السبت، 3 نوفمبر 2018

KWANCIYAR HANKALI A MUSULUNCI


HUDUBAR MASALLACIN ANNABI NA SHAIKH ABDULMUHSIN ALKASIM 24 -2-1440AH
HUDUBAR FARKO :
  Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin sarki  muna gode mishi kuma muna neman taimakonsa , muna neman gafarar sa  , kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu , da munanan ayyukanmu , duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi , duk wan da ya batar kuma babu mai shiryar da shi , na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya , kuma na shaida Annabi Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa  da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa .
Bayan haka:
Ku ji tsoron Allah - ya ku bayin Allah – cancancin tsoronSa da shi ne ake neman ni'imomi  kuma ake tunkude azaba.
Ya ku musulmai!
Duniya gidan jarrabawa ne da gwaji, an dabi'antar da ita bisa gurbata da da kuma wahala,mutum zai yi kokari a cikinta tare da wahala Allah Madaukakin sarki ya ce : ( Hakika mun haliccin mutum cikin wahala)
Rayuwar mutum a duniya kadan ne, bai da wani abu a rayuwarsa sai abin da ya tsarkaka,
Kuma hutu da gushewar bakin ciki da bacin rai abin nema ne ga kowani dan –adam, da haka ne zaa samu daddadan rayuwa, da morewa na jin dadi.
Dukkan halittu na cigiyar walwala da jin dadin rayuwa kuma suna nemanta, Asalin sa'ida shi ne yelwatar zuciya, da samun kwanciyar hankali, idan Allah ya nufi bawa da alheri zai fadada kirjinsa babu wata  ni'ima mafi daukaka da ta kai ta, ita ce sababi  mafi girma na shiriya da ni'ima mafi daukaka, Ibnul Kayyim Allah ya mishi rahama ya ce : (kamar yadda yalwar zuciya take sababi na shiriya to kuwa asali ne na dukkan ni'ima da Alheri)
Sabo da girman wannan ni'imar ne Annabi Musa ya roki UbangijinSa  Allah ya mishi baiwar wannan a farko lokacin da ya tura shi zuwa ga Fir'auna sai ya ce : (Ya Ubangiji na ka bude Min kirji na)
Allah ya fara kirgo ni'imarsa da shi ga Annabi sai ya ce : (  shin bamu bude kirjinka ba ne).
Allah ya sanya shi sababi na dukkan komi a duk lokacin da abu ya yi girma to sabuban shi sai su  yawaita,samun shi ya saukaka,mafi cikan sabuba da kamalarta shi ne wanda sharia ta yi nuni gare ta ta  shiryar,   Babu abin da ya fi buda kirji kamar sanin Allah da sunayenSa da sifofinSa da kadaita shi da bauta,-tsarki ya tabbata a gare shi, gwargwadon haka da karfinSa gwargwadon  budewar zuciyarsa da samun sawabarsa, Ibnu Hazmi Allah ya kara yarda a gare shi ya ce " Na yi tunani game da ayyukan bayi sai naga duka suna neman  abu guda ne,ko da kuwa hanyoyinsu ya sha banban gurin samun shi amma gaba daya na ga suna yi ne don tunkude bakinciki da bacin rai daga kawunansu,ban ga hanya ba cikin hanyoyi da zai kai gare shi,- watakila wasun su ma suna kai wa ga akasin haka ne –sai da fiskantar Allah shi kadai da fifita neman yardarsa akan duk wani abu da ke kishiyantarsa, bawa bai da abin da ya fi wannan hanya kuma yafi sadarwa zuwa ga walwala da jin dadi kamarsa".
Mafi kamalan  halittu  a dukkan wata sifa da ke sanya walwala da jin dadi shi ne Annabin mu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma mafi koyi da shi cikin mutane shi ya fi samun cikakken natsuwa da budewan kirji da jin dadi da samun ni'ima.
Mafi girman abin da ake samun walwala da jin dadi shi ne imani da aiki na kwarai, da su ne zuciya da gabbai ke gyaruwa, da daidaituwar ciki da waje,da shi ne ake samun daddadan rayuwa da walwala na har abada, Allah Madaukakin sarki ya ce  : (wanda ya yi aiki na gari na miji ko mace alhali yana mumini lalle zamu raya shi rayuwa daddada ) AL Nahl :97
Ba abin da ya fi sa walwala da jin dadi da kwanciyar hankali kamar kaunar Allah da komawa gare shi da jin dadin bauta masa, Shaikhul Islam Allah kara ya rahamce shi ya ce : (Idan baka jin dadin aiki a cikin zuciyarka ba da kwanciyar hankali to ka tuhumi zuciyarka don kuwa lalle Allah Mai girma  Mai yawan godiya ne )  
Zabin Allah ga mutum ya fi zabinsa ga kansa, Allah shi ya fi tausayawa bayi akan kansu, wanda yayi imani da kaddara  na alherin sa da sharrinsa zai samu kwanciyar hankali da budewar kirji,Allah Madaukakin sarki ya ce : ( Wanda ya yi imani da Allah zai shiryar da zuciyarsa)  Alkama Allah ya mishi rahama  ya ce :(shi ne muminin da musiba zata same shi sai ya san daga Allah ne sai ya yarda ya mika wuya)
Bayi suna kai komo  ne a rayuwarsu a tsakanin sauki da tsanani  ba wanda ya isa ya fita daga dayan biyun ko ta kaka, samun walwala cikin hukuncin Allah da godiya a halin yalwa da hakuri a halin kunci  ko cuta Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : Mamaki da al'amarin mumini, lalle al'amarinsa duka alheri ne a gare shi, ba wanda ke da haka sai mumini, in yalwa ko  sauki ya same shi sai ya yi godiya, sai ya kasance alheri a gare shi, idan tsanani ya same shi sai yayi hakuri sai ya zama alheri gare shi.) Muslim ne ya rawaito.
Abin da Allah ya hukunta wa bawansa shi ya fi alheri gare shi, ya yin da Allah ya jarrabi Maryam da haihuwar yaro ba tare da Uba ba sai ya ce da ita : (To ki ci ki sha ki sanyaya idanuwanki)
Wanda yayi imani da gamuwa da Allah da ladarSa sai ransa ya ta' allaka da Maifalala akan abin da bai kai shi falala ba,sai abin da aka alkawarta masa ya rarrashe shi daga abin da aka rasa  shi,  da wannan ne duniyarsa  da lahirarsa zasu  gyaru,
Kyautata zato ga Allah na cikin ibadoji da ke haifar da aminci da walwala ma'abocinta, baw na da abin da ya zata game da Ubangijinsa in alheri ya samu alheri in kuma  sharri ya samu sharri, Allah Madaukakin sarki ya ce a hadisin Alkudsi : (Ni ina gun da bawa na ya zace ni) Bukhari da Muslim suka rawaito.
Fatan nagari na kawo budewar kirji da kwanciyar hankali,kuma yana daga cikin  kyautata zato ga Allah Madaukaki.
Mabudan al'amura da ragamarsu na hanun Allah ne shi kadan shi, yana juya zukata yadda ya so wurin baci ko gyaruwa ko kunci ko kwanciyar hankali da walwala, da jin dadi ko tashin hankali, to dogaro ga wanda hakan ke hanunshi da maida al'amari zuwa gare shi da aminta da shi wajibi ne a sharia, kuma garkuwa ce ga ma'abotanta, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Duk wanda ya dogara ga Allah to Allah ne ma'ishinsa)
To arzikin bayi a hanun Allah ya ke ba wani rayi  da zai mutu sai ya kammala  cinye  arzikinsa to ka yarda  ka gamsu ka ji dadi da abin da Allah ya baka na kasonka,
Duk wanda ya koma zuwa ga Allah to Allah zai taimake shi ya shige mishi gaba ya isan mishi,Allah Madaukakin sarki ya ce: ( Wadan da mutane suka ce da su Lalle mutanen sun muku gangami ku tsorace su, sai  hakan ya kara musu imani kuma suka ce ;Allah ne Ma'ishinmu kuma madallah da abin dogaro. Sai suka juya da ni'ima daga  Allah da falala, ba mummunar  abu  da ya shafe su kuma suka bi yardar Allah Allah ma'aboci falala ne mai girma ).
Duk wanda ya yi kwadayin samun  sa'ida da walwala da kwanciyar hankali to ya kwankwasa kofar Mai karamci to lalle Allah na kusa da wanda ya roke shi, kuma bai tabar da wanda ya yi fata daga gare shi, da adua ne al'amuran duniya da lahira ke gyaruwa, na daga cikin adu'o'in Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi (Ya Allah ka gyara min addini na wanda shi ne kariya ga al'amari na, ka gyara min duniya ta wacce cikinta rayuwa ta  take, ka gyara min lahira ta wacce gare ta zan koma ka sanya rayuwa gare ni kari ne ga dukkan alheri , ka sanya mutuwa ta zama hutu gare ni daga dukkan sharri)Muslim ne ya rawaito.
Ambaton Allah na da tasiri na ban al'ajabi wurin samar da kwanciyar hankali walwala da natsuwar zuciya da gusar da bakin ciki da bacin rai Allah ya ce : (wadanda suka bada gaskiya zuciyarsu take natsuwa da ambaton Allah, to da ambaton Allah zukata ke natsuwa,)
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance  yana cewa yayin bakin ciki : (   "La ilaha illallahul-Azimul-Halim. La ilaha illallahu Rabbul-'Arshil-'Azim. La ilaha illallahu Rabbus-samawati, wa Rabbul-ardi, wa Rabbul-'Arshil- Karim.) Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Maigirma mai hakuri .ba abin bautawa da gaskiya sai Allah ubangijin Al'arshi mai girma, Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah ubangijin sammai kuma Ubangijin  kasa  kuma Ubangijin Al'arshi mai girma)  Bukhari ne ya rawaito
Bukhari ne ya rawaito
Mafi  falalan zikiri shine Alkur'ani mai girma shi ne maganar Allah  akwai shiriya tattare da shi da waraka, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Ya ku mutane hakika gargadi ya zo muku daga Ubangijinku da waraka  ga abin da ke cikin kiraza da shiriya  da jinkai ga muminai )
Mafi cancantan  wadanda zasu samu  walwalar zuciya da kwanciyar hankali a halittu sune mahaddatan Alkur'ani, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Taha. Bamu saukar da Alkur'ani gare ka don ka wahala ba )   
A Tasbihi da Tahmidi  da yawan sujada  da dimantan biyayya  akwai samun annashwa da kwanciyar hankali, da tafiyar da bakinciki da kunci,  Allah Madaukakin sarki ya ce : (Hakika mun san lalle kirjinka na kuntata  sabo da abin da suke fada. To sai ka yi tasbihi da godiyar Ubangijinka kasance cikin masu sujada . ka bautawa Ubangijinka har mutuwa  ta zo ma.)
Da lazimtar tsoron Allah akan samu yayewan bakin ciki da tafiyar  da bacin rai, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Duk wanda ya ji tsoron Allah zai sanya mishi mafita ) kuma da ita ne akan samu saukin abubuwa Allah Madaukakin sarki ya ce : (Duk wanda ya ji tsoron Allah zai sanya mishi sauki cikin lamuransa)  
Sallah haske ne ga ma'abocinta  kuma tana taimakawa  wurin samar da kwanciyar hankali da natsuwa da tafiyar da bakin ciki Allah Madaukakin sarki ya ce : (ku nemi taimako da hakuri  sallah)
Na daga cikin koyarwan shi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi idan wani abu matsananci ya  dame shi sai ya  bazama zuwa ga sallah.) Abu Dauda ne ya rawaito.
Idan bawa ya bude wuninsa da sallah sai sauran wunin nasa ya yi kyau, to duk wanda ya yi sallar asuba yana cikin kariyar Allah, wanda ya yi ta tare da nafilarta Allah zai isan masa karshen wuninsa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Lalle Allah yana cewa ya Dan-Adam : kar ka gaza yin raka'a hudu a farkon wuni to zan kare ka karshensa)Ahmad ne ya rawaito.
Ilimin da aka gado daga Allah da manzonsa tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi  idan ya hadu da aiki yana sanya kwanciyar hankali da walwala har zuciyar ta fadada ta fi duniya fadi, ma'abota ilimin kuma zasu fi kowa kwanciyar hankali cikin mutane da walwala da fadin kirji da jin dadin rayuwa, kuma mafi kyan mutane dabi'u.
A duk lokacin da ilimin bawa ya karu to zai dada samun kwanciyan hankali da walwala a zuciyarsa , Allah Madaukakin sarki ya ce : (Shin kuma wanda ya kasance matacce  sa'annan muka rayar da shi kuma muka sanya wani haske dominsa, yana tafiya da shi yana zama kamar wanda misalinsa yana cikin duffai, shi kuma ba mai fita ba daga gare su?)
Ibnul kayyim ya ce game da shaikhul Islam : "Ban ga wanda ya fi shi jin dadin rayuwa ba duk da matsatsi da yake ciki da rashin wadata na abin duniya,sai dai ma kishiyan hakan, tare da daure shi da ake yi da tsoratarwa da tursasawa, amma duk da haka yana cikin wanda ya fi mutane jin dadin rayuwa  ya fi su fadin kirji da kwanciyar hankali, da karfin hali da dadin rai ga fiskarsa cike da fara'a da walwala ta ni'ima."
Kyautatawa mutane alheri ne bai kawo wani abu sai alheri, ba za ka taba ganin mutum mai karamci mai kyautata wa mutane ba face shine mafi kwanciyar hankali cikin mutane, kuma mafi zama cikin dadin rai a mutane  kuma mafi ni'imar zuciyarsa  a cikinsu, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Misali marowaci da mai sadaka, kamar mutane biyu ne ke sanye da sulken yaki ya takure hannayensu zuwa nononsu da hakarkarinsu  a duk lokacin da mai sadaka ya yi  sadaka sai  silken ya dada fadada  har ya suturce shi  zuwa yatsun shi yana share gurbin sa, amma shi munafuki a duk lokacin da ya nufi sadaka sai sulken ya kuntata  ko wani da'ira na sarkan  ya manne a gurbin shi.) Muslim ne ya rawaito.
Wanda ya muamalanci mutane don Allah ya huta  domin ba zai nemi tsinkayan  yabo  ko kuma  nadaman suka ba  halin shi tamkar misalin fadin Allah ne . ( Tamkar fadin Allah  madaukakin sarki ne :-   Lallai mu muna ciyar da ku ne  ,  don neman yardan Allah  ba ma bukatan sakayya ko godiya daga gare ku  ).
Hakan na dada karfafa a wurin mu'amala da  makusanta  da  kuma wanda ke da karfin alaka da su .
 Hakika za ka ga abin da ba ka so daga wasu mutane ,  to, mai hankali  bazai tawaye kyautatawan su ba sabo da tawaya  da ya fito daga gare su  ko ka yanke musu zumunci sabo da gajartawa  da haka ne mutum zai rayu  cikin tsanakin shi  da kwanciyan hankali  a ko wani hali  , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : - (Kar mumini ya tsani mumina –wato: kar ya ki ta – idan ya tsani wani hali daga gareta to zai yarda da wani halin) Muslim ne ya rawaito
A cikin zama da salihai da ma'abota ilimi da addini  akwai wani abu na debe kewa da samun walwala  kuma a nan ne mutum ke samun ilimi da hikima  zuciyar sa ta tsarkaka  ya zama mai kyau a cikin abokan sa  wanda ya koma zuwa ga ma'abota shawara da hankali  cikin al'amuran sa  zai samu kwanciyar hankali da waraka na zuciya  abinda ya rikice mishi zai gushe  Allah madaukakin sarki ya ce :-(Idan wani al'amari ya zo musu  na aminci ko tsoro sai su yada shi , dama sun maida shi  zuwa ga Manzon Allah  da jagororin su  ma'abota ra'ayi a cikin su  da wadan da suke tsinkayo fahimta ko hukunci  da sun san shi daga cikin su ).
Kiyayyan shaidan da dan adam baya yankewa   cikin yin neman tsari daga shaidan akwai koran wasuwasin na shi  dake jirkita   kwanciyar hankalin dewa daga cikin mutane ,  musulunci  na kwakwari don samar da sabuban   da za su kwantar da hankali su haifar da walwala ga musulmi tun lokacin da ya tashi daga baci shaidan na aiki don akasin haka  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Lallai shaidan yana   kulli  uku  a karshen kayin dayan ku  idan ya yi barci  yana buga ko wani daya daga cikin kullin  kana da  dare mai tsawo , ka kwanta   to idanya tashi ya ambaci Allah sai kulli guda ya warware in ya yi alwala sai kulli guda ya warware idan ya yi salla sai kulli guda ya warware  sai ya wayi gari mai kuzari  cikin tsarkakakken rayi   idan baiyi haka ba sai ya wayi gari yana da kazantaccen rayi mai kasala    ) Buhari da muslim ne suka rawaito
Kuma karfin mumini tushe ne mai girma   na samun  warakan zuciya  da walwala  ba zai biyewa abubuwa na wahami ba  zai kuma saki jiki don bakin ciki ba ko ya samu rauni  a gaban abubuwa na ki  sai dai ma zuciyan shi na kafe  yana kuma  tare da yakini da sakankancewa   cewa   lallai tare da  wahala akwai sauki   idan bawa ya halarto da falalar Allah  da ni'imar sa a gare shi hakan sai ya haifar masa  da  sabon godiya  da zai kwantar mishi  da hankali   kuma   ya sanya mishi walwala  .
Kuma wadatar zuci tushe ne na arziki,    kuma yana daga cikin mafi amfanin abin da ake yin magani da shi na zukata , abinda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya nusar zuwa gare  shi a fadin sa (ku yi dubi zuwa ga wanda ke kasa da ku kar ku yi dubi zuwa ga wanda ke sama da ku  don hakan shi ya fi dacewa  da kar ku raina ni'imar Allah  a gare ku)Buhari da muslim ne suka rawaito shi
Wanda ya tattara zuciyar sa  a bisa wunin sa da lokacin sa  zuciyan shi za ta natsu ba zai yi bakin ciki ba cikin abin da ya shude  ba zai bata rai ba cikin abin da yake fiskantowa   to abinda ya shude ba zai dawo ba  . Abu mai fiskantowa kuma gaibi ne rubutacce na daga cikin adu'o'in shi Manzon Allaha tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi   akwai ;;;( Ya Allah ina neman  tsarin ka daga  sharrin bakin ciki da bacin rai)  . Buhari ne ya rawaito
           Rashin amfana da  lokaci  tushe ne na bakin ciki da bacin rai  ,    wanda ya raya lokacin shi da aiki na kwarai ko ilimi mai amfani  wannan duka zai tafi daga gare shi, abunda ya tattaro walwala da sa'ada na cikin   neman taimakon Allah bisa ga abin da zai amfanar  da yin nesa da abin da zai sanya rauni ga bawa  ko ya raunana  zuciyar sa    da  karfin sa  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :-( Ka yi kwadayi bisa ga abin da zai amfane ka  ka nemi taimakon Allah , idan wani abu ya same ka kar ka  ce ba don na yi kaza-da kaza ba da kaza zai kasance domin lau tana bude aikin  shaidan )Muslim ne ya rawaito .
      Zunubai kofa ce  da musibu ke zuwa  ta gunta  ga bayi ,  da abin da ake sakawa mai laifi   da ita na daga bakin ciki da bacin rai da kunci    na zuci da kekasan zuciya  don ya zama ukuba na duniya  kafin na lahira  mafita daga haka shi ne yin nesa  daga sabo  da tuba zuwa ga Allah don ya warware  wurin kuncin  da  fadaduwan zuciya  haka nan kuma a wurin kadaici ya sanya debe kewa  .
     Tsarkake zuciya daga cututtukan sa yana kawo yayewan zuciya  ta samu walwala  yana kuma fadada shi  yana daga cikin adu'ar mumini  (Kada ka sanya kulli a cikin zukatan mu game da wadan da suka yi imani  ya Uabangijin mu lallai kai mai tausayi ne mai jin kai) bisa ga wannan sifa 'yan aljanna suke kasancewa Allah madaukakin sarki ya ce:-   (Muka  ci re daga cikin kirajen su  na kulli  kwaramai yana gudana a karkashin su kuma suka ce dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah   wanda ya shiryar da mu  zuwa ga wannan  ba mu kasance da  mu shiryu ba ba don Allah ya shiryar da mu ba  )
                BAYAN HAKA:
YA KU MUSULMAI:-
  To shi musulunci tushe ne na dukkan alheri   kuma  masdari ne na  dukkan samun sa 'ida da walwala   ma'abotan shi suna cikin aljanna  na gaggawa da ni'ima da baya yankewa  Allah madaukakin sarki ya ce :-(Wanda suyka kyautata a nan duniya da kyakkyawa suna  da kyakkyawa kuma  gidan lahira ya fi alheri  madalla da gidan masu tsoron Allah )
  Duk wanda ya san  shakawa irin na  jahiliyya da ma'abotan shi  zai san falala na ni'imar musulunci  da ma'abotan sa ba abin da zai  isar mishi sai godewa Allah bisa ga  hakan ,  da kuma riko da addinin sa da alfahari da shi  da tabbatuwa a kan shi da kiran halittu zuwa gare shi.
 Ina neman tsarin Allah daga shaidan abin jefewa 
Duk wanda Allah ya nufi ya shirye shi zai fadada zuciyar shi don musulunci,  wanda kuma ya nufi ya batar da shi zai sanya kirjin sa a kuntace cikin kunci  kai ka ce  yana haurawa ne  cikin sama  haka ne Allah yake sanya kazanta ga wadan da ba sa imani  ya Allah ka sanya albarka gare ni da ku a alkur'ani mai girma .
 HUDUBA NA BIYU
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah    bisa kyutatawan sa   da godiya a  gare shi bisa datarwarsa  da baiwar sa  na shaida  ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya  ina mai girmama sha'anin sa kuma na shaida Annabi Muhammadu bawan sa ne kuma Manzon sa ne   tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabban shi da amincin tabbatacce mai yawa da aminci mai kari .

YA KU  MUSULMAI:-
Allah ya yalwata kasar saudiya da ni'imomi masu yawa wanda ya fi ko wanne a cikin su shi ne ni'imar musulunci  da yaduwar shi  da kuma raya masallatai biyu masu alfarma da musu hidima da girmama wanda suka fiskanto su da bugawa da yada alkur'ani mai girma  a cikin sararin duniya  da bawa musulmai kulawa da musu hidima   a al'amuran su da yin hukunci da shari'ar Allah a kasar sa  kuma  ya sanya ta alkibla na musulmai , kuma zuciyar duniyar musulunci tare da abin da ya ni'imta a gare su na daga aminci da zaman lafiya da yalwa na rayu da jin dadin shi da kuma hadin kan jama'anta   da dunkulewan su  dukkan hakan da wanin sa  a falalan Allah ne  shi kadan shi  da kuma datarwa da Allah ya yiwa jagororin  ta   suka sanya abu na farko mafi muhimmanci  tun daga kafa wannan daula na musulunci tabbatar da kadaita Allah da bin Annabin sa  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  da hidima wa musulmai da yada ilimi na shari'a   wanda aka ciro shi  daga  littafi da sunna  da kuma bin sawun magabata na wannan al'uma  kuma duk yanda abu ya caccanza  da sautukan  wadan da suka saba mana  ba abinda zai karawa wannan kasa face  riko da musulunci da haduwa a kan kalma  tsakanin mabiya da jagororin su.
 Ya wajaba ga musulmai su kau da kai daga  wasu   jefe –jefe   da   jita-jitan masu  tada zaune tsaye  da rashin sauraro zuwa gare su   da shagaltuwa da abin da zai amfanar  . 
 Sannan ku sani lallai Allah na umartan ku da salati da aminci ga Annabin shi sai ya ce  a cikin littafin shi mafi hikima da  saukar :- (Lallai Allah da mala'iku suna salati ga Annabi  ya ku wadan da suka yi imani ku yi salati a gare shi  da aminci tabbatacce )
       



الجمعة، 19 أكتوبر 2018

FALALAR AYATUL KURSI


HUDUBAR MASALLACIN ANNABI NA SHAIKH ABDUL BARI ASSUBAITI 10-2-1440AH
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah,tsayayye Rayayye, ina gode mishi tsarki ya tabbata a gare shi,bacci ba ya daukan shi ko gyangyadi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya,Madaukaki Mai girma, na shaida Annabinmu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne,ya nusar da mu zuwa ga tafarkin Allah mikakke, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  da iyalan shi,da sahabbansa masu tafiya akan tafarki mikakke, bayan haka,
Ina muku wasiya da ni kai na da ku ji tsoron Allah ,Allah Madaukakin sarki ya ce : (Ya ku wadan da ku ka yi imani ku ji tsoron Allah cancancin tsoronSa, kar ku mutu face kuna musulmai)
(Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ya Abul Munzir ! ko kasan wace aya ce mafi girma ka ke da ita a cikin littafin Allah? Yace sai na ce :Allah da Manzonsa ne suka fi sani, sai yace: ya Abul Munzir ! ko kasan wace aya ce mafi girma ka ke da ita a cikin littafin Allah? Yace sai na ce : (Allahu La'ilaha illa huwal Hayyul Kayyum) sai ya buga kirji na yace " Madalla da ilimi irin naka ya Abul Munzir",   
Ayatul kursi ta zama aya mafi girma ne sabo da ta tattaro tushen sunayen Allah da sifofinsa, ta bayyana kudura na Allah Mai girma.
 (ALLAHU LA'ILAHA ILLAHUWA) :- Allah ba abin bautawa da gaskiya sai shi ) ,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :- (Imani  kashi saba'in da dori ne ko sittin da dori  mafi girmanta shi ne fadin LA'ILAHA'ILLALLAH ;  )    shi ne mai gaskiya tsarki ya tabbata a gare shi , fadin sa kuma shi ne gaskiya alkawarin shi ma gaskiya ne  addinin shi ma  shi ne na gaskiya , kuma littafin shi ma gaskiya  kuma duk abin da ya bada labari gaskiya , kuma duk abin da ya yi umarni da shi gaskiya ne  a zatin sa da sifofinsa  mai cikakken sifofi , shi ne wanda bai gushe ba kuma ba zai gushe ba ya siffantu  da daukaka da kyau da kamala   haka nan kuma  bai gushe ba kuma ba zai gushe ba  wanda aka san shi da ihsani .
        ( ALHAYYUL –KAYYUM) :-Rayayye tsayayye  shi dinnan shi ne rayayye wanda baya mutuwa ko ya halaka ; yana da rayuwa na dindindin da wanzuwa  wanda  bayi da farko ko karshe   da za a iya iyakance shi  kuma (ALKAYYAUM)   ya kunshi  kamalar wadatuwar sa da kamalar kudurar sa  domin shi tsayyayye ne a kan kansa  sannan kuma  yake  dawainiya da wasu  ,  wanin sa ba zai iya tsayuwa ba sai da tsayuwar sa  wadan nan sunayen biyu sai suka kintsu  wajen tabbatar da kamalar sa  to, sai ya kasance shi ne abin neman agaji  da wadannan sunaye biyun  kuma ana neman agaji da dukkan suna daga cikin sunayen Ubangiji  madaukaki da kuma dukkan siffa daga cikin siffofin shi  , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance maiyana yawan adu'a da wadannan sunaye biyun ,   idan wani abin bakin ciki ya same shi sai ya ce :-  (YA HAYYU-YA KAYYUM  BI RAHMATIKA ASTAGIS)   Rayayye tsayayye  da rahamarka nake neman agaji . Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata  a gare shi ya ce  duk wanda ya ce Astagfirulllahal lazi la'ilaha illahuwal  hayyul kayyum wa atubu ilaik)    ina neman gafaran Allah wanda ba abin bautawa da  gaskiya sai shi rayyayye tsayayye  kuma ina tuba zuwa gare shi ,  to,   za a gafarta mi shi zunuban shi ko da ya gudu daga fagen yaki ne .
    Idan Musulmi ya lura  ya san cewa Ubangijin shi dinnan rayayye ne tsayayye  ( sai  zuciyan shi ya samu natsuwa  da kwanciyan hankali  ;    hakika an  isar mishi  daga bakin cikin duk wani shiri , kuma an bashi kariya daga dukkan wasu sharrace-sharrace da laifuka .
  ( LATA'AKUZUHU –SINATUN WALA NAUM)    Gyangyadi ko bacci bai daukan shi  to shi mabuwayi mai daukaka ya tsarkaka daga dukkan wata nakasa  ko gajiyawa ko aibi  irin wanda ke tattare ga bayin sa : -  Yanda duniya  ke gudana cikin tsari  shaida ne akan haka ,  haka nan yanda rayuwa  ke tafiya , da kuma yanda halittu ke rayuwa   ( LATA'AKUZUHU –SINATUN WALA NAUM) Gyangyadi ko bacci bai daukan shi, in ba don haka ba kuwa da wannan duniyan ta rikirkice ,  tafiyar sa ya baci ,   tsarin sa  ya rikirkice ,,(Bai dace ga rana ba ta riski wata  ko kuma dare ya sha gaban yini ) da  kuma ruwan koguna sun rinka ambaliya  da koramai .
      A lokacin da  idanuwa suka yi bacci   taurari     suka bayyana to lallai wasu mutane cikin muminai hakarkarin  su na yin nesa daga makwanci :-  suna ganawa da wanda gyangyadi ko bacci bai kama shi ,  sai ya amsa musu  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce :- (Ubangiji mu  mabuwayi da daukaka na sauka  a dukkan dare  zuwa ga saman duniya  daidai sulusin karshe na dare  sai ya ce :- wa zai roke ni na amsa mishi  kuma wa zai tambaye ni na bashi kuma wa zai nemi gafara ta na gafarta mishi).
      Abin da ke cikin sammai da kassai duka na shi ne  dukkan komai da ke cikin su  yana karkashin mulkin sa ne da kudurar sa  da kuma kaddarawan sa da  falalan sa   da fifikon sa da hukuncin sa  da hikimar sa   falakoki da duniyoyi masu girma : shi ne mahaliccin su,Mai mallakansu abin bautansu,ba abin bauta da gaskiya koma bayanSa  basu da wani Ubangiji koma bayanSa,                     
(wanene zai yi ceto gaba gare shi in ba da izininSa ba)? Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Wanda ya fi samun ceto na ranar Alkiyama shi ne wanda ya ce La'ilaha illallah yana mai ikhlasi daga zuciyarsa).
(yasan abin da ke gaban su da abin da ke bayansu, ba su iyakance wani abu na iliminsa sai abin da ya so) Shi ne wanda tsarki ya tabbata a gare shi Mai ji Mai gani Masani kuma Gwani,   yana ganin  tafiyan bakar tururuwa  akan sandararren dutse  a cikin dare mai duhu  yana ganin abin da ke damfare da jijiyoyin ta da gudun abinci a cikin  gabbanta  .
  ( Yana da mabudan gaibi ba wanda ya san su sai shi   kuma ya san abin da ke tudu da kogi , ba wani abu da ke faduwa na ganyen itaciya face ya sani ko kwaya a cikin duhun kasa  , ko danyen abu ko busasshe face yana  rubuce a littafi bayyananne )  ba abin da ya kewaye ilimin sa Mala'ika ne na kusa  ko wani Annabi manzo , to, ta yaya  masu duba da bokaye da 'yan tsubbu  za su iyakance ilimin shi ,  wadanda  suke da'awan sanin abin da zai faru nan gaba  Allah madaukakin sarki ya ce :-  (Ba wanda ya san gaibi cikin wanda suke sammai da kasa   face Allah ) .
     (wasi'a kursiyyuhussamawati wal ardi )  kujerarSa ta fi fadin sammai da kasa   abin mamaki da girman Allah  abin bauta maigirma madaukaki  kudurarSa ta bayyana tsarki ya tabbata a gare shi  , idan wannan shi ne girman kujerarSa  na cewa ya fi fadin sammai da kasa  duk da girman sunnan  da girman wanda ke cikin su  to ina ga girman mahaliccin su   da kuma wanda ya kirkire su   , to shi ne;   tsarki ya tabbata a gare shi mai yalwa a iliminSa , kuma mai yalwa a wadatarSa  kuma mai yalwa a falalar sa  da ni'imtarwanSa  da kyautarSa  shi ne kuma mai yalwa a karfinSa da kasaitarSa   kuma shi ne mai yalwa a  ikon sa,   kuma mai yalwa a hikimarSa kuma mai yalwa a gafararSa da rahamarSa .
  To Musulmi  yana bautawa Ubangiji wanda kyautarSa na da yalwa a dukkan komai  ,  falalarSa kuma ta ketare dukkan abin da ake fata  Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi umarni   game da rokon mai adu'a ga UbangijinSa   ba tare da ya ga  cewa ya yawaita mishi ba sai ya ce , (idan  dayan ku ya zo roko to ya yawaita domin Ubangijinsa fa ya ke roko).
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Idan za ku roki Allah to ku roke shi Aljannar firdausi don ita ce tsaka –tsakin Aljanna kuma mafi daukakanta, kuma samanta Al'arshin Mai rahama yake daga nan ne koramun Aljanna ke bubbugowa).
(Kiyaye su ba zai nauyayi Allah ba) Dukkan wani abu da ke duniya na cikin kiyayewa na Allah ne, shine Alhaafiz kuma Alhafeez) shi ne mai kiyaye ayyukan Mukallafi, kuma shi ne mai kiyaye sharri da cuta da bala'i ga wanda ya so.
Na daga ciki aduar da Annabi ya koyar da mu ita (Ya Allah ka kiyaye ni ta gaba na da ta baya na da ta dama na da ta hagu na, kuma da ta sama na, ina neman tsarinka da kasaitarka da a mini kisan gilla ta kasa ta.)
Allah- Mai tsarki -shi kadan shi ne mai kiyaye mutum in ya kiyaye dokokin Allah ya nesaci abin da ya haramta.
Allah Madaukakin sarki ya ce :(To managartan mata masu bi ne  ga mazajensu masu kiyayewa ne a fakuwa, sabo da Allah ya kiyaye su da yiwa maza wasiyya dasu )
Ayatul kursi : ganima ce ga musulmai kuma ni'ima ce daga cikin  ni'imomin Allah  mafi girma, tana daga cikin zikiri mafi karfi na safiya da maraice , wanda da ita ake samun kiyayewa mai karfi na Allah, game da ita ne manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Duk wanda ya karanta ayatul kursi karshen kowace  sallah ba abin da zai hana shi shiga Aljanna sai mutuwa) kuma idan ka karanta yayin da ka zo barci (Bai zai gushe ba kana samun kariyan Allah kuma  ba wani shaidan da zai kusance ka har ka wayi gari)
HUDUBA TA BIYU
Alokacin da magana ta yawaita kuma tashoshin watsa labarai suka cika da naji ance(kila da kala) to wajibi a kan musulmi shi ne ya auna abin da yake gani da abin da ya ke ji da abin da yake fada bisa mizani na sharia da hankali,idan ka samu kalma da zata kashe fitina ta sanya fata na gari ta kawo zaman lafiya ta karfafi kwanciyan hankali, ta kuma binne balbali ta rufe kofar fitina kuma ta rinjayar da maslahar kasa kuma zata taimaka guri dunkulewar Al'uma ta kuma kiyaye wa jagororin Addini hakkokinsu, to wannan ita ce kalma mai kyau.
To idan kalma na kara wutan fitina ne, ta na gusar da zaman lafiya kuma tana tada balbalin bala'i  tana girgiza aminta da jagororin Addini, tana taba mutuncin malamai tana kawo rarrabuwar al'uma kuma tana cin karo da maslahar kasa, to wannan ita ce kazantacciyar kalma, to binne ta tun tana karama ya fi dacewa, kuma kaurace mata shine tafarki mafi daukaka.
Kasar saudiya tana da gini mai karfi wanda ta kafu a zuciya, taba darajarta kaskanci ne, duk wanda ya yi gaba da ita zai fadi ya kaskanta, yin kokarin kawo mata zaman lafiya da amincin masallatayya biyu masu alfarma,kuma tare Masun da aka nufe ta da su, da karfafa dunkulewarta abu ne na wajibi a sharia, kuma abu ne da ya dace duk wani maihankali ya nema, (To su bautawa Ubangijin wannan daki. Wanda ya ciyar da su daga yunwa, ya amintar da su daga tsoro.)  

الاثنين، 15 أكتوبر 2018

Tsarkake Rai


HUDUBAR MASALLACIN ANNABI  25-1-1440 NA SHAIKH  ABDULLAHI BIN ABDURRAHMAN AL-BUAIJAN
HUDUBAR  FARKO
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga wanda ya halicci zukata ya daidaita su, ya  kimsa fajircewarsu da takawar su, kuma ya wajabta  rabauta ga tsarkake ta, hasara ta tabbata ga wanda ya  biye wa son ransa.
Muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunan mu da munanan ayyukanmu, wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi, wanda ya batar da shi ba bu mai shiryar da shi,
Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, dahir kuma tabbas, kuma na shaida cewa Annabi Muhammad bawan sa ne kuma Manzonsa ne,tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, aminci tabbatacce mai yawa,
Bayan haka, mafi alherin zance shi ne maganar Allah,kuma mafi kyan shiryarwa shi ne koyarwar Annabi Muhammad, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, mafi sharrin al'amura sune fararrunta, kuma dukkan fararrun abubuwa bidi'a ne, kuma dukkan bidi'a bata ce.
Ya ku bayin Allah !
 ina muku wasiyya da ku ji tsoron Allah, da ku yi wa kan ku hisabi, ( ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah kuma rai ya yi dubi ga abin da ya kaddamar don gobe, ku ji tsoron Allah. Lalle Allah masani ne ga  abin da ku ke aikatawa ,)   ALHASHR 18
Ya taron musulmi !
Lalle Allah ya hallici mutum ya sanar da shi fasaha, ya bashi kyautan hankali da harshe, ya nusar da shi hanyoyi  biyu, ya bayyana mishi hanya ko ya gode ko ya butulce.
Ya jarraba shi da kiyayyar rayi da shaidan ya rubuta masa dace  ko tabewa, ya sanya makomansa wuta ko aljanna.
Ya shar'anta  sharia sabo da shi, ya saukar da littatafai ya turo manzanni  suna masu albishir masu gargadi, cikin mutane akwai wanda ya amsa kira ya tsarkaku, duk wanda ya tsarkaka to don kansa, daga cikin su akwai wanda ya juya baya ya ki ya warware, wanda ya warware to don kansa.
Ya jama'ar musulmi!
 Ku sani rai abokin gaba ne kuma mai umarni da mummuna ne,mai yanke tsakani zukata da Ubangiji  masanin gaibi.
Rai a dabi'arsa mai kwadayi ne ga abin  sha'awe sha'awe  da son jin dadi, mai nawa ne gurin da'a  da ayyukan alheri, rai abin hawan shaidan, ne motarsa ne, kuma wasilarsa ne , kuma kayan alatonsa ne, ta hanyarsu ne ake masa biyayya, kuma hujjarsa ne kuma katangarsa ne. (sai iblis ya fada yayin da aka hukunta Al'amari Lalle Allah ya muku alkawari alkawarin  gaskiya ni kuma na yi muku alkawari na karya na saba muku, kuma ba ni da wani karfi  akan ku, sai dai na kira ku ne ku ka amsa min, kada ku zarge ni ku zargi kawunanku) Ibrahim 22
Rai na yawan umarni da mummuna, mai yawan karkata ga son rai  (Amma wanda ya ji tsoron tsayuwa gaban UbangijinSa ya hana kansa ga barin   soye-soyen rai , to, lallai aljanna ita ce makoma)  kuma ya ce :-(Ase baka ga wanda ya riki abin bautar sa son ransa ba kuma Allah ya batar da shi bisa ilimi ya toshe jinsa da zuciyan sa  ya sanya rufi a ganin sa  to wa zai shiryar da shi bayan Allah ).
    Rai  matattara ce ta alheri da sharri  Allah madaukakin sarki ya ce :-(  Wanda a ka kiyashe shi kwadayin kan sa wadancannin ka su ne hakikanin marabauta)  al hashir aya 8 ,  kuma ya ce:- ( Lallai rayi  mai yawan umarni ne da mummuna ) .
 Ya ku bayin Allah ;
 Lallai Allah yana yiwa zuciya ilhami na alheri da na sharri , kamar yanda Allah madaukakin sarki ya ce :- ( Da rayukan dan adam da wanda ya daidaita su . kuma ya kimtsa mata fajircin ta da tsoron Allah ) surah asshams aya 7-8 .
 Kamar yanda Allah ya bawa mutum kyautan ji na zahiri , to, haka kuma ya bashi kyautar rayi  wanda ita ce ta tattari basira na ciki  Allah madaukakin sarki ya ce :-(  Bari !  shi mutum malami ne a bisa kansa  ko da zai zo da hanzare-hanzaren sa )
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi nuni zuwa ga haka  sai ya ce:- (Shi laifi shi ne abin da ya sosa a zuciyan ka ka sani mutane su gane shi )
YA KU BAYIN ALLAH:
Lallai rayi na da bukatan kulawa  da sa ido  da tarbiyantarwa  da kuma tsarkakewa da bibiya    sabo da haka ne annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da husaini dan munzir : - (Ka ce ya  Allah ka  kimtsa mini shiriya ta  ka kare ni daga sharrin rayi na )  ya zo a cikin khudubatul haja (  Muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunan mu ).
YA JAMA'AR MUSULMI:
Lallai hanyar kubuta daga sharrin rayi shi ne a tsarkake ta  a bata kulawa  a kuma bibkiye ta ,  kuma hakika Allah ya yi rantsuwa a cikin littafin shi a wurare goma sha daya a jere  bisa ga rabautan  wanda  ya tsarkake  ta  , kuma da hasaran wanda ya turbude ta  sai  ya ce :- (Allah ya yi rantsuwa da rana da hasken walahan ta .    Da wata  idan ya bi ta .     Da wuni idan ya bayyana rana   .     Da dare idan ya lullube ta.    Da sama da  wanda ya gina ta.    da kasa da wanda ya shimfida ta .  Da rayukan dan adam da wanda ya daifdaita ta  kuma ya kintsa mata fajircinta da tsoron Allah.   Hakika wanda ya tsarkake ta ya rabauta.   Hakika wanda ya turbude ta ya tabe.
      Allah ya yiwa muminai baiwa da ni'ima mafi girma sai ya ce : -( Hakika Allah ya yi baiwa  bisa muminai  da ya aiko Manzo a cikin su daga kawunan su  yana karanta ayoyin sa a gare su  yana tsarkake su yana sanar da su alkur'ani da hikima , hakika  su sun kasance gabanin aiko shi  lallai suna cikin bata mabayyani ).
          Allah   ya bada labari kan cewa tsarkake rayi wasila ce  na samun babban rabo da rabauta da aljanna  sai ya ce  : -( Hakika  wanda ya tsarkaka ya rabauta , ya ambaci Ubangijin sa  ya yi  salla ).
      Kuma ya ce :- (Amma wanda ya ji tsoron tsayuwa gaban UbangijinSa ya hana kansa ga barin   soye-soyen rai , to, lallai aljanna ita ce makoma)  
YA KU BAYIN ALLAH :
 Lallai tsarkake rayuka  bai samuwa  sai da matsayi na  ihsani :-  Kan ka bautawa  Allah kamar kana ganin shi , in kai baka ganin shi to shi yana ganin ka .
 Baya samuwa sai da sabawa son rai  da lazimtar tsoron Allah  kuma bai samuwa sai da sabawa rayi mai umarni da  mummuna , da kyale abubuwa na jin dadin rai da sha'awe-sha'awenta.
To duk mai ciyar da rayi abin da take sha'awa
Tamkar mai ciyar da wuta ne busasshen kirare

To duk wanda  aka datar ya fi karfin zuciyar shi to ya cinma manufa kuma ya habaka rayin sa.    Wanda ya sake mata linzami  sai ta wurga shi  cikin hanyoyi na  halaka.
Duk  wanda ya kauracewa jin dadi zai cinma manufa
Wanda ya dukufa akan ababan jin dadi zai yi nadama
Daukakan rai na cikin tunkude sha'awarta
Cikin  samun abin da yake sha'awa   akwai kaskanci na har abada
Kar ka shagalta sai da abin da zai kawo ma daukaka
Kar ka yarda da halaka ga rai mai tsada
                                                                                                                                                                                                                               
YA KU JAMA'AR MUSULMAI :
Jihadi shi ne kololuwan tozo na musulunci  farilla ne   mafi  girma daga cikin farillai  mafi girman jihadi shi ne jihadin rai  , ku sa mata linzami game da abubuwan jin dadin ta , ku yaye ta daga sha'awe-sha'awen ta , daukakan ta na daga cikin fin karfinta game da sha'awe-sha'awen ta,  kaskancinta da walakantar ta na cikin bata dama game da sha'awanta
 Rayi kamar jariri yake wurin shan nono  in an kyale shi sai ya girma
a kan haka  in an yaye shi sai ya yayu
Ka yaki ranka da shaidan ka saba musu
Idan sun maka  nasiha to ka tuhume su
 Kar ka yi biyayya gare su  suna abokan jayayya ko hukunci
Domin kai dinnan kasan kaidi irin na abokin jayayya  da kuma mai hukunci

Gaba irin na rayi kwatankwacin gaba irin na shaidan ne  kuma hakika Allah ya gargade mu game da musu da'a a cikin alkur'ani ((Amma wanda ya ji tsoron tsayuwa gaban UbangijinSa ya hana kansa ga barin   soye-soyen rai , to, lallai aljanna ita ce makoma).
Allah ya sa muku albarka ni da ku  a cikin alkur'ani.
HUDUBA TA BIYU
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah da ya halicci  mutum ya daidaita shi ya girmama shi ya fifita shi , ya kuma kalifantar da shi ya ba shi aminci ,  kuma ya ba shi kiwo  ya daga  darajar shi kuma ya azurta shi  kuma ya masa baiwa ya mar kyauta   .
Tsira da amincin Allah su tabbata ga wanda Allah ya zaba  Annabin mu Muhammad dan Abdullahi   da iyalan sa da sahabban sa da duk wanda ya bi tafarkin sa kuma ya bi shiriyar sa .
 YA JAMA'AR MUSULMI:
Rayi mai yawan umarni ne da mummuna   ita dinnan ta hada yawan zalunci da kuma yawan jahilci, tana yin jiji da kai da kuma nuna girman kai  da kuma hasada da riya   da fushi da kuma  kwadayi ,  da handama da babakere,  da rowa da  kankamo   da tsoron talauci da kuma   da sauran su na daga cututtuka.
    Tsarkake ta  shi ne  a cire mata wadan nan  sifofin  .
   Tsarkake rayi shi ne siffantuwa da kyawawan dabi'u  da kuma kyawawan halaye da laduba irin na shari'a   kamar  kauna  da ikhlasi da hakuri da gaskiya  da kuma kankan da kai  da tsoro da fata  da karamci da kyauta da tuba da istigfari ,  da kuma tuna mutuwa da karewa  da juya baya ga duniya  da fiskantar Allah madaukaki.
  Tsarkake rayi  yana tabbatuwa ta hanyar sabawa son arai da rashin amsa bukatun ta , da kuma yaye ta daga sha'awe-sha'awen ta   da jin dadin ta  da kuma yi mata inkari  da zarginta  Allah madaukakin sarki ya ce: - (Duk wanda  ya tsarkaka ya rabauta  . Ya kuma ambaci sunan Ubangijin shi.  Ya tsarkake  sunan Ubangijin shi mafi daukaka  )
  YA KU BAYIN ALLAH :
Ku yi kokari wurin tsarkake rayuka   kafin mutuwar gaggawa ta zo mu ku  da kuma yin da na sani ,(Ranar da ko wace rai take samun abin da ta aikata  na alheri  abin halartarwa da abin da ta aikata mummuna   tana burin da hakika akwai fage mai nisa ).
     Ku yi kokari wurin tsarkake rayuka  kafin  rayi ya zo ya ce ya hasara na bisa ga sakaci da na yi a sha'anin Allah  ko da kuwa na kasance cikin masu yin isgilanci  ko kuma ta ce  ina  ma da Allah ya shiryar da ni  da na kasance cikin masu tsoron Allah  , ko kuma ta ce ya yin da ta ga azaba  ina ma da  ina da kome sai in kasance cikin masu kyautatawa.
  Ku yi kokari  wurin tsarkake rayuka  kafin a toshe baki ba zai iya yin furuci ba , shaidu za su tsaya abokan jayayya  sune gabbai  kamar yanda Allah ya ce :- ( A yau ne muke yumkewa  bakunan su , hannayen su za su yi mana zance , kafafuwan su za su yi mana magana   za su shaida  bisa ga abin da suka kasance suna aikatawa)
(Ranar da muke tara makiya Allah to su ana kora su  (zuwa wuta). Har yayin da suka zo mana  sai kunnuwan su da idanuwan su da fatun su suka shaida a gare su da abin da suka kasance suna aikatawa ,  za su fada ga fatun su don me kuka yi shaida a kanmu , sai suka ce Allah ne ya furtar da mu  wanda ya furtar da ko wani abu  shi ne ya halicce ku  marrar farko izuwa gare shi ake komawa da ku.   Ba ku kasance kuna buya ga miyagun al'amura  don kunnuwan ku da idanuwan ku   da fatun ku su yi muku mummunar shaida ba, kai dai kun yi zato ne ya yin buyan ku cewa  hakika Allah bai san yawanci daga abin da kuke aikatawa ba , abin da kuke boyewa ba  .  Wancannin ku zaton ku wanda kuka zata ga Ubangijin ku shi ne ya halakar da ku  ku ka zamanto daga cikin tababbu .
   In sun  yi hakuri  to wuta ne makomar su , in suka nemi a yarda da su to su basa daga cikin ababen yarda . )
         Ku yi kokari wajen tsarkake  rayi  kafun  ranan da zai zame a cikin shi ( Ranar da mutum zai gujewa dan uwan shi.    Da uwar sa da Uban sa .   Da matar sa da diyar sa . Ko wani mutum a cikin  su a wannan ranar yana da sha'ani da zai shagalar da shi .
  YA KU BAYIN ALLAH:
Mai wayo shi ne wanda  ya yiwa kan sa hisabi ya yi aiki domin abin da zai zo bayan mutuwa , shi kuma gajiyayye shi ne wanda ranshi ya bi abin da yake so , ya yi ta gurace-gurace a wurin Allah  .
   Ku yiwa kan ku hisabi kafin a yi muku hisabi  ku auna kafin a auna ku  , lallai hakan ya fi saukin hisabi a gobe   idan kuka yiwa kan ku hisabi a yau   kuka yi ado  domin halartowa a wuri mafi girma , a wannan ranar ne za a kawo ku  babu wani mai tsoro a cikin ku .
  Wata rana Umar dan khaddab Allah  ya yarda da shi ya  shiga wani kango sai ya kebanta da ranshi yana mata hisabi  Anas dan Malik Allah ya yarda da shi yana sa mishi ido daga nesa ta inda  baya ganin shi  , sai ya ji umar shugaban muminai  yana cewa  sannu, sannu  na rantse  da Allah ya kai dan Khaddab  ko dai ka ji tsoron Allah ko Allah ya azabtar da kai .
  Ku ji tsoron Allah ya ku bayin Allah , ku sani fa zaku hadu da shi
Ya Allah zukatan mu ka bata tsoron Allah
Ya Allah ka daukaka musulunci ga musulmai .      

الجمعة، 28 سبتمبر 2018

TABKIN ALKAUSARA


Hudubar Masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi   11-1-1440AH na sheikh Ali Abdurrahman Al-Huzaifi
HUDUBAR FARKO
 DA SUNAN ALLA MAI RAHAMA MAI JIN KAI
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mabuwayi mai yawan kyauta mai gafaran zunubai mai karban tuba , mai tsananin ukuba   ma'abocin yalwa ,  ba abin bautawa da gaskiya sai shi komawa na gare shi  ina  kyautata yabo ga Ubangijina kuma ina gode mishi , ina tuba zuwa gare shi  kuma ina neman gafarar sa, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya madaukaki mai girma ,  kuma ina shaidawa Annabin mu Muhammadu bawan sa ne kuma Manzon sa  ne ,  mai albishir kuma mai gargadi , ya Allah ka yi dadin tsira  da aminci da albarka bisa ga bawan ka  kuma Manzon ka Muhammad  da iyalan shi da sahabban shi  wanda suka tsere zuwa  ga dukkan falala da alheri   .
BAYAN HAKA: - Ku ji tsoron Allah ta hanyar bin umarninsa  da nisantar abin da ya hana ya tsawatar, ya ku bayin Allah;  ku yi aiki irin ayuka na kwarai domin gyara lahiran ku   kada ku bata ayukan ku sai ku yi hasara wa kanku  Allah madaukakin sarki ya ce (  Ka ce ku yi aiki  Allah zai ga ayukan ku da Manzon sa da muminai sannan a maice ku zuwa ga masanin gaibi da shahada , sai ya baku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa )
     Allah madaukakin sarki ya ce : (Ya ku wadan da suka yi imani ku yi da'a ga Allah ku yi  da'a ga Manzo kar ku bata ayukan ku ).
Kuma Allah madaukakin sarki ya ce : (Lallai hasararru su ne wadanda  suka yi hasarar  kawunan su  da iyalan su ,  ranar alkiyama , wannan shi ne hasara mabayyani )
Ku gyara duniyan ku ta hanyar neman halal da ciyar da  shi cikin kofofin alheri na wajibi da mustahabbi  da kuma  halal , ku sanya wannan duniya din ta zama guzuri a gare ku  zuwa gidan ni'ima   kada  kawa ta duniya ta rude ku  ko  ta fitine ku game da lahira , ka yi aiki ya kai Musulmi domin gyara duniyar ka,   ka yi aiki kuma domin gyara lahirar ka , ya zo a hadisi   ba mafi alherin ku shi ne wanda ya bar lahirar sa don duniyar sa ba  , ko kuma wanda yabar duniyar sa don lahirar sa ba   ,  An karbo daga Mustaurid  dan Sadad Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : (   Mun kasance a wurin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  muna tuna duniya da lahira  ,  wasun su suka ce  duniya kawai guzuri ne zuwa ga lahira  ,  acikin ta akwai aiki akwai salla ,  akwai zakka , wasu daga cikin su  kuma sai suka ce  lahira a cikin ta akwai aljanna  suka fadi abin da Allah ya so su fada, sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :-Misalin duniya in an kwatanta da lahira kamar dayanku ne  ya tafi kogi ya sa yatsarsa ciki ya fitar to ruwan da yatsar ta debon shine duniya,) Hakim ya rawaito a cikin Al Mustadrak, kuma Hakim ya rawaito daga Sa'ad dan Darik daga baban shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:  (Madalla da gidan duniya ga wanda ya yi guzurin lahirar sa daga gare ta  har ya yardar da Ubangijin shi , tir ga wanda ta kange shi daga lahirar sa  ta gajarta mishi samun yardan Ubangijin shi ).

     Hasanul-Basari  Allah ya mishi rahama ya ce : - ( Madalla da gidan duniya ga mumini  sabo da ya yi aiki dan kadan a cikin ta ya karbi  guzurin sa daga gare ta zuwa aljanna,   tir  da gidan  da ta kasance ga munafiki da kafiri sabo da ya sarayar da dararrakin sa sai guzurin sa ta kasance a cikin ta zuwa wuta Ahmad ne ya rawaito a cikin littafin zuhud .
   Kowa ya san dahir cewa shi din nan  mai kaura ne  daga  wannan gidan  kuma ya bar abin da Allah ya bashi anan duniya a bayan shi  ba abin da zai kasance tare da shi sai aikin shi,  in alheri ya yi ya ga alherin sa in kuma sharri ya yi ya ga sharrin sa   to idan har ya kasance halin ko wani daya zai kai ne zuwa ga wannan gayan kuma zai kai ga wannan makomar    , to ya wajaba a gare shi da ya kaddamar da aiki mafi daraja da zai iya yi ga ubangijin shi  na daga cikin ayuka na kwarai  ba wata wasila tsakanin bawa da Ubangijin shi sai da wannan  Allah madaukakin sarki ya ce :- ( Ba wai dukiyan ku ne ba ko 'ya'yan ku  ne suke kusantar da ku zuwa gare mu kusantarwa ba  face wanda ya yi imani ya yi aiki na kwarai to wadancannin ka suna da  sakayya na ribi sabo da abin da suka aikata   alhali kuma suna cikin benayen aljanna  a cikin aminci ).

   Babban damuwar ka ya kai musulmi shi ne ka samu rabauta da sha daga tabkin Annabi  shugaban 'yan Adam tsira da amincin Allah  su tabbata a gare shi , (To yaya za ka cimma wannan manufan?   shi ne farkon abin sha na 'yan aljanna, to duk  wanda Allah ya datar da shi ya mishi baiwan sha daga wannan tafkin  to babu tsoro a gare shi bayan haka , wanda ya kasance  daga cikin wadan da za su zo ga Annabi  su  sha a tafkin Allah zai saukake musu  fitintinun  kafin  haka.
  kuma imani da tafikin imani ne da ranar lahira , wanda bai yi imani da tafkin ba  bai da imani  sabo da rukunnan  imani  ba a rarrabewa tsakanin su to duk wanda ya bar wani rukuni daga cikin rukunnan imani hakika ya kafurce da su  gaba daya .
      Shi Tafki wani kyauta ne daga Allah zuwa ga Annabi sa  Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,    al'umar sa za su sha daga gare shi a kasar da za a tattara al'uma a wurin hisabi ranar alkiyama   a wunin da  mikidarin sa ya kai shekara dubu hamsin ga kafura  Allah zai gajarta shi ga muminai   zai  lullube mutane  a  wannan ranar   awurin hisabi  tare da  bakin ciki  wanda ba za su iyada shi ba ba don Allah ya bawa jikkunan su karfin juriya ba da wanzuwa ba da duk sun mutu gaba daya  kuma zai jarrabe su da kishi  mai tsanani  wanda ke kona hanta a gun tsayawa na hisabi  zai jefa kishi mai tsanani a cikin ciki irin kishin da ba su taba yin irin shi ba ,  Allah zai karrama Annabin sa Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da tafki domin al'uman shi su sha daga gare shi , shi kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana tsaye a gindin tafkin  yana dubi zuwa ga al'umarsa   yana jin dadin haka,  jin dadi mai girma  yana kiran al'umar sa don su sha  ,  fadin tafkin da yalwan sa , hadisai masu  dumbin yawa sun zo wurin bayanin sifar ruwan   da yalwan shi   haka kuma alkur'ani ya zo da ambaton sa a cikin suratul kausar   kuma ko wani Annabi na da tafki , an karbo daga Samarata Allah ya kara yarda a gare shi ( daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce lallai Annabawa za su yi tinkaho a tsakanin su ko wane ne ya fi yawan  mabiya  a cikin al'uman sa to ina fatan ya kasance a wannan ranar na fi su duka  mazowa sha  kuma ko wani  mutum a cikin  su  a wannan ranar yana tsaye a kan tafkin cikakke  yana tare da sanda  yana kiran duk wanda ya sani a  cikin al'umar sa  kuma ko wace al'uma na da alama  wanda Annabin su  zai gane su da ita). Tirmizi da Dabarani suka rawaito.
    Kuma tafkin Annabin mu shi ya fi girma kuma yafi dadi kamar dai shari'arsa   An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : - daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (  Lallai  tafki na ya fi nisan daga garin Aila zuwa Adan  , kuma lallai ya fi nono fari ya fi zuma zaki ya fi kankara sanyi,  kuma  adadin kwanukan shan shi ya fi yawan taurari ) Muslim ne ya rawaito, a wata ruwaya da ba na muslim  ba  ya fi turaren almiski  kamshi.
  An karbo daga Abu Zarri Allah ya kara yarda a gare shi  ya ce:- Daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :- (Na rantse da wanda rai na yake hanun shi ,; kwanukan shan sa sun fi adadin taurarin da ke sama  da kuma  manyan taurarin ta na sama a cikin dare mai duhu,  kwanon aljanna kuma  wanda ya sha daga gare shi ba zai ji kishi ba har abada  yana  tsatssagowa daga gare shi  indororo guda biyu na aljanna ),  Ahmad ne ya rawaito da Muslim da nasa'i   
An karbo daga Abu Umama Allah ya kara yarda a gare shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce (Tabki na ya kai kwatankwacin Adan da Amman, ya fi girma kwarai akwai  magudanar ruwa guda biyu :na azurfa da zinari, ruwansa ya fi nono fari, ya fi zaki akan zuma, ya fi turaren Al miski kamshi,duk wanda ya sha daga shi ba zai ji kishi bayan haka, fiskarsa ba zata bakanta ba har abada,) Ahmad da Ibnu Maja da Ibnu Hibban.
An karbo daga zaid bin khalid Allah kara yarda a gare shi, daga Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Shin ko kun san Alkausar? Wani kogi ne da Ubangiji na ya ba ni a Aljanna, yana da alheri mai yawa a cikin shi, Al'uma ta zata sha daga gare shi ranar alkiyama, kwanukan shan sa kamar adadin taurari, zaa fizge bawa daga  gare su sai na ce : ya Ubangiji na ai ya na cikin Al'uma ta sai ace : Ai baka san me ya farar a bayanka ba,) Ahmad ne da Muslim da Abu Da'uda,.
Tafkin  kasa ne mai  fadi, Allah zai cika shi da ruwan Alkausara, yana kwarara a cikin sa Indororo guda biyu na zinari da azurfa  na daga kogin Alkausara, wannan tafkin bai raguwa, kuma kowani mumini da muna zasu sha daga shi, bisa ga kishi mai tsananin gaske, to bayan an sha ba za a ji kishi ba har abada, masu zuwa ga Annabi a tafkin su ne masu bin sunnarsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da kuma masu nesatan manyan zunubai, Allah Madaukakin sarki yace : In  kun nesaci manyan zunubai da muka hane ku, zamu kankare muku zunubanku kuma mu shigar da ku mashiga mai girma (Aljanna).
Tare da bin sunnar Annabi suna kira zuwa ga Allah bisa basira, Allah Madaukakin sarki ya ce : (ka ce wannan ne hanya ta ina kira zuwa ga Allah bisa basira ni da wanda ya bi ni, tsarki ya tabbata ga Allah kuma ni ba na cikin masu shirka.)  sai su kira zuwa ga shariar Annabi Muhammad,su nesaci bidia da fararrun abubuwa a  addini, da abubuwan da sharia ta ki na munkari, kuma suna lazimtar Ikhlasi mai kore  riya  da neman aji, da nau'uka na shirka, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Da sunan Allah mai rahama mai jinkai, lallai mun baka Alkausar, ka yi sallah don Ubangika kuma ka yi suka,) Assura
Allah ya sa min Albarka ni da ku a alkur'ani mai girma.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ma'abocin girma da karramawa,da mulki da ba a samun irin shi, da buwaya wacce babu zalunci,ina kyautata yabo ga Ubangiji na kuma ina gode mishi bisa ni'imtarwa masu yawa,na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, Mai mulki kuma tsarkakakke, kubutacce daga aibi, na shaida cewa Annabinmu kuma shugabanmu Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne,kuma Manzonsa  ne,tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa masu daraja, bayan haka ku ji tsoron Allah cancancin tsoronsa, ku yi riko da igiya mai karfi na musulunci,
Ya ku bayin Allah! Abin mamaki da falala irin na wanda Allah ya mar falalar zuwa tabkin Annabi na Alkausara ya sha daga gare shi, ba zai ji kishi ba har abada, kuma abin mamaki da girman hasarar wanda aka hana  shi sha kuma aka kore shi daga gare shi, Ubangijinka bai zaluntar kowa,.
Ya ku Musulmai! Na daga cikin abubuwan da ke hana isa a sha daga wannan tabkin akwai kirkiran bidi'o'i   da farar da abubuwa cikin addini, da kuma yin saddu ga musulunci ta hanyar fadi ko aiki, kamar yadda ya zo a hadisan da aka rawaito kan sababin koran wasu daga cikin wannan al'uma.cikin wadannan hadisan akwai fadin : (Ba ka san me suka farar ba a bayanka,sai manzon Allah ya ce : Nesa daga rahamar Allah ga duk wanda ya canja a baya na, )>
na daga cikin abin da ke hana sha daga tabkin alkausara  akwai manyan zunubai, domin suna kazanta zukata, haka nan riya da son a sani ko son a ji na daga cikin abubuwan da ke hana samun isa ga tabkin alkausara, haka hakkokin wasu da aka zalunta na cikin manyan abubuwan da ke hana samun sha daga tabkin, kuma sakayyar ta yi daidai da aikin ga wanda ya yi lura, domin wanda ya bi shariar Annabi Muhammad a nan duniya ya kuma bi koyarwarsa to zai sha daga tabkinsa, wanda kuma ya sanja ya yi bidia sai ahana shi sabo da saddu da ya yi ga Allah.
Lalle Allah da mal'ikunsa suna salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce.