Hudubar Farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah muna gode masa kuma muna
neman taimakonsa da gafararsa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu,
da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi,
kuma duk wanda ya batar babu mai shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da
gaskiya sai Allah,shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, na kuma shaida
Annabinmu Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne, tsira da amincin Allah su
tabbata gare shi da iyalansa da sahabbansa da aminci tabbatacciya mai yawa.
Bayan haka,
ku ji tsoron Allah yadda ya dace a ji tsoron
shi, ku yi riko da igiya mai karfi na musulunci.
Ya ku Musulmai!
Ranaku da dararraki na ta
tafiya da sauri,ga shekara na kokarin nade tabarmarsa da gaggawa,.bayi na
tafiya zuwa ga Allah ! kuma su riski ayyukansa.
Na daga falalar Allah da
karamcinsa ya zaba mana wasu lokuta na da'a, ya zabi wasu ranaku da dararraki
da wasu sa'o'i, domin kwadayin rahamar Allah ya yawaita a samu karin kaimi da
masu zage damtse,da gasar masu gasa cikin ayyukan alheri, a duk lokacin da
jinjirin watar ramadana ya kada sai ya buso mana da wasu albarka masu yawa, sai
musulmai su fiskance shi da annashawa, zukatarsu su cika da farinciki sabo da
shi,ta iya yiwuwa sa'a guda da zaa riska ta daga darajan mutum ta sa Allah ya
yarda da shi ya kuma samu walwala,
Ga wata mafi daraja ta
dumfaro mu,lokaci ne mai girma da Allah ya kebance ta da daukakawa da
girmamawa, sai ya turo manzonsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,
ya sauke littafinsa a cikinta,ya wajabta azumtarta, sa'ointa na da albarka,
lokutan cikinta ana raya su da ayyukan alheri, alheri na bibiyan juna a
ciki,albarka na gamewa a ciki,lokaci ne na kyautatawa da bada sadakoki, lokaci
ne na gafara da kankare laifuka, wuninta azumi darenta kuma tsayuwan dare ana
nafila, ana raya ta da sallah da karatun Alkur'ani,Ana bude kofofin Aljanna,ana
kulle kofofin wuta,ana daure shaidanu a cikinta, a cikinta akwai dare guda da
ya fi watanni dubu, wanda ya rasa alherinta lalle ya yi hasara.
Ramadana fage ne mai fadi na
gasa cikin ayyukan da'a, kuma wani
kyauta ne na tsarkake rayuka daga kazanta da laifuka,wata ne mai girma ana
ribanya ayyukan Alheri, ana kankare kusakurai da laifuka, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi ya ce :(Salloli guda biyar da juma'a zuwa juma'a da Ramadan zuwa ramadan
kankara ne ga abin da ke tsakanin su muddin aka nesaci manyan zunubai)Muslim ne
ya rawaito
A cikin ta musulmai ke sauke
rukuni daga cikin rukunan musulunci, kuma wani abu ne na aiki bayyananne da ke
nuna girman wannan addini da hadin kan musulmai, a cikinta ne fadin Allah
Madaukakin sarki ke bayyana na cewa : (Lalle
wannan Al'umarku ce Al'uma guda Ni kuma Ubangijinku ne to ku bauta mini).
Ribatan lokutan alheri budi
ne daga Allah ga wanda ya so na daga bayinSa, a cikin Ramadan tushen ibadoji kuma mafi girma ke haduwa ga musulmai, sallah
sadarwa ne tsakanin bawa da Ubangijinsa, bata rabuwa da musulmi a dukkan
rayuwarsa,sallan mutum cikin jam'I farilla ne ta fi sallarsa a gidansa da
kasuwansa da lada ashirin da bakwai.
Ya dace ga musulmi da ya nemi
taimako da azuminsa bisa sallarsa, kuma ya zama yana kaso mafi girma na sallah
To ( wanda ya yi tsayuwan Ramadan bisa imani da
neman lada zaa gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa)Bukhari da muslim ne
ya rawaito. Duk ( wanda ya yi tsayuwan
dare tare da liman har aka tashi za a rubuta mishi cikakken tsayuwan dare )
Tirmizi ne ya rawaito.
Zakka da sadaka tsarkaka ne
da habaka ga dukiya kuma wadata ne ga
zuci da tsarkaka, tasirinta a bayyane yake ga rayi da dukiya da da, tana tunkude bala'I, tana janyo
yalwa, wanda ya yi wa bayin Allah kyauta Allah zai yi masa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
ya ce :(Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: Ya kai dan Adam ka ciyar zan ciyar da
kai)Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Dukkan mutum na karkashin
inuwar sadakarsa ranar alkiyan, to ku yi sadaka ko da da dan kadan ne, ka jiyar
wa kanka dadi, ka sadar da zumunci da shi ga wanda bai da shi, Duk wanda ya
shayar da mai azumi to yana da kwatankwacinsa na lada, kuma na daga cikin
kyautarsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi akwai ciyarwa da kuma
kyauta, yana bada kyautar mutumin da bai tsoron talauci, in ya ciyar zai bada
da yawa, in ya bada kyauta zai yawaita , ba ya maida mai tambaya. Baa tambayarsa
wani abu ba face sai ya bada,
Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance mafi kyauta a
cikin azumi to shi yafi iska mai busawa.
Azumi shi ne
alami mafi girma cikin alamomin addini
a cikin wannan wata mai falala musulmai na guzurin tsoron Allah a
cikin shi, Allah madaukakin sarki ya ce :-(Ya ku wadanda suka yi imani an wajabta muku yin azumi kamar yanda aka
wajabtawa wadanda suka gabace ku ko za ku samu tsoron Allah)
Ladan shi ba yi da kididdiga ko iyaka, Allah Madaukakin
sarki ya ce a hadisin Alkudsi: ( Dukkan aikin dan adam na shi ne sai azumi, lalle shi
nawa ne kuma ni nake sakanya wa game da shi) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Kuma ( wanda
ya yi azumin ramadana yana mai neman lada an gafarta mishi zunuban sa)
Azumi kan yi shamaki tsakanin
ma'abocin shi da sharrace-sharrace da
laifuka Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce:- ( azumi garkuwa
ce ).
Umra na daga cikin ayukan da ake riba ta a wannan
wata Manzon Allah tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi ya ce :- (yin
umra a watan Ramadan na dai-dai da Hajji )Buhari da muslim ne suka rawaito
Kuma kur'ani maganan Allah ne madaukaki kuma hujjan sa ne
kan halittun shi , kuma shi wani mabubbuga ne na hikima , kuma aya ne na sako babu hanya zuwa ga Allah sai ta hanyar
shi babu tsira gare mu ba tare da shi
ba haske ne na basira
da kuma gani wanda ya kusance shi
zai samu daukaka , wanda ya yi riko da shi kuma zai samu buwaya karanta shi lada ne da kuma shiriya , bitar
sa kuma ilimi ne da tabbatuwa akan tafarki
aiki da shi kuma wani katanga ne da kuma aminci , koyar da shi kuma da
kira zuwa gare shi kambi ne akan kawunan
masu da'a , a cikin ramadana ne kur'ani
ya sauka sabo da haka ake karfafa yawan
karanta shi a cikin sa da lura da ma'anonin shi
da koya da koyar da shi da kuma aiki da shi da riko da koyarwar sa ,
Allah mabuwayi da daukaka ya ce:- (watan ramadan wanda aka saukar da kur'rani
acikinta shiriya ne ga mutane, kuma da bayyanannu na daga shiriya da kuma
rarrabewa).
Jibrilu alaihissalatu wassalam ya kasance yana bitar alkur'a ni da Annabin
mu tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi sau daya a ko wani shekara , a shekaran da ya rasu kuma ya yi
bita da shi sau biyu amincin Allah ya tabbata a gare shi .
Adu'a ibada ce kuma kusanci ne wani garabasa ne ba tare da wahala ba , kuma riba ne da ba tsiya tare da shi kuma shi yana janyo yalwa , kuma makiyi ne ga
dukkan wani bala'i mutum ba zai taba halaka ba muddin yana tare
da adu'a da shi ne bawa zai kai ga burin shi ya kuma riski bukatar shi , sau dayawa yakan kusanto
da abin da ke nesa kuma sau dayawa yakan saukake abin da ke da tsanani , sau
dayawa yakan yaye bakin cikin abin da akwai bakin ciki a ciki, kuma mafi karbuwan adu'a shi ne wanda ya kasance a cikin yankin karshe na dare idan bawa ya marairaice gaba ga Ubangijin shi to, Allah zai amsa rokon shi , idan rayi ta ji yunwa sai zukata su yi taushi , mai azumi
ba'a maida adu'ar sa Ibn Rajab Allah ya
kara mishi rahama ya ce :-(Mai
azumi yana cikin bauta ne a daren sa da wunin sa ana kuma amsa mi shi adu'a a azumin shi ya
yin shan ruwan shi , to, a haka shi mai azumi ne kuma mai hakuri a daren shi kuma yana mai ci kuma mai godiya
) .
Wanda aka yiwa dace shi ne wanda ya yawaita
kwankwasa kofar sama ya sanyawa kanshi cikin wadannan kwanaki da
dararraki hyana mai adana .
Ambaton Allah
ibada ce mai girma kuma mai sauki wanda
ya ambaci Allah Allah zai ambace shi , bawa idan harshen shi bai shagaltu da
zikiri ba to maganganu marasa amfani za su shagaltar da shi da kuma sabonnin su .
Addini mu'amala
ne mafi dacewan halittu da kyautatawan ka shi ne wanda Allah ya hada hakkinsa da na su , to iyaye biyu aljannan ka ne kuma wutan ka
su suka fi dacewa a cikin mutane wurin kyautata mu'amala da su , Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce :- ( Hancin shi
ya dumbuli kasa , kuma hancin shi ya dumbuli kasa kuma hancinsa ya dumbuli
kasa! Sai aka ce :wanene ya Manzon Allah? Sai yace : duk wanda ya riski
iyayensa a halin girma dayansu ko dukansu biyu kuma bai shiga Aljanna ba)Muslim
ne ya rawaito. kuma (Zumunci na danfare da Al'arshi yana cewa: duk wanda ya
sada mini Allah zai sada mishi, wanda ya yanke min Allah zai yanke mishi, wanda
zai burge shi a yalwata mi shi arzikin shi a kuma jinkirta mishi a bayan shi to ya sada zumuncin shi .) Buhari
da Muslim ne suka rawaito
Yan daga cikin cikan da'a a kiyaye ta daga dukkan abin da zai tawaye ta ko
ya warware ta mai azumi yana da tsananin bukatan
kiyaye ibadar sa da kiyaye azumin shi daga abubuwan da za su kyata
shi ko bata shi Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce:- (Idan ranar da dayan ku ke azumi ne kada ya yi batsa kada kuma ya yi hayaniya , idan wani ya zage shi ko ya nemi fada
da shi to ya ce lallai ni mutum ne mai azumi) Buhari
da Muslim ne suka rawaito .
Ya kasance daga cikin koyarwan magabata Allah ya musu
rahama idan sun yi azumi sai su zauna a masallatai
sai su ce :- za mu kiyaye azumin mu ba za mu ci naman wani ba Imamu Ahmad Allah
ya mi shi rahama ya ce :- ( Ya dace ga
mai azumi ya kula da azumin shi daga
harshen shi kar ya yi musu ).
BAYAN HAKA YA KU
MUSULMAI:
Biyayya baya
cika kuma baya tsayuwa a kan kafan
sa ya zauna da gindin sa face da
kauna wanda za ta yi riko da ma'abocinta
zuwa ga ikhlasi , da kuma gaskiyan da
zai yi nuni da kyakkyawan bi, kuma aiki baya kasancewa kusanci sai idan har abin
da ya sa a ka yi shi imani ne ba al'ada ba ko son rai ba kuma neman suna ba ko don
riya ba , har sai ya kasance
babban manufan yin shi shi ne neman lada a wurin Allah da kuma neman yardan sa , idan imani da neman lada ya hadu a aiki , sai karbuwan aikin da kuma gafara ya
tabbata.
Ina
neman tsarin Allah daga shaidan abin jefewa
(Ku
yi gaggawa zuwa ga neman gafara daga Ubangijin ku da aljanna wanda fadin ta sammai da kasa an tanade shi ga masu
takawa).
HUDUBA TA BIYU
Dukkan yabo sun tabbata ga Allah bisa kyautatawan sa godiya kuma ta tabbata a gare shi bisa
datarwan sa da baiwan sa , na shaida ba
abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya ina mai girmama sha'anin sa , na shaida
Annabin mu Muhammad bawan sa ne kuma Manzon sa ne tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi da iyalan sa da
sahabban sa da aminci tabbatacce mai kari .
YA KU MUSULMAI
Duniya za ta kare da farin cikinta da bakin cikin ta shekaru kuma su kare da tsawon su da kuma
gajartan su , kowa ya hadu da Ubangijin shi
to anan ne fa dukiya ba zai yi amfani ba ko da sai wanda ya zo wa Allah da zuciya lafiyayye , to ku fiskanci watan ku da tuba
na gaskiya , ku kulla azama bisa ribatan
shi da raya lokutan shi da da'a rayuwan
duniya fa ba wani abu ba ne sai wani 'yan numfasawa ne kididdigaggu da kuma
ajali iyakantacce to ku ribaci lokuta
mafi daukaka , kuma hasararre shi ne wanda ya riski watan azumi ba a gafarta
mishi ba .
Manzon Allah tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :-( Hancin shi ya dumbuli kasa, hancin shi ya dumbuli kasa
, mutum da ya riski ramadan har ya fita ba a gafarta mishi ba)
Tirmizi ne ya rawaito
(Duk
wanda bai bar fadin zur ba da aiki da shi ba , to Allah baya bukatan ya bar
abin cin sa da abin shan sa ) buhari da
muslim ne suka rawaito
Mafi girman Abin da ke gyara zuciya ambaton Allah, da lazimtar kur'ani mai
girma, da tsayuwan dare , da zama da salihai.
Sannan ku sani hakika Allah ya umarce ku da salati da
aminci ga Annabin shi.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق