daidai da waninsa?)
Ya kai mai tsere zuwa ga aikin alheri a ramadan, ka yi gaggawa  a tafiyarka zuwa ga ubangijinka.
Hasara dukkan hasara shine a haramtawa bawa ni'imar sujada gaba ga Ubangiji.
Idan dan'adam ya karanta sajada sai yayi sujada sai shaidan, sai shaidan  ya kebe yana kuka yana cewa : ya bonenSa- A riwayar Abu kuraib "ya bone na"
An umarci dan Adam da sujada sai yayi to yana da Aljanna.
An umarce ni da sujada sai na ki to gashi zan shiga wanda) Muslim ne ya rawaito
Duk wanda ya yi girman kai bai yiwa Ubangiji sujada  ba a duniya ba, to ba  zai   iya yin haka a lahira ba in an kiraye shi da haka.
An karbo daga Ada'u dan yasar daga Abu Said Allah ya kara yarda a gare shi yace  :Na ji  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:UbangijinMu zai yaye kwabrinsa sai dukkan wani Mumini da mumina, su yi sujada  sai yasaura kawai wanda ya kasance mai yin sujada don riya da neman a ji. Sai ya je don yayi sujada sai bayansa ya zamza  shinfida guda).Bukhari ne ya rawaito


  



ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق